Showing 54001 words to 57000 words out of 61789 words

Chapter 19 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel

Fauzah   

04 Nov 2025

188

ne naji shiru sannan banƙara ganin kiba sai yau ina doba ƙofar ɗakin ku sosai amma bana ganin fitowar kowa ko shigar wani", To shikenan yanzu sauri nake idan nadawo zan ne miki, " To adawo lafiya Sajeedah ta furta cikin sanyin murya" Suhaima ta lura yarinyar kamar akwai magana abakin ta to amma saboda sauri take shiyasa tace ba damuwa nagode Sajeedah amma tasa aranta tana dawowa zata nemi Sajeedan, "amma anty bansan sunan kiba" Suhaima wadda hattafara tafiya ta tsinci muryar Sajeedah akunnuwan ta SUHAIMA Sunana, tafaɗa batare da ta jiya ba ta cigaba da tafiya cikin sauri da alama dai uzirin ta babba ne,

Ɗaya daga cikin matan dake zaune a tsakar gidan, cikin sauri ta janyo Sajeedah tare da Faɗin ke gidan uban wa kikasan wannan mai kama da aljanar kuma sannan ba Hajiya fanteka tace kada wanda ya shiga harkar suba babu ruwan mu dasu suma babu ruwan su da mu kina ganin fuskokin su kullum a rufe alamar babu gaskiya a tare da su kina ganin yanzu ma da ta fito babu wanda tayi wa magana kanta a ƙasa ko cikin idon ta bata bari a gani saboda rashin gaskiya, jin surutun matar yaƙi ƙare wane Sajeedah ta janye hannun ta daga ruƙon da tayi mata batare da tace mata cikan kiba, haka sauran mutanan dake gurin suka haɗu akan Sajeedah kowa da abunda yake faɗa hadda masu cewa sai sun gayawa Hajiya fanteka idan ta dawo wasu kuma na zagin Su Suhaima,

Bayan fitar Suhaima daga cikin gidan wata baƙar mota ta hanga daga ɗan nesa da ƙofar gidan ƙirar TOYOTA hatta glasses ɗin motar tinted ne, murmushi Suhaima tayi mai sauti saboda taga wadda take cikin motar Hajiya fanteka ce zaune ita da wani alhaji a gidan gaba wani irin ƙaton mutum ne baƙi gashi lukuti sai faman hura hanci yake kamar botorami, saida ta ɗan jima tana kallon mutar kafin ta juya ta nufi titi, Ɓangaran Hajiya fanteka kuwa batasan Suhaima ta gansuba saboda tana ganin ai glass ɗin motar tinted ne, batasan Suhaima tafi ganin abunda ke acikin duhu ba sannan duk yadda take nesa da abu to tana iya ganin sa tar tar,

Waccan fa wace ce tafito daga cikin gidan ki fuskar ta a rufe? gashi naga ta daɗe tana kallon motar nan, wannan mutumin ne dake zaune gefan Hajiya fanteka a cikin mota yayi maganar yana kallon ta, hhhm saida ta numfasa kafin tace itace fa sheɗaniyar Yarin yar danake faɗa maka hatsabibiya komai nata ba irin na mutane ba bana son gani ta Sam kwana biyu, nane mesu narasa a gidan ita da ƴar uwar ta sannan kowa na tambaya zai ce bai ga sanda suka fita ba, shiru mutumin yayi alamar yana nazari yaɗan jima ahaka kafin ya kalli Hajiya fanteka yace tabbas akwai babban al-amari atare da Yarin yar nan dole sai kin kula sannan kinyi ta katsan tsan duk abunda zai kawo mana matsala acikin tafiyar mu kawar dashi muke, sama da shekara 30 babu wani abu daya shiga tsakanin mu da harkokin mu to kikula sosai, saida yakai ƙarshan maganar tashi Hajiya fanteka ta ɗora da cewa kada kadamu alhaji Talle zankula da komai a ɓangare na don nima banyar da da Yarin yar ba kwata kwata, da wannan maganar ya tashi motar suka fita daga Layin,

_.....RAILWAY QUARTERS ARAB ESTATE_

Tsaye Suhaima take a gaban babban gate ɗin Estate ɗin tana kallon manya manyan gida jan dake ciki amma babu hanyar shiga yaushine zuwan ta na huɗu 4 kullum saidai ta gaji da tsaiwa da zagaye ta koma gida duk zuwan da take koda mahaluƙi ɗaya bata taɓa gani ya fito ko ya shiga ba tasha yin mamakin to ko dai babu mutane ne a gida jan abun na kulle mata kai, amma a yau taci alwashin sai tashi estate ɗin nan Koda kuwa shine silar Rayuwar ta koda zai zama idan ta shiga shine zai zama bugun numfashin ta na ƙarshe,

Bayan ta nutsa cikin tunanin da take tasamu guri ta zauna dagacan gefe kaɗan jikin wata ƴar ƙaramar bishiya mai kyau ganyen jikin ta sai ƙalli yake, babu zato ba tsammani abun tamkar a majigi tafara ganin wannan tangame man gate ɗin yana zugewa da kanshi sannu a hankali yana buɗewa da mamaki Suhaima taciga ba da kallon iKon Allah gashi dai taga babu wani ɗan Adam a gurin koda mutum ɗaya bare tace shi yake buɗewa, a ranar da tafara zuwa gurin taga faruwar hakan amma sai tayi tunanin gezo ne idanuwan ta sukai mata ko kuma don tana cikin tashin hankali ne shiyasa,

Batare da tsayawa wani dogon tunani ba Suhaima ta tura kai cikin Estate ɗin batare da jin ko ɗar acikin zuciyar taba cikin nutsuwa tafara tafiya akan dogon titin da yayi ciki sosai daga inda take bata iya ganin ƙarshan sa saboda yayi kwana kaɗan, kamar wadda akabawa umarnin ta juya, da sauri ta waiwaya baya ganin gate ɗin tayi Yakoma ya zugewa da kanshi kamar yadda yake tun farko, Take taji wani irin mummunan faɗuwar gaba take taji wani irin yanayi ya lulluɓeta cikin ranta tafara tunanin tabbas akwai wani babban al-amari acikin gidan nan saboda tasan bata taɓa jin irin yanayin nan sai idan wani abu zai faru da ita ko kuma zai faru da wani a gaban ta, tafiya ta cigaba da yi faɗuwar gaban ta na ƙaruwa da duk wani Taku da zata yi izuwa ciki, takun mutane taji abayan ta alamar ana nufu inda take cikin mamaki Suhaima ta cigaba da tafiya batare da ta juya ba,

Amma tana jin takun naƙara kusan to inda take, magana tafara ji da wani kalar yari wanda ita bata mataɓa jin irin sa batare da sanin Meye ake faɗaba ta cigaba da tafiya abun ta ƙinjinta sai lugude yake saboda tsabar faɗuwar gaba, ta tabbata ba tsoro take jiba to amma kuma akwai baƙon yanayi atattare da ita gashi jikin ta ya ɗauki wani irin zafi duk da sanyi da ake agari ga kuma sanyi yamma ya sauka don yanayin garin hadda HAZO, maza ne su biyu suka tare ta kallon su tayi ɗaya bayan ɗaya tun daga sama har ƙasa Uniform ne a jikin su da alama Securities ne don hadda bindiga a Saƙale a wuyan ko wannan su, dukan su BUZAYE Ne magana ɗaya yake yi mata cikin harshen su na Buzaye amma dai batasan Meye yake faɗa ba, ɗayan ne ya lura bata gane maganar ɗan uwan nasa, sai ya matso cikin Hausar shi da bata fita sosai yace mata "kibuɗe fuskar ki yanzun nan sannan kifaɗa mana zuwan Meye kike wannan gurin yau kwana huɗu kenan kullum sai kinzo"

Mamaki ne ya kama Suhaima a ranta tace ashe dama suna kallo na to ta ina suke ganina nikuma bana ganin su, kamar yasan abun da take tunani kenan ya ƙara ce mata "kullum sai munganki ta Camera fuska a rufe baki da gaskiya dole a kama ki nan ba gurin wasa bane" jin yadda yake magana dalla dalla Hausar tashi abun dariya hakan yasa Suhaima yin dariya ƙasa ƙasa batare da tace masa komai ba sannan bata da niyar cire mayafin fuskar ta ta, kafin yace komai Telephone ɗin hannun sa irin ta police aka fara magana daga ciki, magana yafara amma bata gane abunda yake faɗa shima na cikin wayar batasan Meye yake cewa ba duk da ana iya jin komai abu ɗaya ta fahimta shima kuma a ƙarshan wayar ne security ɗin ya faɗa "to yallaɓai" shi kaɗai ta iya gane wa, kallon ta yayi tare da Faɗin kibiyo yafaɗa tare da yin gaba babu musu Suhaima tabi bayan sa shikuma ɗayan security ɗin ya koma inda suka fito,

Tafiya suke tun Suhaima nasa ran ganin sun isa inda zasu je har tafara gajiya tacire rai tana bin ko ina da kallo cike da mamakin irin gine ginan cikin Estate ɗin wani irin haske mai jan hankali tafara hangowa kusa dasu kaɗan, har ta matsu su ƙarasa gurin taga hankyan Meye haka cikin Taku kaɗan suka isa inda wannan hasken yake, masha Allah Suhaima tafaɗa a fili, ganin wannan haɗaɗan kuma tsararran ROUNDABOUT ɗin dake a tsakiyar titi nan cikin Estate ɗin shagala tayi wajan kallon sa batare da sannin wannan security ɗin yayi gaba yabar taba baƙaramin jan hankalin ta wannan ruwan dake fitowa daga ƙasa yayi ba ga duwatsun dake kwance cikin sa sai suka ƙarawa ruwan kyau wanda yake fari tasss, saida ta kai hannu tasha wa ɗan nan kyawawan furannin dake zagaye da gurin, tama rasa me zata tsaya kallo komai ya nagurin ya matuƙar burgeta, ɗaga kanta sama tayi tare da kai duban ta kan wannan doguwar bishiyar kwakwan dake a tsakiyar cikin Roundabout ɗin saida ta ɗau lokaci mai tsayi kafin ta dawo da kanta ƙasa,

Ganin wannan security ɗin yayi mata nisa ne hakan yasa ta bin bayan shi a sukwane tana isa kusa dashi, sai ga wata mota nan tayi parking a gaban su ba shiri suka tsaya cak, wani ne yafito daga cikin motar da alama driver ne, kallon Suhaima yayi tare da Faɗin kishiga muje tare da buɗe mata back side na motar saida ta ɗanyi jim kafin ta sa kai ta shiga, za gayawa driver ɗin yayi, ya shiga kai tsaye ya zarce kan titin ALHAJI IMRAN ARAB STREET, Zare ido Suhaima tashigayi ganin kamar suna shirin barin gari kuma wai duk a cikin Estate ɗaya, amma aranta ko ɗar babu na alamar tsoro saidai kawai tanajin matsanancin faɗuwar gaba, bayan sun shiga house ɗin Alhaji imran har bakin ƙofar shiga cikin babban parlourn saida driver yakai ta sannan yace tashiga ciki, ba musu ta nufi ƙofar glass door ɗin ta zuge kafin tashiga da sallama ƙasa ƙasa jin ta taka wani abu mai laushin gaske hakan ne yasa ta saurin ɗagowa takai duban ta idan ta taka da ƙafar tata wani lallausan carpet ne tamkar audiga cikin jin daɗin yanayin ta ƙara nitsa kyakkyawar ƙafar ta aciki fara tasss mai ɗauke da dogayen yatsu, ganin babu kowa acikin ƙaton parlourn ne yasa Suhaima ƙara taka watayi zuwa ciki tare da kallon cikin make kyan haɗaɗan parlourn wanda ya tafi da tunanin gaba ɗaya, ganin babu motsin kowa sannan babu alamar wani zai fito cike da kwarin gwaiwa Suhaima ta ƙarasa ciki tasamu ta zauna kan kujera..!!

Ayi hkr da wannan

_F pen's_

What's app channel👇

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_AHALIN MU DAYA_

💗💗💗

_CREATED AND WRITTEN_

_BY_

_Fatima Y zakariyya_

_😍Oum Ameerah_😍

*Nazari writer's ass......📚*





_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_

_(THE QUEEN👑)_

________Dedicated to anty salma💎

*Page* 4️⃣9⃣↔️5⃣0⃣📖

Ganin babu motsin kowa sannan babu alamar wani zai fito cike da kwarin gwaiwa Suhaima ta ƙarasa cikin kata faran parlourn tasamu guri saman kujera ta zauna, lumshe kyawawan idanuwan ta masu wani irin sihirtaccan kyau da jan hankali mai kallon su a wasu lokutan kuma subada tsoro ga wanda ya ɓata mata rai, sosai ta lunshe su sakamakon jin daɗin sanyin A. C yana ratsata tun daga tafin ƙafar ta har kai, ga wani dadda ɗan ƙamshin turare wanda tama rasa daga inda yake, dama tana matuƙar ƙaunar weather na sanyi sai hakan ya ƙara mata jin daɗi da nutsuwa,

Baffa ne zaune shida Uncle Yusuf a private parlour ɗin shi, hankalin su gaba ɗaya Yakoma kan wata ƙara mar T.V dake gaban su saman wani ɗan madai dai cin table, "cikin nutsuwa uncle Yusuf kai duban sa kan baffa kafin yace amma baffa wannan Yarin yar da alama bata da gaskiya gashi kace a shigo da ita hankali na sam ya kasa kwanci" yakai ƙarshan maganar tasa tare da ƙara kai dubansa kan T.V ɗin wanda Suhaima ce gata nan zaune a inda ta zauna kan kujera fuskar Nan a rufe kamar kullum sai ido kawai ake gani, ita ce suke gani kafin baffa yace wani abu kawai Suhaima tabuɗe idon ta tare da ɗan ɗaga kanta ta kalli saman parlourn sai tin CAMERA ɗin Wanda ita batasan ma da wani C.C.B.T ba a parlourn, lokacin da uncle Yusuf yaga Ash eyes 👀 ɗin ta saida ya zabura tare da Faɗin "baffa kagani ko wannan daka gani ma ba mutum bace kalli idanuwan tafa launin TOKA," yayi maganar tare da nuna fuskar Suhaima ta cikin T.V ɗin saida baffa ya ɗanyi gyaran murya sannan uncle Yusuf ya dai dai ta nutsuwar shi saboda shi ya ma manta a gaban baffa yake,

Shiru baffa yayi shima ya zubawa T.V ɗin ido yana kallon idanuwan Suhaima sosai wanda take ta juya su alamun ta kallon wani gurin a cikin parlourn, sai da baffa yayi nazarin ta sosai kafin yanisa, cikin dattaku irin nasa yafara magana da ɗan nasa uncle Yusuf, ".

...Yusuf ina son ganawa da Yarin yar nan saboda a jiki na nakejin ita ɗin ba cutar damu tazo yiba, sannan ina ganin kwarin gwaiwa a tattare da ita katuna fa tsawan kwana huɗu 4 tana zuwa nan kullum sai mun ganta har tagaji ta tafi, to akwai wani dalili mai ƙarfi dayasa takezuwa nan ɗin, saboda haka inaso abata dama, sannan maganar launin Ida nuwanta baka ganin cewa Allah zai iya halittar ta a haka ko fiye da hakan ma, idan ka duba ma ai Sulaim shima wani lokacin launin idon sa yana canza wa daga asalin brown ɗin Sa, Abu na ƙarshe danakeso kasani shine bana son kowa yasan da zuwan yarinyar nan cikin Ahalin mu daga ni sai kai shiyasa ma nace a kashe gaba ɗaya Cameras ɗin gidan nan har sai an shigo da ita, saboda akwai wani baƙon al-amari dan gane da Yarin yar inaso nagaba da ita ni kaɗai idan da yiwuwar wani yasani to zan haɗa taro zuwa gobe"

Sai da uncle Yusuf ya tabbatar baffa ya kai aya ya tsaya sannan yace"insha Allah baffa duk yadda kace haka za ayi, babu wanda zan sanar wa da wannan maganar matuƙar ba kai kabani dama ba, Allah yasa muji alkhairi akan Yarin yar,

"Ameen ina fatan haka cewar baffa kafin yace zaka iya tafiya zangana da ita Yarin yar kashigo da ita ciki"

Muƙewa uncle Yusuf yayi tare da Faɗin "to" aranshi kuma yana mamakin yadda akayi baffa yayi saurin amincewa da Yarin yar haka bugu da ƙari har cikin kuma yace a shiga da ita har babban parlourn sa, wanda idan aka cire su ƴaƴan sa to ko jikoki ba kowa ya isa shigaba sai Sulaim shine wanda bashi da wani shamaki da ko ina na cikin ARAB ESTATE sai dai inda bai so shigaba,

Ɓangaran Suhaima kuwa batasan wainar da ake toyawa ba sosai take jin sake wa aranta ta rage jin fargabar da take saboda addu'oin da take ta karan towa cikin iKon Allah abun ya lafa mata, har da jingina bayanta ajinkin lallausar kujerar wadda sai ka rante da audiga akayi ta bada soso ba, tare da lumshe idanuwan ta wani irin dadda ɗan bacci tafara ji yana fizgar ta, tana shirin kwantar da hanta saman kujerar yadda zata ɗan ji daɗi, kawai tafara jin alamar motsi ana tahowa da sauri ta gyara zaman ta tare da dai dai ta nutsuwar ta tayi ƙasa da kanta,

Da sallama uncle Yusuf ya shiga parlourn da take, acan ƙasan maƙoshin ta ta amsa sallamar take taji tsohuwar ƙiyayyar da take yiwa Ahalin Arab ta dawo sabuwa acikin ranta har wani zafi take ji acikin ran ta da zuciya, kallon ta uncle Yusuf yayi sosai ana ƙara karantar Suhaima wadda kanta ke ƙasa tasan da shigowar mutum amma tayi kamar batasan da hakan ba, "zaki iya biyo ni uncle Yusuf yafaɗa batare da ya zauna ba yayi gaba abunsa aransa yana tunanin to ko dai kurma ce bata magana ko kuma gaisuwa ne bata iya ba" Suhaima taji abunda yace saboda haka ta tashi tabi bayan sa zuwa parlourn da baffa yake zaune yana kallon duk abunda kefa ruwa har saida yaga suna bakin ƙofa zasu shiga sannan ya juya T.V ta kalli baya ta yanda mai shigowa bazai iya ganin abun da ke ciki ba, a ƙofar shiga uncle Yusuf ya tsaida Suhaima ta hanyar ɗaga mata hannu ba musu taja ta tsaya cak sai da yafara shiga baffa yabada izini sannan yayi mata iso zuwa ciki, kanta a ƙasa tayi sallama ƙasa-ƙasa sai da suka kai har inda baffa yake sannan uncle Yusuf ya russuna a gaban mahaifin nasu tare da Faɗin " baffa na barku lafiya" jin jina kai kawai baffan yayi shikuma yajuya ya fita zuwa house ɗin shi zuciyar sa duka babu daɗi saboda bai yadda da Suhaima ba a ransa kuma yana fatan Allah ya tsare mahaifin nasu da ga sharrin komai gashi baffan ya hana shi zama bare yaga abunda zai faru amma aransa yace dole zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login