Showing 39001 words to 42000 words out of 61789 words

Chapter 14 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel

Fauzah   

04 Nov 2025

168

hakan aransa kansa a ƙasa saboda tsabar kunyar dayaji"

"Murmushi ummeetha kawai tayi ganin saleem ɗin duk ya wani diriri ce, tace"

"Ƙale ta yaro na kutaso muje dinning area breakfast is ready"

"Kafin mommyn ku da daddy su shigo bata rufe baki ba sai ga sunan"

"Gaba dayan su suka nufi dinning area ɗin"

Bayan sun gaisa ummeetha ta sanar musu angama komai gobe zasu wuce *MASARAUTAR GABAS* har ma ta sheda musu da wuwar yariman gabas ɗin wato Sultan"

"Mommy tace kice kenan sulaim ma zai iya bin mu kenan Tunda mutumin nasa ya dawo ƙasar"

"Eh to ba mamaki cewar ummeetha"

Don har cikin ranta bata kawo zai bi sun ba

__________________________

____________________

_____________

"Suhaima ko cewar DR. Muhibbah wadda ta shigo duba jikin khaltum bayan sun gama breakfast"

"Ciki da girmamawa Suhaima tace eh suna na kenan"

Dr.muhibbah taci gaba da cewa yauwa naga jiki yayi kyau sosai"

"DR. Sulaim yana hanyar zuwa idan yaƙarasu za a aiko kizo dama nayi miki alƙawarin yau zaki jikomai ko"

"Ɗaga kai Suhaima tayi alamar To daga can ƙasan zuciyar ta kuma tana mai mai ta sunan DR. Sulaim"

"Batare da sanin Meye dalilin yin hakan ba"

"Waye shi DR. Sulaim ɗin"?

"Babu shiri taji tambayar ta kwace mata da sauri ta dafe bakin ta"

"Murmushi Dr.muhibbah tayi sannan tace kibari yazo za kisan koshi waye"

Batajira cewar Suhaima ba ta juya ta nufi ƙofa cikin ɗan saga murya khaltum tace mun gode sosai"

Ɗaga kai kawai Dr.muhibbah tayi batare da tajiyo ba.!!!

*Comment nd share more like fisabilillah*🙏

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp channel

*AHALIN MU DAYA*

*CREATED AND WRITTEN*

*BY*

*Fatima Y zakariyya*

_😍Oum Ameerah_😍

*NAZARI WRITER'S ASSOCIATION*📚

_Sarauniyar👸Nazari writer's association_

______Dedicated to aunty salma💎

*Page* 3⃣ 7⃣↔️3️⃣8⃣📖

Batajira cewar Suhaima ba ta juya ta nufi ƙofa

"Cikin ɗan ɗaga murya khaltum tace mungode sosai"

"ɗaga kai kawai Dr.Muhibbah tayi batare da tajiyo ba"

"Cikin nutsuwa yagama breakfast din nashi amma duk hankalin shi yana kan asibiti"

"Ya rasa Meye dalilin hakan"

"Sallah ma sulaim yayiwa baffa sannan yanu Part din su ummeetha don ya shida musu tafiyar sa zuwa *BARNO STATE*"

"Yana fita suka haɗo da barrister Sulaiman ɗan gidan mai girma hasheem yana ƙoƙarin shiga perlon baffa sai sauri yake dagani wani abune yakawo sa"

"Ɗauke kai barrister Sulaiman yayi kamar baiga sulaim ba"

"Shiko sulaim bama shine agaban saba yi yayi kamar Bai san da wanzuwar mutun a gurin ba ya bude mota ya shiga ya fisge ta da gudun gaske"

"Kamar sakarai haka barrister Sulaiman yabi bayan motar da kallo"

"Cije lips ɗin sa yayi naƙasa cike da takaicin sulaim bai kula shiba"

"Da haka ya shige ciki afili yace zaka gane kuranka barganin kamar kafi kowa acikin dangi"

"Babu ko salla haka ya fada cikin perlon baffa yana tafaman surutu shi kadai"

"Ke kuma kukan Meye kike yi kida bakya rabo da kuka cewar Hajiya Turai tana kallon sabrina"

"kamar wadda ke jira haka sabrina ta zabura ta dago daga saman bed din da take kwance fuska duk hawaye"

"Haba mameey tunjiya nake kiran yaya sulaim amma baya picking call sannan Yanzu NA tashi tun ɗazun tana ta ringing amma yaki dauka na sake kira kuma busy"

Takai karshen maganar tata da cikin kuka sosai

"au dama ke saboda ɗan iskan yaron nan ne kike so kisawa kanki cutar hawan jini da ciwon zuciya Haba daughter na bana ce dole zaki aure shiba damuwar duk ta Meye? "

Bata ƙarasa ba suka tsinci muryar anty jamila tana magana daga bakin ƙofa"

"Lallai Yarin yar nan kin haɗa kaki da aiki wlh yanzu ke akan wannan mara lafiyar yaron kike so ki kashe kanki to Bismillah"

"Ki kashe kan naki bayankin mutu zai aure mata har hudu bashida wata asara ke kuma kinyi wa kanki"

"keko kamar ba mace ba"

Ta inda anty jamila take shiga ba tanan take fita ba"

"Hajiya Turai wadda tayi sororo tana kallon ta tama rasa Meye za tace ga baƙin cikin tana yiwa ƴar ta ɗaya tilo fada"

Cigaba da magana anty jamila tayi

"Jinai ance barrister Sulaiman yana sonki sosai amma shine kika tsaya kina fige wanna kazar asara rar ko?"

"Dame ye shi sulaim din yafi Sulaiman babu tsabar jaraba ce irin taki sai kuma kwadayin wannan kyan nasa kamar aljani da kuma kwadayin dukiya wadda shima ai Sulaiman din yana da ita"

"Kinga jamila bazai fa yiwu ba kizo ki rufe min ƴa da fada kamar ke kika haifa min ita"

"Ashe dama laɓe kikeyi mana bansani ba"

"Kuma maganar so baza ta aure wanda bata so ba dole ne ta zabi wanda yayi mata kuma ko waye dole ya aure ta" ehe

Tare ta anty jamila tayi ta hanyar cewa"

Au dama wai Turai kina da wannan kwarin gwaiwar amma aka marar miki ƴar taki amma kikayi shiru"

"Sheƙewa tayi da dariya sannan ta ciga da fadin ai wannan ihu bayan hari ne kikeyi ai kamata yayi kununa musu yadda kike son ƴar taki a gaban su bawai anan ba"

"Ƙuluwa iya Ƙuluwa Hajiya Turai tayi jitake kamar ta tashi ta rufe anty jamilan da duka amma babu hali"

Tabuɗe baki da niyar tayi magana sai anty jamilan ta riga ta ta hanyar cewa"

"Kinga duk ba wannan ne ya kawoni ba gurin ɗan uwa na nazo ayimin iso gurin sa"

Kafin Hajiya Turai tace komai wayar anty jamila ta ɗauki ruri juyawa tayi ta fita daga cikin bedroom din sabrinan tare da kai wayar saitin kunnan ta"

Wata muguwar harara Hajiya Turai tabi bayan anty jamila da ita cikin jin zafi da ƙunar rai "

" Tace ai da biki tafiba naga uban dazai yi miki ison wajan nashi"

Maganar Sabrina ce ta dawo da mameeyn cikin hayyacin ta"

"Lallai ma anty jamilan nan mameeyn kinga fa part ɗin mu tazo Sannan kuma har cikin bedroom ɗina kuma ta fadi abunda ranta yake so tatafi"

"murmushi Hajiya Turai tayi sannan ta ɗora da cewa kada ki damu kinji my lovely daughter"

"Zakiga yadda ƙarshan wasan zaizo akwai abunda ma haifinki yakeso ya mallaka da zarar yasameshi tasu taƙare sannan mukuma zamu koma, *GOVERNMENT HOUSE*"

"Wani irin ihu Sabrina tasa tare da rungume Mahaifiyar tata pls mameey da gaske kike? "

"Eh mnh na taba yi miki ƙarya ne"

Daga kai Sabrina tayi alamar a a"

Take taman ta da batun sulaim ta shigar murnar jin zasu koma *GOVERNMENT HOUSE*

"Mameey kinga za kizama *First lady* nikuma zanzama *star* acikin friend Di na kuma sannan dole yaya sulaim ya aure ni kodan ƙarfin ikon DADA na"

"Takai ƙarshan maganar cike da faɗaɗa murmushin kan fuskar ta"

"Haka ne daughter kada ki damu komai a hannun mu yake zaki zama yadda kike so kishiga inda kike so ki taka wanda kike so cewar Hajiya Turai tana kallon ƴar tata itama da murmushi bisa fuskar tata wadda daka gani kasan tasha man kanti"

"Yes Mameey Sabrina tafaɗa tare da durowa daga saman bed ɗin ta nufi toilet da alama ko salla ma bata yi ba"

Aɓan garan sulaim kuwa bayan ya sanar wa da su ummeetha tafiyar sa zuwa *BARNO STATE* da yamma cin ranar"

"Ummeetha ta nemi ya bari su tafi tare zuwa gobe"

"Yace mata Ai ya gama komai yayi booking flight ✈️ din yamma"

"Bata hana shiba saima fatan nasara da tayi masa tare da addu'ar sauka lafiya"

"saleem da har yace su tafi tare sai kuma yaji bazai iya bin sulaim din ba"

"Gara ya bari sai goban su tafi gaba daya dasu mommy ko banza dai zai ga Suhailat din shi"

"Da wannan tunani ne shima yayiwa sulaim din fatan sauka lafiya sai sun hadu acan"

"Ya aka yi ne yanzu cewar uncle Mansur yana kallon barrister Sulaiman"

Ɗan muskutawa Sulaiman din yayi kadan kafin yace"

Gaskiya uncle iya bincike na babu wata Yarin ya da suke tare da sulaim"

Har asibitin sa naje kuma nayi bincike amma bansamu komai ba akan hakan"

Sai waya ta likita mai suna DR.Anisha itace ma take ɗan shige masa to amma babu alamun shi ɗin ya sake da ita kunga kenan bata da wata hanyar zuwa gidan nan har ta zauna ta kawo mana matsala,

"shiru ne ya ɗan biyo baya kafin He excellency Sambo yafara magana"

"shikenan amma ba hakan ke nuna zamu dai na binciken akan saba zamu cigaba da bibiyar sa"

"Nifa dama gaskiya duk ban yadda da wannan zancan boka yan ba duk ƙar yace kawai zamuyi duk abunda yadace dakan mu"

"Uncle Mansur ne yayi maganar don shi dama tun asali bai yadda da bokaye ba yafi ganewa ya kulla makirci da kansa "

"Harara mama bilki tabishi da ita kamar idon ta zai faɗo tsabar jin haushin maganar tasa"

" Magana mama bilki tafara Ai dama baza kagane amfanin malamai mai ba Tunda an haife ka to badan boka zarshima ba da ba a haifi ɗayan ku acikin wannan daular ba"

"Shidai mai girma hasheem bai ce komai ba saboda shiba abunda ya yadda dashi daban bai yadda da bokaye ba"

"He excellency Sambo shima har ga Allah yafi yadda da bokan yarsa ta kan tsauni duk aikin da ba ita tayi ba gani yake aikin banza ne"

"ahaka dai duk suka tashi suka bar parlon Mahaifiyar tasu kowa ya nufi inda zaije batare da sun samu wata tsayayyar matsaya akan maganar ba"

Bayan sun gama fita ɗaya bayan ɗaya"

"taɓe baki mama bilki tayi tana mamakin anya ƴaƴan nan nata basu fita son zuciya ba"

"Don ta fahimci kowa burinsa yake so yacika shiyasa duk suke wannan abun"

Anty jamila ce ta katse mata tunanin nata ta hanyar cewa

Mama yanzu gashi anjima zankoma Abuja kuma ba a tsaida komai ba"

Nisawa mama bilki tayi sannan tace ke bari zuwa nan da kwana uku 3 mana sai ki koma kafin nan mun samu madafa"

"Gaskiya mama bazan iya ƙara kwana koda ɗaya ne anan ba saboda can ma inada wasu ayyukan a gabana sannan wannan Abban Reeyam din ya takura kan sai nadawo yau"

"to shikenan komai akayi zakiji ta waya kada ki damu"

"Tunawa tayi da maganar boka zarshima"

"Tabbas idan ƴaƴanki basu hada kai ba sannan basu yi imani da muba to baza ku taba cimma abunda kuke so ba"

Kamar karatu haka mama bilki ta shiga mai maita maganar"

"Aranta ta ƙuɗurce kome za ayi dole duk su yi imani dashi kuma su hada kansu kodan samun abunda sukeso"

Amma ta yaya?

"Kanta tayiwa tambayar batare da sanin Meye amsarba"

__________________________

___________________

______________

"Tafe suke amma bugun zuciyar ta ƙaruwa yake a duk sa'ar da ta ƙara Taku sai yayi dai dai da bugun zuciyar Suhaima"

"bin nurse ɗin kawai take a baya tayi tunanin office din Dr.Muhibbah zasuje amma ina saitaga inda suke tun kara ko hanya basu hada da office din Dr.Muhibban ba"

"Dai dai bugun zuciyar ta mai ƙarfi a lokacin nurse ɗin tayi knocking wata ƙofa haɗaɗiyar ƙofar office dake agaban su"

"Suhaima zata iya rantsewa Tunda suka zo asibitin nan bataga ƙofa mai ƙyan wannan ba Bakuma taga irin taba kwatakwa"

"Tana can tana zancan zuci sai gani tayi nurse ɗin ta tura kai cikin office din da sallama dauke a bakinta"

"ganin ƙofar tana ƙoƙarin rufe wa yasa Suhaima tai saurin tura kai ciki"

Batasan Meye dalilin da yasa zuciyar ta take canza salon bugu ba"

Maybe don zasu yi miki zancan kudi ne gashi bakida su shiyasa"

Zuciyar tace ta bata wannan amsar"

Shiru Suhaima taji babu wanda yayi magana ɗan ɗago da kanta tayi ta kalli nurse ɗin wadda itama tana tsaye ta goya hannayan ta a baya"

Magana Suhaima take ji ƙasa ƙasa hakan yasa Takai duban ta inda take jin tashin maganar"

"kujera ta gani tana ɗan juyawa da mutum a kai amma ba a ganin komai daga gareshi sai bayan sa"

"Da alama yana jin daɗin wayar da yake hankalin sa kwance"

"Ɗan tsaki Suhaima taja kaɗan ƙasa ƙasa tanajin haushi wannan tsaiwar da suke yi alhalin ga gurin zama nan sai wanda kazaɓa"

"Take taji wannan ko waye yabata haushi ko mace ce"

"Taya za ai yaji zuwansu amma kuma ya juya abunsa sai waya yake ko sai waya take don ita yakasa tantance muryar mace ce ko namiji saboda sanyin muryar gashi ƙasa ƙasa ake maganar"

Ƙara kallon inda nurse ɗin ke tsaye tayi aranta tace wlh idan aka ƙara wasu minti nan ko biki zauna ba ni sai na zauna idan kukun saba tsayawa a wulaƙan Taku ni banga wanda ya isaba,

"kodan kun taimaka mana ai Bamu muka saka kuba kuma sannan kufadi kudin ku zanbiya"

Masifa take bilhaƙƙi da gaskiya ita kadai kuma a zuciyar ta"

"Sudama ai masu kuɗin nan haka suke mtsss aikin kawai"

"Tsintar muryar nurse ɗin tayi tana magana"

Hakanne ma ya sa ta saurara da zancan zucin da takeyi"

"Ranka ya daɗe gatanan ita ce ƴar uwar mara lafiyar"

"Zaki iya tafi cewar DR Sulaim"

"jin muryar sa kadai yasa Suhaima son ganin waye mamallakin wannan muryar dadai tayi alƙawarin baza ta ɗagoba amma kamar ana zugata haka take ji"

"Bata san lokacin da nurse din ta fita ba kawai dai ta kalli inda take tsaye bata gantaba"

Ɗan Kallon ta DR. Sulaim yayi take yaji Yarin yar tabashi haushi"

Bata iya gaisuwa ba shi take jira yafara yi mata magana sannan ko Meye take nufi gashi shi aƙa ida baya yiwa wanda ya rufe fuskar shi magana"

To ita idan ba idanuwan taba ma babu abunda ake iya gani,

"Raini yana ɗaya daga cikin abunda Sulaim baya ɗauka akan kowa"

"Idan ran Suhaima yayi dubu to yaɓaci"

"Meye wannan mutumin yake nufi da nine saboda kudin su shine zai wulaƙan tani to bazai yiwu ba"

Juya wa tayi a fusace zata fuce daga office din zuwa na Dr.Muhibbah tafaɗa mata su rubuta kudin su taje tane momusu tabiya dan bazata ɗauki wannan wulaƙancin ba"

Da ƙarfin ta taja handle ɗin ƙofar amma taji a rufe cike da mamaki taɗan kara ja still ko motsi ƙofar ba tayi ba"

"Abinda Suhaima bata saniba ƙofar da na'ura take amfani kuma ya riga ya rufe ta daga inda yake zaune"

"Mamakin ƙarfin halin Yarin yar ne yaka mashi wato da tayi mishi magana gara ta koma ta fita kenan,

cikin jin haushi da baƙin ciki Suhaima ta juyo da nufin bal baleshi da masifa saidai duk abunda zai faru ya faru,

"Ɗif maganar da ta ɗakko ta maƙale mata a maƙoshin ta,

kallo ɗaya tai masa da sauri ta maida kanta ƙasa zuciyar ta har wani zillo take"

"an ya wannan ba aljani ba ni Suhaima Tunda nake bantaba ganin mutun irin wannan ba"

"jitayi baza ta iya yi masa koda magana ba wannan mutumin a T.V take ganin ire iren su suma kuma basu kai shi kyau ba wai ahaka ma kansa na ƙasa"

"shi ko Sulaim bai san ma ta kalle shiba yana can yana rubutu a jikin wani file mai dauke da sunan asibitin asama"

"ahankali ta dawo inda Tabari amma tana jin bazata iyayi masa magana ba sannan lokaci daya taji bata son shi ta tsane shi Tunda ya kasan ce mai wulaƙan ta mutane,

Bayan ya gama rubutun bai ko kalli inda take ba waya yaɗauka yayi magana bata ji Meye tafaɗa a wayar ba don kamar ma ba da Hausa yayi maganar ba"

Tana tsaye cikin ƙunar zuciya taji anturo ƙofar da Salla a bakin wanda ya shigo"

"Bayan wanda ya shigo ya ɗan wuci inda take tsaye jitayi kamar ta fice sai kuma tafasa tana jira taga iya gudun ruwan wannan mutumin,

" wannan file ɗin da Dr. Sulaim yagama rubutu shi ya ɗauka ya bawa security din da yashigo batare da yace komai ba"

"Karɓa yayi babu musu ya miƙawa Suhaima kallon shi tayi kafin tamiƙa hannu ta karɓa"

"Tana karɓa security din yace mata yallabai yace zaki iya tafiya"

"Juyawa Suhaima tayi jiki duk babu kwari ta buɗe a wannan karon tana jan handle din ƙofar ta buɗe tafita"

Dayake ta gane hanya ɗakin da suke kawai tanufa kai tsaye ba tare da taduba Meye acikin file ɗin ba,

"Da sauri Dr.Anisha ta ƙaraso amma ko da ta iso Suhaima ta riga ta ɓacewa ganin ta mamaki tafara yi duk da Batasan Suhaima ba amma a jikin ta take jin kamar wadda ta kawo ƴar uwar ta jiya asibitin nan,

" Wadda suke zaton gudu wa tayi Tunda suka ce taje ta buɗewa ƴar uwar tata file sannan tabiya ku ɗaɗan amma bata dawo ba,

Gaskiya ba ita bace saboda taga wannan kayan jikin ta ma na alfarma ne"

To amma ai itama wannan ta rufe fuskar ta sannan taga daga office din Dr. Sulaim tafito"

"Hmmm doguwar ajiyar zuciya Dr.Anisha tasaki ganin tana nema ta bawa kanta wahala ta hanyar tunanin wani abu daban"

Shiga tayi office din Dr. Sulaim ɗin tare da kauda tunanin wannan Yarin yar a ranta,

Barka da rana Dr. Arab tunkafin ta zauna tafurta hakan"

Ɗagowa Sulaim yayi yakalleta sai sakar masa murmushi take"

Zaki iya zama yace mata"

Nagode ta furta tare da zama kujerar dake fuskantar shi sosai"

"Dr. Jabir fa? ya tambaye ta batare da ya sake kallon taba"

"Gaskiya yau bai samu shigowa da wuri ba yace ya kira wayar ka amma bata shiga amma yana kan hanyar zuwa nayi magana dashi"

"Oky zan wuce gida yanzu idan yazo kice ya sameni a gida around 4:00pm,

Bataji daɗin hakan ba sam taso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login