Showing 6001 words to 9000 words out of 61789 words
Chapter 3 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel
mother tafaɗi hakan tana janye su daga jikin ta kuka suka sake saka wa sosai bama kamar suhaima datakejin mother din tamkar itace rayuwar ta data tafi shikenan 😭😢 Allah sarki haka mother ta juya ta tafi batare da tasake bari sun haɗa ido dasuba tana ɗagamusu hannu haka ta tafi ko juyowa ma taka sayi,
Kai kajimin shaqiyayyun ƴaƴa to kubita mana wlh kunga tafiyar mu kai Kaga tada mota muje cikin ɗaga murya da alama da direban motar da zasu hau take da sauri suka juya suma suka nufi motar suna dubawa suka ga babu gurin zama a back sit saidai gidan gaba
Kaltum ta kalli suhaima cikin dashewar murya irin ta wanda yayi kuka sosai tace suhaima a ina zamu zauna dan naga da alama muna da yawa wadanda zamu tafi tare dasu,
Suhaima batace komai ba ta bude gidan gaba ta shiga ta zauna ta kalli Kaltum alamar itama ta shigo haka ta shiga suka zauna a takure babu wada taccan guri suhaima tayi hakan ne saboda tasan Kaltum zata iya cewa zata tambayi hajiya fanteka a ina zasu zauna to ita kuma sam tatsani yin magana da tsohuwar ko taga Kaltum tayi mata shiyasa kawai tashiga bawai don tana so ba saboda tayi imani matar bata da gaskiya,
KANO UNGUWAR KWANDILA👉
Parking motocin sukayi guda biyun suka shiga fiffito sai raba ido ƴan matan suke yi wasu ma manyan mata ne, basu suka sauka a sai gabanin magrib yamma sosai,
Kaltum ce ta kama hannun suhaima tariqe gam gam Allah sarki ida nuwan su duk sunyi ja alamar sunsha kuka har suka zo cikin Kano daga bichi kuka sukeyi amma irin mara sautin nan saidai hawaye kawai
Kallon komai suhaima take na gurin ɗaya bayan ɗaya tun daga kan unguwar wadda take babu hayaniya sosai mutanan ma kaɗan kaɗan take gani suna wucewa ga kuma wasu kantuna a jere kusan guda goma sha biyu ko wanne da abunda ake saida wa kallon ta takai saman shagunan saitaga ma ashe plaza ce ƊANKOLI plaza saman ma shaguna ne kamar yadda na ƙasan suke amma abun da yabata mama ki duk a rufe suke a zuciyar ta tace to ko dai don lokacin salla yayi ne oh tabawa kanta amsa
Waiku baza kushigo bane dalla malamai duk kun wane kama kunrfe fuska kamar wasu ƴan boko haram wata mata ce ke maganar daganin Kaga ƴar duniya gashi taci uban bleaching din ta ga hudar hanci sai faman taunar wani abu take,
Kallon ta suhaima tayi tare da kama hannun Kaltum suka fara Taku zuwa gate din shiga cikin gidan dan ita bata masan sauran sun shigeba tana can tana kalle kalle da salla suka shiga gidan suka tarar da kowa tsai tsaye ga hajiya fanteka a tsakiyar su da alama raba mu ɗakin kwana take, gidan babban gidane mai hawa biyu sama da ƙasa ga babban tsakar gida ɗakuna ne a jajjere kai kace islamiyya ce sbd yadda aka jera ɗakunan ta ko wane ɓangaran gida,
To ku nazo kanku yanxu zaku cire wannan abun na fuskar kune ko kuma yaya dan baza mu zauna har mu kwana da waɗan da ba muga fuskokin su ba Bamu san kuma su waye ba nifa koda uwar marayu tace ku ƴaƴan tane ban yadda ba saboda nasan ta taɓa aiki a gidan marayu to ba mamaki kuma aciki ta ɗakko ku gakunan da wasu manya manyan ida nuwan ku aiko manyan matan nan daba abasu ɗakiba duk suka saka shewa hada tafi da alama dai suma waɗannan duk tafiyar su ɗaya,
Magana nakeyi muku fa cikin tsawa wannan karon tayi magana,
Suhaima ce ta saki hannun Kaltum ta matsa gaban hajiya fanteka sannan ta fara magana, don girman Allah kiyi hkr kibar mu da niƙabin mu dole wata rana zakiga fuskokin mu badan niba dan Allah ta hada hannayen ta guri daya alamar roƙo🙏🙏
Kallon ta hajiya fanteka take wani sheƙeƙe irin kallon baki da hankalin nan to ki wlh bari kiji yau duk abunda kike jidashi nataurin kai nafiki sai kun buɗe fuskokin ko kuma kusan inda dare yayi muku badai nan ba, yo muda muka yi zaman ƙasan gada har a gaya mana rashin ji atare suka ƙarasa tsowa haɗi da dariya wasu daga ciki suna faɗin Allah dai yabiya hajjaju 👍
Hhmm kawai suhaima ta furta a hankali kafin ta qara faɗin kinuna mana ɗakin mu zamuyi salla muhuta kuma wannan karon cikin gadara tayi maganar tana ɗan zare manyan idanuwan ta wadda su kaɗai ake ayi gani,
Cikin fusata da zafin zuciya hajiya fanteka tameƙe tsaye da nufin ta wanka wa suhaima mari kawai sai taji kamar an ruƙe mata hannu ta juya da niyar taga uban waye wannan sai taga babu kowa tashin hankali, ƙara wani yunƙurin marin suhaiman still taqarajin an ruƙe mata hannun saida tayi hakan sau uku ana ukkun ne suhaima ta Taku gabanta cikin takun ƙasa ita wadda ni tun gani na da ita banga irin wannan ƙasaitar atare da itaba sai yanxu,
Idon hajiya fanteka ta zazzaro waje saboda ganin abunda bata taɓa gani ba idon suhaima ne yakoma rainbow colour blue red green ash black and white, tab zokaga tashin hankali gurin hajiya fanteka ƙarasuwa suhaima tayi gaban ta dab da dab sannan tafara magana cikin wata irin murya wadda da bada ita take magana ba,
Zaman lafiyar ki shine kibar mu muyi abunda yakawomu garin nan sannan ki atunaninki zaki iya marina to haryanzu ba a haifi wannan mai iya marin fuska taba kuma da kinyi hakuri tabbas da zakiga fuskokin mu daza rar lokacin hakan yayi to amma kash kinkasa saida na biyo dake ta hanyar lalama to Tunda baki gane waccan hanyar ba sai mubi wannan tana takai ƙarshen maganar tare da sakin wata irin dariya mai sauti,
Sannan ta kai bakin ta saitin kunnan hajiya fanteka tace ki roƙi Allah yasa aikin daya kawoni kada ya biyo ta kanki don tabbas baki da gaskiya to amma yanxu bakice agabana ba saina gama da...... Sai kuma tayi shiru taja baya ta runtse idon ta takuma bude sai ya dawo yadda yake kamar ba shine ya caccanxa kala ba, kallon Kaltum tayi tace muje ko suka nufi wani ɗakin daba kowa suka shige abun su,
Tabar hajiya fanteka tsaye cikin tashin hankali hadda fitsari a tsaye,
A a hajiya lafiya kuwa kamar fa fitsari kikayi ga kuma uban gumin da kike yi duk sanyen garin nan amma kike gumi,
Sai sannan hankalinta ya dawo jikin ta cikin rawar baki tace wai kuna nufin bakuga abunda ya faru yanxuba??
Meye kuma ya faru suka haɗa baki wajan furta hakan
Tab inna lillahi yau ni fanteka na ɗebo ruwan dafa kaina,
Wai Meye hajiya? A a ba komai kudai kutafi kawai to amma kada wanda ya shiga waccan dakin ta nuna da kin da su suhaima suka shiga,
Amma hajiya Meyasa? Dalla yanxu ba lokacin tambaya bane kutafi kubani guri ke kuma Larai kiji rani yau tare zamu kwana to hajiya wannan wadda tayi wa suhaima magana a bakin ƙofa ce hajiya ta kira da Larai
To yau kuma hajiya a dakin ki zan kwana lallai naciri tuta, hmm kawai hajiya fanteka tace saboda ita kaɗai taga abun da tagani da kuma tashin hankalin da take ciki da tsoro da kuma fargaba.
*BACK TO ARAB ESTATE*👉👉👉
Haryan zudai muna farko kuma somin taɓi cikin wannan littafin mai ciki da sarƙaƙiya ban al'ajabi makirci cuta ban tausayi sai kuma uwa uba soyayya ❤️ wadda itace sular haɗuwar mu baki ɗaya🤝✊
💕 *Ahalin mu ɗaya*💕
_Comment share and like fisabilillah_🙏
*Story by*°°°📖
💞Fatima Y zakariyya 💞
_Oum Ameerah_😍
_Muje zuwa_✍️✍️✍️
*Bismillahi Rahmanir Rahim*
_NAZARI WRITER'S ASSOCIATION_📚📚📚
*🖊️ALƘALAMI YAFI TA KOBI*⚔️⚔️
*Dukkan yabo da godiya su tabbata ga allah mahaliccin ko wa da komai Allah kayi dadin tsira abisa shugaban mu annabin mu annabin rahma Muhammad (s.a.w)*
*Ina roqon Allah yadda nafara rubuta wannan littafi Allah kabani iKon kammala shi lpy abun da na rubuta dai dai allah kabamu ladan Wanda nayi kuskure Allah kayafemin Ina roqon Allah kaqarawa iyayen mu lpy Imani da nisan kwana 🤲
*Sadaukarwa ga dukkan daukacin masoyana Allah yabar zuminci kune kwarin gwaiwata Baki daya Kuma Ina godiya da adduoin ku agareni"
Wannan littafi na rubutashi ne domin fada kar wa ilmantar wa tare da nishadan tarwa ban rubuta don son zuciya taba ko Kuma wulaqanci gawani idan kaji labarina yayi kaman ceceniya da rayuwar ka to Ina neman afuwarka ko Kuma idan kinji ko kaji yayi shige dawani labarin to gaskiya arashi ne akasamu*
👍 JINJINA GA YAN FREE GRP
* Ummu safwan💝
* Mrs Muhammad s🤩
* Bin abdurrahman🌹
* Nanjid👩❤️👩
* Nusaiba M zakariyya✨
*💖 SPECIAL GIFT 🎁 TO MY BIG BROTHER Abba Maifata💯*
*AHALIN MU DAYA*
*NA*
💞Fatima Y zakariyya💞
{😍Ummu ameerah😍}
_🫅Gimbiyar Nazari writer's association_ 🫅
_____ Dedicated to aunty Salma 💎
*Page* 9️⃣▶️🔟📖
ARAB ESTATE
Kwance yake yayi rubda ciki a saman tangameman gadon sa ƙirar Italian bed Ga dukkan alama ba bacci yakeba yanitsa cikin tunani yajiyo wayar sa tafara ruri saida ta katse wani kiran yafara shigowa amma ringtone ɗin ba irin na farko bane wannan da sauri ya miƙa hannu kan bedside drawer ya ɗauko ta ya kara a kunne batare da ya tashi daga kwanciyar da yakeba,
"Hello", ummeetha barka da da rana,
" yauwa na duba ka banganka ba kuma nasan tare muka shigo",
"na koma part ɗina ne ta ƙofar baya na bi shiyasa,
" OK kazo muyi launch mana,
"ummee kuyi kawai yanxu zanshiga masallaci ne,
" Ba damuwa tace tare da yin rejected call ɗin
Duk wannan wayar daga kwance yayi ta tashi yayi gaba ɗaya ya tare da dafe kansa idanuwan sa a rufe suke kamar ko yaushe idan ya kasan ce shi kaɗai iska ya furzo daga bakin sa alamar gajiya,
Bayan wasu ƴan sakanni yana ahaka sai kuma ya ware ida nuwansa akan screen ɗin wayar sa da ya dauki rure ɗan tsaki sulaim ya saki saboda ba ya son abunda zai takuramishi ko kaɗan,
Ajye wayan yayi sannan ya tashi ya nufi toilet,
Dinning table Ne dogo mai ɗan faɗi kaɗan yana ɗauke da kujeru guda goma sha biyu 12 chairs suna zazzaune kowa anyi saving ɗin shi abinci ne kala kala kowa da irin wanda ke gaban sa,
Mommy wai su daddy da yaya saleem sai yaushe zasu iso yanzu da suna nan da tuni hadda su muke launch ɗin ko, ta kafe mommy da ida nuwa tana jiran taji mai zata ce,
Eh auta da tunifa da su amma ai sai dare zasu shigo nayi magana dasu kinga sai muyi dinner a tare ko? Ita ma mommy tambaye princess fuskantar da murmushi,
Eh haka nee mommy amma......
Amma me waike salma bakinki bazai taɓayin shiru ba kibar mana mommyn mu taci abinci kada takware Tunda ke kinsaba kina cin abinci kina surutu ko gajiya bakya yi Haba,
Wata budurwa ce tayi magana wadda dagani kasan ta girmi princess
Mommy kinga auntie suhailat ko 😢 wai salma take cemin kuma bayan an dena faɗamin wannan sunan tafaɗin hakan idon ta har yaciko da kwalla don ita mantawa ma take da sunan Idan ba a school ba, cikin kuka tace mommy ko friend ɗina diamond suke cemin fa,
Wai salma bazakiyi mana shiru ba cewar ummeetha dake dariya ƙasa ƙasa
Tab yau fa kun taro mana cewar mommy kafin ta rufe baki tuni princess ta tashe dagudu tayi haura upstairs tana kuka,
Auta auta ina tayi sama Haba ummee kunfa korar mun daughter ta tana cin abincinta mommy ce tayi maganar wadda da ita wasa ta ɗauki maganar ashe ita princess da gaske take,
Ummeetha tace ƙaleta dama fa ta ƙoshi don bikiga ciye ciyen da tayi a motaba dama idan muna son tabar guri kotabar wani abun anace mata salma yanxu zata bari ita saidai princess salma saboda haka mutanan masarautar GABAS suke ce mata,
Dariya suka sa gaba ɗaya hada saleema da hankalinta na akan wayar ta tunzaman ta gurin abinci ma ba wani ci takeba burinta kawai taga ta inda sulaim zai shigo saboda tanaji sanda suka yi waya da ummeetha taso ace yazo cin abincin nan da ta ƙare masa kallo yadda takeso,
Suhailat tace Mommy Ai biki san wani abuba yanxu bari kiga anjima idan za aje gaida su grandad haka za tace babu inda zata je saboda hajiya umma salamatu take ce mata shiyasa ta tsani zuwa part din su,
A lallai dole taƙizuwa bari ingama inje in lallashi auta gaskiya bakwa kyauta wa 😅
Tashi suka yi kusan atare suhailat dake kokarin tashe ita kuma saleema har tama tashi ummeetha bari inshiga cikin inada exam. Gobe har 3
To Allah yabada sa'a
Ameen ta amsa tare da wucewa
Dai dai hawa sama suka haɗu saleema nashirin wucewa suhailat tace barka da zuwa NIGERIA sister saleema fatan kun iso lpy,
Oh dakinso ganin yadda muka iso da har airport zaki samemu taƙara yunƙurin wucewa,
Suhailat tasha gabanta Haba saleema kiyi hakuri mana wlh naje school saboda exam nakeyi shiya kuma naso insameku ko a airport din ne dana taso sai ummeetha tace kawai muhaɗu a gida saboda a time ɗin kunkusa ƙaraduwa gida,
Oky yayi lpy muka zo ta furta hakan tare da wucewa sama abunta itama suhailat din ta wuce duk bata ji daɗin abunda saleema tayi mata ba amma tayi alƙawarin bazata sake damuwa da harkar taba yanxun ma don kada tace ta ɗora alhakin rashin yi mata magana akanta shiya amma tasan halin saleema akwai wulaƙanci ga girman kai to shiyasa ma zata ja mutuncin ta duk da ko ashe karu ba wani girman ta tayiba,
Mommy da ummeetha Suma sungama har sun koma palo suna hira jefi jefi mommy tace wai ya batun lafiyar sulaim? Abun na raina wlh
Kamar dai kullum yadda kika sani to amma dai alhamdulillahi kawai za ace cewar ummeetha wadda damuwa ta bayyana akan fuskarta dagani kasan maganar ta taɓa ranta sosai
Mommy kibari kiƙara hutawa sai muyi wannan maganar,
To mommy tace do ba yadda taso,
IN THE NIGHT
WANI dattijon balarabe na hango zaune a tsakiyar kujirun wani palo mai girman gaske da ya gaji da haduwa komai na cikin palon white colour new hatta da kujerun ciki,
Fuskar dattijon mai ɗauke da cikakkiyar kamala da kwarjini gawani yalwataccan murmushi abisa kyayyawar fuskar tashi, yana zaune a ɗaya daga cikin kujerun da suka zagaye tsakiyar palon, wani ƙaton hotoni irin na mutanan dacan wadda fari da baƙi kawai ake ayi gani a jikin hoton shine a maƙale a jikin bangon palon an ƙayata hoton yayi kyau aciki amma baka iya gane mutanan dake cikin hoton idan ba gaya maka akayi ba,
Sai wani hoton shima amma yafi wancan girma shi wannan da ganima ba awani daɗe dayin saba daga saman hoton an rubuta ARAB FAMILY da man yan baki, kowa yana zazzauna acikin palon wasu na daddana waya wasu kuma nayin magana ƙasa ƙasa daga gefe da Gafan hannun sa na dama matar sa ce uwar gidan hajiya umma sai gefan hagun sa mama bilki itace ta biyu dama matan ALHAJI IMRAN MUHD ARAB Biyu ne sannan yana da ƴaƴa guda goma sha uku 3, hajiya umma na da yara bakwai 7 ita kuma mama bilki yara shidda 6,
Ƴaƴan hajiya umma,
Hameed, Bello, shaddad, Aliyu, Abubakar,
Bahijja, sai autar su hauwa u suna kiranta da jiddah
Ƴaƴan mama bilki,
Hasheem, Mansur, Sambo, Yusuf,
Jamila, sai Saratu suna kiranta da SARA,
Kowa yana zaune a palon tare da Ƴaƴan sa matan ne kawai babu mutum biyu suma da yake auran nesa suka yi sara ɗiyar mama bilki da kuma Bahijja babbar ɗiya mace a gurin hajiya umma, dune kawai babu a taron muta nan gidan,
Gyaran murya alhaji IMRAN ARAB yayi cikin muryar dattaku da girma ya fara magana banga sulaim ba ko baya nan ne? Yayi tambayar yana kallon inda yaran sa maza suke baki ɗaya suma akan kujera suke zaune ko wanne da matar sa sai jikoki maza suma suna zaune daga ƙasa? Don bazai taɓa furta komai batare da rabin ran nashi nan akusa dashiba wato sulaim Tunda yafito bai ganshiba yaji duk ya takura,
Magana nake kunyi shiru
Gashinan zuwa yanzu insha Allah aranshi kuma yana addu'ar Allah yasa sulaim ɗin ya taho Tunda shidai kawai faɗaya yayi don yasanya yayan nasa bazai taɓa magana ba saboda sulaim shine ɗan fari a gurin sa, cewar daddyn Canada wadda dashi akayi sallar isha'i acikin estate ɗin nasu shida ɗan sa saleem da suka biyo jirgin yamma daga Lagos zuwa Kano,
Gudu yake cikin cikin mota sosai Haba sulaim kabi a hankali mana cewar saleem dake zaune a gefe,
Ni fa saurin da nake daban bawai na meeting ɗin nan bane duk yau banga baffa na ba wlh jinake tamkar kaina zai tarwatse idan ban ganshi ba, seriously yayi maganar tashi babu alamun wasa ko dariya,
Dariya saleem yasa don shi bai yi tunanin har yanxu wannan ƙaunar nan tsakani sulaim da kakan su alhaji imran ba wanda suke kira da baffa,
Dai dai lokacin da ya hau wannan titin dayi gabas wanda daga gefan titin akan ƙaramin allon akasa ALHAJI IMRAN MUHD ARAB STREET,
amma da naga da ƙafarka ka