Showing 57001 words to 60000 words out of 61789 words

Chapter 20 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel

Fauzah   

04 Nov 2025

191

sa ido sosai har naga fitowar Yarin yar,

Kallon Suhaima baffa yayi wadda take tsaye a kanshi lokaci ɗaya yaji ƙirjin sa ya buga da ƙarfi har sai da ya dafe shi ya furta "hazbunallahu wani'imal wakil" cikin zuciyar sa tare da jin Yarin yar har cikin ransa bai san kuma dalilin hakan ba gashi dai ko fuskar ta bai gani ba" ƴa ta samu guri ki zauna kinji" baffa ne yafaɗa cikin nutsuwa, Suhaima wadda tunda taji muryar baffa gaba ɗaya taji wani abu ya daki tsakiyar zuciyar ta wanda itama batasan dalilin hakan ba, lokaci ɗaya kuma taji daɗin kiranta da yayi da ƴar sa da yayi wanda batayi tsammanin hakan ba duk zaton ta ba zo a haka ba tayi tsammanin zasu wulaƙan ta ta ko suci mata mutunci, ko su sa akulle ta shiyasa itama tazo da shirin ta kullum da shirin tun karar su take tare da ɗaukar wa kanta alƙawarin sai ta wulaƙan a halin gidan ta tona musu asiri sannan ta kashe duk wani wanda yake da sa hannu a tarwatsa farin cikin rayuwar su tundaga ƙuruciya, kisa mai haɗe da tsanin azaba ɗaya bayan ɗaya saboda ita aranta take da yaƙi nin basu isa suyi mata komai ba dole ta ɗau fansar ta,

Sai da baffa ya ƙara Faɗin ko dai ƴar tawa kurma ce," cikin nutsuwa Suhaima ta russuna a gaban dattijon wanda taji gaba ɗaya jin nauyinsa yakama, ta furta " barka da yamma" bai amsa ba sai cewa da yi zauna sosai saman kujera, tashi Suhaima tayi ta zauna, sai da ta zauna sannan baffa yace, "barka dai sannan ya ɗora da cewa" a madadin Ahalin gidan nan inayi miki barka da zuwa, yaci gaba da cewa "Yarin Ya yau tsawon kwana huɗu 4 kenan kina zuwa nan kullum ina ganin zuwan ki da tafiyar ki ina so ki sanar dani dalilin zuwan ki nan ɗin saboda mu masu mara ba da kowa ne,

Ɗan jim Suhaima tayi don bata iya ƙarya ba tana son tafaɗa masa don ba tsoro take ji ba, sai kuma wani sashe na zuciyar ta yake bata umarni kan kada tafaɗa ɓoyewar shi zai bata damar ai watar da aikin ta yadda take so kafin lokacin bayyana musu gaskiyar yayi, take ta buɗe baki tace "babu wani abu dama gurbin aiki nake nema a gidan nan koda wanke-wanke ne da shara" ta kai ƙarshan maganar a ɗan sanyaye jin wani abu ya to kare mata a maƙoshi,

Shiru baffa yayi yana nazarin ta sosai, har saida Suhaima tafara tsarguwa jin shirun da yayi kaddai ace ya gano ta, katse mata tunani yayi ta hanyar Faɗin " To amma ƴa ta wani yace miki muna neman masu aiki ne ko kuma kawai zuwa kikai?" a a babu wanda yafaɗa min hasali ma bansan nan ɗin ba dalilin wani ɗan gidan nan ne da yayi mana alkhairi nida ƴar uwata shine ni biyo bayanshi ranar domin yi masa godiya kuma bansamu damar hakan ba, bayan naga inda ya shiga saina koma ganin babban gida ne sainayi tunanin dawo wa ko zansamu aikin yi saboda Kula da kanmu"

" To amma ina iyayan ki sun san kina zuwa nan ko su suka ce kine mi aiki" baffa ya ƙara jefa mata tambayar, babban abunda Suhaima ta tsana kenan tambaya, a taƙaice ta bashi amsa da " mu marayu ne Bamu da kowa dagani sai ƴar uwata" taɓoye mishi maganar mother, cike da tausaya wa baffa ya ɗago ya kalle ta sosai har cikin ranshi yaji son yarin yar tamkar shi yahaifeta Tunda ta shigo yake ji wani tsohon al-amari na taso masa amma yakasa tuna Meye wannan ɗin gashi har ga Allah ya yarda da ita ɗari bisa ɗari saboda yadda yaga tana magana cikin nutsuwa da kwarin gwaiwa, " cikin halin tausayi yace" Allahu akbar Allah yayi musu rahma, ina mai Baku hak'urin rashi, sannan mu ɗaukar masu aiki duk ƙarshan shekara kai tsaye ake kawo mana su daga wasu yankunan ƙasa shan da kuma na wannan ƙasar ba'a daɗe da ɗibar ma aikatan ko wane ɓangare da ke cikin gidin nan ba, amma kukan ku yazo ƙarshe ƴa ta zaku dawo nan keda ƴar uwar taki sai asamu inda za abaku kurinƙa kulawa dashi,

Karo na farko Suhaima ta ɗago kai don ganin wannan mutumin mai imani da tausayi yahar haka, a lokacin da tayi arba da fuskar baffa take taji wani ya kwanta mata acan ƙasan ranta take jin kamar tana da alaƙa dashi saboda yadda zuciyar ta ta karɓe shi lokaci guda duk da wutar tsana da kuma ƙiyayyar da takeyi wa mutanan gidan, kwar jinin sa da cikar kamalar sa da dattaku irin nasa taji cewar tabbas akwai sabon al-amari dake shirin faru, "a hankali kuma ta furta muna godiya sosai Ranka ya daɗe Allah yasaka da alkhairi"

Murmushi baffa yayi tare da Faɗin Allah yayi miki albarka zaki iya kirana da baffa saboda haka ƴa ƴa da jikoki ke kirana dashi, amma yanzu a ina kuke da zama sannan duk zuwa dakike bantaɓa ganin ki da ƴar uwar takiba, "shiru Suhaima tayi don ƙaryar ta takusa Ƙarewa dabara ce tafaɗo mata tace muna zaune a gurin wata mai saida abinci ne kuma tace nan da gobe zata sallame saboda itama zata yi tafiya zuwa garin su kuma dama a gidan ta muke da zama" jin jina kai kawai baffa yayi alamar gamsuwa da maganar taya, kafin yace yanzu zansa a ɗauke ki amai dake gidan naku sai kitaho da ƴar uwar taki zanyi magana akan inda za abaku ku zauna, amma ƴata kafin ki tafi inason ganin fuskar ki idan babu damuwa saboda idan kuka dawo za a wuce daku ne ba lallai kudawo tanan ba sai na ne meku sannan ba dole guri ɗaya zaku zauna ba keda ƴar uwar taki.

Babu musu Suhaima tasa hannu tare da fara kunce ɗaurin mayafin da ta rufe fuskar tadashi akaro na farko wani ko wata basu taɓa cewa tabuɗe fuskar ta kuma taboɗe ɗin saidai su gaji su ƙale ta hatta a garin su ko malaman su ɗai ɗai kune sukan fuskar Suhaima, amma wannan babu musu jitayi tamkar ana bata Umarnin buɗewa..!!

🌹🌹🌹

___________-------___________

_BARNO STATE_

_Masarautar Gabas_

........Shirye shiryen hawan da yarima Sultan zai gabatar ake tayi daga kowane ɓangare nacikin masarautar kowa yana ta hidima sai ka rantse bikin salla ko bikin aure akeyi acikin masarautar ɓangaran Ummul bait baƙi ne sosai daga wasu masarautun na kusa da nanesa,

Hajiya mai soro ce zaune saman kujera sai kuma wata doguwar matashiyar budurwa zaune tana fuskantar Hajiya mai soro, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya dagane kasan akwai mulki a tare da ita magana tafara tare da kai hannu ta dai dai ta zaman siririyar BARIMAR zinaran dake hancin ta, " umma kuna da tabbas akan maganar da jakadiya ta kawo nacewa yarima shigar ɗawisu zaiyi?" ta kai ƙarshan maganar tare da kallon Hajiya mai soro wadda suke kira da ummah, "tabbas wannan maganar haka take Sultana saboda mahaifan ki shima ya ƙara tabbatar min da maganar" ɗan Farr Gimbiya Sultana tayi da ido kafin tace "to shikenan a shirya min komai Tunda zuwa 4 ne za a fara gabatar da taron kuma sannan a ƙara yawan ƙaututtuka ga yarima Sultan wanda zan gabatar dasu a gareshi don ina sane da isowar Shaheedah cikin masarautar nan zuwa nan da jimawa, cikin isa da izza take maganar tamkar itace mahaifiyar lokaci zuwa lokaci tana ɗan kaɗa ƙafar ta a hankali"

Tana kai ƙarshan maganar tata tamiƙe tabar parlourn zuwa nata ɗakin, kallo Hajiya mai soro tabiya dashi dan ita kaɗai tasan abunda suka shirya wa yarima sultan a wannan hawan da zaiyi Sunyi alƙawarin ko yayi hawan bazai sakko lafiya ba, don ita fa duk yadda takeson Sultana ta auri Yarima sultan bai kai yadda take ƙaunar taga mijin ta akan mulki ba wato Galadima ƙanin sarki saboda haka take son idan har mijin ta bai samu damar hawa jaragar sarki ba to ƴar ta ta auri sarkin gobe Wato Yarima Sultan sai su samu sugama dashi da mahaifin sa sarki Yusuf Shareef su mulki yankin GABAS ita da mijin ta Murtala shareef,

Tana cikin wannan tunanin tasamu isowar jakadiya take ta bada izinin ta shigo dama ita take jira, da sauri jakadiya ta ƙaraso tare da zuɓewa a gaban Hajiya mai soro ta kwashi gaisuwa, saida ta bata damar magana sannan ta ɗora da cewa, "Ranki ya daɗe an gabatar da komai yadda kuka tsara, komai na ai watar dashi yadda ya kamata hatta dokin dazai yi hawan dashi nabawa sarkin doki ya shafa maganin a bindin Dokin kamar yadda kika bada umarni, kallon ta Hajiya mai soro tayi " aiki mai kyau jakadiya to shi wanda nace ki binne akan hanyar sa tazuwa ɗakin taron kinyi hakan? Ƙara russunawa jakadiya tayi tace a a ranki shi daɗe hanyar Da yarima Sultan zai bi babu gurin da za a binne wani abu saboda babu ƙasa amma dai munyi amfani da ta kalmin da zai sa yayin tafiyar sa zuwa gurin,

Dakyau naji daɗin hakan zaki ita tafiya amma yaya ɓangaran Fulanin sarki (ummu Safwan) babu wani abu da take shiryawa ko wani makirci, "eh to ranki shi daɗe bani da labari a taɓan garan ta saboda ta hana bada izinin shiga amma nasan duk wani shirin ta akan Yarima da Gimbiya Siyama ne... Tunkafin jakadiya takai ƙarshe Hajiya mai soro ta daka mata tsawa tare da Faɗin a gidan ubanwa tazama gimbiya ƴar ruƙo cefa acikin masarautar nan taya zata zama gimbiya?".

Saida jakadiya ta ɗan tsorata tare da Faɗin tuba nake uwar ɗaki na uwar mu maganin kukan mu Allah ya huci zuciyar ki da yaddar ubangijin sama sai Galadima yazama sarkin Gabas, "wani katsaitaccan murmushi Hajiya mai soro tayi tare da faɗin kin wanke laifinki Yalabarin gimbiya Shaheedah?

Yanzu naji ana sanar da tafiya ɗakko ta daga filin jirgi ta iso cewar jakadiya, shiru Hajiya mai soro tayi kafin tace zaki iya tafiya kome kenan ki sanar dani cikin gaggawa, "jakadiya ta amsa da cewa angama uwar mu maganin kukan mu nabarki lafiya"

🦋

Princess ce ki tafiya sannu a hankali cikin sanɗa a wani Ƙaya taccan (garden) mai girma ya haɗu iya haɗuwa ga wasu kyawawan shuke shuke a gurin sai wani irin ƙamshi yake mai daɗin gaske ga wasu haɗaɗɗun runfuna da suke ciki guda uku ko wace runfa da akwai kujeru biyu acikin ta da ɗan ƙaramin table a tsakiyar su, ga yanayin garin hazo akeyi cikin jin daɗin weather ɗin taɗan yi tsalle tare da faɗin masha Allah can kuma tafara murmushi saboda ta hango wani ɗan ƙaramin ruwa yana ta gudana fari tasss kana iya ganin komai dake cikin sa,

cikin ranta tace nasamu ruwan da za rinƙa yin wanka aciki har mubar masarautar nan da sauri ta ƙara sauri zuwa bakin ɗan ƙaramin ruwan mai ƙayatar wa batare da wani tunani ko bata lokaci ba Princess ta zuge zif ɗin doguwar a bayar dake jikin ta zif ne wanda tun daga sama har ƙasa ta gaba, ta rage daga ita sai dogon wando baƙi wanda ya kama jikin ta sosai sai black T-shirt Mai ɗan ƙaramin hannu wadda itama da kaɗan ta rufe mata cibiya idan tayi kwakkwarar motsima za a iya ganin cibiyar tata,

viel ɗin rigar wanda ta ɗan yafa shi akanta shima tacire shi tare da warware yalwataccan gashin kanta baƙi wilik wanda har gadon bayan ta sai ƙalli yake da wani irin ƙamshi naman gashi saboda yana samon gyara koda yashe saida tagama kintsawa sannan ta riƙe ƙugu tana kallon ruwan sai kuma ta tsugunna takai hannu tataɓa taji ko da sanyi, gama makin ta sai taji ruwan ɗumi kamar wanda aka tafasa aka suka da nasanyi duk sanyi da ake a garin amma kuma ruwan dake buɗe a sararin subahana, ace bai ɗau sanyi ba, lokaci ɗaya kuma ta kawar da tunanin da tatuna ai suma na Estate ɗin su haka yake akwai Heater aciki idan sanyi yayi sanyi tana kunna kanta, Kamar Wadda aka cilla cikin ruwan haka Princess Salma tafaɗa ruwan cike da nishaɗi da jin daɗi take wasa da ruwan wanda yayi mata daɗi sosai sai ta nitsa kanta aciki ta fito dashi,

gaba ɗaya gashin kanta ya jiƙe sharkaf da ruwa ya kwanta saman fuskar ta da bayan ta, tanusta sosai cikin duniyar farin ciki, can tajiyo wayar na ruri alamar ana kiran ta wadda ta ajiye ta saman wani dutse dake kusa da ruwan, jin mai kiran yaƙi ba saura rawa ne yasa tafara yunƙurin fito wa daga cikin ruwan amma ina takasa tayi tayi tafito amma takasa take tafara kuka tana ɗaga hannu alamar a temaka mata duk da tasan babu kowa a gurin tana ta yunƙuri tare da ihu iya ƙarfin ta,

Babu tsammani princess taji an kamo hannun ta tare da ɗagota daga cikin ruwan cak ta runtse idanuwan ta jin anyi sama da ita kwantar da ita yayi saman faffaɗan ƙirjin sa tamkar wanda. Ya ɗauki ƴar tsana haka ya juya batare da ya ɗauki komai na princess salma ba, sai da sukai nisa sannan ta gane cewar anfito da ita daga ruwan saboda tsabar ruɗani data shiga, ahankali tafara ɗagowa jin alamun tafiya ake da ita kuma sannan kamar a hannun mutum take, idanuwan tane suka sauka cikin kyawawan nashi idanuwan, ƙara zaro ido waje tayi tare da son gano wannan waye haka saboda yasa marks ya rufe fuskar shi dashi iya idanuwan sa kawai ake iya gani sai kuma lallausan sajansa, wata irin isaka aka buso ga hazo da matsanancin sanyi babu shiri Salma ta ƙara shige wa jikin Sa tare daƙara tura kanta cikin ƙirjin sa sabon wani irin gigitaccan sanyi da taji ya kwashe ta ga jikin ta a jiƙe yake sharkaf da ruwa babu shiri tafara rawar sanyi bakinta har ƙara yake haƙoran ta na sama na dukan na ƙasa,

Cikin sassarfa ya ƙarasa shiga ɓangaran nasa dayake ta ƙofar baya ne babu wanda yahaɗu dashi, kai tsaye ya nufi bedroom ɗin sa da ita saɓe a hannun sa, kwantar da ita yayi saman tangame man bed ɗinsa Wanda aka shinfiɗa masa lallausan bedsheet white colour Komai na bedroom ɗin white colour NE hakan yabawa ɗakin yin wani irin haske mai kyau, gado ne irin na sarakai mai rumfa asaman shi gefe da gefan bed ɗin bedside lights ne sai Kuma wani hayaƙin turaren wuta dayake tashi shi kin wani irin salo mai jan hankali ga dadda ɗan ƙamshi,

Bayan ya kwantar da ita yaja lallausan blanket mai kyaurin gaske ya lulluɓeta dashi ganin har lokacin rawar sanyi take hakan yasa shi kunna masuburbuɗar zafi wato (room heater) kallon a gogon dake maƙale a bangon ɗakin yayi ganin 3:25pm hakan yasa shi faɗa wa toilet daniyar yin wanka,

Tashi princess tai saboda jin ɗumi take tako ina gashi dai kayan jikin ta a jiƙe suke amma ta rage jin sanyi sosai, kallon ɗakin tashigayi ganin komai fari hakan ya burge ta tare da ƙayatar da zuciyar ta, ganin ta tayi a tsakiyar makekyan gadon wanda zai ɗauki irin ta 20 kowa kuma a wadace ƙafar ta tazuro a hankali ta sakko, mamaki ta farayi to shin wannan waye ya ɗakko ta daga cikin ruwan, aranta kuma tana tunanin tabbas tasan wannan ƙamshin turaran wanda ya ɗakko ta wanda gaba ɗaya itama ya kama mata jiki, tana cikin wannan tunanin ne tafara jin motsin mutum abayan ta, cak ta tsaya amma takasa juyawa saboda tsabar tsananin tsoro, jin shiru ne yasa ta juyawa cikin a hankali, "Laaa laaa laaa Yarima Sultan sai kuma tayi saurin dafe bakin ta ganin ya kafeta da manyan idanuwan sa take tafara tarayu abunda ya faru acikin ranta tace kaddai ace Yarima ne ya ɗakko ni daga ruwa to idan bashiba waye?,

Raɓata yayi yawuce wanda fitowar sa kenan daga wanka ya zura jallabiya kafin yashirya zuwa wajan taro saboda yaga lokaci ya kusa, guri yasamu saman wata kujera wadda ke a ɗakin itama fara ce tass tamkar ba a taɓa zama a kanta ba,

Ganin bashi da niyar yi mata magana hakan yasa ta Faɗin yaya yarima barka da yamma, kallon ƙasan ido yarima sultan yayi mata wanda ita bata ma kula da hakan ba, saida ya mula ya sha iska kafin yace" Meye yakawo ki ɓangaran nan sannan ya akayi kika iya shigowa" a jere yayi mata tambayoyin,

Ranka ya daɗe niba bansan yadda akayi nazo nan ɗin ba nidai kawai nasan munje sashen Ummul bait nida su ummeetha shine na fito na barsu acan saboda nafiso inzagaya cikin masarautar, bansan ta yadda nazo nan ɗin ba fakar idon fadawan dake ƙofar shigo wa nayi sannan nasamu na shigo saboda naga babu yawan jama'a a gurin yanzu gashi bazan iya komawa bama saboda bazan gane hanya ba,

Baisan lokacin da ya shagala wajan kallon princess ba wanda take maganar cikin shagwaba tare da turo ɗan ƙaramin bakin ta gaba, jin shiru ne yasa ta ɗago dakai tana kallon sa, suna haɗa ido ya kyauda kansa cike da basarwa tare da ɗaure da ƙara ɗaure fuska sosai,

Cikin isa da izza irin tashi yace kin isheni da magana maza kiɓa cemin daga gani yanzun nan,

Kamar me jira princess ta nufi ƙofar da sauri batare da ta ƙara cea komai ba, jin ƙofar tayi a rufe ƙara kama handle ɗin tayi daniyar buɗewa still a rufe jiya wa tayi ta kalle shi idanuwan ta cike taf da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login