Showing 36001 words to 39000 words out of 61789 words
Chapter 13 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel
yazo gidan nashi kawai sai su tafi idan suka gama meeting ɗin sai ya wuce Niger,
Dahaka suka yi salla alhaji imran yabawa driver ɗin nasa umarnin su nufi gidan alhaji idris ɗin tsaye,
Babu musu ya ɗauki hanyar unguwar gadon Ƙaya, zuwa gidan alhaji idris ɗin Tunda dama ya sani,
Babu ɓata lokaci suna zuwa, alhaji idris yaga shirya musu komai, kawai hanyar Katsina State su ɗauka,
A ranar meeting sukayi sosai da wasu mutanan da suke kasuwanci dasu mazauna ƙasar Australia 🇦🇺kan wani sabon company da suke so su kafa a ƙasar ta Australia, take alhaji imran ya wakilta babban ɗansa HAMEED ARAB kan wanda zai wakilcesa zuwa ƙasar Australia 🇦🇺
Sanda suka gama meeting ɗin around 6:44pm magrib tayi,
Kabari mana zuwa gobe sai ka wuce Niger ɗin nima saina koma gida, Tunda dare ya ƙara to kuma dama inaso mu tattauna akan wasu batutuwa cewar alhaji idris, wanda ke kallon alhaji imran ɗin,
Dan Jimm alhaji imran yayi kafin yace to Allah ya kaimu lafiya, ba don taso ba ya so ganin uwar gidan sa kuma farin cikin sa a ranar to amma ai duk ɗaya ne a gurin Allah da haka ya kau da tunanin nasa,
A wani guest house ɗin alhaji imran suka sauka wanda ke acikin garin Katsina dama yakan sauka anan ɗin idan dare yayi masa a hanya,
Sosai alhaji idris yabawa alhaji imran shawara kan ya rage tunanin dayake yawanyi,
saboda doctor ya faɗamin wancan lokacin da ya duba ka jinin ka ya hau sosai, duk nameye wannan ɗin?
Ka ƙara hak'uri sosai idan har ƴar uwar ka da mahaifan ka naraye zaku gana kuma zamu cigaba da bibiyar garin da harzuwa sanda Allah zai sa a dace,
Sosai alhaji imran yaji daɗin maganganun abokin nasa kuma aminin sa duk da ya sosa masa inda yake yi masa ƙaiƙayi gashi dama a ɗan tsakanin nan yana yawan mafarkin ƙanwar tasa wato BAHIJJAH Sai dai kawai yayi addu'ar Allah yasa duk inda suke suna cikin ƙoshin lafiya,
Sannan alhaji idris ɗin ya ƙara da cewa, kuma baka ganin kana ɗan matsawa HAMEED da harkokin nan kuma na fahimci kamar yafison karatun sa,
Alhaji idris kenan ai HAMEED dole shi zai tsaya akan komai kaga kuwa dole yafara sabawa da su tun yanzu,
Jinjina kai alhali idris yayi alamar gamsuwa, da haka dai suka cigaba da tattaunawa da kuma bawa juna shawar wari game da rayuwar su,
Bayar da wuwar alhaji imran ARAB Nigeria aka fara zuba kaya acikin estate ɗin wanda tsayawa faɗar tsarin sa ma ɓata lokaci ne komai na amfanin gida kama daga furnitures, daga ƙasashe daban daban aka kawo su,
Mama bilki kullum farin cikinta zata mallaki estate mai girman gari guda, daga ita sai ƴaƴan ta,
Aranar da suka dawo nan bata san Hajiya umma kwanan su na biyu kenan aciki, tana ta haukan ta,
Saida alhaji imran yace zai shirya zama da dukan su sannan tasani baƙaramin tashin hankali ta shiga ba tama rasa tunanin Meye zata yi, to aikin bokan tane bai yiba koko ita tayi kuskure wajan aikin, ta tambayi kanta,
Tare da masifar ai alhaji imran yaci amanar ta bai faɗa mata ya ɗakko matar shiba, gashi boka ZARSHIMA yace mata duk wadda tafara shiga cikin estate ɗin acikin su to ita zata mallaki komai sannan ƴaƴan ta zasu jagoran ci komai na ARAB family,
Tuna wannan maganganun bokan ne yasa ta ƙara jin kamar tayi hauka, amma bazata haƙuraba dole tasan abunda zata yi,
Da yake gogaggiyar ƴar duniya ce bata taɓa nuna mugun halinta a fili ko hassadar ta akan Hajiya umma da ƴaƴan ta,
Rayuwa mai daɗi suke gabatar wa acikin estate Ɗin amm banda mama bilki wadda kullum tunanin ta da lissafin ta taya zata kai Hajiya umma ƙasa,
Bayan wani lokaci hasheem yazo da maganar aure, alhaji imran bai hana shiba saboda yana ganin kamar hakan zai sa ya gara halayen sa,
Fatan alkhaeri alhaji imran yayi masa tare da bashi mukullin house guda ɗaya acikin estate ɗin,
Hasheem baiyi wani farin ciki ba saboda shi kuɗi yake so kawai a sakar masa, shikuma alhaji imran yace bazai bashi ba amma shi zai yi koma ya zaɓi ko Meye yakeso afaɗin Kasar Nigeria da ƙetare zai yi masa shi,
Amma ina hasheem yaƙi yadda daga ƙarshema sai yayi zuciya yace bazai zauna acikin estate ɗin ba shida matar tasa,
Alhaji imran bai ƙara bi takansa ba yaci gaba da harkokin sa na yau da kullum cikin farin cikin rayuwa da ahalin sa wanda ya daɗe yana mafarkin tarawa, don a lokacin duka matan sa sun gama haihuwa saidai wasu daga cikin ƴaƴan suna ƙanana ne,
Lokaci ɗaya hameed da ɗan uwan sa Bello suma suka fidda matan da zasu aura, wanda duk a makaranta ɗaya suke karatu, *BAYARO UNIVERSITY KANO* *(B. U. K)*
Hameed wadda yakeso ƴar garin BARNO State ce mai suna maryam ƴa ce ga wazirin babbar MASARAUTAR GABAS dake a cikin garin jihar Maiduguri,
Hameed Arab da maryam iliyas waziri sun shaƙu sosai har soyayya ta shiga tsakanin su suna son junan so sosai tare da bawa soyayyar tasu cikakke yar kulawa soyayya mai tsafta suke yi maryam akwai ta da son mutane sosai amma kuma akwai jan aji wanda wannan jinin na sarauta ne ke yawo acikin jikin ta ga miskilanci amma bata da wulaƙanci,
Ahaka aka je nimar wa hameed auran maryam har masarautar su, cikin iKon Allah suka bashi maryam ɗin kuma hadda shima sunga daga babban gida yafito,
Batare da wani ɗan kan lokaciba aka ɗaura auran su, hameed da Bello da Mansur ɗa na biyu a gurin mama bilki,
Duk a lokaci ɗaya aka ɗaura musu aure, kamar yadda alhaji imran ya bawa hasheem key ɗin house Suma haka yabasu gaba ɗaya acikin ARAB ESTATE ɗin,
Wanda shi Bello dama yagama komai jira yake bayan biki da wata 2 ya wuce Canada inda acan zai ɗora dakaratunsa, shima kuma matar tasa ƴar garin Kano ce ƴar gidan wani babban attajiri ne sannan tsohon ministan lafiya na ƙasa, sunan ta safiyya, itama dai auran soyayya suka yi ita da Bello sannan kuma ra'ayin su komai yazo ɗaya,
Haka rayuwar ahalin alhaji imran ARAB ta cigaba da tafi, duk wani jika acikin ARAB Estate aka haife shi...!!!!
*Comment share nd more like fisabilillah*🙏
https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V
WhatsApp channel
*AHALIN MU DAYA*
*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍
*NAZARI WRITER'S ASSOCIATION*📚
_Sarauniyar👸Nazari writer's association_
______Dedicated to aunty salma💎
*Page* 3⃣ 5⃣↔️3️⃣6⃣📖
Haka rayuwar ahalin alhaji imran Arab ta cigaba da tafiya, duk wani jika acikin Arab Estate aka haife shi,
Ƴaƴan shi sun taso suna kiran shi da ABUYA daga baya kuma sai suka koma ce masa baffa saboda ƴa ƴan abokin sa alhaji idris haka suke ce wa abokin ma haifin nasu baffa saboda su Fulani ne,
Shine dalilin da yasa suka tashi da baffa abakin su kuma sunan ya bishi hadda jikoki haka suke ce masa, baffa
Daga baya shima Bello ya ɗauke matar shi safiyya da ɗan sa na fari saleem wanda aka haife su kusan lokaci daya da sulaim, suka koma Canada da zama baki daya sabo da yafara aiki acan ɗin,
Komai na dukiyar alhaji imran Arab ɗan sa hameed yaɗora akai mahaifin sulaim saboda yanada amana sosai duk abunda ba nashi ba baya taɓa sai rai akanshi shiya alhaji imran ɗin yake son shi sosai kaf cikin ƴaƴan daga BAHIJJAH wadda yasakama sunan ƙanwar sai shi hameed ɗin,
Sannan ya tara ƴaƴan nasa baki ɗaya da matan sa ya basu labarin *HATIMIN MALLAKA* tare da danƙawa alhaji hameed amanar sa,
Tunda suka ji labarin wannan HATIMI hankalin kowa ya tashi wasu tsoron sa suka ji wasu kuma baƙin ciki suka ji kan anbawa hameed Arab ɗin tare da ɗaura aniyar ko tawane hali sai sun mallake shi,
Shiyasa babu jituwa tsakanin ƴaƴan hajiya umma dana mama bilki,
Yusuf ne kawai ya fita zakka acikin ƴaƴan mama bilkin saboda shi babu ruwan sa kowa ma nashi ne gashi da son ƴan uwan sa, shiyasa yayyin sa suka tsane shi itako mahaifiyar tasuma cewa tayi ta yafe shi cikin ƴaƴan ta Tunda yahaɗa kai da maƙiyan ta,
Lokaci daya hasheem Sambo Mansur, sukyi alƙawarin Tunda mahaifin su ya ware su baya sa kasu cikin dukiyar sa, to sai sunyi kudi na ban mamaki sannan ta ko wace hanya,
Aduk lokacin da mama bilki tayi aiki akan Hajiya umma ko ƴaƴan ta sai aikin ya lala ce, daganan ta ɗauri aniyar duk yadda zata yi sai ta tarwatsa Hajiya umma da ƴaƴan ta,
Da kuma jika mafi soyu wa a cikin family ɗin alhaji Arab, wanda Tunda aka haife shi kowa yaki ƙaunar shi saboda sulaim akwai shiga rai,
Tunda ya taso da farin jini sosai kowa yana son ya zauna da sulaim saboda ko babu komai zaka ƙaru dashi ta fuskoki da dama yana da alkhaeri ga son jama'a gashi da ƙoƙari da hazaƙa,
Tunda ga wannan lokacin sai sulaim ya koma abun harin, mama bilki da ƴa ƴan ta, basa son sulaim basa son ganin sa ko kadan,
A cikin ƙanƙanin lokaci sulaim Yakoma abun tausayi kullum cikin faɗuwa aka rasa Meye yake damun sa Yakoma baya son mutane, ko kadan baya son hayaniya, bai son kallo, bai son yawan magana, miskilanci ya zama ɗabi ar sa, karatun sa kadai yake bawa mahimmanci, sosai
Daga ƙarshe alhaji hameed mahaifin saya ɗauke shi gaba ɗaya yamaida shi ƙasar *AMERICA* 🇺🇸 *UNITED* *STATE* acikin babban birnin _Las Vegas_ _(Nevada)_ don yacigaba da karatun sa nazama cikakkyan likitan zuciya *CARDIOLOGIST DOCTOR*
Alhamdulillahi komai na tafiya dai dai a taɓan garan karatun nasa amma dai game da rayuwar sa abun sai ahankali,
Alhaji imran ya shiga tashin hankali sosai ganin jikan sa mafi soyuwa a gareshi cikin wannan halin wanda da bahaka yakeba kullum cikin yi masa addu'a suke tare da kai masa ziyara lokaci zuwa lokaci,
Ummeetha ko tasha kuka a lokacin har Allah yasa ta dangana ta cigaba dayi masa addu'a, amma kullum cikin tunanin Meye wannan yasameshi lokaci daya sun kai shi asibiti kala kala har ƙasar *INDIA* 🇮🇳 suka fita amma maganar ɗaya ce babu wata matsala ake ce musu,
*WANNAN SHINE ASALIN LABARIN ALHAJI IMRAN ARAB DA IYALAN SA, MUKOMA ASALIN LABARIN MU DOMIJIN YADDA ZATA KAYA* *LABARIN AKWAI TSARƘAƘIYA AMMA MUJE ZUWA*
*In the morning*
"Da wuri saleem ya tashi ya shiga babban perlon Part ɗin don so yake yau ayita taƙare tsakanin sa da suhailat"
"Tunda ya furta yana sonta shikenan suke wasan ƴar ɓuya bata ƙara bari sun haɗu ba ko da gano shi tayi sata koma da sauri" ,
"Ya rasa Meye dalilin ta tayi mishi haka da yana tunanin ko kunya ce,"
"To amma yanzu gani yake kawai bata sonshi ne kuma aganin shi ai gara ta fito tafaɗa masa kawai amma sai ta rinƙa gudu wa idan tagan shi,"
"Tabbas rashin ganin ta baƙaramin cutar da zuciyar sa yakeba tare da idanuwan sa, ko dinning ta daina zuwa, duk dan saboda shi" ,
"Zancan zuci yake tafaman yi shi kadai abun duniya duk ya ishe shi,"
"Cikin shigar sa mai kyau na shirin zuwa office yafito yayi shigar favourite colour ɗin shi white and black hannun shi ɗa ruƙe da suit Kamar koda yaushe kunnan sa ɗaya maƙale da _pot_"
"Kai tsaye wuce Part ɗin baffa dama can ɗin yake fara zuwa kullum",
"tunani ya farayi aransa anya bai yi wuri ba Ace yaje yanzu duk da yasan baffa ya tashi amma dai bai son shiga da wuri haka"
"Da wannan tunani ya ƙarasa shiga parlon saboda bazai iya tafiya batare da yaje gurin kakan nasa ba"
"Kodan addu'oin da yake yi masa da salla ya shiga," cikin perlon
"Yaci sa a kuwa yana parlon zaune shida uwar gidan sa Hajiya umma,"
"Barka da asuba baffa"
"Da murmushi akan fuskar shi ya amsa barka dai sulaim katashi lpy? "
"Alhamdulillahi" cewar sulaim dai dai yana zama kusa da kakan nasa kuma abokin sa"
"Kallon sulaim alhaji imran yayi cike da mamakin ganin sulaim ɗin da shirin sa na fita da alama kuma hospital ya nufa abunda baitaɓa gani ba Tunda aka gina ma sulaim asibitin,
" Dumin kyau da tantama sai yace sulaim ina zaka Tunda wuri haka?"
" Batare da da jinkomai ba sulaim yabashi amsa da"
"Zanje office ne, bai jira cewar baffa ba yaɗora da cewa sannan inaso da yammacin yau zan wuce *BARNO STATE* insha Allah YARIMA SULTAN SHAREEF ya dawo daran jiya"
"Magana yake amma tamkar bashi ke yin maganar ba cikin sanyin sa yake maganar"
"Masha Allah hakan yayi dai dai allah yakaimu anjima ɗin cewar baffa wanda duk shifa duk abunda sulaim zaiyi bazai hana shiba matuqar bai saɓawa adduni ba"
"Tashi yayi da niyar tafiya sai ya tsinci muryar Hajiya umma tana magana"
"Wai kai me kaɗau keni ne ina zaune a gurin shine zaka gama magana da wanda kafiso katashi ka tafi ko?"
"Duban inda Hajiya umma ke zaune sulaim yayi saboda shi tsakanin sa da Allah bai san tana gurin ba hankalin da bai kai gurin taba"
Ɗan dafe kai yayi ƙaɗan kafin yace mata
"barka da fitowa" don shi duk tunanin sa a lokacin tazo"
"kallon shi tayi sannan tace Au cemaka akayi yanzu na fito,"
"Kuma haka zaka fita bakaci komai ba to Kazauna kayi karin kumallo" idan ba shiba waye Hajiya umma zata yiwa haka kaf cikin jikoki ta" da wani ne da yasha fada,
"Babu musu sulaim Yakoma ya zauna don shi da wuya yayi musu da manya koda bazai yi abunda suka ce ba to bazai Musa bisa yadda suka ce ɗin ba"
"Jamila Waike bakya tunanin anya bokan da matar nan kebi bai fi namu iya aiki ba,"
"WA kenan cewar anty jamila dake kallon Mahaifiyar tasu"
"Akan wa zanyi magana kuwa idan ba Amina ba (Hajiya umma),"
"Au lallai ma mama to ke sai yau kikasan da hakan aini na dade dangane wa, saida na gaya miki mu canza gurin malami amma kinkafe akan wannan ɗin"
"Jamila kenan kebaza kigane ba yanzu haka da kike gani na bashi sabon wani aikin, mai girman gaske wanda ya tabbatar min idan har"
"Muka kawo masa HATIMIN mallaka to tabbas aikin gama ya riga ya gama takai ƙarshan maganar tare da sakin wani shu'umin murmushi, mai wuyar fassarawa,"
"A wai da gaske fada min wannan wane irin aiki ne haka, cewar anty jamila tana washe baki taji mugunta"
"Matso kiji matsawa anty jamilan tayi saitin kunnan ta mama bilki ta raɗa mata wata magana, kamar sababbin kamu gaba daya suka sheƙe da dariya abunsu kamar ba uwa da ƴa ba hadda tafawa"
"Tab lallai mama kin iya haɗa tuggu kinsan ma Kasar mutum, amma kuma abunda nake tunani ta yaya zamu samu HATIMIN nan kinga kowa fa yana so,"
"sannan kuma itama fa Hajiya maryam (ummeetha) dakike gani a tsaye take saboda kinsan mutanan me dugurin nan babaya ba suna"
"gashi ta ka mai mai ba musan inda zamu samoshiba" lokaci daya ƴar fara ar dake saman fuskar ta ta gushe"
"Ɗan shiru mama bilki tayi bayan tagama sauraran jamilan"
Eh gaskiya ba musan inda yake ba a yanzu amma za mu sani nan kusa sannan na fahimci kowa yiwa kansa yaƙin nan yake"
"to saboda haka zamu ciga ba da tafiya da hasheem, da Sambo, da Mansur han asamu nasarar samoshi daga ƙarshe nasan yadda nayi na raba su dashi"
"Azahiri dariya anty jamila ta saki tare da furta da kyau uwata nasan zakiyi kuma za ki iya"
"A zuciyar ta kuwa cewa tayi lallai ma ai wlh baza ta saɓu ba ku gama lissafin naku ni zan mallaki wannan HATIMIN mallakar"
"kodan na juya Abban Reeyam yadda nakeso da mitsiya tan dan ginsa wato mijin ta"
"Kamar daga sama saleem a tsinci muryar princess tana masa maga"
"good morning yaya saleem"
"Morning little princess"
"Dariya tayi har kyawawan haƙoron ta suka bayyana"
"Ina tamaga amma ba kaji ba sai yanzu hope dai lpy"?
"Tafaɗa tare da zama akusa dashi tana kallon sa"
"Lpy
yabata amsa a gajarce"
"Saboda baya son tada meshi da surutu shi kadai yasan abunda yake ji, sai kuma wata zuciyar tace masa to ka tambaye ta game da suhailat mana ko zaka samu wani abu akai"
"Aiko babu ɓata lokaci yajuya sosai ya fuskanci princess sannan yace"
"Ƙanwata bana ganin Suhailat 2days Allah yasa dai lafiya"?
"Ɗan ɗaga kai princess tayi alamun tana tunani kamar wata babbar mace," dama princess badai iyayiba da manyan ce"
"Nima dai naga bata fitowa yanzu sosai sai zata tafi school ummeetha ta tambaye ta lafiya"
"Tace lafiya kawai karatu ne yayi mata yawa ga exam." abinci ma kai mata akeyi upstairs"
"Saleem yaji daɗin jin tana lafiya ke nan tabbas shi take ɓoyewa kanta kenan"
"Suna zaune ummeetha ta sauke ita da abiiy"
"Gaida su saleem yayi da fara'a ɗauke a fuskokin su suka amsa masa"
"Abiiy yace tana nan ta cika ka da magana ko?
"Dariya Saleem yayi kafin yace Eh Abiiy tunɗazu tanan tana aikin nata"
"Har zillo princess take wajan cewa kai yaya saleem bakai ne ka tsaida niba kana tambaya ta ina aunty Suhailat shine zakace na adameka ko sarkin kuka idon ta har ya cika da hawaye"
"Shiko saleem jiya yi tamkar ya nitse don kunya Yarin yar nan tagama dani ya furta