Showing 18001 words to 21000 words out of 61789 words
Chapter 7 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel
nufin shiga perlon sai ta ƙara jiyo muryar sabrina na cewa ke yama kike da sunan magana nake so nayi dake fa kuma kinganni shine zaki wuce ciki, saboda raini ko Meye,
Suhailat wadda mamaki ya hana ta cigaba da tafiya ta ƙara jiyo wa don bata amsa, kafin tayi magana har ta rigata yi,
"kinga dama banason shiga wannan perlon naku mai kama da makarantar islamiyya kana shiga za a dameka da maganar gaisuwa to ni ba wannan ne yakawo niba, inaso ne kifaɗawa yaya sulaim nazo duba shi idan ya fito yazo Part ɗin mu da yamma don yanzu fita zanyi, kuma nakira wayan shi amma baya amsawa, tana kai wa nan ta juya abunda zata tafi kawai suka yi karo da, saleem wanda dama ya tsaya kwaso wa suhailat ta kaddun tane a mota dasuka dawo,
Dan ja baya tayi kaɗan tare da yin tsaki cikin zafin rai tace kai dalla malan baka ganin mut.... Kyakkyawan marin da saleem ya sauke mata ne yasa sauran maganar tata maƙalewa a maƙoshi, tare da furta mata shashasha, nonsense kawai,
Kamar ba takalmi mai tsine bane aƙafar taba haka ta nufi motar ta Da gudu cikin kuka dafe da kuma tun ta,
Tunda suhailat take zata iya cewa bata taɓa ganin ɓacin rai akan fuskantar yaya saleem ba sai yau har wani huci yake yi, lokaci ɗaya fuskar sa tayi jawur abunka da farin mutum,
Cikin zafin nama ya wuce suhailat fuuuuu zuwa ciki hannun sa riƙe da takaddun ta da yaruƙo,
"" Bazaka iya gane a wane yanayi suhailat take ciki ba, tabbas bata ji daɗin abunda sabrina tayi mata ba kuma har cikin house ɗin su aran ta tace wannan ai wulaƙan cine, amma bazan taɓa biye mata ba saboda akwai banbanci tsakanina da ita, da zancan zucin da takeyini ta shige ciki itama dama ga gajiyar school ga hayaniyar wannan mara lissafin cewar suhailat.
____________________✍️
🌹
Dr sulaim laptop yake dannawa ceke da kwarewa da alama ma ya hadda ce keypad ɗin a kwakwalwar sa, saboda dannawa kawai yake yi batare da yana kallon suba, fuskar laptop ɗin kawai yake kallo, kamar Bai son dawani ɗan adam zaune aga bansa ba bare ma ya dubi gurin, can kuma ya ɗago yakai dubansa kan DR anisha dake zaune shi kawai take kallo, komai nashi burge ta yake yi,
Zaki iya koma wa bakin aiki, sai mu zauna anjima ko.......???
*Wannan kenan...!*✍️
*More Comment More Reactions🤝*
*Oum Ameerah💋*
https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V
*AHALIN MU DAYA*
*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍
*NAZARI WRITER'S ASSOCIATION*📚
_Sarauniyar👸Nazari writer's association_
*Page* 1️⃣9️⃣▶️2️⃣0️⃣📖
Wash Allah na ni Anisha nagaji wlh, ta faɗi hakan tare da zama akan kujerar dake fuskantar wadda Dr.jabir yake zaune,
Kallon ta Dr. Jabir yayi ta lumshe ido sannan ta ɗan zame kaɗan wanda hakan yabata damar kwantar da kanta saman kujerar,
sannan yace Dr. daga ina haka?? zuwa na biyu office ɗinki bakya nan,
Ɗan buɗe idon ta tayi kaɗan wanda Tunda ta zauna ta rufe su alamun gajiya tare da ɗago da kanta,
Naje office ɗin Dr. Sulaim ne taba shi amsa a gajar ce,
"oky good
Ƙara gyara zama Anisha tayi sosai ta fuskanci Dr.jabir,
DR. Kasan Meye?? Ta tambaye shi cike da kwarin gwaiwar,
" A a sai kin faɗa"
"Komai nashi burgeni yake kullum na tashi daga bacci burina kawai inyi tozali da kyakkyawar fuskar shi, idan bangan saba jinake kamar banida lafiya, kuma zan ta tunanin sane daga safe har zuwa dare bacci ɓarawo yayi gaba dani duk acikin tunanin sa, duk ranar da bai zo hospital ba sai inji Kamar nabi sa gida inganshi, koda na 1mint ne hakan kaɗai ya isheni kuzari yinin ranar, ko fushi yake ƙara kyau yake ko mai nasa abun burgewa ne, kowace mace zata yi burin ace ta mallaki DR. Sulaim a matsayin miji, matashin likita, ga ado, ga gayu, ga kyau, ga aji, ga kuɗi, ga nasaba, uwa uba kuma ilimi, ta ƙara kallon Dr. Jabir sannan tace,
Dr. Na San zakamin kallon kamar wadda ta zauce a a, kawai ina son shine,
Don wlh"
_He is so cute👌, he is so beautiful🌹, he is so sweet😘_
Wani irin kallo Dr.jabir yake yiwa Dr.Anisha,
Ya kasa cewa komai,
Murmushi tasakar masa sannan tace DR kennan baza ka gane abunda nake ji a zuciya taba har sai kakamu da soyayya mai zafi💥 sannan zaka ji irin abun da nake ji, yanzu duk wannan kallon da kake yimin nasan kallon bani da hankali ne,
Uhm Dr. Jabir kawai yace sannan ya tashi zuwa fridge yabuɗe ya ɗakko ruwa mai sanyi guda biyu haɗe da wani glass cup da ya ɗakko daga cikin fridge ɗin, ya dawo ajiye wa Dr.Anisha ruwa ɗaya yayi agaban saman table tare da glass cup ɗin yayi sannan yazagaya Yakoma mazaunin sa da ya tashi hannun sa riƙe da ɗayan ruwan, ɓalle bakin gorar ruwan yayi sannan ya kafa a baki bai wani sha dayawa ba ya sauke tare da ɗan dafe kanshi kaɗan,
Yanzu Dr. Duk sanyin da ake agari amma ruwan sanyi zaka ɗakko mana, Anisha wadda tayi maganar hankalin ta na akan wayar ta da ta ɗakko, jin shiru ne bai bata amsaba yasa ta ɗagowa ta kalle shi, Hope dai lafiya? naga kadafe kai,
Lpy" yabata amsa batare da ya ɗago da kan saba,
To nibari na koma office ɗina tafur ta hakan tare da miƙewa ta bar ruwan da ya ɗakko mata anan ta fice abunta,
Bin bayan Dr.Anisha yayi da kallo, sannan a fili ya furta *Ya rabb* Ka kawo min sauƙi cikin zuciya ta, son Anisha yana nema ya tarwatsamin kwakwal wata,
"Zuciyar sa ce ta bashi amsa ta yaya zaka samu sauƙi Tunda ka kasa tunkarar ta kafaɗa mata, har yaushe za ka kai kana ɓoye hakan a Ranka,"
a fili shima yabawa zuciyar tasa amsa, to ai son maso wani nakeyi,
"Sai kafara jarraba sa'ar ka sannan zaka gane a wane mataki zata ɗauke ka,"
To ai aboki na takeso,
"Dameye abokin naka yafi ka, idan kuɗi ne kuma kuna dashi, idan nasaba ce kaima kana da ita, kai ma ai ɗan gayu ne na ajin farko to kawai katun kare ta kafaɗa mata a yau ba sai gobe ba,"
Wani faffa ɗan murmushi Dr.jabir yayi sannan ya duƙule hannun sa ya naushi iska, tare da furta yess yess, muna fitowa daga meeting zan faɗa mata,
______________________
Kan babbar bala'in nan mari kika ce marin ki fa yayi?
Sabrina wadda hawaye suka gama yi mata kwalliya a fuska, cikin shashsheƙar kuka tace wlh mameey mari na yayi a duka kuma tuna, takai ƙar she tare da ƙara fashewa da wani kukan,
Au ashema marin ba ɗaya bane biyu yayi miki, lallai to wlh bazan ɗau wannan cin mutun cin ba, idan bikiyi abunda kike so acikin gidan kuba ina zakije kiyi, to wlh ko ba acikin gidan kuba wani bai isa yamare ki ya zauna lafiya ba, saboda kawai kinje neman wancan mara lafiyar yaron shine, hajiya maryam tana kallo akaci miki mutun ci ko, saboda ɗan nata na gold ne to wlh tagama abunta Tunda kikace shi kike so sai kin aure shi ko ana so ko ba aso, hajiya Turai ce kita faman bala'i matar he excellency Sambo, saboda an taɓa mata shalelen ƴar tata,
Zunbur Sabrina ta tashi daga kan cinyar mameeyn nata tana goge hawayen fuskar ta da tissueee, momeey da gaske zaku aura min yaya sulaim? Kamar ba wadda ke kuka ba tayi tambayar,
Kwarai da aniya sai kin aure shi ko me za ayi, ke dai bari kawai mahaifin ki yadawo ayi komai agama, shikuma saleem wlh bai mari banza ba dole ara ma miki,
Rungume mameey ɗin tayi tare da furta,
_Love you more mameey u are special_
sannan ta tashi ta haura upstairs da gudu kamar ƙaramar yarin ya,
__________________
Saleem ne yake sakko wa da sama rannan nashi ahaɗe babu alamar wasa a tattare dashi kamar ba shine sarkin fara aba a ko da yaushe,
Suhailat dake zaune a perlon ƙasa tana duba wasu ta ƙadda, gefe kuma syrup ne na lemon acikin wani haɗaɗan cup da alama sha takeyi, jin takun mutum ne yasa takai duban ta gurin da take jiyo ƙarar takun,
Sanye yake cikin wani ɗan yan yadi launin milk colour sai tashin ƙamshi yake mai daɗi kamar wanda yayi wanka da ruwan turare, gashi kannan sai ƙalli yake yasha gyara gashi baƙi wulik babu hula akan nashi, sosai yayiwa Suhailat kyau,
Masha Allah ta furta acikin ranta don ita zata iya cewa bai fi sau biyu ta Taɓa ganin saleem da manyan kaya ba shima kuma a biki ne ranar ɗaurin aure, to sai yau
Tayi mamakin ganin ganin ransa ahaɗe kamar wadda bai taɓa dariya ba, lallai sai yau Suhailat ta tabbatar wa kanta yaya saleem soja ne, abaya kafin yanzun ko ce mata a kai ya iya haɗe rai bata yadda ba sai gashi yau tagani da idon ta,
Yaya saleem barka da yamma"
Bai amsa mata ba saida ya samu guri ya zauna saman kujerar dake fuskantar tata sannan yace,
"barka dai" yaciru wayar sa yafara dannawa,
Shiru suhailat tayi itama tamai da hankalin ta kan ta kaddun gabanta, lokaci zuwa lokaci sai ta ɗago ta ɗan saci kallon sa, duk bata jin daɗin ganin yanayin shi ahaka, a zuciyar ta tace ko dai tun abunda ya faru ɗazune tsakanin sa da Sabrina? Ta tambayi kanta sai kuma tace to ai naga ni tayiwa bashiba Meye yasa zai damu? Ta sake tambayar kan ta, zuciyar ta tabata shawarar ta gwada yi masa magana, koda hak'uri ne ta bashi abisa abinda ya faru,
Uhmm yaya saleem,
Ɗagowa yayi ya kalle ta batare da ya amsaba,
Ɗaga mata gira yayi alamar lafiya kuwa? Takira sunan sa tayi shiru?
Dama so nake nabaka hak'uri"
Da mamaki ya sake kallon ta sannan yace hak'uri kuma nameye?
Suhailat tace bisa abun da ya faru ɗazun tsakanin ka da Sabrina, amadadin ta ina baka hak'uri pls,
Murmushi ya sakar mata tare da cewa kin taɓa ganin wanda bashi yayi laifi ba kuma yabada hak'uri? "
Eh mana to nawa ma akayi idan ma ba atabayi ba yau gashi anfara akai na,
Girgiza kai kawai saleem yayi tare da dan ƙara yin murmushin gefan baki,
Itama murmushin tayi saboda taji daɗi ko banza dai ya ɗan saki ransa,
Har ta maida kanta zata cigaba da duba takaddun sai kuma tace, yaya saleem shine akan lefin wata zaka zo kana haɗe ma mutane rai ashe kaima ka iya wannan haɗa ran fiye da na yaya sulaim, tafaɗi hakan cikin sigar zaulaya sai yau na tabbatar da kai ɗin soja ne,
Hhh ƴar dariya yayi kafin yace, laaa laaa ni zakiyi ma sharri ai shi sulaim kwata kwata baya dariya,
Dariya suhailat tayi, to shikenan yaya saleem da Allah kadaina damuwa da irin abunda yafaru ɗazu kaji,
Ƙara haɗe rai yayi don baya son maganar kuma yaci alwashin sai ya hukunta Sabrina sosai,
Lura dabaya son maganar suhailat tayi sai ta ɗan matsa kusa dashi kaɗan sannan tace, _it's oky_ yayana bazan ƙara maganar ba tuba nake hada kama kunne tayi, yadda tayine baƙaramin dariya yabawa saleem ba, amma bai tanka mata ba,
Kuma kaga yadda kayi wani irin kyau kuwa, to baka taɓa yin irin saba, zaro ido yayi yana kallon ta,
Ɗaga masa kai tayi yess baka taɓa ba, _beside ma you are handsome guy🌹👌_
Dariya yayi sosai wadda ta bayyana fararan haƙoran sa sosai, jinsa yayi a wata irin duniya can can sama saboda tsabar daɗin kalaman suhailat,
Itama dariyar tayi ko banza burunta ya cika tasa shi cikin yanayi mai daɗi, ita har ga allah babu komai aran ta da zuciya ɗaya tayi hakan, amma banda goga saleem ai shi ya fasssara abun ta hanyoyi da dama,
_____________________
*Suhaima*
Doctor to yanzu dan Allah yaza muyi wlh ƴar uwa tace ita kaɗai gare ni acikin garin nan banida kowa sai Allah sai ita, suhaima ce ke zaune gaban Wani likita a office tana masa bayani, da kaji muryar ta kasan tana cikin damuwa sosai,
To gaskiya munyi iya bakin ƙoƙarin mu iya abunda za mu iya yi mata kenan, shawara ɗaya zan baki,
To Doctor ina jinka tafaɗa cikin zaƙuwa,
Akwai wani asibiti, asibitin iya masu irin lalurar ta suke dubawa masu matsalar zuciya akwai kwararrun likitoci aciki, to amma private hospital Ne, Don ma mai asibitin yana biyawa mutane 30 kullum komai daza su kashe ko da takai millions naira ne ko sama da haka, to saidai ku tafi can idan Allah yasa kuna da rabo sai su karɓi yar uwar taki su duba ta, cikin yaddar Allah zata farfaɗo, amma mu nan kinga ba muda wasu wada tattun kayan aiki ga ba likitoci sosai, tun jiya muke kanta amma har yanzu babu wani cigaba,
Shikenan doctor katura mu can ɗin nagode,
Biro yaciro daga gaban aljihun rigar sa, ya ɗanyi rubuce rubuce akan wata takadda sannan yamiƙa mata, tare da faɗin asibitin akwai tsaro sosai idan kina buƙatar shiga dole sai kin buɗe fuskar ki Tunda munan munyi munyi kinƙi buɗewa, da address da komai yana cikin ta kaddar,
Suhaima wadda jinsa kawai take burin ta sutafi inda za a duba lafiyar kaltum ɗin wadda Tunda tafaɗi jiya har yanzun bata farfaɗo ba,
Shikenan zan buɗe idan munje can ɗin yanzu yanzu dai bari intaro mai napep,
To babu wanda zaku tafi tare dashi, ne
Eh babu tafaɗi hakan tare da ficewa da office ɗin aranta tanajin haushin tambayoyin likitan, a zuciyar ta tace wlh ba don ina sauri ba danayi maganin ka mtss tana tafi ita kaɗai tana zancan zuci bata kai bakin gate ɗin asibitin ba taga wani me napep ya ajiye wasu,
Sai ta tsaida shi,
Ina zakije? Me napep ɗin ya tambaye ta,
Asibiti ta bashi amsa
Wane asibitin saboda ai nan ma asibiti ne
Ya salam ta furta tare da kai duabanta kan takar dar da wannan likitan yabata, don ganin sunan asibitin da address ɗin,
*ARAB CARDIOLOGIST HOSPITAL*
Tagani rubuce Arab saida ta mai maita hakan sau 3 sannan ta kauda tunanin daga ranta amma tabbas kamar tasan wannan inkiyar awani guri ganin zata batawa kanta lokaci yasa ta cewa,
Rubaɗo road Arab cardiologist hospital za kakai mu, bari aɗaukko mara lafiyar, ka ƙara so bakin Emergency room ɗin can za afito da ita...!
*Beside on creative life story*👌
_Oum Ameerah_😍
*More like more comment* 🙏
https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V
*AHALIN MU DAYA*
*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍
*NAZARI WRITER'S ASSOCIATION*📚
_Sarauniyar👸Nazari writer's association_
*Page* 2️⃣1️⃣▶️2️⃣2️⃣📖
*RUBAƊO ROAD ARAB CARDIOLOGIST HOSPITAL*
Can zaka kaimu, bari a ɗakko mara lafiyar, ka ƙara so bakin emergency room ɗin can, za a fito da ita,
Suhaima ta shiga gaba, me napep na biye da ita, aranshi yana mamaki irin na saurin wannan baiwar Allah,
Dai dai ƙarasuwar su ana fitowa da khaltum a irin gadon marasa lafiyan nan mai tayoyi, wasu nurses ne guda biyu suka turo gadon, shikuma likitan yana bayan su biye dasu, ahaka suka temaka wa Suhaima akasa sa khaltum aciki, saida Suhaiman ta fara shiga sannan suka kamo khaltum ɗin wadda idanuwan ta arufe baza ka taɓa cewa tana numfashi ba indai ba hannun ka ɗora asaitin zuciyar taba,
Suka kwantar da rabin jikin ta kanta asaman cinyar Suhaima jikin ta akan site ɗin napep ɗin ƙafa fuwan ta kuma sun sauka ƙasa,
Fatan samun lafiya suka yi ga khaltum ɗin tare da tausaya wa Suhaima ganin ita ka ɗai tun jiya take ta faman abu ɗaya ko bacci batayiba haka ta kwana akan khaltum ɗin tare da addu'ar Allah yabata lafiya,
Suhaima tace wa me napep ɗin muje ko, tuni suka fita daga cikin asibitin suka ɗauki hanyar asibitin da zasu je,
Koma wa likitan yayi ciki yana mamakin hali irin na wannan yarinyar gata ba wani shekaru ba amma tana komai nata cikin nutsuwa da taka tsantsan, sannan ko ta ɗan leƙo da kanta tace musu ta gode a a batayi hakan ba, sai kuma wani sashin na zuciyar sa yabashi amsa, ai wataƙila ta shiga tashin hankali ne shiyasa, shidai da wannan tunani ya ko office ɗin sa,
Tsaya wa me napep ɗin yayi,
Suhaima wadda hankalin ta nakan khaltum tana tayi mata addu'a, bata masan sun tsaya ba,
har saida mai napep ɗin yayi magana munƙa rasu fa, ashe har cikin haɗaddan hospital ɗin ya shiga dasu duk bata saniba, yayi parking a harabar asibitin ganin wasu manya manyan motoci a parking space ɗin shiyasa ya tsaya anan Tunda ba daɗewa zai yiba,
To kwai tace sannan tasa hannu ta ciro kuɗi acikin aljihun doguwar rigar atamfar dake jikin ta ta miƙa masa, sannan ta fita tafara ƙoƙarin kamo khaltum ta goya ta,
Chanji yamiƙa mata sannan yace ko ate maka miki ne,
Karbar chanjin tayi tare da cewa a a nagode,
Sai dai ya tabbatar