Showing 33001 words to 36000 words out of 61789 words
Chapter 12 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel
yayi mamakin jin labarin shi wannan HATIMIN,
Imran yana da son yara sosai komai ya samu ko mahaifin sa yabashi sai yaje yaraba wa ƴan ƙananan yaran dake kusa da su wato maƙotan su, saboda babu yaro ko ɗaya a gidan su sai shi ƙadai yanaso yaga shima ace yau yana da ƙani ko ƙanwa,
Haka rayuwa ta cigaba da tafi kwatsam, Mahaifiyar Imran, wato sa'ada ta samu juna biyu, murna agurin mln Muhd kamar wanda bai taɓa haihuwa ba, shi ko Imran Ai gani yake ko mahaifin nasa baikai shi murna da farin ciki ba, Imran fa ya koma zama a gida ko nan da can baya son zuwa, yana tare da Mahaifiyar sa wadda yake kira da ummee sa'ada duk abunda take buƙata da rawar jiki zai tashi yayi mata idan na ɗakko wa ne ya ɗakko mata baya so wai ta tashi tasha wahala kada ƙannan sa suyi kuka ace warsa,
Kwana ke suna shuɗe wa, watanni na wucewa shekara naƙara towa, acikin wata na tara da samun juna biyun sa'ada, Allah ya sauke ta lafiya tare da azurtasu da ƴara mata biyu wato tagwaye ta haifa duk mata, farin ciki da murna ba a magana wajan ɗa da mahaifin, gata kuwa sa'ada ta ganshi a gurin uban da ɗan, washe garin haihuwa ɗaya ta koma, ya rage saura Yarin ya guda ɗaya,
Imran yayi kuka kamar zai shiɗe, ƙan war shi ɗaya ta rasu, daƙar aka samu yadaina kukan, amma kullum yana rungume da ɗayar jaririyar wadda aka raɗawa suna BAHIJJAH,
Ahaka suka cigaba da rayuwa cikin so da kaunar junan su, imran nason ƙanwar nan tashi sosai baya son koda jin kukan ta, komai ya samu na tane duk kuwa son da yake yima wannan abun,
Mln Muhd kuma arziƙi a cigaba da bunƙasa Allah yasa mai albarka sosai acikin neman nasa, har yafara, tafiye tafiye donmin cin kasuwannen wasu garuruwan dake makwaftaka dasu, hadda ma ƙasashen kusa dasu irin su MALI yankin Niger, babu inda baya shiga don harkar sa ta kewo da kayan hatsi, a lokacin imran ya tasa sosai don har yafara bin mahaifin nasa saboda girma na ta cimma Mln Muhd ɗin, a wani lokaci ne Mln Muhd ya ɗakko wannan HATIMIN ya danƙawa imran tare da bashi sharaɗi akansa, tare da faɗamasa cewa ya kula dashi sosai saboda, wannan HATIMIN yana rarraba kan al umma, sannan yana kawo gaba a tsakanin masoya da ƴan uwa, ka ajiye shi kamar yadda nima na ajiye shi, har sanda Allah zai sa lokacin gushe warsa yayi, don tabbas zai gushi, ya tashi kamar Bai taɓa wanzuwa a bayan ƙasa ba, da haka Mln Muhd ya danƙawa ɗan sa imran HATIMIN mallaka a hannun sa, da bashi labarin irin rigimar da aka sha akansa da kuma yaƙin da akayi saboda asalin sa daga wata masarauta yake,!!!
Sannu ahankali, imran ya fahimci komai akan harkokin mahaifin nasa,
Alokacin Mln Muhd yafara baro imran a idan suka yi tafiya a wani gari wanda akecin kasuwa a sati sau 4 mai sunan *BAITURRUMAN* asalin garin rumawa ne suka kafa shi don anan suke yada zango daga garuruwan su na Larabawa, har Allah ya sawa garin albarka mutane iri iri naziyar tarshi domin saye da siyarwa,
Shima Mln Muhd Allah yasa ya mallaki rumfa acikin wannan kasuwa ta garin BAITURRUMAN, sai ya kasance imran ne yafi zama acikin wannan kasuwa akan mahaifin nasa, shiya kan je ya dawo saboda iyali,
Bayan wani lokaci shiru shiru Mln Muhd, bai zo wannan gari da suke kasuwanci ba, tun imran nasaka ran ganin shi yau ganin shi gobe amma shiru, sai yafara tunanin gaskiya gida, zaije aga ko lafiya mahaifin nasa bai taɓa ɗaukar irin wannan dogon lokacin baizoba,
Take imran ya shiga yiwa BAHIJJAH ƙanwar sa siyayyar kaya na sawa kala kala saboda yarinyar masha Allah, komai ya gani Indai zai yi dai dai da ita sai ya ɗauka, hada kayan wasa sosai yayi mata siyayya sannan yayi wa mahaifiyar tasu itama,
Saida ya haɗa komai tsaf sannan ya ɗauki hanyar garin su wanda zai ɗauke shi tsawon kwana 3 kafin yaje cikin murna da zumuɗin ganin BAHIJJAH da ummee sa'ada yake tafiyar, yana tunkarar garin nasu yana ƙara jin bugun zuciyar sa na ƙaruwa, fargaba yake ji, sai ya koma ambaton Allah tuni yaji abun na raguwa,
WAni irin duhu ne ya mamaye idanuwan imran yayin da ya shiga cikin wani ƙauye wanda daga shi sai ƙauyansu, na DARUTTURAB, Tashin hankalin wanda ba'a sami shi date,
Kasa gasgata abunda idanuwan sa suke gano masa yayi, gani yake kawai idanuwan sa ne suke yi masa gizo, ba gaskiya bane, dake idan mutum ya sauka a mota saida ya shiga cikin ƙauyen a saman doki ko raƙumi ko jaki,
Kafin imran yace komai, mai raƙumin yace bawan Allah amma kai baƙoni anan ko?
A a garin mune, imran ɗin yabashi amsa,
Gaskiya to kaɗan jima bakazo ba ai ni iya kaci na nan saboda yanzu daga nan ba'a wuce ko ina saboda babu kowa acikin ƙauyan DARUTTURAB,
Cikin kaɗuwa dajin batun wannan bawan Allah, imran yace to ina mutanan garin,?
Kai baka ganine ai ba tashin su akayiba, faɗa ƙabilanci ne akayi shine aka ƙone garin, wasu sun mutu wasu kuma da dama sun gudu, daga nan ɗin wasu kuma antafi dasu,
Imran bai tsaya ya gama jin wannan, magan ganun mutumin ba masu kama da saukar aradu a kunnuwan sa, sai jiyowa mutumin yayi yaga babu imran ɗin sannan yabar masa wasu kaya asaman raƙumin, cike da tausayin imran ɗin mutumin yajuya da raƙumin sa Yakoma inda suke ɗaukko mutane, sannan yayi alƙawarin ajiye wa imran ɗin kayansa da ya bari har sanda zai nemeshi ya karɓa,
Imran bawan Allah cikin ƙyauyan DARUTTURAB yanufa bayaji baya gani don har a lokacin gani yake gizo akeyimishi, ko inda yake saka ƙafarsa ma bai sani ba,
Tsayawa yayi cak don ƙara tabbatar da abunda yake gani ɗin a zahiri ne tabbas wannan ba mafarki bane, gaba ɗaya ƙauyan yayi baƙiƙƙirin ga hayaƙi yana tashi, ko ina toka baka iya gane komai saboda babu komai ɗin sai bakin hayaƙi da ƙauri, da baƙin tashin hankalin da imran ɗin ke gani acikin ida nuwan sa,
Baiga kowa ba bare ya tambayi wani abu, ya kasa koda motsawa kuka yaƙi zuwa sai tsananin tashin hankalin da yake ciki, yanzu shi koda cewa akai ya gano inda gidan su yake ai saidai akashe shi, jiya ke ina ma shima ace ya mutu agurin nan, saboda bai san inda zai saka rayuwar saba, babu wanda ya sani shi iyayensa kaɗai yasani bai san kowa ba sai dangin Mahaifiyar sa, wanda a yanzu bai san inda zai same su ba,
Ina kuka shiga kada ku tafi kubarni zuciyar sa tafara rawa take wani azababban kuka yazo masa, aiko babu ɓata lokaci yafara rairai abunsa, zama yayi dirshan ƙasa cikin toka yana wannan kukan, wanda babu mai rarrashi, jiyayi duniyar sa tayi duhu tayi masa nauyi, Alokacin yafara tunanin she kenan bashida kowa a rayuwar sa, babu bahijjan sa babu ummee sa'ada, babu abokin sa wato mahaifin sa, ina kuka shige? Ya tambaye kansa,
Cikin rashin makama da abun yi, imran ya tashi da nufin zai zauna a wancan ƙauyen ko Allah zai sa aji labarin su, dan shi gani yake sunanan kuma zasu dawo gareshi, kwata kwata bai kawo musu mutuwa ba,
Tausayin kansa ne ya kama shi, tabbas imran yasan ana faɗan ƙabilanci a yankin su amma rabon da yaga anyi tun yana ƙara min yaro, kuma ba ayi wani tashin hankali ba sosai, amma gashi wannan antashi gari ma gaba ɗaya,
Bayan sati biyu 2, da imran yayi a wannan ƙauyan na kusa, kullum sai yaje nasu ƙauyan wai kozai gansu sundawo amma kullum jiya iyau harta kaima ya daina ganin koda hayaƙin dake tashine, saidai toka,haka yi waɗan nan kwanaki hatta abinci baya iya ci daya fara sai yafara tunanin, duk inda iyayan sa suke aisuma basu ciba, sai kuka ya kwace masa, da haka har ya tashi yabar abincin iya ruwa kawai yake iya sha shima ruwan kansa ɗacin sa yake ji,
Abu kamar wasa aka kwashe wata ɗaya babu labarin komai, imran yayi rashin lafiya kashi kashi a wannan ɗan tsakanin, dama zaune yake gidan wani tsoho shi kaɗai ne a gidan sa sai imran ɗin, shima ganin imran ɗin yayi kwance ƙasan wata bishiya babu koda shimfiɗa, shine yace yazo gidan sa yazauna har sanda zai tafi, tsohon ne ma ya ƙara yi masa bayanin duk abunda ya faru, hatta ashe har Mln Muhd mahaifin imran tsohon yasani,
Baƙaramin tausaya wa imran yayi ba, kullum cikin yi masa nasiha da kuma ya rungumi ƙaddarar da tazo masa Allah yana sane dashi,
Da haka yake samu hankalin imran ɗin ya ɗan kwanta, amma yananan ya kukan zuci, a duk lokacin da yaje sai yaga wasu suma sunzo duba ƴan uwansu suna kuka, to koda bai yi niyar yin kukan ba sai yayi,
Sosai tsohon nan yayi wa imran nasiha kan ya koma inda mahaifin sa yabar masa kasuwancin sa don kafa kansa da abunda zai dogara dashi a rayuwar sa idan da rai da rabo watarana zai gana da iyayensa idan har suna araye, dawannan nasiha ne, imran ya koma garin, *BAITURRUMAN* cike da maraici da kaɗai ce, don cigaba da harkokin mahaifin sa, ya dangana ya maida komai zuwa ga Allah, sannan duk sanda yayi salla sai yayi masu addu'a sannan ya kan yawan yin sadaka, Allah ya bayyana mai su idan kuma sun mutu Allah ya jiƙan su, duk sanda zuciyar sa ta raya masa cewa sun mutu to sai yayi hawaye,
Bayan lokaci mai tsaye imran harkokin sun bunƙasa komai ya ƙara zama yadda ake so ya dawo cikin hayyacinsa, yana shiga yankin ƙasar Niger sosai da kayansa, a lokacin ma yayi auren sana fari ya auri wata buzuwa acikin garin *AGADAS* mai suna Amina amma suna kiranta da SHAWAI,
Sun zauna acikin babban birnin *Niger republic* *YAMAI* yana zaune da matarsa SHAWAI cikin kwanciyar hankali, Alokacin har NIGERIA ya kan shiga domin kasuwanci ya siyar ya saro, sannan ya kan ziyarar ci ƙauyan su lokaci zuwa lokaci amma dai kullum labarin guda ɗaya ne, bubu canji amma bai taɓajin ya sare ba, matar sa kullum cikin ƙara kwantar masa da hankali take, a wannan lokacinne Allah yabasu ɗa namiji wanda yaci suna Hameed,
Imran yaji daɗi sosai shima yafara tara iyali, sannan yana da burin Allah yabashi ikon tara babban ahali guda...!!!
*Share nd comment, more like fisabilillah🙏😢*
https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V
WhatsApp channel
*AHALIN MU DAYA*
*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍
*NAZARI WRITER'S ASSOCIATION*📚
_Sarauniyar👸Nazari writer's association_
______Dedicated to aunty salma💎
*Page* 3⃣ 3⃣↔️3️⃣4⃣📖
Imran yaji Dadi sosai Shima yafara Tara iyali, sannan Yana da burin allah yabashi iKon Tara babban ahali guda,
Babu laifi yadan samu kwanciyar hankali alokacin, Imran yakan shiga Nigeria sosai saboda harkokin nasa sun rabu biyu rabi Niger rabi Nigeria,yakan Yi kwanaki baya nan, ahaka suka fara fidda kayan su qananun masa na'antu, (Company's) shida wani abokin kasuwan cin sa Mai suna alhaji Idris, alhaji Idris dan kasar Nigeria ne, saboda haka Imran bashida wata matsala idan yaje kasar,
Wani zuwa da Imran yayi Nigeria ne abokin sa alhaji Idris yake cemasa, alhaji Imran Arab, kadai qi qara aure ko?
Sunan da mutane suke Kiran Imran dashi kenan,wasu ma iya Arab din kawai suke ce masa, saboda Koda ba'a fada Maka ba dakagansa kaga jinin larabawa,
"
alhaji Idris ne yaci gaba dacewa,Yanzu da ace kana da iyali anan qasar aikaga daka huta dakama hotel din Nan dakakeyi tunda kace baza ka iya sauka a gida na ba, kaga kenan idan kazo nan kana da iyali sannan idan ka komai can ma haka,
Murmushi kawai Imran Arab yayi batare dayace komai ba Amma Kuma tabbas Shima ya dade Yana wannan tunanin acikin Aransa, Kuma sannan kobanza burin sa natara iyalai dayawa zai cika idan har allah yakawo rabo,
Take mahaifin da yafado masa a Rai, cikin zuciyar sa yafara tunanin da ace mahaifin da ya Tara mata da yawa ai Shima yanzu dabai rasa Dan uwa ba, take yabawa kansa amsa ta hanyar cewa aikomai na Allah ne sannan ya qaddara komai,
Da wannan tunani yakoma gida *Niger republic*
Baiyi Wani tunanin ya sanar wa matar sa Amina maganar auran da yakeso zaiqara saboda baya boye mata komai Koda kuwa Hakan bazai Yi mata Dadi ba,
Taji Babu Dadi sosai Amma sai ta shanye a lokacin Dan su hameed Bai wuce shekara 2 ba,
Cikin qanqanin lokaci alhaji Imran Arab yafara shirin aure da wata Wadda suka hado, a Wani gidan cin Abinci *restaurant* a jahar katsina, Mai suna bilkisu, yarinyar Mai gidan abincin ce dama ta dade tana nuna masa tana sonshi a duk lokacin da suka zo Amma Bai taba Bata dama ba,
Wannan batu baqaramin Dadi yayiwa bilki da mahaifiyar taba, bayan an daura auran sa da bilki,
Sai ya ajiye ta a Wani gidan sa da ya dade da siya a Nasarawa, cikin garin Kano,
Bilki maca ce Mai son zuciya, son abun duniya, zata iya yin komai saboda ta samu abunda takeso,
Akusan lokaci ɗaya bilki da Amina suka haihu, wanda duk suka haifi ƴaƴa maza, bilki haihuwa fari wanda ɗan yaci suna Hasheem,
Itakuma Amina haihu ta biyu ne tayi wanda aka sawa ɗan suna Bello,
Ahaka alhaji imran Arab ya cigaba da gudanar da harkokin sa cikin tarin nasarori da cigaba, iyali suka cigaba da haɗuwa da ta kowane ɓangare daga matan nasa, baya wani samun tashin hankali daga gare su saboda ko wacce ƙasar da take zaune daban,
Ko wacce cikin su ya kai ta *UMRA* da aikin *HAJJI* hada ƴaƴan sa a lokacin kasuwancin sa har ƙasa shan waje sosai yake fitar dasu, komai tare yake yi da babban ɗan sa hameed
tun hameed ɗin baya so amma ya hakura saboda shi yafison aikin gomnati akan kasuwanci sam baya burgeshi,
Amma da haka har ya hakura ba yadda ya iya,
A lokacin ne alhaji hameed ARAB yafara tunanin haɗe iyalinsa guri ɗaya, yafara tunanin a wace ƙasa zai zauna tsakanin NIGERIA da NIGER,
Duba da yanayin komai nasa yafi ƙarfi a Nigeria hakan yasa shi zarɓar haɗe su acan ɗin, take aka fara dan ƙara ginin babban ESTATE unguwa guda saboda alhaji imran yana da burin hatta jikokin sa idan suka tashi aure anan zasu zauna,
Yaɗora babban ɗan nasa hameed akan ginin estate ɗin da akeyi, komai daza abuƙata na ginin daga ƙasar waje aka kawo sa,
Ko engineer ɗin daya zana ginin ba a ƙasar nan yake ba shima kansa saida abun yabirgeshi saboda Tunda yake zane bai taɓa mai girman wannan ba kuma yabirgeshi haka ba,
Ya jinjinawa alhaji imran sosai saboda komai bada naira aka biya ba anci kuɗi sannan kuma an ɗan ɗauki lokaci anayi, hameed ne ki tsaye kan komai duk da yana fama da school matakin Masters,
Lokacin da Alhaji imran yajewa da uwar gidan sa wadda suke kira da Hajiya umma, batun koma warsu NIGERIA gaba ɗaya ƙin yadda tayi saboda tana ganin ga dan ginta da ƴan uwan ta zata tafi tabar su, daƙar dai alhaji imran ya samu ya shawo kanta ta amince badan tana soba,
Tunda hasheem yazo ganin ginin estate ɗin da mahaifin nasu keyi, yaga komai ɗan uwansa hameed ne akayi, yaje yabawa mahaifiyar su labari wadda suke kira da mama bilki shikenan hankalin ta yaƙara tashi ainun,
Ta ƙara ɗaura ɗamara gurin bin bokayen ta kala kala, duk wata hanyar banza ta sani ita ke ɗora ƴaƴan ta a kai bama kamar babban ɗan nata wanda take ganin alhaji imran ɗin baya saka shi cikin kasuwancin sa,
shikuma yana ƙin ɗora shine saboda yafison yaga ya nutsu sannan, saboda hasheem irin mutanan nan ne masu san sharholiya da son duniya, ga shaye shaye ga son zuwa club kullum shine zuwa mashaya (BAR),
Shiyasa alhaji imran baya saka shi acikin komai nashi saboda yafa himci bashi da nutsuwa,
Duk tunanin mama bilkisu Yakoma kan duk yadda zatai zata yi saboda kada Hajiya umma ta dawo cikin estate ɗin da zasu koma, tafi son yazama daga ita sai ƴaƴan ta,
Tabi boka ye kala kala suna bata asiri saboda duk dan kada su haɗe a guri ɗaya amma ina, duk sanda zata yi abun babu nasara,
Naƙar she ne ta samu a wajan wani bokan ta mai suna ZARSHIMA yabata wani ruwan magani yace ta tabbata ta dafa wa alhaji imran abinci dashi wannan ruwan, a ranar da zai koma ƙasar Niger, Idan har ya haɗu da matar sa Hajiya umma a wannan ranar to ko ƙasar Nigeria bazai taɓa barin ta tazo ba bare ma su zauna guri ɗaya,
Haka kuwa akayi ranar da ta tabbatar zai tafi da wuri ta tashi ta shiga kichin da kanta don yi masa breakfast dakan ta saboda tasamu ta sarrafa shi da wannan ruwan da boka ZARSHIMA ya bata,
Aiko cikin sa'a alhaji imran yaci abincin sosai sannan yayi mata sallama da niyar ya tafi, baƙaramin daɗi ne ya rufe mama bilki ba don tasan komai ya tafi yadda ta tsara kuma takeso,
Alhaji imran da yanu airport domin komai a tsare yake jirgin safe zai hau zuwa *Niger republic*
Akan hanyar sa ne abokin sa alhaji idris yakirashi kan duk abunda yake yazo zasu yi zaman gaggawa yau ɗin nan a garin Katsina,
Alhaji imran ya faɗa masa Niger yanufa amma Tunda a Katsina nane bari