Showing 45001 words to 48000 words out of 61789 words

Chapter 16 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel

Fauzah   

04 Nov 2025

169

su ga wani brown shoe sai kalli yake kyakkyawar ƙafar sa sai taƙara yin kyau aciki wani irin ƙamshine ke tashi a jikin sa wanda mutum idan ya shaƙa bazai so ya dainaji ba kuma duk inda ya zauna sai yabar ƙamshin nasa haɗaɗɗan agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannun sa ya duba 5:11pm"

"sosai ummeetha tayi masa addu'a tare da fatan sauka lafiya ita kaɗai ce a parlon babu kowa duk sun tafi gidan bikin ƴar gidan uncle tahir yayan mommy"

"Hakan yasa sulaim jin dadi sosai babu mai tsaida shi "

"kai tsaye suka nufi Airport dama saida yafara yiwa baffa bankwana shima yayi masa addu'a sosai kafin ya nufi Part din nasu"

🌹🌹🌹

*BARNO STATE*

*MASARAUTAR GABAS*

Masarauta ce mai tsohon tarihi da ƙarfin mulki arziƙi da kuma tsantsar izzah,

" cike da ƙasai ta matashin saurayin ke tafiya cikin aji da nutsuwa mulki ya gama ratsa ko ina nasa ga wasu fadawa guda 4 abayan sa suna take masa baya"

" wani katafaran perlon alfarma ya nufa dai dai ƙofar shiga fadawan nan suka tsaya cak suka ƙame tare da fadin Ranka ya dade a fito lafiya"

"Saboda sun sani babu wanda ke shiga wannan parlon sai wanda yakasan ce najikin Yarima sultan ko kuma shakikin abokin sa wato Sulaim wanda duk ya kwana ya tashi a cikin masarautar gabas asan waye Sulaim a gurin Yarima Sultan"

"cike da izzah ya ƙarasa shiga perlon cike ganin sa yasa Sulaim ɗan tashi daga kishin gedan da yake tamkar shine yariman"

"hannu Yarima Sultan yabode wa aminin nasa ba musu sulaim ya Mike suka rungume juna"

"barka da zuwa daular Sultan ya fada asaitin kunnan sulaim "

"barka dai mutanan Koria"

"fatan ka iso lafiya?" sultan din ya tambayi sulaim"

"lafiya fatan kaima haka"

"Zama suka yi atare kan wata kujerar alfarma tamkar gadon sarauta haka kujerar take"

"cikin muryar sa mai daɗin sauraro yafara magana"

"nayi kewar ka sosai amini na cewar yarima sultan yana kallon sulaim"

"abunda bantaba ganiba shi sulaim yayi wato murmushi shima bawai can ba"

"kafin yace ba kayi kewa taba da kayi ke wata da ka dawo Nigeria ko sau daya baka ziyar ce niba amma ni zuwa na Koria uku 3 ganin ka"

"ayya yanzu dai ba lokacin ƙorafi bane kasamu ka huta sosai kaci abinci sai muje kai gaida *UMMUL BAIT* na nufin uwar gida wato mahaifiyar Yarima sultan itace suke kira da UMMUL BAIT.!!!

*SHARE AND LIKE FISABILILLAH*

*AHALIN MU DAYA*

💗💗💗

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp channel

*CREATED AND WRITTEN*

*BY*

*Fatima Y zakariyya*

_😍Oum Ameerah_😍

______Dedicated to aunty salma💎

*Page* 4️⃣1️⃣↔️4️⃣2️⃣📖

"Ayya yanzu dai ba lokacin ƙorafi bane kasamu ka huta sosai kaci abinci sai muje sai muje ka gaida *UMMUL BAIT*

" Ɗan ɗaga kai Sulaim yayi batare da yayi magana ba"

"miƙewa yarima Sultan yayi tare da Sulaim sukanufi wata hanya acikin parlourn kamar corridor sai gashi yaqara fita wani babban parlourn mai dauke da 4 bedroom sai kuma upstairs,

Room din farko Sulaim ya shiga yayi wanka yana fitowa ya ga kaya gefan saman make kyan bed ɗin baiyi mamaki ba saboda yasan Sultan ne yasa aka kawo su saboda idan yazo harya koma kaya iri daya suke sawa saidai wani lokacin kawai kala ce zata ban banta shima ba ko yaushe ba,

Cikin ƙanƙanin lokaci ya shirya cikin kayan da Yarima Sulaim ya aiko dasu don jin daɗin sa,

Wani ɗanyan yadi ne launin ruwan madara mai turuwa wanda ake kira da butter milk bashida nauyi rigar taɗan haura gwaiwa kadan mai gajeran hannu iya gwaiwa yayi kyau sosai,

Sanda yafito a parlourn ya tadda Yarima Sultan shima cikin shigar sa sak irin ta Sulaim komai da komai ban bancin daya ne Yarima Sultan yaɗora alkyabba bisan kayan nashi,

Barka da fitowa Amini na cewar Sultan,

Allah yasa Yarima baiyi Fushi ba Sulaim ya faɗa cikin sigar wasa,

Murmushi Sultan yayi kafin yace hukunci ya tabbata akan wanda ya ɓatawa Sultan rai,

Shima murmushin Sulaim yayi batare da yace komai ba,

Naga lokacin sallah ya gabato mu fara muje masallaci bayan mun gabatar da salla sai munufi *FADA* gurin mai martaba,

Sulaim yace hakan yayi

Kallon Sulaim yayi kafin yace Wato kana nan da halinka wai Meyasa baka son alkyabba ne? naga acikin kayan da na aiko maka hadda ita,

Zata dame ni ne abunda sulaim yace kenan

Murmushi Sultan yasakyayi akaro na biyu idan kaine a matsayi na yazakayi kenan?

Sulaim yace Yadda nayi yanzu,

Batare da Yarima Sultan ya ƙara cewa komai ba haka ya tashi suka fita,

Baƙaramin kyau suka yi ba tamkar ƴan biyu sai haske suke tamkar wata daran goma sha biyu,

*YARIMA SULTAN* kyakkyan wane ajin farko ga kyau ga mulki ga izza ga kwarjini ga ilimi dukiya kwa ba a magana ɗan gayu yana da miskilan ci amma bai kai Sulaim ba gashi fari ne tas amma farin nasa irin jannan ne launin mutanan Koria dogon hancin sa har wani dan lankwasawa yayi ga dara daran ido farare tasss kwayar ciki kuma baƙa siɗik tana yawo saman farin idon da har wani farin ruwa ne aciki tamkar yawaye amma ba hawaye bane halittar sa ce ahaka, lips din da red colour tamkar yasamusu Kala,

Yana da bayyanan nan kyau ga tsayi kamar Sulaim komai nashi mai jan hankali ne,

Bayan sun fito daga babban masallacin cikin masarautar Yarima Sultan ya samu labari mai martaba sarki yayi baƙi,

Sai suka fasa zuwa fadar suka wuce Layin UMMUL BAIT Sufara gaisa wa da ita suka barshi zuwa gobe sai gana da mai martaba,

Zaune take tana fuskan tar qofar shigowa parlourn qafafuwan ta saman kushin gaban ta Wani babban tire ne na kayan marmari nau'i kala kala kama daga kan, tuffa, zaitun, ayaba, lemo, inibi, da dai sauran su,

Ta Dora alkyabba saman Wani hadaddan lace Wanda Bai sai antsaya gaya Maka kudin saba, wuyan ta da hannun ta sun Sha kayan a do na zinare sai kalli suke,

Matar fara ce sosai da kaganta zaka iya cewa balarabiya ce ko Kuma help CAS gata doguwa duk da a zaune take Amma yanayin ta yanuna Hakan Daka ganta kasan Ita ta haifi Yarima Sultan duk da shi farin sa irin na mutanan yankin qasar koria ne, ta Dan manyan ta Amma dayake akwai hutu baza kataba gane Hakan ba bugu da qari yar gayu ce sosai don ta Dan girmi ummeethar mahaifiyar Sulaim,

Wasu kuyangu ne guda hudu a gefe da gefan ta suna zaune daga qasa,

Ga wasu kuyangin suna ta aiki acikin parlourn wasu na goge goge wasu na aikin turaren wuta suna ta Kai kawo,

Jin sallama ne yasa ta dago ta kalli kofa ganin Yarima Sultan tare da Sulaim yasa ta fadada murmushin ta tare da amsa sallamar tasu cikin sautin da ba aji sosai,

Tunkafin su qara so ciki gaba daya bayin suka tashi suka hau zubewa suna kwasar gaisuwa wajen Yarima Sultan da Sulaim haka sukai tayi duk Wadda ta gaishe su saita bar parlourn saboda Indai Yarima ya shigo to Babu Mai zama aciki sai Wanda aka nawa Umarni,

Ga kujeru kala kala ga kushin ga wasu kujerun Suma kamar gadaje duk a parlourn Amma suka zauna a San carpet dai dai qafafuwan ta duk da Shima carpet din saboda laushi tamkar audiga,

Parlourn yayi kyau sosai idan kagani dole zai burgeka duka kwalliyar sarauta akayi masa sai wasu manya manyan hotuna guda biyu maqale a jikin babban bangon parlourn daya na Yarima Sultan ne yayi kyau sosai cikin shigar sarakai shikuma dayan hoton na wata kyakkyawar jaririya ce Wanda dagani jaririyar batafi wata daya ba akayi mata hoton,

Ko wace ce oho!

Haka suka zauna Sulaim bangaran daman ta shikuma Yarima Sultan bangaran hagu,

Barka da dare UMMUL BAIT Allah yasa Kuna cikin ameenci, Sulaim ne yafadi Hakan kanshi aqasa,

Ameen barka dazuwa *DAULAR SULTAN* Dana Sulaim Allah yasa kana lafiya, tafada cikin kulawa,

Sulaim ya amsa da Lafiya alhamdulillah

Ta tambaye shi su ummeethar yace suna Lafiya Suma suna hanya zuwa gobe da yaddar Allah,

Barka da hutawa fatan mun sameku cikin ameenci, cewar Yarima Sultan Wanda tunda suka shigo sai yanzu yayi magana,

Kallon Inda yake UMMUL BAIT tayi tare da fadin alhamdulillah fatan Dana Sulaim yasamu kyakkyawar tarba daga Sultan,

Dan murmushin Yarima Sultan yayi kafin yace Anyi duk abunda yadace,

Dakyau tafada ataqaice,

Dakaga yadda suke magana kasan mulki yagama zama a wannan gurin suna yin komai cikin girmamawa ga riqo da al'adun su kala kala,

Tashi sukayi kusan atare suka Dan russuna kafin Sultan yace,

MUN barku Lafiya Shima abunda Sulaim yace kenan,

Daga Kai kawai tayi sukuma suka fita

Murmushi UMMUL BAIT tayi harcikin ranta takeson Sulaim sosai jitake tamkar Ita ta haifeshi tana so taga yazo Hakan baqaramin Dadi yakeyi mata ba,

Suna tafe suna Dan hira jefi jefi sai wasu fadawan Yarima Sultan din guda uku 3 da suke take musu baya, kowa ba gwanin magana bane acikin su shi Sultan hadda mulki shikuma Sulaim haka take dama,

Gidan BABA WAZIRI suka nufa kakan Sulaim mahaifin ummeethar kenan Wanda gidan sa Akwai yar tafiya tsakanin bangaran dasuka baro na UMMUL BAIT

Badann Yarima Sultan yaso ba haka yake tafiyar qasan dama Indai ba Sulaim ne yazoba baya taba zuwa gidan baba WAZIRI aqafa sai dai a mota ki doki saboda Yana son tafiya doki,

danshi baiyason wahala Bai nasan taba shikuma Sulaim Yana son yaga Yana tattaki shiyasa mafi akasarin lokuta yake zuwa house din baffa aqasa daga house din su duk nisan dake tsaka nin su baya Jin komai,

Ko Ina haske gaba daya cikin masarautar tamkar da rana don ko allura ce yafadi zaka iya ganin ta,

GA kuyangi da bayi suna tafaman zirga zirga wasu da kaya a hannun su wasu babu suna tashi ga kowane Layi da bangarorin cikin ma sarautar tamkar da rana kamar kuma ana wani taro ko biki ko kuma daran sallah,

Duk inda Yarima Sultan yazo wucewa sai shida sulaim sai an buɗa musu sannan kuyangin ko bayin sai sun zube sun kwashi gaisuwa,

Ko ta kansu basa bi kawai tafiya suke cin nutsuwa da ƙasaita,

Fadawan dake bayan su ne suke amsawa da cewa Yarima ya amsa ya kuma gaishe ku,

Sulaim ne yace naga taron Meye akeyi ne?

Sultan yace akwai taron murnar dawowa ta masarauta gobe sannan akwai Hawa wanda za ayi ni zan gabatar da guda ɗaya,

Idan muka koma zanyi maka bayanin yadda taron zai kasance,

Kallon ko ina na masarautar Sulaim ya shiga yi tamkar yau yafara ganin ta shidai yana son irin gine ginan masarauta suna bashi sha'awa,

Dogayen gine gine ne irin nada da kuma soraye irin na masarauta saidai an sabunta wannan ginin ai maida komai na zamani amma batare da an rushe wancan na asalin ba ko wane gini yana da zane irin nasa da kwalliyar sa da kuma irin ginin dutsan nan da akeyi, wani irin ƙaton zaki ne na ƙarfe launin zinare a tsakiyar masarautar idan mutum bai taba zuwa ba idan ya gani sai yabashi tsoro ya zanu sosai zakin,

Sosai gwaggo Murja taji daɗin ganin jikan nata wato Sulaim,

Saida suka gaisa sosai sannan tasa aka gabatar musu da abinci kala kala irin na gargajiya,

Kallon su gwaggo murjan tayi sannan tace kudai ga kunan kunzama tuzurai amma babu mai aure acikin ku sai jajayen kunnuwa kamar ƙosai,

Kai Sultan da ina ganin kamar kaine za kayi sai kasa shi ahanya amma naga duk tafiyar Taku ɗaya,

Idan ma kun rasa masu son nakune to ai akwai ƴan mata kala kala ni sai na samo muku,

Murmushi Yarima Sultan yayi saboda dama sun saba sukan ɗan taɓa wasan jika da kaka duk da ba kakar sa bace da ko ganin shi ba tayi amma sanadiyyar Sulaim suka saba,

shi ko Sulaim ɗaure fuska yayi tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa shifa baya son zancan aure kwata kwata idan ma aka fiye yi masa tashi yake fice,

Sultan ne yace to aini nafaɗa miki saidai ki hakura da auran baba waziri ki aure ni don ni idan bakeba to gaskiya saida kisamomin wata kamar ke don ni haryanzu banga matar aure ba kuma bazan iya zama da Yarin yaba,

Dariya sosai gwaggo murja tayi kafin tace to bari kaji nafaɗa maka idan ma aka nemi mata kane ma tun da wuri saboda nida iliyasu waziri mutuwa ce kadai zata rabamu,

Shima dariyar yayi har kyawawan haƙoran sa farare tasss suka bayyana ga wata siririyar wushirya a tsakanin hakuran Yarima Sultan,

To shikenan idan lokaci yayi zamuyi ne nida amini na,

Eemm gwaggo murja tace tare da taɓe baki yo shi wannan aminin naka gashinan wani dunkum dashi kullum rai ahaɗe babu annuri a fuskar sa ba dole ma ya rasa matar aure ba yanzu daga maganar aure ya tashi yawani ƙara haɗe fuska,

Shiru Yarima sultan yayi don shima yakai geji a maganar tasa kuma shi idan zai ji antaɓa masa Sulaim to duk sai yaji babu daɗi,

Shiko Sulaim maganganun nata sunfara hawar masa kai dama shi ba don Sultan din ya matsaba da bazai zo yau sugaisaba sai gobe idan su ummeethar sunzo sai ya shigo

Gani yake gwaggon nada haya niya ga tada takura shiyasa baya marmarin zuwa inda take,

Kafin gwaggo murja ta ƙara furta komai Suka jiyo muryar baba waziri yana shigowa da sallama,

Amsawa suka yi bandan Sulaim ko ya amsa a zuciyar sa Oho,

Marhaban lale da zuwan ku ashe manyan baƙi ne damu yanzu nasamu labarin iso warku baba waziri ne ya furta hakan dai dai yana zama saman kujera,

Barkan ku da zuwa,

Barka dai baba waziri Sultan ne ya amsa,

Barka da warhaka fatan munsameku cikin ameenci cewar sulaim,

Lafiya alhamdulillah ashe mutanan Kano tadabo ne a masarautar tamu to muna maraba dakai,

Hira suka taɓa sama sama rabin hirar madai gwaggo murja ce da mijin nata sai kuma Yarima sultan shima dai jefi jefi,

Akwai girmamawa tsakanin baba waziri da Yarima Sultan bashida raini sam bashida kuma girman kan shedai akwa izzah wanda dama ba araba jinin sarauta da wannan,

Saɓanin sauran ƴan uwan sa wanda suke uba ɗaya basa ganin kowa da gashi sun raina kowa mahaifin su ne kaɗai abun girmamawa wato *SARKI YUSUF SHAREEF*

ganin dare yafara yine gashi Sultan yasan Sulaim bazai yadda su koma Part ɗin sa a mota ba to gara su tashi su tafi tun yanzu koya samu ya huta,

To bari mu wuce gwaggo munbar ku lafiya

Sulaim wanda duk ya gama gajiya dama jiya ke kamar akan Ƙaya yake yariga Sultan din tashi tsaye da haka suka yi sallama da baba waziri suka nufi ƙofa,

gwaggo murja tace Allah ya shirye ka dunkum kawai kuma wlh ka shirya dole mu aurar dakai a shekarar nan ko kana so ko baka so mutum har yazama riƙaƙƙyan tuzuru amma babu aure Allah ya kyauta,

Sulaim wanda duk yaji abunda tace ransa ne ya ƙara ɓaci amma baiko juyaba bare tasa ran zai bata amsa,

Shidai Yarima Sultan aransa yace wai dai gwaggo bata so nayi hira da aminina cikin daɗin rai,

A parlourn farko suka zazzauna kafin su je su kwanta alkyabbar Sultan ya cire sannan ya zauna cikin siririyar murya yace wash Allah _Am tired_

Kallon shi sulaim yayi shima ya gajin yasakar masa murmushi,

Sannan yace kaifa duk ka lala ce da raganta yanzu Meye kayi naga jiya anan?,

Ido Sultan yazaro waje yace yanzu duk wannan tafiyar da muka yi ba aiki bace aini rabon da nayi irin wannan tafiyar tun wancan zuwan naka kafin na tafiya Koria,

Jinjina kai Sulaim yayi alamar lallai ma,

Lafiyayyan juice ne wanda akayi shi da zallan kayan marmari sai ƙamshi yake yi ga sanyi acikin wani Ƙaya taccan jog wanda koshi ka kalla zaka iya ji ka ƙoshi da abunda ke ciki tsabar kyan jog din wata amentacciyar kuyangar UMMUL BAIT ta kawo parlourn Sultan saida akayi mata iso sannan ta samu izinin shiga kai saƙon shima dan Yarima sultan din yaji ance ƴar aikyan daga gurin ummul bait tazo shiyasa yace ace mata tashigo,

Sai da ta ajeye tiran da aka ɗoro jog ɗin lemon a kan table din dake tsakiyar parlourn sannan ta zube ƙasa ta ce Allah yaƙarawa yarima lafiya sarkin gobe da izinin ubangijin sama,

Gimbiya kuma uwar gida tace a gayawa ɗan ta da yazo tana masa bangajiya sannan wannan ita ta haɗa tace a kawo masa yasha cikin salama,

Ƙara russuna wa tayi sosai kafin tace tuba nake Ranka ya daɗe ɗan zaki magaji kake kafi gwani,

Zaki iya tafiya cewar yarima Sultan,

Tashi tayi da sauri tare da furta na barku lafiya,

Bayan tafita Yarima ya kalli Sulaim wanda yaɗan kishingi ɗa kaɗan saman kujera,

Yace to ga saƙonan daga UMMUL BAIT nakane kai kaɗai asha daɗi lafiya,

Sosai Sulaim yayi murmushi sannan yace godiya mara iyaka zuwa ga uwata ya futa hakan tare da tashi yaje inda aka ajeye juice din ya ɗauki cup guda ɗaya ya zuba sannan ya koma inda ya tashi ya zauna,

Baƙaramin daɗin juice din yaji ba ga ƙamshin kayan marmarin sai tashi yake ga sanyi mai ratsa zuciya,

Kallon inda sultan yake yayi yace masa ba kaji daɗi ba kamar kada nabar sha gaskiya banji daɗi ba da babu kai acikin nikadai zan shanye,

Dariya Yarima sultan yayi tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login