Showing 15001 words to 18000 words out of 61789 words

Chapter 6 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel

Fauzah   

04 Nov 2025

180

abada abunda bazan doba kenan ko da bayan raina ne, azahirin gaskiya nafiso yakasan ce a hannun mahaifin ka to amma, bazai yiyuba saboda ƴan uwansa suna baƙin ciki da hakan, shiyasa natara su gaba ɗaya ajiya agaban kowa nace hameed ya dawo da HATIMIN zan ajiye da kaina, nayi hakanne domin samun dai dai to atsakanun su, wannan HATIMIN da kake gani sulaim akwai taren ɓoyayyan al amari atare dashi wanda nataɓa bawa ƴaƴa na labari tun suna matasa wannan shine dalilin da yasa kowa ke son mallakar shi acikin su,

To amma baffa ba katse kanayiba, Meye shi wannan ɓoyayyan Al amarin dake tare dashi,

Hhmm sulaim kenan bari in faɗa maka a taƙaice duk wani ƙarfin mulki da kake nema ko wata ɗauka ka ko wani suna to tabbas zaka same shi idan kana tare da wannan HATIMIN, nima mahaifina ne Yabani shi tun ina ƙaramin yaro, amma Tunda na girma nagane babu mai yi sai Allah shine mai komai da kowa ban taɓa sawa zuciya ta zan samu wani abun duniya ba saboda wannan HATIMIN ni nasan Allah ne kaɗai mai badawa a lokacin da ya so kuma shike hanawa a lokacin da yake so, shiyasa nake so ka ɗauke shi har zuwa lokacin ɓace war sa na har abada, ina kuma fatan hakan idan Allah ya so,

Baffa amma Meye yasa su ƴaƴan ka suke so su mallake shi wannan HATIMIN?? Wanda afahimta ta nidai babu alkhaeri atare da shi,

Sulaim kai yaro ne abunda zan faɗa maka kawai shine kaso duk wani wanda ya kasan ce ɗan uwankane da duk wanda yaso ka saboda Allah, da zuciya ɗaya babu hassada saboda ita mugun ciwo ce, zaka dawwama cikin baƙin ciki da ɓacin rai idan har kace zaka damu da arziƙin wani, kasani kowa da arziƙin sa sannan kowa da irin rabon da Allah ya tsaga zai samu a rayuwa babu wanda ya isa ya canza abun da Allah ya ƙaddara, ina so ku so junan ku ku zama abu daya saboda ku AHALI DAYA NE, da sannu zaka gane komai danake faɗa maka harma wanda ban faɗa maka ba, ka nemi tsarin Allah saboda shi kaɗai ne mai kariya, mai kuma bada mulki, da arziƙi, ga wanda ya so,

Yanzu a ina zaka ajiye shi wannan HATIMIN?

Hmm baffa kamar yadda ka ɗauki wannan abu kabani a matsayin ajiya to Insha Allah zan ajiye shi a inda koda ƙuda bai isa shiga ba sai idan ninayi niyar ya shiga, kamar yadda ka yadda dani kabani wannan abu to Insha Allah zan tabbatar da wannan yar dar kawai fatana kakwantar da hankalin ka kuma nayi maka alƙawarin babu wanda zai ji maganar nan Indai taɓan gare nane saidai idan kai kafaɗa ma wani,

Murmushi mai sauti baffa yayi wanda sosai ya bayyana ta cikin recorder ɗin, kafin yace nasan zaka iya sulaim na yadda da kai sosai saboda haka banida wani kokwanto akan ka, akwai abubuwa dayawa danaso faɗa maka dangane da HATIMIN nan to amma sai munsake zama ai yanzu ba kaji komai ba, kuma kaga lokaci ya ja zaka tafi asibiti,

Eh baffa sai na dawo kawai a fili sulaim ya furta (QAUSIN HATEEM). Cikin harshen su na Larabawan yankin Africa,

Ɗif recorder ta tsaya alamun maganar da aka naɗa taƙare,

Kallon kallo tsakanin mai girma hasheem, He excellency Sambo, uncle Mansur, barrister Sulaiman, Sun Kai kusan minti 2 ahaka kowa yayi shock acikin su banda Sulaiman wanda dama shi yaji ya ƙara ji ba wannan ne na farko ba,

Cikin fushi uncle Mansur yace amma kai wlh Sulaiman shashasha ne har kasan da wannan recording ɗin amma kaƙi Bamu muji komai, ai da tuni wani zancen ake ba wannan ba,

Hahaha Ai yanzu kun tabbatar da magana ta ko wannan abun da muka daɗe muna nema yana hannun shegen sulaim ɗin nan ko gidan uban wa yaɓoyeshi Oho amma dole sai mun nemo sa har yana wani cewa wai ko ƙuda bai isa shigaba to ni gani zanje ko inane yaɓoyeshi kuma zanshiga in ɗakko shi,

Sulaiman meye yasa tun sanda dabarar saka recorder tazo maka baka faɗa mana ba, ai da sai asa darect recorder Wanda a lokacin da suke tattaunawa zamuji komai kai tsaye Kaga da yana fitowa da HATIMIN zamu bige shi mu ɗauke, amma yanzu gashi kusan shekara 2 ake magana muna ta fafutuka, cewar Sambo wanda ya ajiye karan sigarin sa yana kallon Sulaiman,

Tunanin hakan bai zomin ba (DADA). Cewar Sulaiman wanda Sunan da suke kiran he excellency Sambo dashi kenan DADA, kuma sannan bayan na ɗakko recorder ɗin daga private perlo ɗin wannan tsohon naku (baffa) sai nanemi recorder ɗin narasa shiyasa ma ban faɗa muku ba sai yanzu da naganta last week, nace to zakuji komai amma sai mun shirya zama,

To amma taya akayi ka iya shiga private perlon sa har ma kasamu damar saka audio recorder ko shine yakira,

Kallon mahaifin nasa Sulaiman yayi kafin yayi wata ƴar dariya irin ta mutun ya raina wayon ka kenan, zan faɗa muku amma bayau ba,

Daga nan kawai kamar haɗin baki suka fashe da wata irin mahaukaciyar dariya mun samo abun harin mu, suka furta atare cikin kausashshiyar murya,

SUHAIMA.

*Wannan kenan...!*

_Akwai tsarƙaƙiya masu karatu kada kubari aba ku lbr_🤗

*💕AHALIN MU DAYA*💕

*🖊️🖊️Alƙalami yafi takobi*⚔️

*Story & writeen°°°*✍️

*💞Fatima Y zakariyya*

💞

_😍Oum Ameerah_😍

_Taku har kullum mai son farin cikin ku_❤️

*Sarauniyar 🫅nazari writer's association*📚

_Muje zuwa ✍️yanzu ma akafara_

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

*✍️📚Nazari writer's association✍️*📚

_Kyakkyawan nazari kafin rubutu na ɗanfare da bin ƙa ido jin rubutu_

_Cikyakkyan nazari kafin rubutu kan Ƙaya ta duniyar adabin hausa_

_Ina godiya da fatan alkhaerin da kuke agare ni tare da addu'oin ku ina jin daɗin hakan matuƙa🤗 thanks u fan's_❤️❤️❤️

*AHALIN MU DAYA*

*NA*

*💞Fatima Y zakariyya*💞

_{😍Ummu ameerah_😍}

*Sarauniyar👸👸nazariwriter's association*📚

*Page* 1️⃣7⃣▶️1️⃣8⃣📖

SUHAIMA_

tanitsu sosai tana sauraran sauraron hajiya fanteka dake tafaman kwararo mata bayani, ita da khaltum, suna zaune daga gefan kate farsu suna sauraron ta fuskokin nan nasu kamar kullum a rufe suke da mayafi sunyi irin na ɗin buzaye, ita kuma tana daga ƙasa saman ɗan abun salla (salla ya).

Gaskiya suhaima saidai kuyi haƙuri don bansan ta inda zan fara ne momuku wannan unguwar ba bare har akai ga samun gidan da kuke nema kinga Kano da girma idan baka san guri ba to za kasha wahala kafin ka samo shi idan ma kasa meshi ɗin kenan, kuma sannan nifa hajiya zaituna ba haka mukayi da itaba cewa tayi, mu taho tare ane momuku gidan da za kuyi aiki kawai haka tace, kuma kinga duk wadda kika gani acikin gidan nan to aiki za a samo mata kuma duk inda aka samu suka ɗauki mutum to anan zai hakura ya zauna, kinga ke yanzu ba lalle asamu gidan daza su ma ɗauke ku kubiyun ba saidai ko wacce da inda za a kaita,

Kallon ta suhaima take ido cikin ido wanda dama ita hakan ɗabi ar tane bata jin shakkar kallon mutum cikin ido duk girman sa ga idanuwan masha Allah,

Bashiri fanteka tayi ƙasa da idon ta don ita wlh tsoron wannan hatsabibiyar yarin yar take, wadda take da tabbacin aljana ce ko kuma rabin ta mutum rabi aljana, ita fa Tunda take yawan barekin ta bata taɓa haɗuwa da abunda ya firgita taba kuma yake kan firgita ta irin yarin yar nan ita fa har addu'a takeyi kar Allah yasa taga fuskar suhaima don tasan babu alkhaeri a ganin fuskar ta saboda iya idon ta ma abun tsoro ne bare akai ga fuskar gaba ɗaya, ita bata sani ba iya ita kaɗai take ganin ida nuwan suhaima haka ko kowa ma haka yake ganin su, ace wai idon bil adama ne haka babu kalar dababu acikin kwayar sa rainbow colour, acewar fanteka fab amma,

Shirun fanteka taji yayi yawa shine ta ɗago don ta saci kallon suhaima, kawai taci karo da waɗan nan idanuwan na suhaima da suke furgita ta tafita da ga hayyacin ta saboda tsoro, da sauri ta ɗauke idon ta tamai da kan khaltum, don ita taga ya yanayin taya ke saboda taga ita ko magana bata fiyaye ba,

Suna haɗa ido khaltum ta watsawa fanteka harara tare da faɗin zaki iya tafiya kibamu guri,

Ko ƙala hajiya fanteka bata ƙara furtawa ba tatashi tana ɗan ɗingisa ƙafar ta ɗaya har ta fuce musu daga ɗagaki aranta tace waisu waɗan nan mai suke nufi dani ne so suke su kasheni Tun lokacina bai ƙare ba, gaskiya dole in rage jin tsoron nan nasu ta haka ne zan nuna musu basu isaba idan aljanune da su to ai nima ina dasu ahe takai ƙarshan zancan zucin nata tare da yin ga tsine kamar gaske, amma taɗauki alwashin yaran nan ko turo su akayi baza su taɓa gane komai Akan taba,

Aɓan garan su suhaima kuwa tana fita suhaima ta kwashe da dariya khaltum kuwa sai kallon ta takeyi saida tayi mai isar ta sannan ta tsaya da dariyar,

"Wai Meye yabaki dariya? cewar khaltum

Wlh matar nan ce nafaɗa miki babu gaskiya acikin lamarinta ko sannan ina sane nake bata tsoro saboda kada ta samu damar hanamu ai watar da aikin mu cikin daɗin rai, shiyasa, nake yi mata haka,

To Meye rashin gaskiyar da take ai ka tawa? Khaltum ta sake tambayar suhaima akaro na biyu,

Bata da gaskiya sosai ma kuwa sannan ke kina ganin matan da suke shigowa gidan nan da waɗan da take ɗakko wa daga ƙauyen wai atunanin ki aiki ake kawo su? Hmm Khaltum kenan sana ɗiyar matar nan Allah ne kaɗai yasan ƴan matan da rayuwar su talalace wasu kuma suka salwanta anraba su da iyayen su na har abada,

Emm amma ke taya akai kikasan du wannan abubuwan?

***

Khaltum kenan to tun ganin fari da nayi wa wannan matar nagane akwai wani abu a tattare da ita sannan bugu da ƙari tunshigowar mu gidan nan nagane hakan, amma duk ma ba wannan ba ni yanzu ba wannan ne agabana ba kamar yadda nayi mata alƙawari zandawo kanta to tabbas zai cika alkawari na, ke bama iya wannan ne laifin taba a raina nakeji aikin da yakawo mu garin nan to itama tana cikin criminal, amma bazan gane hakan yanzuba dole sai nafara shiga wannan gidan,

Take kwayar idanuwan ta suka juye, zuwa asalin kalar su wato ruwan toka ash, ya kan koma rainbow colour Ne Idan zatayi mugun ta, tabbas akwai wani lamari mai nauyi game da rayuwar suhaima,

Nifa kinsan Meye yake hanani yiwa matar nan magana? Khaltum ce ta tambayi suhaima,

A a, tabata amsa ataƙaice

Wlh ko son ganin ta banayi bare har inji ina son yi mata magana, na tsane ta,

Mtsssss takai ƙarshan maganar tare da jan dogon tsaki, sannan ta ɗora da cewa,

Da ina saran zamu bar gidan nan nankusa amma yanzu kinaji ko unguwar bata sani ba bare ma tasan gidan yanzu kenan ya zamuyi?

Suhaima wadda ta ɗan lumshe idanuwan ta tana sauraron Khaltum, buɗe su tayi a hankali, kada ki damu kanki ukhteey, sunan da suhaima take kiran Khaltum dashi kenan (ukhteey). Zamu bar gidan nan zuwa nan da kwana biyu 2 wannan alƙawari nane,

To ta yaya kenan Khaltum ta ƙara tambayar suhaima,

Zuwa yanzu nima bansaniba taɗan faɗa a ƙufule alamun tafara gaji da tambayoyin da Khaltum ɗin keyi mata, suhaima bata son tambaya ko kaɗan bare ma game da rayuwar ta, yanzu za kuyi faɗa da ita kuwa,

Itama Khaltum ɗin tasan hakan, ahaka ma gani take yau tayi mata mutunci da tayi ta tambayar ta kuma tana bata amsa, idan ba mother ba babu wanda ya isa ya tambayi suhaima wani abu dan gane da rayuwar ta, ta tsaya kula shi harma ya samu amsa daga gareta,

***

Salama alaikum, wata doguwar yarin yace mai dogon hanci black beauty tsaye tayi musu sallama sai faman rarraba manyan idanuwan ta takeyi, da hanzari suka kai duban su bakin ƙofar atare, don ganin waye wannan, domin su wannan abun mamaki ne agurin su, jin wani abakin ƙofarsu abunda tun zuwan su gidan banda hajiya fanteka da ta shiga ɗakin nasu itama yau, to babu wanda ya taɓa gigin shiga gurin su Tunda kowa ya fahimci ko fitowa ba sayi daga ɗaki to babu mai zuwa inda suke, gashi kullum ko fitowa suka yi zuwa toilet fuska arufe take, dayawa ma daga cikin, ƴan mata da zawarawan dake gidan tsoron su suhaima suke ji gani suke yi kamar basu da gaskiya, bugu da ƙarima fanteka ta tarasu baki ɗaya ta faɗa musu babu ruwan su da su suhaima kada su sake sushiga harkar su, to shiyasa ma tsoron nasu yaƙaru, amma acikin su akwai masu target ɗin sai sun kama su sunyi musu shegyan duka kuma sannan suga fuskar su wai Tunda baƙarfin su suka fiba,

Sallama ta ƙara yi musu akaro na biyu 2, cikin haɗa baki suka amsa, da sauri suka kalli juna don suma abun ya basu mamaki, jin sun amsa mata atare,

Suhaima tace ƙarasu ciki mana, ita kuwa baiwar Allah jikin ta yaƙarayin sanyi ga tsoro, tanaji don dagani kasan ba ason ranta itama ta shigo musu ba,

Ƙarasawa tayi ciki hannun ta riƙe da wani ɗan madai dai cin food flask, daga ɗan nesa dasu ta tsugunna,

cikin rawar baki tace dama hajiya ce tace na kawo muku abinci,

Mungode zaki iya tafiya, da sauri tamiƙe tanufi ƙofa suhaima tabita da kallo cikin nazarin yarin yar, bata kaiga fita ba suhaima tace kinga, baiwar Allah, cak ta tsaya amma bata jiyo ba tana tunanin da ita ake ko a a,

Kamar suhaima tasan abunda take tunani kenan, tace mata eh dake nake, jiyo wa tayi amma bata ƙara koda Taku ɗaya bani tana daga inda take tace gani,

Dariya suhaima tayi wadda har ana jiyo sautin dariyar duk da ba a ganin fuskar ta, ita abunda yabata dariya ganin yarin yar duk tabi ta firgice, ita dai khaltum sai kallon su kawai takeyi saboda dama alama ita ba ma abociyar dariya bace ko da yaushe, ba kamar suhaima ba,

Idan baza ki shigo ba to kiyi ta tsayiwa a...... Bata ƙarasa sauran maganar ba kawai taga yarinyar agaban ta, gani nazo,

Wata dariya tasakyayi sosai abunta, don suhaima idan taga abu yabata dariya ko agaban waye sai tayi iya mai isar ta,

Yauwa dama sunanki zaki faɗamin suhaima tayi mata maganar tare da tsare ta da waɗannan idanuwan nata masu bawa mutane tsoro,

Sunana sajeedah" cewar wannan doguwar yarin yar,

Oh Masha Allah naji zaki iya tafiya abunki yanzu, amma zan ƙara nemanki,

To, sajeedah tace tare da ficewa asukwane,

Da kallo suhaima tabita kafin ta maida dubanta ga khaltum da take ta kallon ta tunɗazun, tana jira taji dalilin da yasa suhaima ta kira yarin yar nan,

Suhaima tafa himci hakan daga khaltum ɗin amma mai makwan tabata amsa sai ma ta kauda zancan ta hanyar janyo wannan food flask ɗin da sajeedah takawo, tare da faɗin ki sakko kici abinci ko, tana ƙoƙarin buɗewa kai masha Allah, kinga ma favourite food ɗin kine aka kawo, taliya ne jollof kuma da zafin shi ki sakko kici,

Hmm kawai khaltum ta furta ahankali tasan a yanzun ko tafi ƙuda naci Tunda suhaima tayi haka to baza taji komai daga bakinta ba yanzu,

_____________________________

Wai kai yaya saleem baka gajiya ne wlh kana bama kan ka aiki ace kullum sai ka kaine school kuma ka ɗakkoni, nifa ina da driver ɗina, cewar suhailat dake zaune a gidan gaba gefan driver site, shikuma saleem yana driving ɗin su, GA wani Ƙaya taccan murmushi, dayake tayi akai akai kamar wani sabon ango da alama yana jin daɗin magan ganun suhailat,

Kallon shi taɗan yi tacikin mudubin gaban motar, sannan ta ɗora dace wa kuma naga ma yaushe kazo ƙasar nan kofa wani hutawa baka yi ba, gashi next month zaka wuce aiki naji ummeetha tace Lagos akayi post naka ko??

Kai kawai ya ɗaga mata alamar eh da murmushi akan fuskar sa har a lokacin,

Yanzu kallon shi sosai suhailat tayi, sannan tace gaskiya yaya saleem Kanada fara'a sosai, kullum fuskar ka cikin murmushi, wlh su saleema, sunji daɗin su, dama muma haka yaya sulaim ɗin mu yake,

Kada ki damu suhailat, sulaim zancan zashima insha Allah, aida can damuna yara shima ba haka yakeba, daga baya ne Yakoma haka amma muna sa ran insha Allah, zai koma kamar yadda yake ada can,

Eemm Allah yasa haka, zamuyi farin ciki idan hakan ta kasan ce, cikin sanyin murya suhailat tayi maganar ciki ciki kamar wadda bata so yaji abunda take faɗa,

Ameen insha Allah shima ya faɗi hakan a hankali domin yaji babu daɗi ganin duk yanayin suhailat ɗin ya canza,

Shiru babu wanda ya ƙara tankawa acikin su, suntafi duniyar tunani, kowa da abunda yake saƙawa aranshi,

Shiga dai saleem bai ji daɗin wannan shirun da suhailat tayi ba,

Amma bazai takura taba, ahaka da wannan tunanin suka ƙarasa gida,

Yauwa ke ke zonan, suhailat wadda takusa shiga perlo kenan ta tsaya tana kallon wadda kezuwa, sabrina ce ɗiyar he excellency Sambo tana tun karo ta, da alama itama cikin zata shiga, sanye take da riga da sket rigar iya ciki wanda idan tayi kwakkwarar motsi ana iya ganin cikin ta sosai, sket ɗin ya kama jikin ta sosai ga wata tsaga tage fan sket wadda ta kusa kaiwa gwaiwar ta, kanta sanye da pie cap, ta ɗaure gashin ta abaya wanda ya bayyana sosai don duk cikin ahalin Arab babu baya wajan gashi,

Suhailat wadda tagama kallon ta Tunda ga nesa tsab, kawai ta juya da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login