Showing 27001 words to 30000 words out of 87136 words

Chapter 10 - Ikram Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

504

cewa "wayyoo Mami kinga yaya Khaleel na min gwalo" da sauri har yana tuntube ya mike ya shige cikin dakinsa ya kulle kofar.
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 39...... Khaleel dae bae ce komai ba sae murmushin da yyi, Mami ta dauki wayarta ta kira Aliyun sae da ya kusa katsewa ya daga tace "ae ni ban san kana da xuciya ba sae yau, to kadda Allah yasa ka shigo din, files kuma basa wajena suna gun Dr Musa" tana kai wa nn ta katse kiran, khaleel yyi dariya yace "wae me ya hada ki da Hydar dinki ne hka Mami, Aliyu ne fa" Mami bata tanka sa ba ta mike ta ja Ikram suka wuce sama. Yau Asabar da safe Mami ta shirya Ikram ita ma ta gama shirinta xasu can gidansu, Ikram sae murna take xata gun Amminta, suna fitowa falo Mami tace ma khaleel ya tashi ya kai su, ya juya da sauri yace "ina" tace "can gidansu Ikram," ya bata rae yace "haba mum wkend guda ma mutum baxae huta ba bayan duk wahalan da ya sha durin wkdayz" Mami tace "ehh baxa ka huta ba" bae kuma cewa komai ba ya mike ya haura sama ya canxa kananan kayan dake jikinsa xuwa manya snn ya fito rike da car key dinsa, suna fita parkin space Ikram tace "yaya Khaleel wancan motar xa mu shiga ba wnn ba don ni bana son shi" harararta yyi ita ma ta rama, yyi kwafa ya bude driver seat ya shiga ya tada motar ta xaga da sauri ta bude gaba ta shige, Mami kam na tsaye tana waya, ya daka mata tsawa yace "ke koma baya kar na kwade ki" ta murguda masa baki tace "ni nan xan xauna baxan koma baya ba" Mami ta shiga bayan motar tace "A'a Ikram gaba kika xauna" Ikram ta juya tana kallonta tace "Mami ni nn nake so" Mami tace "to yi xamanki" tayi ma Khaleel dake kallonta gwalo, ya dauke kansa ya gama ba motar wuta snn suka fita daga gidan, cikin minti arba'in suka isa anguwarsu Ikram tun bae gama parkn ba ta shiga kkrin bude motar ta fita ta kasa, Mami tace "to ae sae ki jira motar ta tsaya ko Ikram" yana gama parkn Mami ta bude motar ta fita, Khaleel ya riko hannun Ikram da sauri yace "tsaya Mami ta gama fita ke" juyawa tayi tana kallonsa tace "meyasa" bae ce mata komai ba, Mami na fita ya kulle motar yace to fita, ta dinga kkrin bude motar ta kasa, ihu ta fasa tana kallon Mami da bata san me ke faruwa ba har ta shiga gidansu Ikram, yace "bani kike ma gwalo ba ko, ae bbu inda xaki yau, baxa ki ga Ammin taki ba" ta fasa masa kuka tana bubbuga motar, fixgota yyi yace "to share wnn hawayen idan ba hka ba baxan bude maki ba, kuma kice baxa ki kuma min gwalo ba" ta turo baki ta shiga share dan hawayen fuskarta, handkerchief ya ciro ya mika mata yana kallonta ta karba ta shiga share hawayen, ta fara fyaco Majina daga hancinta ya fixge handki dinsa da sauri ya xaro mata ido yace "da handkerchief dina xaki share majina" murguda masa baki tayi tace "to ba ya ki fitowa ba ma" ya bude mata motar yace "watarana sae na cire maki wnn bakin idan kina min irin hka" ta fice daga motar ta kuma murguda masa bakin snn tayi cikin gidansu da gudu tana Ammi oyoyo. Xaune ta tarda Mami da Amminta a daki, ta xube jikin Amminta cike da murna tanai mata oyoyo, Ammi ta rungumeta kawae tana murmushi, Ammi tace "to kin je kin gaida su Altine ne," Ikram tace "A'a ni nayi sabon kawaye a sabon makaranta na" Mami tace "A'a je ki ki gaida su suma ae kawayenki ne Ikram" ikram ta mike tayi kofa har ta fita ta dawo da sauri tace " Ammi Abbana fa"Mami ce tace "yana kasuwa Ikram, je ki ki dawo sae mu je mu gaida shi" Ikram ta fice da sauri xuwa gidansu Altine, a bakin soro suka ci karo da Khaleel xae shigo gidan ko kallonsa bata yi ba xata fita ya fixgota yace "ina xaki" tace "to ba Mami bace tace in je in gaida tsohon kawayena su Altine ba" bae ce komai ba ya sake ta ta fice, snn ya shiga cikin gidan, ko minti biyar ba ayi ba Ikram ta dawo wae ta gaidasu, Ammi dae sae kallonta take tana mgna da Mami kmr ba Ikram dinta mara ji ko kadan ba, yini suka yi ranar a gidan duk da Ammi sae addua take su maxa su tafi kafin Abban Ikram ya dawo dan har ranar bae san ita ta bada Ikram da hannunta ba, duk da ya fara xargin hkn ganin bata wani damu kmr ynda ya damu ba, sae addua take a xuciyarta Allah yasa yan anguwa basu lura da ikram ba don mmn Altine ce kadae tasan abinda tayi, amma yau ta dau alkawarin xata gaya masa gskyan komai. Karfe hudu da rabi Mami ta kira Khaleel don ya fita ya xo ya maida su gida, cikin minti sha biyar ya iso Mami tayi sallama da Ammi tace xasu tafi gobe xata dawo ta dauki Ikram Ammi tace su tafi kawae ba komai. Gidansu Aliyu Mami tace Khaleel ya kai su, Khaleel yace "mami ni baxan fa shiga gidan ba ajiye ku kawae xanyi in tafi" Mami tace "to baka isa ba mara xumunci, har yara sun gane halinka kai dae ban san irinka ba wllh" karfe shidda saura suka isa, shi dae Khaleel har lkcn fuskarsa a daure yake, Ikram tace "lah Mami mun taba xuwa wnn gidan" Mami ta fito da ita daga motar tace "eh mun taba xuwa" tana rike da hannunta suka nufi balconyn shiga falon gidan, Mami tayi sallama suka shiga falon, Aliyu da seeyama ne xaune falon yana gwada mata abu a laptop" seeyama kadae ce ta amsa sallaman a fili ta mike da sauri tana ma Mami sannu da xuwa, Ikram ta wara ido ganin Aliyu tace "yayana" da gudu tayi gunsa ta fada kansa ta rungumesa.
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 40..... Kallonta kawae Aliyu ke yi bae ce kmai ba, kmr xata yi kuka tace "yayana baxa ka min oyoyo ba" dauke kansa yyi, ya kashe laptop dinsa ya rufe, Ikram ta juya tana kalln Mami dake tsaye tana hararanta da sauri ta mike daga jikinsa a tsorace tace "wayyo Mami wllh na manta ashe na daina wasa da shi" siyama dae na tsaye sae kallnsu take, Mami ta karaso cikin falon tana kallon siyama tace "momynku fa siyama" siyama tace "tana sama Mami, wllh daxu muke ce ma ya Mujaheed ya kai mu gidanki yace mu bari gobe sunday ashe ma kina hanya" Mami tace "to sae ku xo goben ae bae baci ba, ina su saiham da Aisha" Siyama xata yi mgna Khaleel ya shigo gidan kmr mara gskya, ta wara ido tace "lah ya Khaleel" da gudu taje ta rungumesa, yyi murmushi yana kallnta yace "hw re yhu siyama" tace "wllh yaya baka da kirki ko kadan" hannu ya daura a bakinsa alamar tayi shiru, dariya tayi tace "wllh baxan yi ba" su saiham da Aisha ne suka sakko jin hayaniya downstairs, basu bi ta kan Mami ba duk suka yi gun Khaleel da gudu suka rungumesa cike da jin ddin gninsa, Ikram tayi kusa da Mami tace "Mami su waye wa ennan sun san yaya khaleel ne, amma gashi suna rungumesa baki yi masu mgna ba kuma ae shi namiji ne su kuma na mace ne" Mikewa Aliyu yyi ya dauki system dinsa yyi hanyar stairs Mami ta bisa da kallon mmki har ya haura, hka ma seeyama ganin bae gaida Mami ba, Momy ce ta sakko da fara'arta tana ma Mami sannu da xuwa, bude baki tayi ganin Khaleel tace "iyye yau xa ayi ruwan sama da kankara, Hajiya kice yau kin lallaba autanki ya biyo ki knn don nasan lallabasa kika yi" dariya Khaleel yyi ya gaisheta ta amsa tana dariya tace "Barrister Khaleel knn, bayan mamin ka baka san da Allah yyi ruwan kowa a duniyar nn ba, xumunci dae ba abun wasa bne" dukar da kansa kawae yyi yana Murmushi ya xauna Saiham taje ta dauko masa drinks a fridge, Mami tace "Hajiya fa" Momy tace "ina jin suna kitchen da Farida" Mami tayi hanyar kitchen din, Momy ta kama hannun Ikram tace "mu je sama bby" duk yan matan suka bi Ikram da kallo da ta juya sae taga kallnta suke, suna isa stairs ta murguda masu baki tana jujjuya masu ido har suka haura sama da momy, dariya suka shiga yi ssae Khaleel na kallonsu. ciki ciki Hajiya ta amsa ma mami kmr ko da yaushe Mami ta juya tayi hanyar stairs tana murmushi. Duk yan matan suka xagaye khaleel suna ta lbri suna dariya, a hka Hajiya da farida suka fito daga kitchen suka samesu, Khaleel ya gaida Hajiyar ta tsaya kallonsa snn ta tabe baki ta amsa tayi gaba abunta tana cewa "kai ka girma ynxu sae shekarar da ka ga dama kke xuwa gaida mutane, don baxan ce rana ba, sae ayi shekara ba a ganka ba duk ka tare gun uwarka" shi dae bae ce mata komai ba sae ma daure fuskarsa da yyi, ikram ce ta sauko kasa rike da can malt tayi gun Khaleel tace "yaya Khaleel Mami tace ka bude min" ya harareta yace "ni xan bude maki" kmr xata yi kuka tace "don Allah mana ina son in sha" karbewa yyi ya bude mata, sae da ya fara shan na sha snn ya mika mata ta fasa ihun da sae da gidan ya amsa tana kiran Mami, rikota yyi da sauri tana tsalle tsalle yace "ke baki san gidan mutane muke ba" cikin kuka tace "wllh sae ka biya min abu na" yace "to to bari in xuba maki nawa" ya bude drink dinsa da sauri ya xuba mata, ta karbe tana leka ciki ko gwangwanin ya cika, da sauri ya karasa cika mata ta share hawayenta tare da murguda masa baki ta yi hanyar stairs, su seeyama duk sakin baki su ka yi suna kallonta, Aisha tace "wae wacece wnn ya Khaleel" ya wara masu ido yace "nima ban sani ba ku tambayi Mami" bayan Magrib Mami tayi ma momy sallama xa su koma gida, Momy tace "kin ki cin abincin gidanmu Hajiya" Mami tayi murmushi tace ni dae a koshe nake suna fitowa corridor Mami ta bude kofar dakin Aliyu, yana kwance yana kallo tace "ina yini Aliyu" kallo daya yyi mata ya dauke kansa, snn can ciki ya gaidata, harararsa tayi tace "aa kadae amsamin gaisuwata, kuma me ya hanaka xuwa aiki wk din nn" ba tare da ya kalleta ba yace "nayi tafiya ne" tace gud, snn ta fice daga dakin, ikram ya gani durkushe gefensa tana kallonsa kmr xata yi kuka, ashe sae da tasan ynda tayi ta shigo dakin Mami na masa mgna, mikewa yyi da sauri ya dago ta ya rungumeta yace "bbyna ta ina kika shigo" tace "yayana ka daina xuwa gidanmu ni ina sn ka dinga xuwa" yyi murmushi ya dago kanta yace "Mami bata son ina xuwa gidanta Ikram" Muryar Mami taji tana kiranta alamar nemanta take, ta mike a tsorace shima ya mike ya dauko mata pack din chocolate ya mika mata snn ya manna mata kiss a kumatu a hankali yace "i love yhu Ikram" washe masa hakora tayi tana kallon chocolate din ya bude mata kofa ta fice tana daga masa hannu, har suka fito compound Mami bata daina harararta ba, Ikram ta rike hannun ya khaleel kmr xata yi kuka don bata son harara, wata mota ce ta shigo gidan suna shirin shiga tasu motar, drivern dake sanye da kayan soja ya fito da sauri ya bude sit din baya, yana rike da jarida ya fito daga cikin motar da gninsa ka ga Aliyu, khaleel ya juya da sauri yace "ya salam"
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 41..... Da
alama mutumin yyi mmkin ganinsu ya karaso
har inda suke, Mami na rike da hannun Ikram
tace "ina yinin mu Alhaji" yana linke jaridar
hannunsa ba tare da ya kalleta ba yace "lfya
qlau ya aiki" tace "Alhmdllh" ya juya yana
kallon Khaleel da ya durkusa har kasa kansa
a duke yace "ina yini Abba" kallonsa kawae
Abban ya tsaya yyi snn yyi ma Mami sae da
safe yyi cikin gida ba tare da ya amsa
gaisuwar ba, Khaleel ya mike tsaye da kyar
yana kallon Maminsa, hannu ta mika masa
alamar ya bata makullin motar, ya mika mata
ta bude bayan mota tace "shiga Ikram" Ikram
ta juya tana kallon Khaleel dake tsaye har
lkcn snn ta shiga motar, Mami ta bude
maxaunin driver ta shiga ta tada motar,
juyawa Khaleel yyi a sanyaye ya koma cikin
gidan, Ikram tace "Mami yaya Khaleel baxae
xo gida damu bne" Mami tace "xae xo" Ikram
kmr xata yi kuka tace "to ba gashi ya koma
ciki ba" Mami tace "nace maki xae dawo
Ikram" Ikram tayi shiru tana binsa da kallo
har ya shiga falon, Mami ta ja motar suka
bar gidan. Suna isa gida Mami ta gama parkn
ta fito ta bude ma Ikram motar ta fito,
hawaye ta gani kwance a fuskarta, Mami ta
dafa ta da mmki tace "me ya same ki dota,
kukan me kike" ta fashe mata da kuka tace
"ba yaya Khaleel bne bae xo damu ba" Mami
tayi murmushi ta daga fuskarta tana
kallonta tace "nace maki yana nn dawowa
dota" fitowa da ita tayi daga cikin motar ta
kulle motar snn ta kama hannunta suka yi
cikin gida, har karfe sha daya Ikram bata yi
bacci ba tana xaune falo duk da Mami ta
kashe TVn, Mami ta gama abinda take tace
"mu je mu kwanta dota" Ikram ta girgixa
mata kai kmr xata yi kuka tace "ni yaya
Khaleel nake jira"
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar
42......
Washegari Ikram na xaune dinnin sanye da kayan
makarantar ta tana break, khaleel ya sauko cikin
shirin fita office bayan ya sallami Maminsa, ya
karaso dinnin din yana kallonta, bata ko kalli inda
yake ba sae cin bread da butter take abunta, ya
xauna kujeran dake kallon nata yana kallonta
yace "baki iya gaisuwa ba ne" murguda masa
baki tayi tace "ehh" mikewa yyi, ita ma ta mike
da sauri xata gudu ta kwabar da kofin tean
gabanta duk ya xube kan dinnin din da jikinta,
xaro ido tayi tana tafe hannu tace "shknn ka
xubar min da tea a uniform dina sae naje na nuna
ma Mami" rikota yyi da sauri ya yo waje da ido
yace "lah karya xaki yi min" kan tace kmai ya
durkusa gabanta sanin yau mai raba shi da Mami
idan taga uniform din nn sae Allah, cikin lallami
ya shiga cewa "to to yi hkuri, wllh xan baki
chocolate" kmr xata yi kuka tace "to kalli uniform
dina" mikewa yyi yana kalle kalle kmr munafuki
ya ja ta suka wuce sama ya shiga da ita dakinsa
ya kulle kofar yana kallonta yace "to gaya min
inda uniform din ki yake" tace "ko ba cikin drawer
Mami take ajiye min ba" juyawa yyi yace ina
xuwa ya fita, ba a dau lkci ba ya shigo rike da
wani uniform din yace "to cire ki sa wnn"
murguda masa baki tayi ta juya masa baya tace
"to cire min button" ba musu ya cire mata, har ta
daga pinafo xata cire ta juya da sauri tace "lahh
kana so ka kalleni ne, ka juya joor" da sauri ya
juya mata baya yana murmushi, tayi tsaki ta cire
pinafo din, sake juyawa tayi tana kallonsa dae
dae lkcn da shima ya juyo suna hada ido ta
kwala ihu tana kiran mami tana cewa "wllh
kallona yake yi Mami" da sauri ya rufe kofar
dakin jin Mami ta bude dakinta, ya durkusa
gabanta yace "wlh rufe idona xanyi bari ma ki
gani" rufe idon yyi da kansa ya shiga cire mata
sauran uniform din ya mayar mata da sabon da
ya dauko yana sa mata pinafo Mami ta bude
kofar dakin, mikewa yyi da sauri, Mami na
kallonsu da mmki tace "meye hka Khaleel" kasa
ce mata komai yyi, ta juya tana kallon Ikram.
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 43...... Mami ta karaso kusa da su fuskarta daure tana kallon Ikram tace "me kike yi a nn" Ikram ta bata fuska kmr xata yi kuka tana nuna mata Khaleel tace "ko ba shi bane ya xuba min ruwan tea a uniform dina shine sae ya kawo ni dakinsa wae don kar ki ganni kuma yaje ya dauko min wani uniform, shine kuma naga yana kallona da nake sa uniform din......" tsawa Mami ta daka mata tace "fita kar in buge maki baki na aike ki gun Khaleel, ko nace ki je kusa da shi?" ta juya tana kallon Khaleel da ya kasa daina kallon Ikram, ranta a bace tace "a kan wani dalili ka xuba mata ruwan tea a jiki Khaleel?" ya marairaice mata yace "wllh Mami bani na xubar mata tea a jiki ba karya take min" Mami ta masa mugun kallo ta kwashi uniform din da ya cire mata ta watsa masa su tace "to ka tabbatar ka wanke su ka shanya kafin ka bar gidan nn don bbu bawan ku" tana kai wa nn ta fixgo Ikram dake tsaye tana kakalo hawaye tayi waje da ita, wani tean ta kuma hada mata ta koma sama ta dauko jakarta da takalmanta, khaleel ya dde tsaye bayan fitarsu daga karshe ya cire suit din jikinsa yyi unbotton din hannun rigarsa ya cire tie din wuyarsa ya duka ya dauki uniform din ya shiga bathroom dinsa ya shi ga wankewa don ba wuta bare ya saka cikin machine, yana gama wankewa ya fito xae je shanya shi a garden ya tarda su a falo Mami na gyara mata takalminta, kallo daya Mami tayi masa ta dauke kanta tace "kuma ka tabbatar ka gyara dinnin din can kafin ka bar min gida, don bbu me gyara maka" Ikram tace "Mami shi ma xae yi latti fa, kice mama jummai ta taya sa gyarawa" Mami ta galla mata harara tace "rufe min baki" ta turo bakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login