Showing 6001 words to 9000 words out of 87136 words

Chapter 3 - Ikram Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

507

ni yawo a motarki" Mami tayi murmushi tana kallon kyakkyawar fuskarta tace "to naji ikram" Banana bunch daya ta karba gun malam sani, ya sa mata a leda snn ta karba ta mika ma Ikram, da sauri ikram ta karba, Mami tace "to muje," bata yi musu ba ta shiga gaba Mami na biye da ita a baya har suka iso bakin titi gun motarta, Driver ya fito da sauri yace "sannu Hajiya," Mami tace "yauwa Habu, snnu da jira," mami ta bude motar tace "shiga Ikram," ikram ta shiga motar tana cewa "wnn ma yaronki ne Anty," Mami tayi yar dariya tace "A'a driver ne," driver yace "ina muka nufa hajiya?" mami tace "mu tafi gida kawae" hka Ikram ta dinga mata surutu barkatae cikin motar har suka shigo cikin garin Abuja, nan fa ta manna goshinta da glass din mota tana kallon manya manyan Buildings din Abuja da tituna, kauyanci ta dinga yi ma Mami, ko me ta gani sai tayi magana, driver dae sae murmushi yake, ikram duk ta rude ita a barta ta fita tayi tafiya da kafarta wani gun ma idan an wuce sae tace ita bata gani ssae ba, sae Mami tasa driver ya koma snn su ci gaba da tafiyar, wani lafiyayyan Anguwa suka shigo driver yyi horn a wani makeken gida mai kyan gske, mai gadi ya wangale gate, ya ja motar suka shiga, idanuwan ikraam kmr su yi magana tana kikkifta su tace "nan ne gidan mamarki Anty," mami tayi murmushi ta gyada mata kai kawae, snn ta bude motar ta fito da ikraam suka yi balcony din shiga gidan, sae waige waige Ikram take, har suka shiga wani kantamemen falo, ikram ta yo waje da ido tace "ina ne nn Anty, ni dae ki maida ni gidanmu," murmushi Mami tayi ta ja ta suka haura sama, snn ta bude dakinta tana rike da hannunta suka shiga, ikram ta dan marairaice kmr xata yi kuka Mami ta xaunar da ita gefen gado tace "kar ki damu dota, nn ma gidanku ne kin ji," kai kawae Ikram ta gyada mata, Mami ta bude fridge ta ciro lemon five alive ta ajiye gabanta tace "bari na dauko maki kofi dota," nan ma kai kawae ta gyada mata, mami ta fita xuwa kitchen, a hankali ikram ta xamo daga kan gadon ta dawo kasa ta xauna ta cire hijabinta da hula snn ta jawo lemon gabanta ta bude da kyar da hakorinta ta kafa kai, mami ta shigo dakin rike da cup tace "kai dota, ga cup na dauko maki," ko kallonta ikram bata yi ba idonta lumshe sae kwankwadar five alive take, mami ta xauna tana kallonta, cike da sha'awa, Allah yasa iyayenki su yrda su bani ke ikram, abinda ta fada a xuciyarta knn, don kanta ta ajiye lemon bayan ta koshi ta lafta uban gyatsa, Mami ta dawo kusa da ita tace "kina jin yunwa ne ikram," kai kawae ta girgixa mata, mami ta shiga kwance roban da Ammi ta nade mata gashinta da, gashin suka xubo har kusan bayanta, mami ta dauko comb dinta da man kai da ribbons, ta shiga gyara mata gashin, ita ko sae kallon cartoon din da Mami ta kunna mata take, duk inda ta ga ana fada sae ta fasa ihu, mami sae dariya take, har ta gama gyara mata gashin snn ta dauko mata gasasshiyar kaxa a fridge ta dumama mata, tana cikin ci aka bude kofar dakin, wani dogon handsome ya shigo sanye da 3qtre da polo ya fada gefen mami ya kwanta, ta juya tana kallonsa ganin bata ce komai ba yasa a hankali yace "mami ban fa ci komai ba har ynxu, am jet hungry," mami tace "to ban san me kke so
[1/1, 6:29 PM] Aishat muhd: TSAFI 💀 💀TSAFI
💀
~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar
8.....
Ikram ta mike bayan ta rasa inda xata yi da naman gabanta kmr xata yi kuka tana kallon Mami dake gaban computer tace "Anty ki kai ni gidanmu kar Ammina tayi min duka," Mami tace "ynxu xan kai ki Ikram, shiga bayi ki wanke hannunki ki kuskure baki," Ikram tace "ina bayin yake, waje xan je?" Mami ta nuna mata kofar bayi ta shige da sauri, tana shiga da minti uku ta fasa ihu, mami ta mike da sauri ta shige bathroom din a rude, tsaye ta ganta karkashin shower ruwa na xuba tayi jagab, Mami tace "me ya kai ki nn Ikram, ga buta nn kina gani ki tsallake sa," tsalle Ikram ta shiga yi tana cewa "ina son in ga ko menene, ashe abun ruwan sama ne," mami ta kashe showern ta jawo ta tace "haba Ikram dubi ynda kika jika jikinki, to maxa ki cire kayan," ba musu ta fara tube kayanta, Mami ta dauko towel dinta ta mika mata tace "daura wnn," ta karba ta daura, tabi Mami suka fito, dai dai nn Aliyu ya shigo dakin da sallama, Mami ta amsa tace "amma ba dae daga gida kke ba," ya tsaya daga bakin kofar yana kallon Ikram yace "A'a nn kusa nake," Ikram tace "lah wnn yaron naki ne na ranan n Anty," Mami tayi dariya tace "ashe kin ganesa," Aliyu ya xauna kan kujera yace "ina yini Mami," Mami tace "lfya lau ya aiki," murmushi yyi bae ce komai ba, Ikram ta matso kusa da mami a hankali tace "amma Anty yana da kyau yaron nn naki," Mami ta fashe da dariya tace "ko Ikram," tayi fari da ido tace "wllh" dariya ssae Mami take, shi ko sae kallonta yake bae dae ce komai ba, Mami tace "Aliyu don Allah siyo mata dan gown nan kasuwa ta jika kayanta," ya girgixa kai yace "a gajiye nake Mami," Mami tace "to bari in aiki Khaleel, ka bude fridge ka dauki lemo mana," bae ce komai ba Mami ta fita, ya hade rae yana kallon Ikram yace "xo nan ke," ta taho gabansa ta tsaya tana kallonsa tace "gani," ya kauda kansa yana murmushi ganin ynda ta taho ko tsoro bbu, hannu ta daura kan dimples dinsa tace "lah irin abu na," ya juyo da sauri yana kallonta, ta nuna masa nata tana dariya, ya kamo hannunta yace "me kika ce ma Mami" tace "nace mata yaronta na da kyau," wara ido taga yyi yana dariya, ita ma ta fashe da dariyar har da kyakyatawa, baki ya bude yana kallonta, dae dae nn Mami ta shigo dakin, ta hade rae tana kallon Aliyu tace "meye hka Ali," sake hannun Ikram yyi, cikin harshen turanci ta shiga ce masa bata son hka, murmushi kawae yyi ya mike ya fice daga dakin, Mami na kallon Ikram tace "dariyar me kike," Ikram tace "shi naga yana dariya shine nima nayi," Mami bata ce komai ba ta shiga goge mata ruwan jikinta da towel, ta gama ta dauko manta ta shafa mata snn ta gyara mata fuskarta tace "bari Khaleel ya kawo maki sabon kaya ki sa kin ji ko," tana washe hakoran jin ddi tace "to," gefen Mami ta xauna tana ta kallon cartoon har Khaleel yyi sallama, mami ta amsa ya shigo ya tsaya daga bakin kofar yace "gashi Mami," Mami tace "ikon Allah to ka karaso mana ka tsaya daga bakin kofa," karasowa cikin dakin yyi ya mika mata, ya juya da sauri xae fita Mami tace "ka ci abincin Khaleel," bae ce komai ba har ya isa bakin kofa, Ikram tace " kmr tsorona yake Anty," juyawa yyi ya galla mata wani mugun harara snn ya fice, Ikram tace "lah ashe mugu ne ma harara na yake Anty, ni dae na fi son wnn mai kyan, meyasa kika haife shi Anty" murmushi kawae Mami tayi ta fito da ready made din gown din da ya siyo kmr an gwada ta ko dae dae ita, nan ikram aka shiga tsalle tsalle ana juye juye har da rawa, Mami sae dariya take tana kallonta cike da sha'awa, makullin mota mami ta dauka, tasa Ikram ta sa Hijab dinta snn ta kama hannunta suka fita, kwance suka tarar da Aliyu a falo, ya mike da sauri yace "ina xaku Mami" Mami tace "gida xan mayar da ita mana" yace "to bari in kai ku" Mami tace "kai da ka gaji, kayi xamanka kawae xanyi drivn din" da sauri yace "A'a na huta" Mami bata ce komai ba suka fita a tare ta bude back seat suka xauna da Ikram, snn ya tada motar suka fita daga gidan, Ikram ta dasa surutunta daga inda ta tsaya yi take ba full stop kmr radio, mami murmushi kawae take, shi ko sae kallonta yake ta madubi, wani babban supermarket Mami tace ya tsaya, ya samu waje yyi parkin, snn Mami ta fita tace tana xuwa, juyawa yyi da sauri yana kallon Ikram da ke bin Mami da kallo kmr xata yi kuka yace "Ikram" ta daga kai tana kallonsa yyi mata murmushi yace "tana xuwa kin ji," kai ta gyada masa snn tace "wa ya koya maka tuka mota," yace "dawo nn in gaya maki" ta dawo front seat din da yake nuna mata, yana kallonta yace "babana ne ya koya min" ta wara ido tace "lah, to ae ni babana bae da mota bare ya koya min" dariya yyi snn yace "to ni xan koya maki" tace "da gske" yace "eh mana" ta fara tsallen jin dadi daga xaunen da take, kallonta kawae ya tsaya yi har ta nutsu don kanta snn yace "Mami a gidanku ta dauko ki ta kawo ki gidanta," tace "A'a a kasuwa ta daukeni" yyi shiru yana kallonta, xae yi magana Mami ta bude motar rike da manyan ledoji ta shigo motar, "me ya kai ki can Ikram?" Ikram tace "shine yace in dawo wae xae gaya min wani abu"

~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 9..... Mami tace
"dawo inda kike kar mu bata ynxun nn" ba musu
ta dawo, shi kam tada motar kawae yyi yana
murmushi suka bar wajen, tana jikin Mami suka
iso dae dae inda Mami ke shiga mota idan ta fito
daga kasuwa Mami na kallonta tace "ina ne
hanyar gidan naku Ikram" Ikram tace "A'a a nn
xaku ajiye ni ae" Mami tace "aa gun mamarki xan
je Ikram," da sauri Ikram tace "A'a ni dae a nn
xan sauka nace maki bbu kowa a gidanmu" Mami
tayi shiru tana kallonta snn cikin lallami tace "to
Ikram ae Mamanki dukanki xata yi idan kika
koma gida ynxu ke kadae, kinga dare ya kusa,
xata ce daga ina kike" ikram ta girgixa kai alamar
bata yrda ba tace "A'a ae a xaure xan tsaya har
Abbana ya dawo, baxae bari ta dokeni ba" Mami
ta rasa me kuma xata ce mata, can dae tace
"baki son in mayar da ke gidana ki xauna dani ina
sa maki cartoon ina baki naman nn mae dadi
muna tafiya yawo kuma ina siya maki sabon
kaya" da sauri Ikram tace "ehh ehh ina so" Mami
tayi murmushi tace "to ae sae naje na gaya ma
mamarki kar ayi ta nemanki" Ikram ta girgixa kai
tana tabe baki alamar bata yrda ba tace "A'a ni
dae baxan kai ki ba dukana Ammi xata yi da
waya ko muciyan tuwo maman altine ta taya ta,
kinsan maman Altinen nan bata sona" Aliyu da ya
tsura mata ido har lkcn yyi murmushi yana kallon
mami cikin harshen turanci yace "bar ta kawae ta
tafi Mami, xan rakata da kafa sae in ga gidan
nasu, idan yaso ko gobe ne sae in kawo ki" Mami
ta galla masa harara tace "sannunka, to ban yrda
ba" yyi murmushi yace "to ae dats d only option
ynxu Mami" ya maida dubansa ga Ikram yace "to
ni in raka ki gidanku Ikram" Ikram ta juya tana
kallonsa xata yi magana yace "to ae ba shiga
xanyi ba, kawae raka ki xanyi" tace "to" snn ta
shiga tura motar xata bude, a hankali Mami ta
bude mata motar snn ta sakar mata murmushi
tace "to ki gaida min mamanki Ikram" kai kawae
Ikram ta gyada mata ta fice, shi ma ya fito, Mami
ta mika masa ledan tsarabar da tayi mata ya
karba snn ya bi bayan Ikram, ita ko ta dawo
driver seat tana binsu da kallo, tafiya suke yana
rike da hannunta yace "wani class kike Ikram"
Ikram tace "ae primary 5 nake ynxu, amma fa da
a primary 4 nake kawae sae naga an mayar dani
5, kuma ina son makarantar mu ssae don ana
siyar da alawa da madara da ice cream, Ammi
tace baba ne yace a sa ni a makaranta don shafa
da altine ma sun fara xuwa, amma ynxu shafa ta
daina xuwa wae babanta kawu na lado bashi da
kudi, nima kasan wa ke biya min, to ba babana
ke biya min ba don shima ba shi da kudi, malam
habu ne ke biya min," matse hannunta da ta ji yyi
yasa tayi shiru, yace "ca nayi wani class kika ban
ce ki ban lbri ba" ta fixge hannunta tana huci
tace "shine xaka cunkule ni baka san akwae xafi
ba" yyi yar dariya yace "to rama" ta dago
hannunsa ta dage ta shiga yi masa abinda yyi
mata, sae taga dariya kawae yake, bae ankara ba
yaji ta gatsa masa wani mugun cixo, yyi yar kara
ya fixge hannunsa ya saki ledan hannunsa yana
yarfe hannun yana kallonta da mamaki, ta fashe
da dariya ta kanne ido tace "gashi nn na rama"
ya daga hannun yana kallon inda ta cije shi, ta
duka ta shiga kwashe abinda ya xubar snn ta
mika masa ledan tace "ungo" ya fixge yace "wllh
ba ruwana dake daga yau" tayi narai narai da ido
kmr xata yi kuka ta mika masa hannunta tace "to
rama" ya kama hannun ya durkusa gabanta ya
daura hakoransa kan yatsunta, ta rumtse ido tana
yarfe dayan hannun ya gatsa mata cixo shi ma
snn ya sake, ihu ta fasa ta shiga yarfe hannun ta
fashe da kuka tace "wllh sae na gaya ka da
babana" ya fashe da dariya yace "to ae ke kika
ce in rama" rikota yyi ganin guduwa take son yi
tana kuka, don ba karamin xafi cixon yyi mata ba,
da sauri yana dariya yace "srrry kanwata kema
rama kuma" ta fixgo hannunsa ta gatsara masa
wani shegen cixo, yyi kara yana yarfe hannun ya
mike ya dauki ledan yace "to mu tafi" suka ci
gaba da tafiya tana tsotsan inda ya cije ta sae
kallonta yake har suka iso anguwarsu, ta juya
tana kallonsa tace "oya ka tafi to ga gidanmu
can" yace "baki son in gaida mama Ikram" kmr
xata yi kuka tace "to ae dukan mutane take yi,
nima ynxu nasan dukana xata yi" ya tsura mata
ido yace "mu je in roketa kar ta dokeki" da sauri
tace "A'a ae sae ta dokeni, ta bayi na yi tsalle na
fita daga gida daxu don ta rufe kofar xaure wae
baxan fita ba ni kuma ina son in fita" ya xare ido
yana kallonta da mamaki, kan yace komai tace
"lahhh ga Abbana can ya dawo" da gudu ba tare
da ta kuma kallonsa ba tayi gaba, ya shiga
kiranta ta karbi abinda mami ta siya mata amma
ina, dae dae kofar xaure suka ci karo da Abbanta
ta rungumesa tana masa oyoyo yace "daga ina
kike Mamata" tana washe hakori tace "can" jan ta
yyi ba tare da ya lura da kayan jikinta ba suka
shiga ciki, Aliyu yyi murmushi ya juya ya bar
wajen don Magrib yyi. Suna shiga tsakar gida
Ammi ta fito da wayar rediyonta Ikram tayi waje
da gudu tana ihu, Abba yace "wae meye hka kike
Aisha me tayi maki" Ammi tace "ae wlh ta koma
ta shigo gidan nn ta inda ta fita idan ba hka ba
wllh sae na faffasa mata jiki yau"


[1/7, 8:51 PM] ‪+234 810 188 2232‬: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 10..... Ikram na
xaune bakin kofar dakinta washegari da safe ta
rungume hannayenta sae kumbura take tana bin
Ammi dake ta aikace aikacen gida da kallo, ranar
Abba bae fita kmr ynda ya saba fita ba wato da
sassafe, yana xaune tsakar gidan shima, ikram
dae bata kalli inda yake ba don bbu ruwanta da
shi ma, jiya ba karamin duka Ammi tayi mata ba
kuma bae ce kar ta doketa ba har sae da Ammi
ta fasa mata baki, ikram ta tabe baki tuno
shegen dukan da Ammi tayi mata jiya da daddare
ta kuma kwace sabon kayan da Mami ta siya
mata, ssae ta daga ma Ammi hankali jiya don sae
da ta gama basu lbrin duk abinda ya faru jiya duk
Ammi ta rude ta shiga jibgarta kmr xata kasheta,
Abba kam kasa cewa komai yyi don shima tasa
hanklin ya tashi, hkn ne ma yasa yau basu bari ta
je sch ba, sallama aka shiga kwadawa bakin
Zaure Abba ya mike ya fita sae ga shi ya shigo
da kafinta rike da woods a hannunsa, abba ya ce
"ai tun daxu kai nake jira iliya da na dade da
barin gida ynxu"bayi Abba ya nuna masa Ikram
ta bi su da kallo ta dan tabe baki ta dauke kanta,
tana ji kafintan na ta buge buge da guduma a
bayin, Abba na tsaye daga bakin kofa har ya
gama bayan kmr minti talatin snn suka fito, Abba
yace "idan na tashi daga wajen aiki xan biya ta
shagon ka iliya" iliya yace "to" snn yyi masa
sllma ya fita, Ikram ta bisa da kallo tare da
murguda masa baki kmr yana kallonta, Abba yyi
hanyar dakin Ammi ya daga labulen yace "ni na
tafi Aisha" tace "to Allah shi kiyaye Malam" ya
nuna ikram yace "don kaniyarki yau ma ki fita ki
ga idan ban daure ki idan na dawo ba" ta fashe
da ihu kmr jira take ta mike tsaye da sauri ta
shiga tsalle tsalle tana rusa kuka, bae bi ta kanta
ba ya fice, Ammi ta fito da sabuwar bulalan da ta
siya, Ikram na ganinta tayi dakinta da gudu tana
cewa tayi hkuri. Hka ikram ta yini ranar a daki ko
tsakar gida bata leko ba bbu irin kukan da bata yi
ba, abincin da Ammi ta tura mata cikin dakin ma
kin ci tayi, ji take kmr a kan kaya take, ita dae ta
tafi yawo kawae a rayuwarta, ta mike tayi bakin
windon dakinta ta ga ko xata iya fita ta nn,
amma duk irin jijjigar da ta dinga yi ma windon
da duk karfinta kin fita yyi, karfe uku taji ana
sallama a xaure ta mike da sauri ko me ta tuna
ta koma ta xauna kuma, taji muryar Ammi na
cewa "A'a Hinde daga ina hka" yarinyar tace "gida
mana, wae Baba ne yace in xo mu taho da Rabi
da kayanta" Ammi ta dan yi shiru snn tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login