Showing 3001 words to 6000 words out of 87136 words

Chapter 2 - Ikram Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

508

yana kallonta yace "wani dukan kike nufin na sake mata bayan wanda saude tayi mata ynxu," Ammi bata ce komai ba ta shige daki abunta, ya maida dubansa ga ikram yace "ki dinga jin magana kin ji mamata, kuma daga yau kar ki sake fita da daddare, ko kina son na fara dukanki ne" ta girgixa masa kai yace "kin ci abinci," ta juya tana kallon inda ta bar abincinta tace "gashi can," yace "je dauko," ta mike ta dauko tana yatsine fuska tace "ni baxan ci ba Abba datti ya shiga ciki," ya shiga kwala ma Ammi kira ta xo ta xubo mata wani abincin, daga cikin dakin Ammi tace "ban da shi," mikewa yyi ya dauka nasa, suka shiga ci tare ya sa ta wanke hannu tayi alwala tayi slln isha snn ya rakata daki ta kwanta ya tofa mata addu'a ya fito, ya shiga nasu dakin, Ammi na xaune ta hade rae ya xauna gefenta yace "haba Aisha, ikram yarinya ce duka duka shekarunta nawa, wani yaro ne baya kin ji? Sannu a hankali duk xata daina ta nutsu, ki dinga hakuri da ita don Allah, Ammi dae bata tankasa ba tayi kwanciyarta kawae. Washegari da safe Ammi ta shiryata ta tafi sch bayan Abbanta ya fita gun aikinsa, ta hada ta da naira ashirin tace "kuma saura ki ki xuwa makarantar ko kije kiyi dambe a kawo kararki tunda ke kince kin xama jaraba a gari," tana xumbura baki ta fita daga gidan a xuciyarta tana cewa ni bbu makarantar da xan je malama ta dokeni ban ga littafina ba, kmr abun arxiki ta kama hanyar makaranta da yara tana kusa makaranta ta yanke wata hanya daban da sauri da sauri take tafiya kar mutane su ganta har ta isa wata katuwar bishiyar mangwaro, ta haye ta samu branch me dan karfi ta kwanta kai tana ta kallon mutanen dake wucewa wajen, a hka bacci ya dauketa bata farka ba sae karfe goma da rabi, tafara kalle kallen inda take, can tayi hamma ta tsinko wani mango da bae nuna ba ta shiga ci, har ta gama snn ta duro kasa tana waige waige tayi hanyar Canal da saurinta, wasu almajirae yara ta tarar wajen suna kama kananan kifi da karamin hook dinsu da earth worm a jiki, ta bude jakarta ta ciro nata hook din naira ashirin ta siye shi da ddewa, bbu ranar da bata xuwa canal din kama kifi, ta nannade uniform dinta ta shiga tona rami tana neman earthworm har dae ta samu ta dauke shi da dan tsintsiya tayi gun almajiran tace "ku, ku sa min don Allah," ba musu suka karba suka saka shi bakin hook din suka mika mata ta koma can bakin katon canal din ta shiga tsoma hook din cikin ruwa tana jiran kifi ya kama ta fito dashi ga gwangwaninta a gefenta, har ta fara ganin yaran makaranta na wucewa gida bata kama komai ba, tayi tsaki ta jefar da earthworm din ta nannade hook dinta ta mayar cikin jakarta snn ta kama hanyar gida da sauri, bata bi ta kofar gidansu altine ba kar ta ganta tace bata je makaranta ba, Ammi ta kai mata ruwan wanka taje tayi kafin ta ci abinci ta fito ta sa doguwar rigarta Ammi ta ajiye mata abincinta tsakar gida ta xauna tana ci a hankali tana kallonta, gani take kmr xata gane bata je sch ba, tana gama ci ta shiga neman littafinta na xuwa makaranta don gobe xata je kada Altine da mamarta su xo su ca ma Ammi bata je ba. Yau kmr kullum Ikram ta dawo daga sch bayan Ammi ta sallameta ta bata abinci ta dauki hijabinta ikram tace "ina xaki Ammi," Ammi tace "kasuwa xanje siyo yakuwa, kina gama cin abincin ki wanke kwananon kije kiyi bacci, saura ki karar min da ruwan randan," da sauri Ikram ta mike tace "Ammi ni meyasa baki aikeni ba ai ni kike aika," Ammi tace ai ni ynxu na yaye aikenki Ikram, na dinga xuwa da kaina in siyo abinda nake bukata," Ikram ta fashe da kuka tace "wllh Ammi ni se kin aikeni, malamar mu tace mu daina barin mamarmu tana fita siyo abu da kanta bbu kyau, bad children ne ke yin hka," kuka ssae take, Ammi tace "to ai ke din ce ba kya ji Ikram," tana share hawayenta tace "kiyi hkuri Ammi Allah xan dinga ji," da kyar dae Ammi ta bata naira talatin din taje bakin kasuwa ta siyo yakuwar bayan ta ja mata kunnen kar tayi tsokana kuma kar ta dde, ta saka dan hijab dinta ta fita tana share hawayenta, har wani bari jikinta yake kawae ita dae ta ganta a kasuwa, a xuciyarta tana raya kila ma yau xata kuma ganin matar nn ta daukar mata kaya, sae tace ta kai ta yawo a katuwar motarta.

~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 5..... Sae da Ikram ta fara siyan yakuwar da Ammi ta aiketa snn ta shiga cikin kasuwar tana rike da shi a hannu bayan ta cire ledar ta jefar, fada ta tarar wasu nayi ta shige tsakiyarsu da sauri tana kallo duk da irin tunkude tan da ake yi har aka gama fadan ganin kowa ya kama gabansa yasa tayi gaba ita ma, can bangaren groceries tayi tana kalle kalle, dai dai inda ta fara ganin matar nn ta tsaya ta juya tana kallon mutumin dake xaune wajen tace "kai, kai wnn matar nn da ta taba siyan Ayaba a nn da Apple ta kuma dawowa," kallonta kawae ya tsaya yyi ta karaso kusa da shi tace "kai baka ji na ne," yace "A'a ina jin ki mana yarinya, ke hka aka koya maki a gidanku" da sauri ta daga hannu sama tana xaro ido tace "kai ni Ammina shara kawae take koya min da gyaran daki kuma na fara iya wa wllh kaje ka tambayeta ma, amma ita Altine mamarta tace ma Ammina bbu abinda ta iya sae cin abinci, kaga idan Ammina ta aikeni gidansu shafa ma ina ganin tana hura itace tana daura roba a kai xata yi girki amma fa yarinyar lukuta ce kuma bana sonta don tana dukana ni kuma ban iya dukanta ba amma akwae watarana da salame tayi mata duka wae in ji sadiya, kasan sadiya kawar salame ce kuma duk a islamiyyar mu suke, malamin mu kuma yana dukan duk wanda bae iya karatu ba ni dae kuma na iya wllh," shiru tayi tana kallon mutumin ganin ynda yake dariya ga Neighbours dinsa ma na tayasa, ta nemi benci ta xauna tana kallonsa tace "me yasa kke dariya hka, Ammina tace min mahaukaciya kadae ke dariya hka shi yasa nima na daina," dariya yake ssae yana kallonta yace "ya sunanki yarinya," tace "sunana Rabi'a amma Ammi da Abbana da yan unguwarmu suna kirana Ikram, baba yace kawu na lado ne yace a sa min Rabi'a wae sunan yayarsa ce da ta mutu kuma baxata sake dawowa ba, Ammi tace min wae da sunan mamarta xa a sa min amma sae kawu na lado yace baxa a sa ba, kasan kawu na ladon nn mugu ne kuma baya sonta....." ganin ynda mutumin nn ke dariya yasa Ikram tayi shiru tana kallonsa, can ta dan tabe baki ta mike xata yi gaba ya kirata da sauri ta juya tana kallonsa yace "har xaki tafi kawata," tace "ehh mana Ammi ce tace in siyo mata yakuwa xa muyi miya da shi yau, kila baba ya samu kudi ne ya bata, don kullum bashi da kudi yake cewa," Mutumin yace "to dan xauna muyi hira kawata," ta dawo ta xauna tana cewa "amma fa kafin dare yyi xan wuce don Ammi tace kar in dde kuma har ynxu bn dde ba ae, to ya sunanka yaro" yana dariya yace "sunana sani," tace "lah sunan baban Altine ne ae, kasan me yasa na xo nn" mutumin yace "A'a," tace "akwae wata mata da ta taba siyan Ayaba a nn gurin har na taya ta daukan kaya na kai mata bakin titi ta bani Ayaba da apple da kudi, katuwar mota ya xo ya tafi da ita, gurinta na xo ko xan ganta," yyi shiru yana kallonta tace "ta kara xuwa nn," yace "A'a ina xan sani kuwa yarinya, kwastamomi masu kudi da yawa gareni," Ikram tace "to xo ka ban Ayaba don Allah," ta fada tana nuna masa bunch din banana, ya yo waje da ido yace "ina kudin ki," ta dan marairaice tace "ni bani da kudi Ammi da baba basa bani," ya dan yi dariya yace "to idan na baki xaki dinga xuwa taya ni hira kawata," da sauri ta gyada masa kai ya dauki wuka ya yankar mata Ayaba uku ya mika mata yana murmushi don yarinyar ta burgesa ta karba tana tsalle ba ko gdya tayi gaba ta bar masa yakuwar nn kan benci, sae bayan tayi nisa ya gani ya dinga dariya neighbours dinsa na taya sa, yace "lallai yarinyar nn ta tona ma uwarta asiri, kun ga fa ta bar min yakuwar," da gudu da gudu ikram ta isa gida rike da ayabarta guda uku, wajen karfe shidda saura ita da aka aika tun biyu, rabe rabe ta shiga yi bakin xauren, Ammi har ta gaji da jira ta kada kukarta da ruwan miyan taushen, ido hudu suka yi da Ammi tana lekan tsakar gidan, Ammi ta dauke kanta bata ce komai ba, ikram na nn tsaye bakin xauren har Abbanta ya dawo ya kama hannunta suka shiga ciki yana tambayarta me tayi. Tun ranar da Mami suka hadu da Ikram bata sake samun shigowa kasuwa ba sai yau Asabar tana isa gun mai fruits dinta ya gaidata cike da ladabi ya tambayeta me xae bata yau, Mami ta xauna ta lissafo masa abinda take so snn tace "ina son nayi maka wata tambaya malam sani," yace "tambayar me Hajiya," Mami tace "wata yarinya ce ranar da na xo nn karshe ta taimaka min ta daukar min kayana dai dai can," ta nuna masa gun da yatsa, snn ta ci gaba da maganarta "shine nake son tambayarka ko ka santa," malam sani ya dan yamutse fuska alamar tunani yace "Anya kuwa Hajiya, ya yarinyar take kuma meye sunanta, ko dako take yi," Mami tace "tace min sunan ta Ikram," malam sani ya yo waje da ido snn ya fashe da dariya har da kyakyatawa, mami ta tsaya kallonsa da mamaki, yana rike ciki yace "daxun nn ta bar nn Hajiya, ki ce kawata kike nema," Mami ta mike da sauri tana kallonsa tace "don Allah ka santa, wllh ita ce dalilin xuwana kasuwar nn yau," malam sani na dariya yace kwarae kuwa ko ba Ikram Aku ba" Mami tayi murmushin jin ddi tace "to don Allah kasan gidansu,"


[1/2, 10:13 AM] ‪+234 706 205 5793‬: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 6...... Malam sani yace "A'a gskya ban san gidansu ba amma kullum sae ta xo nn" Mami ta dan yi shiru snn tace "to shknn malam sani, amma karfe nawa take xuwa nn din," yace "yawanci idan an tashi daga sch takan yo nn kan ta tafi gida wajajen karfe biyu knn, wani lkcn kuma da yamma take xuwa," Mami tace "talla take yi ne," yace "A'a ko daya wllh shiriritan ta ne ke kawota nn," mami tace "gobe lahadi kana ga xata xo nn," yana dariya yace "ae Hajiya bbu ranar da bata xuwa nn," Mami tace "to shknn gobe da yamman na xo," yace "to Allah ya kai mu Hajiya, in ji dae ko lfya" Mami tayi murmushi tace "bkm malam sani ina son ganin iyayenta ne kawae, bani fruits dina in tafi," ya shiga xuba mata fruits din da take siya yana bata lbrin Ikram da halinta tana dariya. Ikram ce tafe tana dawowa daga sch da su Altine, duk tunaninta na gun ynda xa ayi taje gun mai Ayaba kmr ynda ta sa mashi suna, jiya kwata kwata Ammi bata bari ta leka ko xaure ba, ynxu kam ba daman tace xata tafi ga su Altine su je su gaya ma Amminta, su kadae ke surutunsa ita ko tafiyarta kawae take, har suka iso kusa da wata bishiyar gauva, ikram ta dan tsaya ganin maxa biyu sama suna tsinkar gauva ga wani kuma a kasa yana kwashe su yana xuba su cikin jaka, tana kallon yaron kasa tace "xo ka ban gauva don Allah," ba tare da ya kalleta ba yace "ba a badawa," warce jakar tayi ta sheka a guje yaron ya bi ta da gudu, sauran biyun da suke sama ma suka sauko suka bisu a guje, har suka wuce su Altine, Altine tace "wllh ikram barauniya ce kuma sae na gaya ta da malama gobe a makaranta,"gudu kawae Ikram take da duk karfinta suna biye da ita a baya ga jakar gauva a hannunta yyi mata nauyi, jefa jakar tayi cikin wani katon kwata ta ci gaba da gudunta rike da jakar makarantarta ssae kar ya fadi, da kyar da ikon Allah ta iso gida don sun kusan kamata, ta sakala sakatar kofar xaurensu bayn ta shiga tayi cikin gida tana mayar da numfashi kmr xata shide, Ammi dake alwala ta mike da sauri tana kallonta tace "me ya faru Ikram ke da wa," ta shige dakinta tare da cewa "ba kowa." kofar xauren suka dinga bubbugawa hkn yasa Ammi ta yafa mayafi ta fita tana Adduar Allah yasa ba magana Ikram ta dauko mata ba da rana tsakar nn. Washegari tuesday ikram ta fito tsakar gida bayan ta ci baccinta sanye da sweater dinta don ruwa ssae aka yi daren jiya, hkn yasa Ammi bata tasheta xuwa sch ba da safe, mika tayi tare da hamma snn ta xauna daga bakin kofar dakinta tana kumbure kumburen dukan da Ammi tayi mata jiya don har dare bata bar kuka ba, Ammi na xaune tsakar gidan bakin murhu tana dama koko, ta galla mata harara tace "uwarki xata maki sllhr, sha sha sha kawae," ta mike tana bubbuga kafa ta dauko buta, tana gama break Ammi ta jika mata uniform dinta ta wanke ta yo waje da ido tace "ni safa kadae na iya wankewa," Ammi bata tanka ta ba ta shiga ciki abunta, sae kusan karfe daya ta gama wankin snn ta shanya, ta diba ruwan wanka da gudu ta shiga bayi tayi wanka ta fito ta shiga dakin Ammi tace "xo ki bude min akwatina na dauki kaya Ammi," Ammi ta mike ta shiga dakin ta bude ta ciro mata yar doguwar riga iya gwiwa ikram tayo waje da ido tace "wllh baxan sa ba ni ki bani rigana da skirt," ganin ynda take kuka yasa Ammi ta ciro mata riga da skirt din ta karba tana sharewa hawayenta, Ammi ta fice daga dakin, ta daga doguwar rigar da Ammi ta fara ciro mata tana kallo tace "da da wnn kayan xanje gun mai Ayaba yyi min dariya," ta murguda baki ta wurgar, snn ta saka kayanta ta sa hula ta dan shafa powder ta fito ta shiga dakin Ammi tace "Ammi ni xanje gidansu shafa na karbo littafina," Ammi ta galla mata harara tace "baxa ki je ba don ubanki, fice ki ban waje," tayi waje da gudu ta fashe da kuka, Ammi ta bita ta kulle kofar xauren da dan kwado, daki ikram ta shige tana ta rusa kuka, can ta mike da sauri ta fita, bokitin karfe ta dauka a hankali ta shiga bayin wankansu ta kifa shi a kasa , snn ta hau kai tana lekan waje, dan Zinc din da ya kare bayin ta sama ta cire a hankali ta ajiyesa cikin bayin, snn ta hau kan bangon bayin ta dira kasa, sae da ta fara kakkabe jikinta snn ta saka kai sae kasuwa gun mai Ayaba. Yana jera Apple ta isa tana washe hakora, yace "lah ikram kwana biyu ina ta nemanki kin ma kasuwa kaura," Ikram tace "ba Ammina bane sae tayi ta rufe kofa tana hana ni fita kullum kullum kuma hka jiya tayi min duka don wasu yara sun nemi tsokanata, to shine yau na haura katangar bayinmu na fito" dariya yake ssae yace "kai ikram," ta dan marairaice tace "wllh" yana dariya yace "kinsan wata Hajiya da kika taba daukar ma kaya?" da sauri ta ce "eh ehh" yace "yauwa yau kusn kwana uku knn kullum sae ta xo nemanki," ikram tace "lah ha ila, to me kke ce mata?" yace "nace ban san gidanku ba mana," ikram ta yo waje da ido ta daura hannu biyu a ka tace "ohhw ba gidanmu na can kasan layi kusa da gidansu altine da shagon mai treda ba xaka ce mata baka sani ba," dariya yyi ssae yace "to ki xauna ma ki jirata nasan xata xo anjima," ikram ta xauna da sauri tace "to,"
[1/2, 10:13 AM] ‪+234 706 205 5793‬: Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 7...... Hudu saura Mami ta iso gun mai Fruits, har lkcn ikram na kasuwar amma gun wata mata mai saida cherry ta tafi tana ta mata xuba duk don ta bata cherryn matar dae sae dariya tke, malam sani ne ya shiga kwada mata kira don ba nisa daga shagonsa ta taho da gudu ba tare da ta lura da Mami dake tsaye tana kallonta dauke da murmushi a fuskarta ba, ikram tace "matar nn muguwa ce bata ban agwaliman ba," mami tace "Ikram," ikram ta juyo da sauri tana kallonta da gudu taje ta rungumeta tace "lah Anty yaushe kika xo," Mami tayi murmushi tace "ynxu na xo Ikram, ynxu ki fada min ina ne gidanku mu tafi" Ikram tayo waje da ido tace "me xa kiyi a gidanmu Anty," Mami tace "iyayenki nake son gani" ikram ta dauke kai tace "ba kowa a gidanmu ni dae," Mami ta dafa kafadarta tace "haba Ikram xan siya maki Ayaba da yawa fa," ikram ta washe hakori da sauri tace "to xan nuna maki, amma ni sae kin fara kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login