Showing 18001 words to 21000 words out of 87136 words

Chapter 7 - Ikram Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

503

sae da safe bayan ya dauki makullin motarsa snn ya daga ma Ikram hannu, ta mike da sauri tace " ina xa ka?" Mami ta jawo ta tace "gida xae tafi gobe xae xo kin ji dota" Ikram ta fashe da kuka tayi gun sa tace "ni dae bana son ya tafi ya barni binsa xanyi, to nn ba gidansu bne" da kyar da kyar Aliyu ya lallaba Ikram ya tafi don bae son jarabar Mum dinsa. Ta gama cin kukanta jikin Mami tayi bacci wajen karfe sha biyu knn na nyt,
[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 21..... Washegari
Ikram na tashi da Asuba Aliyu ta fara tambayar Mami dake kitchen tana hada masu break, "kin ji mana Anty ki gaya min ina yake mana" Mami tace "wae wa?" Ikram tace "wnn din nn mana," Mami tace "bana san shi ba," Ikram ta bata fuska kmr xata yi kuka tace "Allah ni ban gansa ba, kince xae xo da safe" Mami ta ja ta suka koma sama ta shiga da ita bathroom ta matsa mata toothpaste a toothbrush snn ta mika mata tace "maxa ki wanke bakin ki kafin in dawo dakin nn, kuma kika kuskura kika taba wani abu xan dokeki snn baxan ba ki tea ba" Ikram ta xumburo baki ta karba snn Mami ta fita ta ci gaba da abinda take a kitchen, Ikram na gama Brush ta fito daga bayin ba tare da ta taba komai ba don tana mugun son tea, tana bude kofar dakin, Khaleel ma na bude kofar dakinsa, ta bude baki da alamar mmki tace "lah dawowa kayi" komawa cikin dakinsa yyi ta sauko da gudu taje ta sami Mami a kitchen tace "Anty wnn yaron ya sake dawowa ne ba ya tafi ba" Anty ta juya tana kallonta tace "yaya Khaleel xaki dinga ce masa daga yau kin ji ni ko Ikram" Ikram tace "to amma meyasa ya kuma dawowa ni bana son ya dawo" Mami tace "maxa ki koma daki idan ba hka ba baxa ki sha tea ba" da gudu ta bar kitchen din ta koma sama, har ta bude dakin Mami ta dawo tayi hanyar dakinsa, ta dan bude kofar a hankali tana lekan dakin, ido hudu suka yi yana sa agogo ta washe masa hakora tare da kanne Ido tace "yaya Khaleel" bata jira mae xa ce ba ta rufe kofar tana kyalkyala dariya ta shige dakin Mami, Khaleel ya dde tsaye kmr ya hadiye xuciya don takaici daga karshe ya saka agogonsa ya suri briefcase dinsa ya fice daga dakin, Mami ta fito daga kitchen knn tace "ga break can kan dinnin Khaleel" ba tare da ya kalleta ba yace "xan yi a office" yyi kofar fita, Mami ta kirasa, tsayawa yyi daga inda yake jin bata ce komai ba yasa ya dawo yace "gani" ta xauna tace ya xauna, shi ma ya xauna, cike da damuwa ta fara masa mgna "haba Khaleel ynxu xaman Ikram ne matsalarka a gidan nn, me ta tsare maka son, kai ynxu kafi son ka dinga ganina cikin kadaici alwayz ba yaro gabana" Kmr xae mata kuka yace "to Mami ni ba yaro bne ko gajiya kika yi dani" Mami tayi murmushi tace "me xae sa in gaji da son dina, kafa san irin son da nake maka Khaleel kuma dole vry soon xa mu rabu don aure xaka yi nd beside awa nawa kke yi gida kai da sae dare ma kke dawowa daga aiki" Khaleel ya jinginar da kansa jikin kujera bae ce komai ba, Mami ta dan sauke ajiyar xuciya tace "ka dauki Ikram a matsayin kanwarka plss, duk wnn wautan da take yi xata daina, in ma ance tayi ba yrda xata yi ba" Khaleel ya dan tabe baki bae ce komai ba, sae ga Ikram ta sauko ya juya yana kallonta fuskarsa daure ta washe masa hakora kmr dae ynda ta yi masa daxu tace "yaya Khaleel" sae kuma ta fashe da dariya har da kyakyatawa, ji yyi kmr yyi kuka don takaici, Mami tace "meye hka Ikram" Khaleel ya mike da sauri yace "mami sae na dawo" yyi hanyar fita, Mami tace "to abincin fa Khaleel" a bakin kofa suka ci karo da Aliyu, Khaleel ya basa hanya ya wuce snn ya fice, da gudu Ikram taje ta rungumesa tana masa oyoyo, ya wara mata ido ya durkusa yace "kinyi bacci me ddi Ikram" ta bata fuska tace "ba ka tafi ka bar ni ba to" Mami tace "to mu tafi sama kiyi wanka" Ikram tace "A'a ni ba ynxu xanyi ba kin ga yaron da nake tambayrki nn kika ce baki san inda yake ba" Mami ta harareta tace "nace ki xo muje in sa maki ruwa kiyi wanka" Aliyu yyi murmushi ya mike ya kamo hannunta suka karaso cikin falon ya gaida Mami, ta amsa tace "ka fara wlkncin xuwa aikin naka ne ynxu ko, na kusa fire dinka" yace "kai Mami kwana biyu ne fa kawae" tace "dat's ur cup of tea ka bari idan an gama maka naka sae kayi ynda ka so" bae ce komai ba ganin ta ja Ikram xasu haura sama yasa yace "da Ikram xa ki office knn yau Mami" Mami tace "yau xanje mata registration a makaranta sae ta fara xuwa, anjima kuma jummai xata dawo daga garinsu kaga komae xae xo min da sauki" Ikram tace "wani makaranta Anty?" Mami tace "school mana" ta kauda kantantana xumburo baki bata dae ce komai ba amma a xuciyarta cewa take ni baxan je ba, Aliyu yace
"ban fa yi break ba Mami" Mami ta galla masa
harara tace "to me xan maka, ina mutane gidan
ku suke" yyi dariya, ta kama hannun Ikram suka
wuce sama, ruwan dumi Mami ta hada ma Ikram
tayi wanka da tafito Mami ta shafa mata mai ta
fito mata da wasu hadaddun riga da wando ready
made ta sa mata, ba karamin kyau Ikram tayi ba,
Mami ta daure mata gashinta da ribbons, sae
murmushi take tana kallon Ikram cike da
sha'awa, Ikram kam duk hnklinta na gun taje
gurin Aliyu kar ya tafi ya bar ta, suna saukowa
kuwa tayi gunsa da gudu a dinnin yana break, ya
ajiye cup din hannunsa ya wara manyan idonsa
yace "waw my Ikram" ta shiga masa juye juye
tace "nayi kyau?" jawota yyi yana kallon
kyakkyawan fuskarta ya daura lips dinsa kan
goshinta, cikin tsawa Mami[truncated by WhatsApp]

[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar
23.....
Mami ta kalli Ikram tace "ae kin iya karatu ssae ko Ikram?" Ikram
tace "eh mana, kije ki tambayi Ammina ma, amma fa ni baxan yi
karatu ba a nn" principal din ta mike ta kama hannun Ikram tace
ma Mami tana xuwa suka fita, ba a dau lkci ba Principal din ta
shigo office din ta ci gaba da fadi ma mami ynda tsarin
makarantar yake, Mami na duba list din textbooks din da ta bata
wata teacher ta shigo da Ikram dake xumbure xumbure, principal
din tace "is she qualify 2 b in basic six" teachern tace "not at ol, i
wil advise dat she shuld...." da sauri Mami ta katse ta ta hanyar
cewa "dnt wrry, dats nt a prblm 4now, plss let her b in class six, i
wil get her a lesson teacher 2 make her catch up" principal din
tace "but yhu knw they wil b writtin their common entrance next
term" Mami tace "i knw Ma, just let her b in basic six plss nd i
assure yhu dat she wil catch up with others vry soon" da kyar
Mami ta samu ta lallaba principal din ta yrda aka bar Ikram a basic
six din, nan take Mami ta biya kudin sch fee da sauran abubuwa
gaba daya ya kama kusan dubu dari biyu, da yake tasan
Makarantar mae tsada ce ssae kudi enuf ta fito da, ta ba principal
hkuri kan baxata iya xuwa banki ba office xata ynxu don har ta
rubuta mata teller taje ta biya, nan aka ba Ikram uniforms har uku
da sport wears biyu, sae excercise books da text buks dinta daga
bookshop din sch din, sae da Mami ta tabbatar bbu abinda ya rage
komai ta siya ma Ikram don gobe tace masu xata fara xuwa, snn ta
masu gdya ta kama hannun Ikram suka fita xuwa gun mota, Ikram
tace "wnn Malamar tsoro take bani ni bana sonta naga tana da
katuwar bulala, kuma ni ina tsoron shi" Mami tace "ae idan baki yi
abun duka ba baxata doke ki ba Ikram, amma kina son Makarantar
ko?" Ikram tace "A'a ni bna son makarantar, lilon Makarantar kawae
nake so" Mami bata ce kmai ba ta bude mata mota ta shiga snn ita
ma ta xaga ta shiga, ta ciro wayrta ta kira Mai gadi ko Jummai ta
dawo, yace bata dawo ba, kasuwa ta shiga da Ikram tayi mata
siyayya na takalman makaranta da jakunkuna da safa, snn ta karo
mata kayan sawa ssae, suka kama hanyar gida don bata son xuwa
office da ita. A bangaren Ammi kam ba karamin tashin hankali ta
shiga ba da suka gano abinda Kawu na lado da Shatu suka yi, kuka
ssae ta dinga yi kmr ranta xae fita, Abban ikram kam tagumi yyi
yana kallon yayan nasa, Na lado yace "kun wani sa ni gaba daga
mai kuka sae mai tagumi, ko ban isa da Rabi bane," Ammi kasa
cewa komai tayi sae kuka take tana kallon Mai gidan nata, a
sanyaye Abban Ikram yace "A'a ba wae baka isa da Ikram bane
yaya, amma fa mutanen nn ba saninsu muka yi ba da inda suka
kae Ikram, ynxu yaya bamu san halin da yarinyar nn ke ciki ba......"
tsawa Na lado ya daka masa yace "ohh munafukar matar taka ce
ta kitsa maka abinda xaka fada min ko, to sayar da Ikram nayi
karewarta knn, kuma ku tashi ku ban waje" kuka ssae Ammi ta
fashe da tace "wllh wllh Na lado ka fito min da ya ta kar in kai ka
kara police station," Shatu ta leko tace "gidan yari xaki kaisa ba
police station ba karewarta knn, yo idan bnda tsiya meye abun
damuwa don mun raba ki da masifa, ke fa da kanki kinsha fadin da
da ynda xaki yi da yarinyar nn da kin yi, to ynxu ga shi Allah ya
kawo ynda xa ayi da ita, har ma xa a dinga baku kudi duk wata"
Ammi ta mike tana huci tace "to mu xuba da ku wllh sae kun fito
min da ya ta mugaye kawae axxalumai mara su tsoron Allah,
meyasa baku dauki shafa kun basu ba, ae wllh bbu ubanda xae
hanani daure ku" tsawa Abba ya daka mata yace "kina da hankali
kuwa Aisha shi yayan nawa kike fada ma mgna hka" tayi masa
wani mugun kallo tace "xa ko kasan bnda hankali yau," tana kai wa
nn ta fice, Abba ya dinga kiranta ko juyowa bata yi ba, na lado yace
"to kai ma tashi ka ban waje munafuki kawae, sae kace ba kai ka
tsara mata abinda xata fada ba, Rabi ce dae na bada ta birni duk
sati xa a dinga kawo maku ita ku gani" Mikewa Abba yyi a sanyaye
ya fice daga gidan. Karfe shidda na yamma Shatu na xaune tsakar
gida tana kulla kuka, Yakumbo da Ammi da wasu yan sanda uku
suka shigo gidan, mikewa Shatu tayi tana salati ta shiga kwala ma
Na lado dake bayi kira "Malam, Malam fito" ya fito rike da yar
butarsa yana cewa "ni fa ban son kira hka kmr wata tsohuwar
makauniya" sororo ya tsaya kallon yan sandan, Yakumbo na nuna
su tace "su ne wa innan, maxa ku kame shegu barayi" Na lado yyi
kofar gida da gudu wani dan sanda ya chafke shi, yan sandan suka
ja shi suka fita hka ma Shatu da sae xaxxare ido take. Ikram na
xaune gaban Makeken plasman dake falo tana kallon cartoon da
duk hankalinta, Mami ta sauko kasa tare da Khaleel da fuskarsa ke
daure ya nufa dinnin, Kashe TV Mami tayi tce "karatu xa kiyi Ikram
gobe xa ki sch" Ikram ta xumburo baki kmr xata yi kuka tace "ni
Anty ki kunna min" Mami ta dagota tace "bari to ki gama karatun
kinji dota" textbuks din hannunta da excercise buk ta ajiye kan
Kujera tana kallon Khaleel tace "son idan ka gama gashi kayi
assistin dinta don Allah ya[truncated by WhatsApp]
[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 25.... Washegari da asuba Mami ta gama shirya Ikram cikin kayan makarantarta, ba karamin kyau Ikram tayi ba cikin dark nd light pink uniform dinta, na cikin light, pinafo din dark, sae ddi take ji ta kasa barin gaban madubi bayan Mami ta gama parkin din mata dogon gashinta da ribbon, tana tsaye gaban mirror har lkcn Mami ta shigo dakin rike da breakfst dinta bayan ta ajiye na Khaleel a dinnin, Mami tace "maxa ki cinye kafin in fito Ikram" kai kawae Ikram ta gyada mata ta xauna gaban break din, Mami ta shiga wanka. Ikram ta mike ta bude kofar a hankali ta fice tayi dakin Khaleel, tsaye ta gansa yana knot din tie dinsa ta washe hakora tace "yaya Khaleel nayi kyau" grin din hakoransa yyi yana mata mugun kallo cikin tsawa yace "get out kar in taka ki, ni kike tambaya kin yi kyau" Ikram ta murguda masa baki tace "shi yasa bana sonka, kuma ko kyau ma baka yi ba, wnn abokin nawa ya fi ka kyau" kanta ya yo ta fice a guje tayi dakin Mami tana kwala mata kira, yyi kwafa ya koma dakinsa, dariya ta dinga yi kmr wata tababbiya bayan ta shigo dakin, tayi mai isarta snn ta fara shan tean ta, ko da Mami ta fito ta gama, Mami ta hade rae tace "me ya fitar da ke? Baki ji ko Ikram" ikram ta dan turo baki bata ce komai ba, Mami tace "dauki kofin nn da plate ki kai kitchen" ba musu ta dauka ta nufi kitchen da su, Khaleel na xaune kan dinnin, ta hararesa ta koma sama da sauri, karfe bakwae da minti goma suka sauko da Mami tana goye da jakar makarantarta, Mami na kallon Khaleel dake xaune dinnin har lkcn tace "ka ba Mai gadi makulli, jummae ta kira ni tana hanya" bae ce mata komae ba har ta isa bakin kofa snn yace "Allah ya kiyaye," tace Ameen snn suka fita, gaban mota ta bude ma Ikram snn ta xaga ta shiga driver seat ta tada motar tayi warm dinsa suka bar gidan, har cikin makaranta ta shiga da Ikram ta hada ta da dari biyar kudin break nn da nn Ikram ta hade rae xata yi kuka wae ita baxata xauna ba, Mami tace "anjima kadan xan xo in dauke ki dota," a hka ta samu suka rabu ta kama hanyar office. Ammi na xaune tsakar gida ta rafka uban tagumi sae kallon Abba da yasa ta gaba sae masifa yake mata, wae suje su sa a saki yayansa da matarsa da suka daure da ita da yayarta, sae da Ammi ta bari ya gama snn ta mike tsaye tana masa mugun kallo tace "su fara fito min da ya ta tukun, ae ko rance xanyi sae nayi naga karshen wa ennan mutanen wllh" a fusace Abba yace "kina da hnkli kuwa Aisha yayana ne fa" Ammi tace "na fi ka sanin wnn" tana fadin hka ta shige daki hawaye cike idonta don ba karamin kewar Ikram dinta take ba ko wani hali take ciki ynxu oho, su Na lado kuwa ana can station ana shan axaba, gashi bae karbi nmbr Mami ba kuma bae san gidanta ba da tuni ya fdi inda ikram take da wnn axaban da yake ci hannun yan sanda. Karfe hudu da minti goma sch bus ya ajiye Ikram a kofar gidan Mami, rana daya a sch duk ta rame ta ci kuka har ta gaji kmr warce bata taba xama a sch ba, ko dayake can gida karfe daya suke tashi daga sch, sae da teacher ta tabbatar Ikram ta shiga gida snn motar tayi gaba, Ikram ta karasa bakin kofar shiga gidan da gudu tana kwala ma Anty kira cikin kuka, Jummai ce ta fito tace "sannu da xuwa yarinya" Ikram ta shige gidan ba tare da ta kalleta ba ta haura sama da gudu sae dakin Mami amma taga ba kowa, saukowa tayi tana kuka tana kallon jummai tace "ina Anty" Jummai tace "tana nn xuwa yarinya xo kiyi wanka kici abinci kafin ta dawo" Ikram ta fasa ihu tana tsalle tana kiran Anty, da kyar da kyar jummai ta lallabata ta cire uniform tayi wanka snn ta bata abinci ta ci, tana ci kuwa tayi bacci nan kan kujera a falon, karfe biyar Aliyu ya shigo gidan sanye da kananan kaya, suka gaisa da jummai dake faman girki a kitchen snn yyi gun Ikram, a hankali ya durkusa gabanta yana kallon fuskarta, hannu yasa ya shafi fuskar ya kira sunanta murya can kasa ta bude idon da sauri, mikewa tayi ta xauna tana mitsike ido tace "ni kaina ciwo yake min" ya kamo hannunta yace "da gske, Ikram ta gyada masa kai" yace "kinci abinci?" ta gyada masa kai nn ma ya mike da sauri ya haura sama ya shiga dakin Mami sae gashi ya sauko da magani ya dauko mata ruwa a kitchen, ba musu ta karba ta sha tana yamutse fuska, yace "ya sch Ikram" ta bata fuska tace "ni baxan sake xuwa ba wllh bna son makarantar" shiru yyi yana kallonta, shigowar mota da yaji yasa ya mike da sauri ya leka yaga motar Khaleel ne, ya dawo ya xauna yana kallonta yace "sbda me Ikram" kmr xata yi kuka tace "malamar muguwa ce wllh" dariya Aliyu yyi yana kallonta, Khaleel ya shigo gidan ba tare da ya kallesu ba ya haura sama, Aliyu ya mike ya dagota yace "xo muje in gaya maki abu" ba musu ta mike da dan gown dinta iya gwiwa, Jummai ta fito da sauri tace "Dr Mami tace kar in bar kowa ya fita da ita wllh" yana murmushi yace "ae ba nisa xa muyi ba kuma Mami sae takwas xaki ganta ta tafi meetn," da dan damuwa tace "to ni dae ka rufa min asiri snn ka bari in canja mata kaya" yace "karki damu" bae kuma jiran me xata ce ba yaja hannun Ikram suka fita daga falon.
[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 26.... Garden din
gidan ya nufa da ita yana rike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login