Showing 15001 words to 18000 words out of 87136 words

Chapter 6 - Ikram Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

500

kudi ya rufe masu ido nd i assume don ba yar su bace yasa suka yi hkn, kuma ko ni aka ma hka baxan ji ddi ba a rabani da 'da na without my knowledge, its beta i take her back 2 her parent, may b sum odza tym" ya daga kai yana kallon Mami yace "to in baki son daukarta ne ni xan dauketa in kai ta gidanmu, don Ikram ba kalar Suleja bace" Mami tace "gidan ku wajen wa?" yace "koma wajen wa" Mami tace "amma nasan ba wajen uwarka ba dae ko" murmushi yyi bae kuma cewa komai ba, ta koma driver seat ta bude ta shiga snn ta tada motar, ganin hanyar gidansu Ikram ta kama yasa Aliyu yace "plss Mami, don Allah ki tafi da Ikram, wllh nasan iyayenta xasu ji ddi daga baya, ynxu kina komawa da ita gida baxa su kuma baki ita ba, but kinga ko da kwana uku tayi gun ki kika kawota taga iyayenta xasu ji ddi ae" da kyar Aliyu yyi convincin din Mami suka kama hanyar Abuja don da gida tayi niyyar maida ikram. Shidda saura suka isa gidan Mami, tana gama parkn Aliyu ya bude motar suka fito da Ikram, Ikram ta jawosa tana yafitosa alamar tana son masa magana ya duka ta shiga masa magana a hankali a kunnensa, Mami dae sae kallonsu take, Aliyu yyi mata murmushi ya gyada mata kai, tana kallon Mami kmr xata yi kuka tace "kice wllh baxa ki yanka ni ba" Mami tayi murmushi ba tare da ta shirya ba, ta dafa ta a hankali tace "sbda ina sonki yasa na dauko ki dota" tana fadin hka ta kuma yi mata murmushi snn ta kama hannunta suka shiga gidan Aliyu na biye da su a baya, sama Mami ta haura da ita ta bude mata dakinta ta shiga bathroom ta hada mata ruwan wanka snn ta fito ta tarda ta tsaye gaban madubi duk ta birkice kayan make up din dake wajen, Mami ta kamo hannunta ta shiga da ita bayi tace maxa ga ruwa nn kiyi wanka ki daura towel ki fito, kuma kar ki taba komai sae soso da sabulu kawae kina ji na, Ikram ta gyada mata kai snn Mami ta fita ta dauki Atm card ta sauko falo, Aliyu ya fito daga kitchen knn ta mika masa tace "kananan kaya xaka fita ka siyo mata don Allah," bae yi musu ba ya karba yace "ok, don Allah Mami ki min cous cous kafin in dawo" tace "in kaje gida nasan baxa ka rasa ba ni kam a gajiye nake" tana kai wa nn ta haura sama, ya girgixa kai ya fice daga falon. Ikram ta fito daga wankan daure da towel amma bata ga Mami a dakin ba, gaban Madubi ta xauna ta dauko wani shower gel ta shiga shafawa, jin budewar gate da shigowar mota gidan yasa tayi gun window da gudu tana lekan ko meye wnn, tana ganin mota ne ya shigo ta bude kofa ta sauka falo da gudu tayi bakin kofar, kasa bude kofar tayi sae turasa take da karfi ita dae taje taga motar, taji an bude kofar ta dan koma baya da sauri, Khaleel ne ya shigo yana danna wayarsa sanye da suit ga briefcase a dayan hannunsa duk da daga aiki yake amma kmr lkcn yyi shirin don yyi kyau har ya gaji, bae lura da ita ba ya shigo falon tare da kullo kofar ya dan tsaya ya gama danne dannensa snn ya mayar da wayar cikin aljihunsa, Ikram dae na tsaye gefensa rike da dan farin tawul dinta sae kallonsa take baki bude xae ci gaba da tafiya tace "kai!" juyawa yyi da sauri tare da komawa baya yana kallonta, bae san lkcn da ya saki briefcase din hannunsa tare da sakin wata yar kara ba yana kiran "mami" ba karamin tsorata Ikram tayi ba ita ma ta fasa Ihu a tsorace tana kwala ma Anty kira ita ma.
Like · 1 · Reply · Report · 4 minutes ago

[2/25, 08:17] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar. 18..... Da sauri Mami ta fito
daga kitchen tana tambayarsu me ya faru, shi kam Khaleel
hanyar stairs yyi da sauri bayan ya dauki briefcase dinsa, Ikram
ta bi sa da gudu ta fixgo hannunsa tana hararansa tace
"meyasa xaka bani tsoro kai" Mami ta karasa stairs din tana
kallon Khaleel tace "magana nake son kuma kana wucewa" ya
fixge hannunsa daga rikon da Ikram tayi masa yana mata
mugun kallo yace "xan take kanki ne" ta xaro manyan idonta
tayi gun Mami da sauri tace "Mami kina jinsa ko, wae xae taka
min kai, wllh kai ma sae na taka maka naka" Kwafa yyi ya
haura sama, Mami na kallon Ikram tace "me ya sauko da ke?"
Ikram ta wara ido tace "ji nayi wani abu yyi wani irin kara sae
na sauko da gudu in gani" Mami ta kamo hannun Ikram tace
"kar ki kuma saukowa falon nn idan bani na sauko dake ba"
ikram kmr xata yi kuka tace "sbda me" Mami bata tanka ta ba
suka haura sama ta shiga dakinta da ita, sae da Mami tasa ta
je ta sake wanka don jikinta duk yaukin shower gel yake, Mami
ta shafa mata mai bayan ta fito snn ta bata wani riga da
wando ta sa, Ikram tace "to ina wnn abokin nawa yake ban
gansa ba" Mami tace "ki jira ni in dauko maki abinci" tana kai
wa nn ta fice, Ikram ta dinga bin dakin da kallo, a hankali ta
bude kofar dakin ta tsaya daga bakin kofar tana kare ma
corridors din dakin kallo, kofofi sun fi biyar ta gani, ta fito ta
shiga bude duka kofofin bbu wanda bata ga makeken gado ciki
da tv ba, kofar dakin dake kallon na Mami ta bude suka yi ido
hudu da Khaleel yana goge kansa da towel da alamar daga
wanka ya fito, bude baki yyi da mamaki yana kallonta cikin
tsawa yace "ohh my God, Mami wae wacece wnn 4 Heaven
sake" ko kallonsa Ikram bata yi ba ta gama kalle kallenta ta
juya xata wuce sae ga Mami, Mami ta hade rae tace "me ya
fito dake Ikram, ba ki jin magana ko?" Ikram ta daga hannunta
sama tace "wllh ina ji Anty, kawae fa don ina kallon ko ina
shine xae dinga ihu yana kiranki" cikin damuwa Khaleel yace
"don Allah ki gaya min wacece wnn Mami, me take xuwa yi a
nn" Ikram tace "sunana Rabi'a, amma Ammi da Abba da yan
anguwarmu suna kirana Ikram, Ammi tace min kawu Na lado
ne yace a...." janta Mami tayi suka fice daga dakin ta kullo
masa kofa tana kallon Ikram tace "idan ina gaya maki magana
baki ji Ikram wllh xa mu bata" ikram ta xumburo baki Mami ta
bude dakinta ta turata ciki tace "kar ki sake fitowa" Ikram bata
ce komai ba Mami ta jawo kofar ta koma kitchen, bude kofar
Ikram ta kuma yi tace "to ae ban gama gaya masa sunana ba"
ta murguda baki tayi hanyar dakinsa kuma ta bude kofar, wnn
karan jallabiya yake sa wa, kasa karasa xura jallabiyan yyi,
Ikram tace "kawu na lado ne yace wae a sa min Rabia wae
sunan kanwarsa ce kuma....." fixgota yyi a fusace ya kulle
kofar dakin da makulli.
[2/25, 08:17] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 19...... Ikram ta buge hannunsa cikin tsiwa tace "meye kke wani rufe kofa" shaqeta yyi yana mata wani mugun kallo yace "me ke kawo ki gidanmu?" Ikram ta fasa wani shegen Ihu tana kwala ma Anty kira, dai dai lkcn da Aliyu da Mami suka hauro sama, Aliyu yyi kofar Khaleel da sauri don har lkcin ihun take da duk karfinta, bubbuga kofar ya shiga yi yana kiransa jin kofar a rufe, ita kanta Mami duk ta rude, khaleel ya bude kofar yana hararan Aliyu yace "lfya kke neman cire min kofa" Aliyu bae bi ta kansa ba yyi gun Ikram dake tsaye har lkcn ta dage sae kakalo ihu take, durkusawa yyi gabanta a rude yake cewa "me yyi maki Ikram" Mami ma ta karaso cikin dakin da sauri tana kallon Ikram tana jiran jin me xata ce, washe hakora Ikram tayi ganin indomie hannun Mami tace "lah Anty wnn na waye" Aliyu ya fixgota ganin gun Mami ta nufa da saurinta, cikin tsawa yace "baxa ki gaya min ihun me kike ba" ta murguda masa baki ta fixge hannunta tace "kai! Kyaleni" tana fadin hka tayi gun Mami tana kallon Indomin tace "Ammina tana dafa min irin wnn amma guda daya kuma bana koshi" Aliyu ya mike ya shake Khaleel a fusace yace "uban me yasa ka rufe kofa, kuma ihun me Ikram ke yi" Khaleel ya shaqesa shima a fusace yace "ubanka yasa na rufe kofar, ci ka ni kar nayi loosin temper na" Ikram ta yo waje da ido ta ja hannun Mami dake tsaye tana kallonsu tace "Anty mu tafi ki ban indomiena fada xa suyi" Mami ta ajiye indomien hannunta gaban Madubi tana kallon Khaleel fuskarta a daure tace "cika sa Khaleel kar in saba maka" turasa Khaleel yyi, yyi kofa yana huci Mami tace "dawo nn" dawowa yyi ya tsaya kansa a kasa yana huci, Ikram tayi sum sum ta karasa gaban Madubin ta dauki indomin a hankali ta fice. Aliyu yyi kofa xae fita Mami ta kirasa shima, ba tare da ya juya ya kalleta ba yace "gida xan wuce" yana kai wa nn yyi gaba. Mami tace "to Allah ya kiyaye" ta maida dubanta ga Khaleel tace "ihun me Yarinyar nn take Khaleel?" a fusace ya fara magana "haba mum wnn wace yarinya ce xata dinga shigo ma mutane gida tana takurasu, don Allah kice ta tafi, wllh ban son ganinta, Allah idan na sake ganinta xan ji mata ciwo" Mami tace "to don uwarka ka fitar min da ita idan har gidanka ne nn, ka fita harkarta wllh don ina iya saba maka sbda ita, kaji min mara hankali" tana kai wa nn tayi kwafa ta fice daga dakin, ya dafe kansa yana huci tare da fadawa kan gado, dakinta ta shiga bata ga Ikram ba ta sauko kasa, xaune ta ganta da Aliyu yana bata indomie sae xuba take masa ratatata kmr radio, shi kam sae Murmushi yake, Mami tace "me nace maki Ikram" Ikram tace "kika ce kar in kuma fitowa daga dakin ki, ae ynxun nn xan koma bari ya gama bani taliyar akwae xafi," Mami ta danne bacin ranta a nutse tace "tashe ki koma dakin kar in saba maki, Allah idan baki jin maganata Ikram baxa mu shirya ba" Ikram ta bata fuska kmr xata yi kuka tana kallon Aliyu, Aliyu na kallon Mami yace "Mami ki bari ta gama cin abincin mana" Mami tana nuna masa kofa tace "tashi ka tafi gidanku kar ka bata min rae Aliyu, ba gida kace xaka ba" Murmushi yyi bae ce komai ba, ta daga Ikram ta dauki kwanon abincin gabanta ta ja ta suka haura sama, Ikram sae waigawa take tana kallon Aliyu kmr xata yi kuka, suna isa daki Mami tace "kar ki sake barin dakin nn, idan ba hka ba xan dokeki" tana kai wa nn ta fice daga dakin, dakin Khaleel ta koma yana kwance yyi rub da ciki, ta xauna gefensa ta kira sa, ya juya yana kallonta, tayi murmushi cikin lallami tace "kayi hkuri Khaleel, Ikram baxata sake shiga sabgarka ba a gidan nn i assure yhu, Aliyu kuma ka daina biye masa kaji son," bae ce komai ba ta shafa kansa tace "ga abincin ka can na hada maka a dinnin" mikewa yyi ya xauna kmr xae mata kuka yace "to Mami me take yi a gidan nn, wllh ni bana son damuwa tana daga min hnkli dayawa bana ma son ganinta" Mami tayi murmushi tace "kar ka damu baxa ka dinga ganinta ba, ita da xata fara makaranta ma" bata jira me xae ce ba ta fita tana cewa "ka tashi kaje kaci abinci son" bin ta kawae yyi da kallo da mamaki, kai Mami ma dae, ynxu a in ta samo wnn abun tsoron, don Ikram abun tsoro ce a wajensa. Mami na komawa daki ta ga Ikram tsaye jikin kofa tana kuka a hankali har da shessheka ga indomin can taki ci, da mamaki Mami tace "Ikram me ya same ki?" tana wasa da rigarta a hnkli tace "ni gurin Ammina xan tafi" Mami ta jawo ta jikinta da mamaki tace "Ikram nan ma ae gidanku" wani ihu mai ban tsoro Ikram ta sakar mata ta fada kasa ta shiga birgima da shure shure tana cewa it gurin Amminta xa ta, Mami kasa rufe baki tayi don mmki sae kallonta take, dagota tayi ta shiga lallashinta amma kmr tana tunxurata duk ta cika gida da Ihu, hankalin Mami ya tashi, ta dauko wayarta da sauri ta shiga kiran Aliyu,Mami na xaune kusa da ita ta xuba tagumi sae kallon haukan da take takeyi Aliyu ya shigo dakin, jallabiya ce jikinsa yyi gunta da sauri ya dagota yace "me ya sameki Ikram" cikin kuka tace "gurin Ammina xan tafi dare yyi" rungumeta yyi yace to fara min shiru tukunna, ba shiri tayi tsit.
[2/25, 08:17] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 20..... Aliyu ya dago kanta a hankali yace "Ikram" ta daga idanuwanta tana kallonsa yace "kukan me kike yi" tace "gurin Ammi xan tafi dare yyi" ya juya yana kallon Mami dake kallonsu snn yyi murmushi yace "to gobe xan kai ki, kinga nan ba a fita da daddare" ta turasa kmr xata yi kuka tace "wllh ka kai ni wajen Ammina ni baxan xauna a nn ba" da harshen turanci Mami tace "Aliyu bari in kai ta gida kawae tun kan dare yyi nisa ta tona min asiri" Mikewa Aliyu yyi ya daka mata tsawa ba shiri tayi tsit a tsorace, yana hararanta yace "na sake jin bakin ki sae na yanke shi, ke jaririya ce da xaki dinga yi ma mutane ihu" Mami tace "A'a bae kai ga hka ba Aliyu daina mata ihu bari in maida ta kawae" Ikram ta mike tayi gun Mami tana ci gaba da kukanta tace "ni bana sonka kuma, kar ka sake xuwa kusa dani" ta karashe mgnr tana murguda masa baki, juyawa yyi ya fice, Mami ta rungumota tace "wajen Amminki xaki ko dota" Ikram ta gyada mata kai, Mami tace "to karki sake kukan xan kai ki kin ji" nn ma ta gyada mata kai snn taje ta dauko indominta ta xauna kusa da ita ta ci gaba da ci, fridge Mami ta bude ta dauko mta juice ta bude ta xuba mata a kofi, snn tace "maxa ki gama cin abincin ki ina xuwa kin ji" Ikram ta kuma gyada mata kai snn Mami ta fita, falo ta sauka gun khaleel ta ga ko ya ci abincin, ta gansa xaune yana kallon American film, ta ce "kaci abinci son" Khaleel yace "na ci" tace "Aliyu ya tafi ne?" bae ce komai ba sae ga Aliyu ya shigo rike da ledan Ayaba, Mami tace "na ma yi xaton wucewa kayi" yace "ban tafi ba, snn ya karaso cikin falon ya xauna" kwanukan da Khaleel ya ci abinci Mami ta kwashe a dinnin tayi kitchen da su, Aliyu ya faki idonta yyi hanyar stairs, khaleel ya bi sa da kallo har ya haura snn ya tabe baki ya ci gaba da kallonsa, bae tarar da Ikram a dakin ba, sae karar saukan ruwa da ya dinga ji a bayi, yace "Ikram" a dan tsorace tace "ehh, gani nn" yyi hanyar bathroom din da sauri ya ganta tsaye karkashin shower duk tayi jagab, tace "kaga fa wanke hannuna na xo yi kawae sae wnn ruwan ya fara xuba a jiki na kuma Anty Ihu xata min ynxu" ya janyota yace "ba ki jin magana ikram" ta xumburo baki tace "to ni ce" mika mata towel yyi yace "cire kayan ki daura" tace "to fita" juyawa yyi da sauri ya fice tare da cewa "na fita" ta cire kayan ta fito daure da towel ya dauko mata daya daga cikin kayan da ya siyo mata ya bata ta sa, tana ganin Ayaba ta shiga tsallen murna, yace "to xo muje falo ki ci" tana rike da ayabarta suka sauko falo, Mami na kitchen tana wanke wanke, Aliyu ya xaunar da ita kan rug shima ya xauna, Khaleel sae kallonsu yake ta gefen ido yana dan buga kafa a tiles, Ikram ta mike tace "ya xa mu xauna a kasa bayan ga kujeru ni saman kujera xan xauna" bata jira me xae ce ba ta haye kan kujera ta xauna ta shiga bare Ayabarta, Mami ta fito daga kitchen tace "me ya sami kayan jikin ki Ikram?" Ikram na nuna Aliyu tace "shine ya canja min" Mami ta juya tana kallon Aliyu da ya bude baki yana kallonta, kan mami tace komai yyi saurin cewa "bathroom fa ta shiga ta kunna shower Mami" Mami bata kuma cewa komai ba ta haura sama, Ikram ta juya tana kallon Khaleel da ya kura ma TV ido duk da ynxu kam ba sanin abinda ake yi yyi ba don duk a takure yake, ta juya tana kallon Aliyu tace "ni kace ma wancan ya tashi ya wuce bana son ya xauna a nn" Aliyu yyi dariya yace "je ki gaya masa" ta mike ta isa kusa da Khaleel tana kallonsa tace "ka tashi ka bar mana wajen mu" daga kai yyi yana kallonta ta murguda masa baki, tace "nace ka tashi" turata yyi da karfi ji kke rigijib a kasa, ta fasa ihu tana kwala ma Anty Kira, ya mike ya tsallaketa xae wuce Aliyu ya sha gabansa yana masa mugun kallo yace "me tayi maka?" Muryar Mami suka ji tana cewa "yau na shiga uku wae wani abu na damunku ne" Aliyu ya turasa da karfi shima, Khaleel yyi kansa a fusace Mami ta daka masa tsawa tace "wuce sama Khaleel," fuu ya wuce sae ga shi ya sauko rike da makullin motarsa yyi hanyar kofar fita. Mami kasa cewa komai tayi har ya fice, karfe goma da rabi Aliyu yace xae wuce gida, Ikram dae nata kallon cartoon kusa da Mami, yyi ma Mami

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login