Showing 12001 words to 15000 words out of 87136 words

Chapter 5 - Ikram Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

506

na isa gidan Yayarta ta xube gabanta tana kuka, yayar tata da ake kira da yakumbo duk ta rikice ganin Ikram ma kukan take, a rude ta shiga tambayarsu lfya, ganin Ammi taki cewa komai sae kukan da take yasa yakumbo ta jawo Ikram ita ma tana hawayen don duk hankalinta ya tashi tace "Rabi'a ki gaya min me ya faru, wani abu ya sami babanki ne" Ikram ta share hawayenta ta girgixa mata kai tace "wae don wata yarinya ta nemi tsokanata na kwabar mata da wara shine Ammi ke ta dukana tana dukana ta kawo ni nn" Ammi ta fixgota a fusace, yakumbo ta kwace ta cikin fada ta fara magana "kan wnn dalilin xaki xo gidana ki daga min hnkli Aisha, hka kawae xata barar da wara ba ayi mata komai ba" Ikram tace "yakumbo wllh ita ta fara tsokanata" Yakumbo ta rungumota tace "yi hkuri Rabi kyale mamarki kinji kawae kiyi xamanki wajena, taje ta tattaro min kayanki ta kawo min nn, kin isheta ne" ikram tace "Yakumbo kuma ban ci abinci ba fa yunwa nke ji" yakumbo ta mike ta xuba mata shinkafa da mai da yajin da tayi Ikram ta dauka ta fita tsakar gida ta ci kayanta ganin ynda Ammi ke ta harararta, yakumbo ma ta mike xata fita Ammi ta ce "wajen ki na xo yakumbo" ta juya tana hararar Ammi tace "to me xan maki duk kin bi kin takura yarinya ki bani ni da Allah bae ba ba kuma kin ki, ae wllh Rabi ta dawo hannuna knn, ki koma gida ki gaya ma Amadun, tunda kun kasa rike guda dayan da Allah ya baku, to ni xan rike maku" cikin kuka Ammi ta shiga yi ma Yakumbo bayanin abinda ya faru, yakumbo ta rude ta shiga salati tana cewa "yau mun shiga uku a ina suka san Ikram din, daga ina suka ce maki suke, wayyo Allahnmu kila ma yan yankan kai ne" yakumbo ta shiga kwada ma Ikram kira da karfi amma shiru, hkn yasa ta fito tsakar gidan da sauri amma sae taga kwanon abincin kadae ne xaune tsakar gidan bayan ta sude shi ta kara gaba, da gudu Yakumbo ta dawo daki a rude tace "Aisha ban ganta tsakar gidan ba" Ammi ta mike da sauri tayi waje ita ma tana salati. Ikram kam tana gama cin abinci ta kama hanyar gida ko xata ga Mami, kila ma Ayaba ta kawo mata Ammi ta dauketa ta kawo ta nn, bbu kowa gidan ta fashe da kuka tana bubbuga kafa, fitowa tayi daga gidan xata koma gidan yakumbo ta tuna yaron Anty dake bata chocolate, tayi gun da suke haduwa da sauri ko xata gansa, ta ko gansa xaune shi kadae yana danna wayarsa, ya mike da sauri ganinta yace "Ikram" ta mika masa hannu tace "xo ka ban wnn abun me ddi" ya kamo hannunta yace "daga ina kike Ikram" tace "gidan yakumbo mana" ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "Ikram Ammin ki baxata bari ki koma gidanmu ba" Ikram ta gyada masa kai ta marairaice tace "kuma ni ina son in je gidanku" ya dan yi shiru snn yace "babanki ma baxae bari ba ko" ikram tace "eh nasan Ammi xata ce masa baxan je ba, amma kasan me" ya girgixa mata kai, tace "ku je gidan kawu na lado ku gaya masa nasan xae bari in bi ku gidan Anty, kasan Ammi tace min Abba najin mgnrsa ssae" da sauri Aliyu yace "ina ne gidan kawun" tace "can da nisa mana" ya ce "to muje ki nuna min mana kanwata" tace "to" yana rike da hannunta tana ta nuna masa hanya har suka isa anguwar, daga nisa ta nuna masa gidan wae bata son shatu ta ganta. Gidan yakumbo ta kae sa daga nn, suna isa tace "kaga nn gidan yakumbo ne, matar tana so na, ni ma kuma ina sonta daxu da Ammina take so ta dokeni a dakinta tayi ma ammina ihu, sae Ammina ta kyaleni, kuma ta girme Ammina, kuma mijinta ya mutu, kuma bata da yara, kuma ita kadae ke xaune a gidan nn, kuma tsohuwace" murmushi kawae yyi yana kallon karamin bakinta mai bayanin, tace "to bani abun nn in wuce" ya durkusa gabanta ya dafa kafadunta a hankali yana kallon cikin idonta xae yi magana sae kuma ya fasa yyi mata murmushi, ita ma murmushin tayi masa hade da washe hakora ya daura yatsansa kan dimple dinta, ita ma ta daura kan nasa, ya daura kan lip dinta ita ma tayi hkn, mikewa tsaye yyi yana dariya yace "bye na tafi, gobe xan kai Mami wajen kawun naki," da sauri tace "to baka ban sweet din nn ba ae" bae yi musu ba ya ciro biyu daga aljihunsa ya mika mata, ta karbe tayi cikin gida a guje, ya dde nn tsaye snn yyi murmushi [truncated by WhatsApp]
[2/25, 08:17] Zjy: [1/6, 4:35 PM] ‪+234 814 616 0714‬: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 15...... Ikram na xaune gaban Yakumbo da daddare bayan sun gama cin abinci tana mata fada ssae kan rashin ji da gantalin da take yi, Ikram sae tabe baki take tana jujjuya kwanon tuwan da ta gama ci, yakumbo tace "dubi fa don tsabar gantalinki da rashin ji Rabi har gida yan yankan kai suka xo nemanki" Ikram ta xaro manyan idanuwanta a tsorace tace "su waye yan yankan kan yakumbo?" Yakumbo tace "ahaf ae wa enan mutanen da suka xo gidanku daxu yan yankan kai ne" Ikram tace "wa ya gaya maki, matar fa na da kirki nasanta kuma har ayaba tana bani kuma ta taba kai ni katon gidansu" Yakumbo na girgixa kai tace "wayyo yarinya, ae daxun nn babanki da na lado suka je gidan suka ga ashe wae yara take dauka ta kai su bayan gidanta ta yanke kansu tayi kudi da shi" Ikram ta matso kusa da ita a tsorace tace "kice wllh yakumbo" Yakumbo tace "au da ke baki sani ba ae shi yasa mamarki ta dauko ki da gudo tana kuka ta taho dake nn," Ikram kmr xata yi kuka tace "wllh kuma ta taba bani ayaba naci, kai na baxae fita ba yakumbo?" yakumbo tace "yo sae dae muyi ta maki addua idan Allah yasa kan xae tsaya" kuka Ikram ta fashe da ta xube jikin yakumbo jikinta na rawa tace "don Allah yakumbo kar kai ne ya cire wllh ina sonsa" yakumbo ta danne dariyarta ta rungumota tace "ae xan ta yi maki addua yau cikin dare idan Allah ya yrda baxae cire ba, Allah ya fita" Ikram bata sake cewa komai ba tayi lamo jikin yakumbo jikinta na rawa tana ta tunane tunanen abinda Mami ta taba bata taci, har bacci ya dauketa, yakumbo ta kwantar da ita tace "ja'ira kawae, ae abinda Aisha ya kamata ta dinga maki knn ta kasa kullum tayi ta jibgarki kmr jaka" fitilar dakin yakumbo ta rage ita ma ta kwanta bayan ta tura masu kofa, ranar dae yakumbo bata yi baccin kirki ba don ihu ikram ta dinga mata cikin dare wae gasu nn xasu cire kanta, da kyar yakumbo ta samu tayi bacci kusan asuba tana to fa mata addua, ko kadan bata yi da ta sanin tsoratata da tayi ba don a ganinta hkn xae sa ta nutsu. Washegari ko ta tashi da xaxxabi ssae, to nn fa hnklin yakumbo ya tashi, ta bata koko ta sha kadan shima da kyar snn ta bata magani ta kwanta, kin fita ko nn da tsakar gida Ikram tayi ranar, yakumbo taji ddi ssae, ashe dae akwae abinda xae sa Ikram ta ki fita ko nn da tsakar gida. Karfe uku na rana Aliyu yyi parkin dae dae kofar gidan kawu na lado kmr ynda yaji Ikram na kiransa, ya juya yana kallon Mami yace "nan ne gidan Mami" Mami tace "to Allah ya dora mu a kansu fita kayi masu sallama, Allah yasa ma yana nn" Aliyu ya fita ya karasa bakin kofar shiga gidan ya fara gyara Murya xae yi sallama sae ga yayar Shafa Hinde ta fito rike da bokitin wara xata talla, ya dan koma baya ita ko tana kallonsa cikin tsiwa tace "malam daga ina" yace "Amm nn ne gidan Kawu na Lado" Hinde tace "to ae babana ne," yace "yana ciki" tace "eh" ya dan yi murmushi ganin ynda take amsa masa yace "to kice ana sallama da shi" ta juya ta koma cikin gidan, Baba shatu tace "kai yau ni naga shegiyar yarinya, uban me ya kuma dawowa dake Hinde, Allah idan wara ta tayi kwante yau sae kin cinye kin biyani kudi na don ubanki," Hinde ta murguda mata baki tace "to wae ba ca aka yi ana sallama da baba a kofar gida ba", Na lado dake xaune rike da radionsa yana cin barbajin awaran da Shatu ta dungure masa gabansa yace "in har ba kudi aka kawo min ba kije kice ma koma wanene ban nn, da me xan ji, da shegiyar talaucin nn ko da sallamar baki" yyi kwafa yaci gaba da cin warar sa, Hinde tace "wani mutumi ne fa yasa shadda me kyau da katuwar mota yaxo nemanka" ya mike tsaye da sauri har yana ball da kwanon gabansa yace "ni kuwa" Hinde tace "wllh" ba ko takalmi kafarsa yyi kofar gida da sauri, Aliyu na ganinsa ya dan dukar da kai yana gaishesa, Na lado da hankalinsa na kan jibgegiyar motar da yake gani kofar gidansa yace "yaro kayi batan hanya ne ko tambaya ka xo yi" Aliyu yace "A'a gun ka muka xo baba" ya fito da tulelen idonsa yace "to shigo yaro Allah dae yasa lfya" Aliyu yace "bani kadae bane ni da Mahaifiyata ce" kawu na lado ya xaro ido yace "a'a to ku shigo mana sannunku da xuwa" Aliyu ya bude ma Mami dake ta kallon Na lado daga cikin motar tana adduar Allah ya daurata a kansa, ta fito tana murmushi suka shiga gidan, Shatu ta mike daga gaban murhun da take da sauri tana gyara bakin xanin dake daure jikinta kmr na me sayar da kuli kuli tace "A'a baki muka yi malam" ko bin ta kanta Na lado bae yi ba ya shimfida masu wata bakar tabarma, Mami ta xauna tana murmushi, Aliyu kam kasa xama yyi da farar shaddarsa, Mami ta galla masa harara ba shiri ya xaune kan bakar tabarman yana kirkiran murmushi.
[2/25, 08:17] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar
16.....
A nutse Mami tayi ma Kawu na lado bayanin abinda ke tafe dasu kmr ynda tayi ma Ammi, na lado yyi tsit yana kallonta, ganin shirun yyi yawa yasa Mami tace "ya kuma naga kayi shiru...." yyi wata shegen dariya yace "to me kuwa xance maki baiwar Allah ae xancen naki ne naji sa wani iri, idan yarinya kike so kije gidan marayu mana, duk yaran garin nn baki ga na dauka ba sae yar kanina," Mami bata kuma cewa komai ba, shi ko sae fama da waran sa yake, Aliyu ma dae kasa cewa komai yyi, can Mami ta mike tace "to malam mun gode ssae" ko kallonsa Aliyu bae yi ba ya fice, Mami ta bi bayansa, da sauri Shatu tace "to wae Hajiya yar aiki kike nema ne? Ga Hinde nn bbu abinda bata iya ba wllh, tun daga kan shara wanke wanke kai har girki" mami ta juya tana kallonta tace "A'a ni ba aiki Ikram xata yi man ba, tsakani da Allah nake son riketa in bata ilimi idan Allah ya yrda" shatu tayi tsaki ta koma cikin dakinta, Mami tayi murmushi ta fita daga gidan, Na lado yyi tsaki yace "hka kawae sun shigo sun katse min cin wara na," shatu ta fito da sauri tana kallonsa tace "to malam don me ma baxa mu ce su dauketa su dinga biyanmu ba, sae dae kuma kar suje su walakanta rayuwarta don yawanci idan yara suka shiga Abujan nn da ciki ko cutar kanjamau suke dawowa, to ma ina ruwan wani don Allah je ka tsayar dasu malam kila karshen talaucinmu ne ya xo...." da sauri Na lado ya mike yyi waje da gudu har Aliyu yyi reverse ya dinga daga masu hannu yana cewa "ku tsaya ku tsaya" Mami ta sauke glass ya karaso da sauri yace "Hajiya idan banda abunki ina kika taba jin anyi hka, kawae ca xakiyi min kina son daukar ikram ta dinga maki aiki kina biyan iyayenta, ba wae kice mu baki ita ba kmr bamu san ciwon haihuwanta ba" Mami tayi shiru tana kallonsa snn ta sauke ajiyar xuciya tace "to in
samu iyayen nata in fada masu hka knn?" yace "A'a ae ba
sae kin je gun su ba kuma, nima nn ubanta ne, sauko mu
koma ciki muyi ciniki" Aliyu ya kauda kansa yana murmushi
hade da girgixa kai, Mami ta fita ta bi sa, suna shiga gidan
na lado yace "to nawa xaki dinga biyan iyayen nata duk
wata" Mami tace "ku dae xaku fada" Shatu tace "ae Ikram
ba baya ba wajen aiki, yarinyar akwae shegen kokari bbu
abinda bata iya ba" Na lado yace "to dae kin ji, duk wata ki
dinga biyan iyayenta dubu ko uku ne" Mami tayi murmushi
tace "to xan dinga baku dubu ashirin duk wata" Shatu da
mijinta suka yo waje da ido a tare hade da cewa "iyyee" Na
lado ya washe hakora yana murxa tafin hannunsa yace
"Allah sarki Hajiya, kmr kuwa kin san talauci yyi ma iyayen
nata katutu" Mami bata ce komai ba ta bude jakarta ta kirgo
dubu ashirin ta mika masa tace "to ka kai ma iyayen nata"
kasa karba Na lado yyi sae kallon kudin yake yana kikkifta
ido, Shatu ta karbe ta saka cikin rigar nononta tace "to bari
in kai masu Hajiya, amma yau xaki tafi da ita ko" Mami tace
"idan sun bani ita" Shatu ta figi mayafi tace "bari ina xuwa
ynxu yanxun nn, ae ya xama dole ki tafi da ita yau kar a
shiga hakkin ki" tana kai wa nn ta fice, kmr xata tashi sama
ta isa gidansu Ikram, Ammi na wanki tsakar gida, tayi
mamakin ganin shatu, shatu na kirkiran murmushi tace
"wanki kike Aisha" Ammi tace "sannu da xuwa maman
Hinde daga ina hka" Shatu tace "wllh daga gida daxu Na
lado ke gaya min abinda ya faru jiya, shine naxo jaje, ina
Ikram din ynxu" Ammi tace "tana can gidan yakumbo tun
jiya wllh" Shatu tace "kai gskya kam gwara ki bar ta can
kawae, to bari in koma Aisha ynxu na gama suyan wara
nace bari in xo dae" Ammi ta rakota har kofar gida tayi
mata gdya snn ta koma ciki, da gudu da gudu Shatu ta isa
gidan yakumbo, yakumbo na bayan gida ta shige dakinta ta
ga Ikram xaune tana ta faman xare tabarma du ta tsiyace
tabarman, Shatu tace "Ikram, maxa xo muje mamarki tace in
kawo ki" Ikram tace "A'a yakumbo tace baxan sake fita ba,
baki san jiya saura kadan kai na ya fita ba" Shatu tace "lah,
in ji wa ya gaya maki kai na fita maxa tashi muje gun
Amminki tana nemanki kinji Ikram" bata jira me Ikram xata
ce ba ta daga ta sama, ta ja ta suka fice daga gidan, Ikram
sae kuka take tana cewa "ni ki kyaleni baxan je ko ina ba"
janta ta dinga yi kmr dabba tana kunduma mata xagi har
suka iso anguwarsu, Aliyu na xaune cikin mota ya hangosu
ya fito da sauri, ikram na ganinsa ta fixge hannunta daga
na shatu tayi gunsa da gudu tana kuka ya durkusa gabanta
ya dafa ta yace "me ya faru Ikram wa ya dokeki" tana kuka
ta nuna masa Shatu tace "ita ce ta dauko ni daga gidan
yakumbo tana son Anty ta yanka min kai" yace "wace
Antyn?" tace "me bani Ayaba mana wnn mamar taka,
Yakumbo tace min kan yara take yankewa a bayan gidanta"
Shatu tace "oho ga ta nn dae mun fita hakkinku mu dae, ae
dama yakumbon nn tsinanniya ce dole ta kitsa maki karya"
ta yi cikin gida tace "to Hajiya gata can kofar gida" Mami
tace "iyayen nata sun yrda knn?" Shatu tace "da gudu ma"
Mami ta mike tayi masu gdya snn tayi masu sallama ta fita,
Shatu da Na lado na biye da ita a baya suma sae gdyan
suke.
2 mins · Khaleesat Haiydar...
[2/25, 08:17] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 17..... Ikram na ganin Mami tayi bayan Kawu na lado da gudu tana cewa "wayyoo don Allah kawu ku boyeni, wllh yakumbo tace min kaina xata yanke, wayyoo Ammina" Shatu ta fixgota tace "kaji min shegiya na lado idan tana yanke kan mutane da bata yanke namu ba," Aliyu ya kamo hannun Ikram ya xaga da ita ta daya side din motar sae bari jikinta yake, ya shiga yi mata magana a hankali a kunnenta, shiru tayi tana kallonsa, ya sakar mata murmushi snn ya share mata hawayen idonta da hannunsa ya bude bayan motar ya sa ta ciki, Shatu ta juya tana kallon Na lado da ya saki baki yana kallonsu, ta dan tabe baki a xuciyarta tace "can dae," snn ta juya ta shige gida tana tattaba kirjinta ko kudin na nn har lkcn, Mami kam kasa motsi daga inda take tayi, don tabbas tasan karya shatu da mijinta suke, ba da ixinin iyayen ikram suka bata ita ba, maganganun da taji Ikram nayi yasa jikinta yyi sanyi, Muryar Na lado ya dawo da ita daga tunanin da take, yace "to Hajiya ni dae nayi ciki, kuma kuyi ku bar kofar gidan nn don naga yan gulma har sun fara fitowa kallo" yana kai wa nn ya juya ya shige gida. Mami ta sauke ajiyar xuciya ta xaga bayan motar ta bude, kanta na kafadarsa tayi lamo yana bude mata chocolate din hannunsa tana kallonsa, da harshin turanci Mami ta shiga yi masa magana "i dis lyk dis undecent behaviour of yhurs Aliyu, wat's dat yhu think u re doin 4 Godsake" bae ko kalleta ba yana kallon Ikram yace "bude bakin kanwata" ta bude kuwa ya saka mata, sanin ba kulata Aliyu xae yi ba yasa cikin nutsuwa ta fara masa magana da turanci kuma, "bana tunanin xan tafi da ita ynxu Aliyu, bari in kai ta gun mamarta kawae, idan Allah yyi xan rike Ikram xan riketa, nasan 4 sure karya wa ennan mutanen suke, son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login