Showing 42001 words to 45000 words out of 87136 words

Chapter 15 - Ikram Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

493

term Break dinta, Mami tayi shiru tana kallonta don ita kam ta rasa me ke damunta, duk ta xama wata silent kmr ba Ikram, Mami bata mata musu ba tace "to bari Khaleel ya dawo ya kai ki, but kinsan kun kusa fara junior waec Ikram ki tafi da buks dinki da xaki karanta a can" Ikram tace "to" snn ta wuce sama Mami ta bita da kallo tana mmkin sauyawanta lkci daya, ikram dae yarinyace bare tace abu tasa a rae. karfe biyar Khaleel ya shigo gidan bayan Mami ta kirasa ya kai Ikram gida, Mami ta hada mata few kayanta da text buks ta sa su a jaka snn ta mika ma Khaleel ya kai cikin mota, juyowa tayi tana kallon Ikram tace "dota ban fa ce ki ba ma Ammi lbrin abinda ya faru ba kar ki kuskura ki ce mata komai kin ji," Ikram ta gyada mata kai snn suka fito xuwa gun mota, Mami ta buda mata front seat ta xauna, Khaleel ya shiga driver sit ya tada motar suka bar gidan Ikram na daga ma Mami hannu, har suka isa suleja be ce mata ba bata ce masa ba. Ya gama parkin karfe shidda dai dai, ta bude motar ta fita ta buda bck seat ta ciro jakar kayanta snn ta juya tana kallonsa tace "bye" ta juya tayi cikin gidansu, binta yyi da kallo har ta shiga snn ya tabe baki ya buda mota ya fito ya shiga gidan shi ma, Ammi na share tsakar gida ta mike tana kallon Ikram da mmki, Ikram tayi murmushi ta rungumeta, dae dae nn khaleel ya shigo gidan, Ikram tayi cikin dakinta da jakarta, ya xauna suka gaisa da Ammi tana tambayarsa Mami da Aliyu, mintinsa goma a gidan yace xae koma, Ammi tayi masa tayin abinci yace "Alhmdllh" tayi masa Allah ya kiyaye hade da gdya snn ya fita daga gidan. Washegari da safe Ikram na xaune tana cin koko da kosan dake gabanta ita da Amminta, Ammi tace "baki da lfya ne Ikram" Ikram ta dago kai da sauri tace "ni Ammi?? Aa ni lfyata qlau, taba jiki na ki ji" Ammi bata ce komai ba ta ci gaba da cin kosan dake gabanta a hankali, abu daya ne Ammi bata ji ddi game da Ikram ba, kuma shine rashin iya aikinta, sam bata iya komai ba, don kasa wanke kwanukan da ta bata tayi, tsakar gida ma sharan hauka tayi masa, bata dae ce mata komai ba amma ta dauki aniyar yi ma Mami mgna ta dinga barinta tana dan aikace aikacen gida tunda mace take kuma aure xata yi, da yamma Ikram na wanke wanken kwanukan da Ammi ta tara mata ta wanke tana xumbure xumbure, Ammi kuma na tankada gari, suka ji ana sallama a bakin xaure, Ammi ce ta mike ta fita dae dae lkcn da ta ci karo da yaron makwabtansu yace "mmn ikram wae ana sallama a waje" kan Mami tace komai suka shigo gidan sun kai su biyar.

2/25, 08:35] Zjy: Khaleesat Haiydar
~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 60...... Mata biyu
da sojoji uku suka shigo gidan matan na yamutse
fuska, duk suka tsaya cirko cirko a bakin xauren
suna kare ma gidan kallo, dae dae lkcn da Abban
Ikram ya fito xae tafi kasuwa don yana daki
dama, Wani Matsiyacin kallo matan ke ma Ammi
da ke tsaye sokoko tana kallonsu, warce ta turo
dankwali gaba tana taunar cingam tace "ke ce
uwar Ikram, wancan kuma ubanta ko?" kasa
cewa komai Ammi tayi sae kallonsu take a dan
tsorace, hka ma Abba dake ta bin sojojin da kallo,
hango Ikram da Hajiya tayi xaune tsakar gidan
yasa tace "Alhmdllh nan ne, to munxo maku
kashedi kan wancan Matsiyaciyar yar taku ce,"
Ammi ta juya da kyar tana kallon mai gidan nata
xuciyarta na bugawa, hajiyar ta ci gaba cikin
gadara tana kallon Ikram tana nuna masu yatsu
uku tace "kwana uku na baku ku aurar da yar
can," tayi wani murmushin mugunta tace "yess
just three dayz idan ba hka ba wllh wllh sae na
daure ku na daure wanda xae tsaya maku gaba
daya har karshen rayuwarku" ta karasa mgnr
cikin tsawa, dayar matar gefenta me taunar
cingam tace "kwana uku kacal, ko ku sha mmki
wllh, don 'dan mu ba sa'ar yar talakawa
matsiyata bne, yafi karfin wancan shegiyar yar
taku, idan yaga tayi aure ae baxae ce xae aureta
ba" suna kai wa nn hajiya ta juya suka fice daga
gidan sojojin suka rufa masu baya, hawaye ne ya
shiga bin kuncin Ammi kmr famfo, taji kafarta ya
kasa daukarta, to su waye kuma wnn, juyawa
tayi tana kallon Mai gidanta taga wani mugun
kallon da yake mata yana buga kafa, kuka ta
fashe da ta juya tana kallon Ikram, hawaye ta
gani ita ma kwance a fuskarta, ta dawo kusa da
ita ta xauna da kyar tana kallonta tace "su waye
wa ennan Ikram?" a hankali Ikram tace "ita ce
momyn Aliyu" da mmki Ammi tace "momyn Aliyu
kuma, dama ba Mami bace mamarsa" kai kawae
Ikram ta gyada mata, a rude Ammi ta shiga cewa
"na shiga uku to me ya hadaku da Aliyun Ikram"
muryar Abba taji yana cewa "kin dae kusa shiga
uku Aisha baki shiga ba tukun, Alhmdllh dama irin
wnn ranar nake jira, ba ke me kunnan kashi da
shegen kwadayi da son abun duniya ba, to yau ga
daya daga abinda nake gudu nake kuma tsoro ya
faru kuma a kanki xae kare bani ba wllh" mikewa
Ammi tayi da sauri tana kuka ssae tace "ynxu ni
xaka kira me son abun duniya malam, ka min
adalci knn" Abba yyi mata mugun kallo yace "an
kira ki din karya nayi, ba ke karatu kike son yar ki
tayi ba baki son tayi aure, kika tashi kika dauke
min ya ta kika damka ma wasu can kuma kika
boye min har na tsawon wata daya to gashi yau
tayi karatun har ta gama, to Alhmdllh kuma wllh
wllh nn da kwana ukun da suka ce xan aurar da
ita, ae ni abun farin ciki na ma ne wnn Allah ya
dawo mun da 'ya ta lfya, aure kuma kmr na aurar
da ita ne ynxun nn, bari ma inje in samu yaya
dama shekaranjiya jiyan nn ya gama min mgnan
ta, ae ni wnn ba wani abu bne a waje na" bae jira
me Ammi xata ce ba ya saka takalminsa ya fice
daga gidan kmr xae tashi sama, xubewa Ammi
tayi gun tana kuka ssae, Ikram ta hade kanta da
gwiwa ita ma tana rera kukan a hankali aka rasa
me lallashin wani.
1 hr · Khaleesat Haiydar...
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 61...... Ikram na xaune
dakinta da yamma rike da literature book dinta bayan
ta gaji da kukan da take tun safe taji an bude kofar
xaure, mikewa tayi da sauri tayi waje don ganin waye,
ita kadae ce gidan Ammi ta tafi gun yayarta yakumbo,
karo suka kusan ci da Aliyu, ta koma baya da sauri
tana kallonsa, shi ma kallonta yake, murmushin ta mai
kyau tayi tace "yayana" shima yyi murmushi yace
"kanwata" hannunta ya kama suka karasa tsakar gidan
ya xauna kan tabarmar dake shimfide ya xaunar da ita
gabansa yana kallonta yace "Ammi fa" ta dan yi shiru
snn tace "Ammi ta tafi gidan yakumbo" ya daga kanta
yana kallon idonta da ya rine, da mmki yace "me ya sa
ki kuka Ikram?" Ikram tayi shiru tana kallonsa, hannunta
ya kamo yace "kiyi min mgna mana Ikram" kmr xata yi
kuka tace "momynka ce ta xo gidanmu da safe take
ma Ammina da Abbana Masifa," "innalillahi wa'inna
ilaihi raji'un" abinda ya iya furtawa kadae knn ya dafe
kansa, xuciyarsa na bugawa, to wa ya kawo ta gidansu
Ikram, dago kansa yyi da kyar idonsa yyi jajur yana
kallonta, xae yi magana Ammi ta shigo gidan, tana
ganinsa ta hade rae, Ikram ta mike da sauri tana kallon
Amminta tace "Ammi sannu da dawowa" Ammi bata ce
komai ba tayi cikin kitchen da ledan hannunta, tana
fitowa Aliyu ya gaisheta kansa a kasa, ta amsa bbu
yabo bbu fallasa ta shiga dakinta, Ikram ta juya tana
kallonsa snn ta bi ta cikin dakin a sanyaye, ba ajima ba
ta fito ta dan durkusa kusa da shi a hankali tace
"yayana xan je in yi karatu na a daki" kai kawae ya
gyada mata ya mike yace "kice ma Ammi na tafi" ita
ma ta gyada masa kan snn ya fita daga gidan, juyawa
tayi tana kallon kofar dakin Ammi hawaye cike idonta
ta nufi dakinta tana murguda baki. Da daddaren ranan
suna xaune da Amminta a tsakar gida, Ammi ta rafka
uban tagumi, ita ko sae kallon tuwon gabanta take taki
ci, Abbanta ya shigo tare da Kawu na lado, ko gaisuwar
arxiki ba ayi ba Na lado yace "dama na xo da kaina ne
in gaya maki cewar ni Na lado na yanke shawarar hada
'ya ta Rabi aure da dan wajen abokina Dan lami, surajo,
kuma insha Allahu jibi asabar xa a daura auren" yana
kai wa nn ya juya ya fice, Abba ya bi bayansa don
rakasa, kuka Ikram ta fashe da kmr warce tasan meye
aure, Ammi kam bata ce komai ba sae hawaye take
don tasan bbu abinda xata ce a nn da xae shigesu,
Ikram ta mike tana rusa kuka kmr xata tsaga gidan
tana cewa "wllh ni bana son surajo, ni baxan aura kowa
ba sae yayana, ni yayana nake so" Ammi ta dago tana
share hawayenta tace "waye yayanki" cikin kuka tace
"yaya Aliyu mana, ni shi kadae xan aura bana son
kowa, baxan aura kowa ba" Ammi ta fixgota a fusace
tace "to don ubanki ki bisa ki auresa mana, shegiya
kawae, ke har kinsan wanda xaki aura ko" har karfe
sha biyun dare Ikram bata bar kukan da take ita kadae
a daki ba duk da dukan fitar hankalin da Ammi tayi
mata. Da safe idonta duk ya kumbura lebbanta yyi jajur,
alwala kawae ta fito yi ta koma daki, bata kuma fitowa
ba har rana ta fito, Abba bae bi ta kanta ba ya fice
xuwa gun kasuwancinsa don shi har Allah Allah yake
gobe yyi ya aurar da Ikram ya huta, karfe tara Ammi ta
tura mata break fst dinta nn bakin kofa ba tare da ta
ce ta dauka ba tayi gaba, bata ko kalli break din ba ta
ci gaba da kukanta daga inda ta tsaya. Karfe sha daya
saura taji muryan Mami tana sallama bakin xaure da
gudu Ikram ta fito daga dakinta tayi gun Mami ta
rungumeta tare da fasa mata ihu, a rude Mami tace
"subhanallahi, me ya same ki Ikram" cikin kuka tace
"ko ba Ammi da Abba ba ne" Mami ta dago fuskarta da
mmki tana kallonta tace "suka maki me" Ammi na
tsaye bakin kofa fuskarta a daure tana kallonsu, Mami
ta daga kai tana kallonta tace "me ya same ta Mmn
Ikram" kasa mata shiru Ammi tayi don tana ganin
mutuncin Mami ssae, Ammi ta dan kirkiro murmushi da
kyar tace "iskancinta ne kawae Hajiya" Mami ta kamo
hannunta suka kara cikin tsakar gidan ta xauna kan
tabarma ta xaunar da ita ta dago kanta tana kallon
kumburarrun idonta, Ammi ta juya a sanyaye xata koma
daki Mami tace "wajen ki naxo mmn Ikram" ba musu
Ammi ta dawo ta xauna ba tare da ta kalli Mami ba,
Mami tace "kuyi hkuri da abunda ya faru mmn Ikram,
duk ni na ja komai...." Ammi ta dakatar da ita da sauri
tace "dama ba ke kika haifa Aliyu ba Hajiya?" Mami ta
dan yi shiru snn tace "ehh bani na haife Aliyu ba,
kawae dae na rikesa ne kuma na taba auren ubansa
shekaru masu yawa da suka wuce don ina gidan aka
haifesa ma, kuma yana da shekaru biyu na bar gidan
duk da karancin shekaransu kuwa ba karamin shakuwa
yyi da ni ba don uwarsa bata da lkcnsa, matar da ta xo
nn jiya ita ce mahaifiyarsa, kuma kishiyata yrs bck,
bamu yi xaman ddi da ita ba kuma ita ce sillar
rabuwata da Mahaifin Aliyu, kuma har muka rabu bamu
samu haihu da shi ba, ina gama idda Allah ya hada ni
da mahaifin Khaleel, shekaranmu daya na haifi Khaleel,
kuma na ci gaba da karatuna na likita don Mahaifin
Aliyu bae barni na ci gaba ba a gidansa, Khaleel na da
shekaru goma sha biyu Mahaifinsa ya rasu ya b[truncated by WhatsApp]
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 62...... Mami tayi shiru na dan lkci snn ta ci gaba "Naji mutuwar mahaifin Khaleel ssae, don Allah ya gani duk iya xamana da shi bamu taba samun matsala ba, mutum ne me saukin kai da kirki ga yawan kyauta, ina gama takaba na koma gun Mahaifiyata da Khaleel, ko kadan yan uwansa basu nuna mana bakin cikin dukiyar da ya mutu ya bar ma Khaleel ko kuma ince ya bar mana me yawa ba don kowa na da nasa, duk family dinsu bbu me karamin karfi, mahaifin Aliyu kuwa ina fita da wata biyu dama ya kuma aure abunsa, kuma kusan a tare muka haihu da amaryar tasa ita ta haifi danta Mujaheed ni kuma Khaleel, makarantar da yaransa maxa ke xuwa na secondary shi Khaleel ma ke xuwa don makaranta ce me kyan gske, lkci daya kwatsan Alhaji ya fara hada sch fees dinsu gaba daya har da na Khaleel ya biya, ni dae ko sau daya ban taba masa gdya ba kuma ban taba nuna na sani ba ma, ana hka dae ya fara xuwa gidanmu yana nuna min Interest dinsa na son na dawo gidansa a matsayin matarsa kuma, har ga Allah ina sonsa, amma ssae nake tsoron xama da matar nn tasa duk da nasan da sabuwar Amaryar da yyi, amma dama Allah ya rubuta dole sae na kuma komawa gidansa, hka kuwa aka yi, ko kadan matan nasa basa shiri da na shiga gidan, amma sae me ina shiga da wata biyu Hajiya ta hade kai da Aishar suka dawo suna shiri ssae, duk suka sani gaba, in takaice maki lbri wllh a daddafe nayi shekara uku a gidan na haifi Seeyama, nn na bukaci ya sallameni bana auren kuma, to dae na wahala kan ya ban takardata, amma kuma yaki bari in tafi da Khaleel da seeyama, ban masa musu ba na bar masa su, na mayar da hankali na ga aikina duk da nasan Khaleel ba jin ddin Hajiya yake a gidan ba, through out stay din yarana a gidan basu yi rashin uwa ba don Mahaifiyar Mujaheed bata taba canxa masu ba, ita ta rike seeyama tun tana karamarta, kuma har yau Seeyama bata sake dani kmr ynda ta sake da ita ba, mun rabu da Alhaji da yan watanni Aliyu ya dawo wajena duk da ba tare da amincewar Mahaifiyarsa ba, ni na rikesa har ya gama karatunsa na likita, su kuma suka rike Khaleel can, to kinji me ya hadani da Aliyu Mmn Ikram, kinga baxan ce maki ba da na bne, ynxu dae abinda nake so daku kuyi hkuri don Allah, iyayensa ne suka takurasa kan aure kuma yace shi Ikram yake so, shine fa ta xo har nn tayi tijarar da ta saba," Ammi tace "bkm Hajiya, Allah yasa mu dace, amma gobe xa'a daura auren Ikram da wani dan uwanta" Mami tace "ban gane ba" ammi ta dan yi shiru snn ta gaya ma Mami ynda suka yi da Hajiya da kuma hukuncin da Abban Ikram da yayansa suka yanke, Mami ta mike da sauri tace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un, anya matar nn xata ga annabi kuwa," ta koma ta xauna da kyar tace "don Allah mmn Ikram kar ku lalata rayuwar yar ku ku bar ta tayi karatu, wllh bata isa aure ba ynxu, irin wnn auren da ake ma yara ke sa xaka ga yarinya na fama da ciwon yoyon fitsari, gasu nn da yawa muna ganin cases irin hka a hsptl " Ammi ta share hawayen dake bin kuncinta tace "to ya xanyi Hajiya, ni ynxu banda abun cewa a nn, ca fa tayi xata daure mu da wnda xae tsaya mana" Mami tayi murmushin takaici tace "ae tana takama mijinta soja ne, yayanta ma hka, amma kyaleni da ita mmn Ikram xan dawo anjima da yamma" Mami na kai wa nn ta fice da sauri, Ikram ta mike da sauri ta fashe da kuka xata bi ta, Ammi ta fixgota ta rungumeta tana kuka ssae. Mami na isa gida ta kira Khaleel tace ya bar abinda yake ya xo tana nemansa, bae mata musu ba cikin minti sha biyar ya dawo gida, ssae Hankalinsa ya tashi ganin mode din Maminsa, ya xauna yana kallonta cike da damuwa yace "baki da lfya ne Mami?" Mami ta sauke ajiyar xuciya tace "lfyata qlau Khaleel, magana xa muyi ne" ya dawo gefenta ya xauna yace "na me fa Mami, hope lfya?" a hankali Mami ta fara masa mgna ba tare da ta kallesa ba "nasan baka taba min musu ba Khaleel, kuma idan na sa ka abu ko bae maka ddi ba kana respectin dina kayi" Khaleel bae ce komai ba sae kallonta yake, a hankali tace "wnn karan ma baxan so ace ka min musu ba Khaleel" Khaleel ya sunkuyar da kansa bae ce komai ba sae dae gabansa faduwa yake, ganin tayi shiru yasa da kyar yace "me kike son in maki Mami" Mami ta sauke wani ajiyar xuciyar tace "so nake in hada ka aure da Ikram Khaleel......" saukowa kasa yyi da sauri cikin tashin hankali yake girgixa mata kai "no Mami kar ki min hka don kinga bana miki musu Mami plss," nan da nn hawaye ya cika idonsa muryarsa na rawa yace "ki bari plss Mami kar kiyi min hka" Mami tayi shiru tana kallonsa, hawayen dake makale idonsa ya gangaro, ta sauko kasa ta dafa sa tace "y son?" ya daura kansa kan kafadarta cikin rawar murya yace "she is nt meant 4 me, snn ni baxan iya aurenta ba sbda abu biyu, na farko na dauketa a matsayin kanwata na biyu kuma, baxan iya cin amanar brotherna ba, plss Mami karki ce min wnn ba reasons bne consider me" hawaye ssae yake yi, Mami ta shafa kansa tana murmushi tace "ya isa son kar ka sake xubar min da hawayenka, i wont force yhu kuma na gamsu da reasons dinka,"
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 63...... Karfe
daya Mami ta isa gidansu Aliyu, tana gama
parkn ta shiga gidan, bata tar da kowa falon ba
kai tsaye ta xarce xuwa dakin Momy, Momy na
ta goge ita daya a daki, tayi mamakin ganin
Mami da rana, Mami ta xauna kan gado ta cire
mayafin jikinta suka gaisa, momy ta xauna kan
kujera tace daga ina kike hka Hajiya, halan baki
je office ba yau, Mami tace "ehh wllh yau ban
je office ba" Mikewa Momy tayi ta bude

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login