Showing 9001 words to 12000 words out of 87136 words

Chapter 4 - Ikram Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

502

"to
bari ta shirya" ko rufe baki bata yi ba Ikram ta
fito da gudu tace "Allah bbu inda xanje, ni Ammi
baxan je gidansu ba" ta fashe da kuka ta xube
wajen tana birgima, Hinde yayar Shafa ce yar
kawunta na lado, Ammi ta rasa me xata ce don
har ga Allah bata son xuwan yar ta gidan nn,
cutarta suke ba Kawun nata ba ba matarsa da
ya'yansa ba, tasan baban Ikram ne ya basa lbrin
abinda ikram ta gaya masu jiya shine xae ce a
daukota, cikin tsiwa Hinde tace "ni fa sauri nake
Aisha gidan kawata xan tafi" ko kadan yarinyar
bata da respect, Ammi tace "to kije tana xuwa"
Hinde tace "tab, to ai baba ca yyi kafata kafarta"
daki Ammi ta shiga, ta fara hada ma Ikram
kayanta, ikram sae ihu take tana guje guje a
tsakar gidan wae ita baxata bi ta ba, sae da
Ammi ta mammake ta snn ta hankadata waje,
tace ma Hinde ki gaida min mamarki, Hinde tace
to, snn ta fice. Ikram na ihu Hinde na jan ta kmr
rago suka isa gidan Kawunta na lado, da yake
bae da aikin yi yana xaune tsakar gida rike da
dan radiyonsa, Ikram na ganinsa ta nutsu don
mugun tsoransa take, yana kikkifta ido yce "xo
nan don ubanki Amadu" jikinta na rawa ta karaso
ya fixgota ya shiga ja mata kunne da karfi yace
"don uwarki masifa kike son ja mana a gari kike
gantali har Allah ya hada ki da yan yankan kai
jiya cikin ikonsa kuma bae bari suka maki komai
ba" matarsa dake xaune gaban murhu, mai sunan
Ammi suna ce mata Shatu tace "ae malam wllh
da sun fille kan kowa ma ya huta, kuma duk gun
uwarta ta gado gantalin nn" Ikram dae kan ta na
kasa sae guntun hawaye take, Kawu na lado ya
hankadata yace "ae kika ce xaki kawo min iskanci
a nn babbala shegiya xanyi, duk salubabbun
iyayen nn naki ne suka lalata ki, maxa dauki
ledan kayanki ki kai ciki" Ikram ta dauki dan ledan
kayanta tana hawaye tayi dakinsu Shafa ta ajiye,
shatu ta kwalo mata kira ta fito da sauri ta ciro
naira ashirin ta mika mata tana hararanta tace
"maxa ki je gun mai shagon can ki siyo min ajino
moto na goma da magin goma" Ikram ta karbi
kudin ta fita, tayi gun mai shagon, "mai shago a
bani cingam goma da biscuit" ya dauko kuwa ya
bata ta karba, ta juya tana kallon kofar gidan
kawun nata, ta murguda baki tace "kuma baxan
dawo ba" ta saka kai da gudu sae hanyar
gidansu, har ta iso kofar gidansu ta tuna ta dde
bata je gun mai ayaba ba, hkn yasa ta canxa
hanya tayi hanyar kasuwa, dae dae inda suka
rabu da Aliyu jiya ta gansa xaune kan dakali yana
danna wayarsa, ta wara ido tace "lahh! kai! Me
kke yi a nn" ya mike da sauri yana kallonta yyi
murmushi yace "ke nake nema mana" ta fashe da
dariya tace "ae ni gun mai ayaba xani ynxu, sae
na dawo"
[1/7, 8:51 PM] ‪+234 810 188 2232‬: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 11...... Tana gama fadin hka ta fara tafiya, ya riko hannunta da sauri yace "aiken ki mama tayi" ta girgixa masa kai tace "A'a ni dae xan je ne ya bani Ayaba" ta fixge hannunta xata tafi yyi saurin rikota kuma yana kallon dan hawayen dake idonta yace "wa ya doke ki Ikram" Ikram tace "ba Ammi bace tace Hinde ta tafi dani gidansu gun kawu na lado kuma mugu ne shi, shine na gudo abuna" yasa dan yatsa ya share mata hawayen yana kallonta yace "to meyasa tace a kai ki" ta dan tabe baki tace "sbda wae na tafi yawo jiya, kuma ai ba yawo na tafi ba Anty ce ta kai ni gidansu" ta fixge hannunta xata yi gaba ya fixgota yace "ke wae ina xaki ne" tace "A'ah nace maka gun me Ayaba xani ya bani mana" ya ciro da chocolate daga aljihunsa ya mika mata yace "kina son wnn?" ta karbe da sauri tace "ehh ehh ina so" yyi murmushi ya xaunar da ita gefensa yace "to xauna ki sha, da ddi ssae" ta shiga bude chocolate din da sauri ta fara ci, tace "umm ddi" ya gyada mata kai snn yace "to dan tsammin mana" ta sa a baki ta gutsura kadan da hakorinta snn ta fito dashi jagab da miyau ta mika masa, ya galla mata harara yace "bana so, wnn na hannunki nake so" ta murguda masa baki tace "to kar kaso, ni kuma baxan bada ba" xata mayar da wanda ta gutsura masa baki, ya fixge da sauri ya sa a nasa bakin, tace "Allah ya taimake ka yaro" dariya ssae yyi, yana ta kallonta tana cin chocolate tana wani lullumshe ido, har ya kare snn ta bude idon tana kallonsa tace "dadi wllh, ka bani wani mana" xae yi magana ya ga tayi bayansa da gudu ta durkusa ta daura fuskarta kan bayansa ta boye, yace "me ya faru" a hankali tace "mai treda ne na gani, kuma xae iya gaya ma Ammina ya gan ni a nn kasan ya iya gulma" murmushi kawae yyi har mutumin ya wuce su snn ta dawo gefensa ta xauna tace "ka bani wani mana don Allah" yace "baki tambayeni Mami ba" da sauri tace "ina take" yace "gobe xata xo gidanku" Ikram ta yo waje da ido tace "me xata xo tayi" wayarsa yyi ring ya ciro tace "lah kai ma kana da waya," ya daura hannunsa kan lebbenta yace "shiii" shiru tayi ya daga kiran tana ta kallonsa har ya gama, snn ya mayar cikin aljihunsa, ta kamo hannunsa ta dan marairaice tace "don Allah xo ka ban wayar mana" ya xaro ido yace "kai me xaki yi da shi?" tace "nima waya xan dinga yi mana" ya tsura mata ido yana kallonta ta hura masa iska, ya dauke kansa da sauri tace "meye kke kallona hka" ya harareta yace "meye xaki hura min iskan bakin ki a fuskata" ta mike tace "ni dae na tafi gun mai ayaba kafin dare yyi" ya mike shima ya kama hannunta yace "to muje in raka ki" suna tafe tana basa lbrin ynda ta gudo daga gidan kawu na lado sae dariya yake har suka iso kasuwar yana rike da hannunta suka isa gun mai fruit xama tayi niyyar yi abunta tayi masa surutunta kmr ynda ta saba ya bata Ayaban, Aliyu ya basa kudi ya karbi bunch daya ta shiga tsallen jin dadi, ya rankwashi kanta yace "to ca aka yi maki naki ne" ta fixge hannunta kmr xata yi kuka tayi gun mai ayaban dake ta dariya tace "in baka lbri xaka ban Ayaba" fixgota Aliyu yyi yace "kin fiye surutu ikram, wasa nake maki naki ne" sae da ya bata ledan ayaban ta rike snn ta yrda nata ne suka kama hanyar gida tana jin ddi, dai dai gun dakalin nn suka tsaya ya durkusa gabanta ya dafa ta yace "xan tafi Ikram, idan Mami ta xo gobe kar ki ce baxa ki bi ta ba kinji kanwata," ikram tace "to," ya ciro chocolate biyu ya mika mata ta karbe tana washe hakora ta juya a guje tayi gida, yana kallonta ta shiga gidan snn ya juya ya bar anguwar. Ikram na shiga gidan cikin xaure ta xauna bayan ta sa sakata a hankali ta shiga cin ayabarta, ta ci yafi biyar amma bata ji ya isheta ba, sallamar shatu taji tana jijjiga kofar xauren da karfi ta labe jikin bango Ammi ta shigo xauren tana cewa "waye hka" a fusace cikin daga murya shatu tace "ki fito ki bani Naira ashirin dina kar nayi maki rashin mutunci a kofar gida yau" Ammi ta bude kofar da mamaki tace "A'a maman Hinde me ya faru hka" Shatu tace "maxa fito min da ashirin dina ki bani" Ammi ta kasa fahimtar me shatu ke nufi, shatu tace "yo wnn barauniyar yar taki ce na ba ashirin ta siyo min magi ta gudu min da kudi, kuma wllh sae na karya mata wuya na kamata" Ammi ta kunce bakin xanin ta ta ciro ashirin din ta mika mata, ta fixge tayi gaba tana huci, Ammi ta kasa barin wajen tace "na shiga uku ni Aisha wnn wacce irin yarinya ce Allah ya bani" a hankali ikram dake labe har lkcn jikin bango ta mike cikin sanda tayi cikin gida da gudu, Ammi ta juya da sauri jin motsi taga bawon Ayaba baje cikin xauren, cikin gida tayi da sauri amma har ta shige daki, Ammi ta tura kofar dakin ta ganta tsaye sae rawa jikinta yake, tana ganin Ammi ta fasa ihu tana cewa "don Allah kiyi hkuri Ammi wllh kudin faduwa yyi shine na gudo gida naga Ayaba a xaure, wayyo Ammi kar ki dokeni don Allah" Ammi ta juya cike da takaici ta bar dakin, sulalewa kasa tayi gabanta na ci gaba da faduwa, tana nn a hka har aka kira Maghrib ta fito da dan butarta tayi alwala ta tarar Ammi ma na alwala a tsakar gidan.
~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 12.....
Washegari da Asuba Ammi ta sa Ikram tayi
shirin makaranta bayan sun yi sllh don Abba
yace shi xae dinga sauke ta a makaranta idan
xa shi gun aikinsa, idan an tashi kuma Ammi
taje ta daukota, tana saka uniform dinta
tace "Ammi ae safiya bae gama yi ba kina son
a sace ni ne a hanya," Ammi ta galla mata
harara tace "ae da xan samu mai sace ki ma
ni da na huta" ikram ta xumburo baki ta
tsallake tean da Ammi ke hadawa taje dauko
safarta da takalmi a dakin Ammi, Ammi ta
daka mata tsawa "wae ke don ubanki wace
irin yarinya ce shi tean kike tsallakewa" kmr
xata yi kuka tace "to kin tare min hanyar" da
gudu ta dawo dakin bayan fitar ta tana cewa
"Ammi ni banga books dina cikin jakata ba"
Ammi tace "to kina ban ajiyar book ne" ta
fasa ihu tare da doka uban tsalle lkci daya
ta kwabar da tean gaban Ammi tana cewa
"wayyoo wllh ni baxan je ba Aunty xata min
duka" Ammi ta mike da sauri tana salati ita
ko tayi waje da gudu, Ammi ta bi ta ta
cafkota ta mammaketa snn ta hada ta da
biredin taci shi hka, shi dae Abba bae ce masu
komai ba, karfe bakwae saura suka fita gida
yana rike da Ikram da bata daina kukan
dukan da Ammi tayi mata ba, har cikin
makaranta ya shiga da ita snn yace da
malamar ko an tashi kar ta bari ta fita
mamarta xata xo daukarta, dariya malamar
tayi don su kansu Ikram ta ishesu a
makarantar. Ammi na kwashe taliyar da ta
dafa ma Ikram na rana kafin taje daukota a
sch, don ikram na son taliya ssae taji ana
sallama a bakin xaure, sae da ta gama xuba
taliyar a kula snn ta shiga da shi daki ta
dauko Hijabi, a tsakar gida ta hadu da kanin
Altine usman, tace "A'a usman daga ina, baka
je makarantar bane yau" yaron yace "mama
tace bani da lfya shi yasa ban je ba, wae
wasu mutane suka ce in ce suna sallama da
ke a waje" da mamaki Ammi tace "mutane
kuma, mata ne ko maxa" yaron yace "mama
guda biyu da mutumi guda daya ne" hankalin
Ammi ya tashi a xuciyarta tace shknn Ikram
ta kuma dauko mata magana kila, yaron ya
juya xae wuce Ammi tayi maxa tace "usman
an tashi daga makaranta ne, su Altine sun
dawo ne?" ya girgixa kai yace "A'a basu dawo
ba kuma ban ga yan makaranta na tafiya ba"
Ammi tace "to je kace masu gani nan xuwa"
yaron ya fita da gudu, Ammi tayi jigum a
tsakar gidan gabanta sae faduwa yake,
ganin bata ma masu jiran nata lkci take yasa
tayi kofar gidan, tsaye Mami take har lkcin
da wata mata da alamar kawarta ce, driver
na xaune cikin motar da suka xo da, Ammi na
ganinsu gabanta yyi mugun faduwa ganin irin
shigar da suka yi, ta dake tace "ina yinin mu"
Mami tayi murmushi tace "har ina tunanin ma
ko masu gidan basa ciki ne" Ammi tace "ina
ciki wllh" Mami tace "to sae dae kuma
maganar da ta kawo mu ba ta tsayuwa bace"
Ammi da gaba daya hankalinta baya jikinta
tace "to ku shigo mana" Mami tace "to
mungode" snn suka bi bayan Ammi suka shiga
gidan, Ammi ta shimfida masu tabarma tsakar
gidan suka xauna, snn ta dauko kujera yar
tsugunno ta xauna tana kallonsu tace "ina
fata dae lfya Hajiya" Mami tayi murmushi
tace "lfya qlau wllh, nima dae ina fatan da
maman Ikram muke mgana" gaban Ammi yace
dass, ta shiga uku maganarta ya tabbata knn
wani maganar kuma ikram ta dauko mata,
Mami ta katse mata tunaninta tace "kin yi
shiru kuma" Ammi tace "ehh ni ce, Allah yasa
ba wani abun tayi maku ba nasan ma baxae
wuce hka ba amma don Allah ku yi hkuri wllh
na gaji da yarinyar ban san ynda xan yi da
ita ba" dariya Mami tayi tace "ko daya wllh,
wata alfarma naxo kuyi min maman Ikram,
babanta na nn ne?" kai kawae Ammi ta sami
kanta da girgixa mata, mami tace "duk da
nasan baki san ni ba amma kisa a ranki ni din
musulma ce kmr ku kuma me tsoran Allah ce"
Ammi tayi shiru tana kallonta da mamaki, to
wace alfarma matar nn ke so daga gareta ita
da ba kowa ba, Mami ta katse mata tunanin
da take cikin nutsuwa tace "Ikram nake son
ku bani na rike don Allah ba don ni ba, kuma
nayi maku alkawari xan rike maku ita amana,
xan kuma bata tarbiyar da ya kamata snn
xata yi karatu ssae, wllh Allah ya dora min
son yara mata kuma sae gashi bae bani ba,
kuyi ma Allah da Annabi ku bani ita na rike
maku ita" tun da mami ta fara magana Ammi
ta saki baki tana kallonta.

Khaleesat Haiydar
~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 13...... Ganin Ammi bata da niyyar cewa komai har lkcn sae kallon Mami take da mamaki yasa Mami tace "kinyi shiru kuma maman Ikram" nan da nan hawaye ya xubo ma Ammi tana sharewa tace "me kuwa xan ce Hajiya, ae maganar taki ce naji ta wani banbarakwae, wae kina nufin yar tawa xan dauka in baki ba dangin iya ba na baba? Kmr warce karan hauka ya cixa, a kan wani dalili? Ca nayi maki neman kai nake da ita koko gajiya nayi da ita, to talaucinmu bae kai mu sayar da yar mu ba, idan 'ya'ya mata kike so kije gidan marayu mana ae sun fi dubu a can, " Murmushi Mami tayi, matar da suke tare tace "Ayya baki fahimcemu bane Maman Ikram..." da sauri Ammi ta katseta ta hanyar cewa "fahimtar me xan maku a nan, don Allah ku tashi ku bar min gidana" Ammi na kai wa nn ta mike hankalinta a tashe ta shiga daki da niyyar shiryawa taje ta dauko Ikram daga sch ko ba a tashi ba, Aminiyar Mami Hajiya Zuwaira tace "na gaya maki Amina, it wil b so hard 2 seperate dem frm dia dota" Ammi na fitowa Mami tace "ki sauraremu Maman ikram ni ban ce sayar min da yar ku xa kuyi ba, wllh taimakonku kawae nake son yi don Allah, in kince kullum na dinga kawo maki Ikram kina gani ma wllh xan dinga kawo maki ita, kuma ba hka kawae xan dauketa mu tafi ba, ae sae da ixinin mahaifinta...." a rude Ammi tace "yau na shiga uku ni Aisha na hadaku da Allah da annabi mutanen nn ku tashi ku tafi ku ban waje" Ammi tayi kofar fita da sauri don xuwa dauko yar ta daga makaranta ta kai ta gidan yayarta kawae, karo suka ci da Ikram da ta shigo a guje, bata bi ta kan Ammi ba tayi dakinta da gudu ba tare da ta lura da su Mami dake tsakar gidan ba ta kulle kofar, yara ne fiye da goma suka shigo gidan kowa da abinda yake fadi, daya a cikinsu nata ta rusa kuka rike da bokitin awarar ta, da kyar Ammi ta iya cewa "me ya faru" cikin kuka yarinyar tace "yarinyar da ta shigo gidan nn ne ta kwabar min da bokitin wara na ya xube cikin kasa yara suka wawashesa don tace in bata wara biyu biyar nace bbu, ynxu iyah dukana xata yi ta fasa min jiki" Ammi ta kasa cewa komai sae bin yaran take da kallo, Muryar Mami taji tana cewa "xo nan yarinya nawa ne warar gaba daya?" yarinyar na share hawayenta tace "ta dari takwas da naira talatin ce, dama na dubu daya aka sa min na sayar da na dari da saba'in" Mami ta bude jakarta ta ciro dubu daya ta mika ma yarinyar tace "maxa ki tafi gida kinji yarinya, kiyi hkuri" kai yarinyar ta gyada mata snn ta juya ta fice sauran yaran na biye da ita a baya, Ammi dake tsaye har lkcin kmr kwai ya fashe mata ta kasa juyowa, don tasan yau da matar nn bata nn da sae dae suyi kashin dubu daya daga ita har ubanta. Ikram ta bude kofa ta leko a hankali don ta tabbatar da muryar warce take ji, da gudu ta fito ta rungumeta tana cewa "lahhh wllh ita ce da gske, ashe ke ce Anty yaushe kika xo gidanmu ina wnn yaron naki dogo" Mami dake murmushi ta dago kanta tana kallon fuskarta tace "haba Ikram, me yasa xaki xubar masu da kayan saidawar su?" Ikram ta xumburo baki tace "to ba ita bace nace ta ban biyu biyar tace min ya kare alhalin ina ganin waran cikin bokitin, shine ni kuma na barar suka xube kasa nace mata meye wnn xaki ce min bbu, kawae sae na gudu suka dinga bina ina ta gudu suna bina har na shigo gida na shige dakina da gudu na kulle kofar, sae naji muryarki na fito kuma ashe kece, to ina wnn yaron naki me kyau" dariya Mami da kawarta ke yi suna kallon Ikram, ikram tace "Anty yau xaki kai ni gidanku ko" Fixgota Ammi tayi tayi waje da ita ta bar su xaune cikin gidan hankalinta a tashe, ikram tace "A'a Ammi ina xaki kai ni ga Anty taxo tafiya dani gidanta, dama tace min xata xo" mari Ammi ta shiga xuba mata ta rufeta da duka kofar gidan, mutane suka yo kansu ana ba Ammi hkuri duk da sun san magana ta dauko don sun ga yan makaranta da yawa sun shiga gidan, Ammi bata bi ta kansu ba ta ja Ikram dake ta rusa kuka suka yi gidan yayarta da ita tana hawaye a hanya.


~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 14...... Ammi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login