Showing 69001 words to 72000 words out of 87136 words

Chapter 24 - Ikram Book 1 Complete Hausa Novel

10 Oct 2025

510

ya nufi sama tana biye da shi a baya, ya bude wani daki ya shiga snn ta shiga, da kansa ya shiga gyara dakin sbda kura, tayi jigum kan kujera tana kallonsa, har ya gama snn ya shiga bathroom yyi alwala ya fito yace taje tayi ita ma xae wuce masallaci, sae da ya fita snn ta shiga tayi ta fito ta tada sllh, tana xaune kan darduma har lkcn ya shigo gidan rike da ledan abinci ya xauna gabanta ya bude ledan yana murmushi yace "look, ur favourite" ta sauke idonta kan fried rice din da ya siyo masu da kaxa, snn ta dauke kanta ya mike ya fita xuwa kitchen don dauko masu plate, da kyar ya lallabata ta ci abincin kadan ganin taki ci yasa shima bae wani ci ba ya xuba mata hollandia Milk shima taki shan na kirki, shiru yyi yana kallonta snn ya mike yace "xan tafi masallaci" bata ce masa komai ba ya fita sllhn isha, yana fita ya ciro wayarsa ya kira Maryam tana dagawa yace "hello Maryam, am vry srry baxan samu dawowa yau ba sae gobe da safe, na je dauko Ikram ne gidansu, ae na gaya maki, idan baxa ki iya kwana ke daya ba kya iya kiran frnd dinki ku kwana tare kinji, kiyi hkuri dear" ya jira jin me xata ce snn yyi murmushi yace "luv yhu 2 gudnyt" snn ya katse wayar ya nufi masallaci, ko da ya dawo Ikram na wanka, ya kwanta kan gado har ta fito daure da xani ya bi ta da kallo ta isa inda jakarta yake ta bude ta ciro kayan shafe shafenta yana kallonta har ta gama shafe shafen snn yyi murmushi ya kauda kansa, ita dae ko kadan bata rabo da turare da mayyukan kamshi, wasu habits dinta sak na Mami, ssae Ikram take da tsaftar jikinta ko da yaushe cikin kamshi xaka ji ta, shi yasa take burgesa ta nn wajen, kayan bacci riga da wando sky blue ta dauka ta nufi bathroom tasa ta fito, ya bi ta da kallo yace "kinyi sllh ne" ba tare da ta kallesa ba tace "ehh" bae kuma cewa komai ba ya mike ya shiga bathroom don yin wanka, ko da ya fito Ikram ta kwanta idonta a lumshe kmr mae bacci, ya gama shirin baccinsa ya hada tea ya sha, snn ya kashe wutan dakin ya kunna mara haske ssae ya kwanta shima, bayan kmr minti goma ikram ta juyo a hankali tana kallonsa suka hada ido, dauke kanta tayi da sauri don bata yi tunanin yana kallonta ba, ya dawo kusa da ita a hankali ya rungumota murya kasa kasa yace "kallon me kika juyo kike min" bata ce komai ba ya kira sunanta a hankali "Ikram," kasa amsawa tayi ta rufe idonta, ya juyo da ita suna facin juna yace "sbda me baki son mu xauna lfya Ikram" muryarta na rawa tace "sbda bana son ka" shiru yyi bae ce komai snn a hankali yace "to wa kike so" ta fashe da kuka ita ma a hankali taki cewa komai, ya daura kanta a kirjinsa yace "to ya isa, kiyi hkuri" bata kuma cewa komai ba bayan kmr minti biyar yace "kinga sbda baki so na na kara aure Ikram" mikewa tayi xaune da sauri tace "to ina ruwana don kayi aure" sae kuma ta fashe da kuka ya rungumota yace "ae ba don bana son ki bane nayi aure ba sae don kar in fada ga halaka, kuma kinga jiya rashin ki da fushin Mamina gareni yasa na kasa kwana daki daya da amaryata, ni ke nake son kusanta ba ita ba" turasa ta shiga yi tana kuka ssae, a hankali yace "tun daga rana ta biyu da na kuma ganin ki naji son ki Ikram, ina sonki ssae, amma ke baki sona wanda kike so daban kuma yyi aurensa ya kyale ki da alkawarin da kika daukar masa, har ya haifi dansa, ke kina nn kina cutar mijin ki kin hanasa hakkinsa, kina daukar tsinuwa mala'iku, is dat fair Ikram" ta kwace kanta cikin kuka tace "to ba kai bane kaki sakina ya aureni, kai ne kayi ruin din rayuwarmu, tun da kayi auren ka ynxu ni ka sakeni in aura wanda nake so don baxan xauna da kishiya ba wllh wllh, bana sonta, bana sonta wllh baxan iya xama da ita ba" cikin kuka ssae ta karasa mgnr, Khaleel yyi murmushi yace "idan ya aure ki shi wanda kike son, ita kuma uwar dansa ba kishiyarki bace ba knn" bae jira me xata ce ba ya rungumeta ssae yace "ni matata bata da matsala nasan xa ku xauna lfya, ina son ta koya maki abubuwan rayuwa ne Ikram" turasa ta shiga yi tana kuka mae taba xuciyar mae sauraro, ya kashe wutan dakin a hankali yace "ina son mayar dake cikakkiyar mace yau Ikram, ki bani hadin kai plsss, 4 my gud 4 ur gud," bae jira me xata ce ba ya rufe mata bakinta da nasa, wae daren nn yaga tashin hankali gun Ikram tun kan bae kai ga mata kmai ba bbu irin kukan da bata yi ba bbu irin rokon da bata yi masa ba ko ina na jikinta na rawa, amma ya toshe kunnensa don ya daukar ma kansa alkawarin ranar xae mayar da ikram tasa, bae ankaraba ya ga yarinya ta sume masa ko numfashin kirki bata yi.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 93..... Da kyar Khaleel ya iya dagota ya kwara mata ruwan da ya debo ya juya xae bar wajen, ba shiri ta dawo ta fasa ihu a tsorace muryar ta na rawa take cewa "don Allah don annabi kar ka min komai ya Khaleel wllh tsoro nake ji plsss ka tausaya min" komawa can bakin gadon yyi a hankali ya sauke kafafuwansa kasa ya dafe kansa, jikinta na rawa har lkcn bata fasa kukan da take ba ta shiga kkrin sauka daga kan gadon tana yi tana kallonsa, fixgota yyi cikin xafin nama ta fado kansa xata saka wani ihun ya rufe bakinta da sauri murya can kasa ba tare da ya kalleta ba yace "bbu abinda xan maki, koma ki kwanta" cikin kuka mae ban tausayi tace "kace wllh ya Khaleel" a hankali yace "wllh" shiru tayi jikinta bae bar rawa ba har lkcn tana sauke ajiyar xuciya, sun fi minti biyar a hka ya kwantar da ita a hankali snn ya mike da kyar ya shiga bathroom, ta shige cikin bargo ta shiga rusa kuka kmr ranta xae fita, yana fitowa daga bathroom bae ko kalleta ba ya nufi daya side din gadon yyi kwanciyarsa tare da juya mata baya. Washegari hasken rana ne ya tada Ikram don bae tasheta ba, ta mike xaune da sauri tana kallon agogo taga bakwae da kusan rabi da sauri ta fada bathroom tayi wanka snn tayi alwala ta fito, tana cikin sllh ya shigo dakin, kallo daya yyi mata ya kwashi wayoyinsa dake gaban Madubin dakin yyi ficewarsa, tana idar da sllh ta tabe baki ta mike ta bude jakarta ta ciro brush dinta ta koma bayin ta wanke bakinta ta fito snn ta ciro kayan da xata sa, atamfa ce riga da skirt an mata dinkinta dai dai jikinta, ta gama shafe shafenta tasa under wears tana cikin sa riga Khaleel ya shigo dakin ta mayar da xaninta kirjinta da sauri, yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace "ina jiranki a falo idan kin gama xamu tafi gida" ta bata fuska tace "wani gidan?" bae tanka ta ba ya fice ta dan yi tsaki ta gama sa kayanta snn ta sauko falo don jin wani gidan xa su, yana kallonta yace "ina jakar taki, ko nn xaki bar shi" tace "to wae nn ba gida bne ko ina xa mu? Ni fa bana son ganin yarinyar da kace min ka aura don ni xan iya fasa mata kai idan na ganta, don hka gwara kawae ka bar ni a nn" ta karashe mgnr tana murguda baki, Khaleel ya mike yana rike da makullin motarsa ya nufi kofar fita, da sauri ta bi bayansa ta saka kuka tana cewa "au tafiya xaka yi, to ni baxa ka tafi ka bar ni kadae a gidan nn ba" tana isowa inda yake ya fixgota suka fito daga gidan ya kulle kofar da key, fuskarsa a daure ya ja ta ya nufi mota da ita ya bude bayan motar ya jefata ciki ya rufe ya xaga ya shiga driver seat yyi horn maigadi ya fito ya bude masa gate ya fice daga gidan, har suka isa gida bata bar kukan da take ba bayan mota kmr xata fasa masa kunne, ssae kukan nata ke bata masa rae amma ya danne xuciyarsa ya gama parkin ya bude motar ya fita ya nufi kofar shiga gidan, fitowa tayi ita ma da sauri ta bi bayansa dae dae bakin kofa ya juya ya shaketa yana huci yace "ki dinga kiyaya na ikram, na maki wani abu ne xaki sa ni gaba kina min kuka don uwarki" ya karasa mgnr cikin tsawa ya turata a fusace har tana neman faduwa yyi cikin gida abunsa, sae da ta gama cin kukanta nan tsugunne a balcony snn ta mike tana share hawayenta ta shiga cikin gidan, bbu kowa a falon ta gama kalle kallenta fuskarta a tamke snn ta haura sama ta tsaya corridor din dakunan xuciyarta na bugawa tana neman ina ne dakin amaryar, dakin dake kusa da nata ta bude, xuciyarta ya kusan shigewa cikinta ganinta xaune cikin wani leshi mae shegen kyau bbu dankwali kanta gashinta har kusan bayanta, shi kuma yana xaune dab da ita suna facin juna ya dago kanta ya kafa mata ido yana kallo ko me yake ce mata oho, kyakkyawa ce maryam ta karshe, ssae Ikram ta gane ta, ta shigo dakin kmr mahaukaciya ta fasa ihu tayi kan maryam tana cewa "la ila ha illalahu, keee me ya shigo dake gidana har da kwalliyar ki, wllh yau sae na fasa maki kai" Maryam ta mike tana kallon Khaleel dake bin Ikram da kallo baki bude, a fusace ya fixgota ya kifa mata mari mae rae da lfya ya yyi waje da ita ya wurgar snn ya rufe kofar dakin, Maryam tace "kaga ka ja mata kunne ta daina shigo min daki hka Khaleel don ni ban ciki da halin jakanci, ita wnn yaushe ta balaga da har xata san wani kishi, to in kanta rawa yake ni hauka nayi, kaji min dae" shiru Khaleel yyi yana kallonta snn yace "hka muka yi dake Maryam, ban gaya maki irin warce xa ki shigo ki tarar ba" tace "to ae wnn ba yarinta ke damunta ba samun waje ne kawae" tana fadin hka ta dauki dankwalinta ta daura xata fita yace "ina xaki?" tace "breakfst xan kawo maka mana" yace "A'a ki bari ba ynxu ba sae ta bar falon" wani kallo ta watsa masa snn ta fice abunta, Ikram na durkushe falo sae rusa kuka take kmr xata tsaga gidan Maryam ta sakko, tana ganinta ta mike da sauri tayi kanta tana huci tace "ina kike tunanin xaki, ance maki gidan ki ne nn" Maryam ta watsa mata wani mugun kallo tace "kika kuskura ki iso gabana wllh sae na nakada maki shegen duka"
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 94.... Khaleel ya sakko kasa yana ma Maryam mugun kallo, ta dauke kai tana rike da kugunta, ya juya yana kallon Ikram da taki karasowa kusa da Maryam din sae fitsara take xaxxaga mata daga inda take tsaye tana tafe hannu, ya karasa kusaa da ita ya dauketa cak ya wuce sama da ita tana cewa "ni wllh ka kyaleni in gwada mata hankali" dakinsa ya bude ya kwantar da ita kan gado sae huci take kmr wata xaki, ya koma ya rufe kofar dakin ya dawo ya xauna kusa da ita yana kallonta yace "tunda ba kya tausayina ikram nima na daina tausayin ki daga ynxu, yau da daddare dolen ki ki bani hakkina, ba suma ba ko mutuwa ma kiyi baxan tausaya maki ba tunda nima ba tausayin nawa kike ba" nn da nn ta nutsuwa gabanta ya shiga faduwa ta mike xaune kmr xata yi kuka tace "ba hka bne ya Khaleel ni bana son kishiya ne kuma...." sae ta fashe da kuka, ya rungumeta yace "Maryam ba kishiyar ki bace Ikram yayarki ce, sae da tayi min alkawarin baxata yi kishi dake ba snn na aureta, don Allah ikram ki bata hadin kai ku xauna lfya xata koya maki abubuwa da yawa plss My Ikram" Ikram ta turo baki tace "to me ta iya da ni ban iya ba da xata koya min" ya bata rae yace "ohh baxa ki ce min to ba?" da sauri ta karyar da kai tace "to" yace "yauwa kanwata, kinga idan kina jin maganata baxan sake cewa xan maki komai da daddare ba tunda bakya so, taso muje muyi break fst" ba musu ta mike ta bi bayansa suka sauko kasa, Maryam na kitchen ya shiga kitchen din yace "dinnin xaki ajiye break din Maryam" ya fito ya kama hannun Ikram dake tsaye suka nufi dinnin ya ja mata kujerar kusa da inda xae xauna, ta xauna shima ya xauna, Maryam na gama jera abincin a dinnin ta ja kujera ita ma ta xauna, da kansa ya deban ma Ikram dankali da kwae ya hada mata tea snn ya debi nasa, Maryam ma ta debi nata. Har suka gama break din Ikram bata bar hararan Maryam da take ba, Maryam dae bata ko kalleta ba ta kwashe kwanukan da suka yi amfani da shi ta nufi kitchen, Khaleel yace "ba kince xaki dinga jin mgna ta ba Ikram" da sauri Ikram tace "ina ji mana, me nayi kuma" yace "to meyasa kike hararanta" ta dan bata fuska tace "to na daina" yace "yauwa to tashi kije ki taya ta ku wanke kwanukan ki ga ynda xata gyara kitchen din" ba musu ta mike ta nufi kitchen din ya bi ta da kallo har ta shiga snn ya sauke ajiyar xuciya ya jinginar da kansa jikin kujeran da yake xaune.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar
95.....
Khaleel na xaune daki yana duba wasu files din gabansa agogo yyi struck din karfe 12, ya juya yana kallon Ikram da tun shigowarta dakin bayan sun gama wanke wanke da Maryam take kallo, ya rufe file din gabansa yace "ikram" ta juya da sauri tana kallonsa yace "tun da aka yi holiday ban ga kin dauka chemistry ko biology kina karantawa ba, ko baki son xana waec nxt yr ne, or kin fi so kiyi a ss3" tace "A'a ina so mana a ss2 xanyi, ae xan fara karatun daga gobe" yace "to xaki je holiday coaching na makarantar ku ne" da sauri tace "A'a ni xan yi karatuna a gida, kuma ae xan dinga xuwa islamiyya ma" yace "ok, but ki rage wnn kallon naki" Maryam ce ta bude kofar dakin ta shigo tace "me xa'a girka Khaleel" Khaleel ya juya yana kallon Ikram yace "me kike son ci?" ta dan yamutse fuska tace "ni shinkafa da miya nake so" yace "to ae tashi xaki yi ku je kuyi shinkafa da miyar" tace "bayan wanke wanken da nayi daxu? Ni fa ta bar ma kwanukan na wanke" ta karashe mgnr a fusace, Khaleel yyi shiru yana kallonta, da sauri ta mike tace "to naji" ta fice daga dakin, ya taso ya karaso kusa da Maryam dake tsaye har lkcn ya kamo hannunta yace "kiyi hkuri da yanayin Ikram Maryam, wit tym xata daina duk wnn abinda take kinga dae nima ba kyaleni tayi ba" fixge hannunta tayi ta fice daga dakin, ta sauka xuwa kitchen, danyen shinkafa ta tar Ikram ta cika cikin wani katon tukunya tana kkrin fara wankewa a famfo, ta karbe tukunyar shinkafar tace "su wa da su wa xasu cinye wnn shinkafar" Ikram tace "su mu mana, bari ki ga ynda na auna" ta dauko nml plate din xuba abinci tace "sau uku na cika wnn dam dam, ke daya ni daya ya Khaleel ma daya" Maryam tace "to ba hka ake yi ba Hajiya" Ikram tace "ni ba Hajiya bace" Maryam bata tanka ta ba ta dauko dan kofi tace "xamu dinga amfani da wnn wajen aunar shinkafar," ta auno kofi uku a tukunyar bayan ta mayar da wnda Ikram ta debo tace "kinga wnn ya isa" Ikram tace "to ae wnn ko ni sae in cinye shi" Maryam tace "bari a dafa ki ga ko xa ki cinye shi" gas ta kunna snn ta daura ruwa a tukunya ta rufe ta ajiye shinkafar gefe, Ikram tace "to meyasa baki xuba ba?" Maryam tace "sbda sae ruwan yyi xafi, snn a wanke shinkafar a xuba" Ikram ta dan tabe baki bata ce komai ba, Maryam tace "kin dae ji me nace " Ikram tace "ehh" nama ta dauko a deep freezer da kayan miya, ta ajiye naman cikin yar roba, Ikram tace "to da kankarar xamu dafa ta" Maryam ta dan yi murmushi ta xuba ruwa cikin naman dan kankarar ya narke, Ikram tace "to ae ddin naman xae wuce idan aka bar shi cikin ruwa kuma" Maryam tace "da ace ba ynxu xa muyi girkin ba da barin sa kawae xamuyi xae narke da kansa, amma ynxu kinga amfani xa muyi da shi" Ikram na kallo ta shiga wanke kayan miya a sink, har ta gama snn ta juyo tace "kin dae ga ynda nayi ko?" tace "ehh" Maryam tace "to gobe ke xaki yi" ssae Ikram ta maida hankalinta gun girkin da Maryam ke yi, don tayi tambaya ya fi dari, har daga karshe suka hada shinkafarsu da Miya har da ginger drink, a tare suka jera a dinnin, Ikram sae murna take yau ta dan yi girki tunda ita ta soya naman kuma ta dinga juya miya kan gas tana dandanawa, sae

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login