Showing 51001 words to 54000 words out of 135778 words

Chapter 18 - Exiled Prince Book Three Complete Hausa Novel

Meerah   

24 Oct 2025

340



E



X



I



L



E



D



⚘❤



P



R



I



N



C



E



⚘❤







(LOVE



MEETS



POWER



)



👑🔥





(



A



heart



touching



love



story



,



Romance



,



injustice



&



destiny



)







STORY



&



WRITTEN



BY



:



MEERAH





🕊

BOOK



________3



👑







P



A



G



E

8

🌹🕊







AFTER SOME MINUTES





INAYA

a hankali ta ware idanun ta ta na karanto kalmar shahada , da ga nan kawai ta shiga kiran sunan yaya Zayd

da sauri RIANNA da ke zaune saman sofa ta tasso ta komo bakin ta zauna ta kai hannu saman face din Inaya ta na cewa " sannu baby ya jikin na ki ? "

cikin sanyin murya Inaya ta ce mata " aunty RIANNA ina yaya Zayd di na ? "

" Kar ki damu baby , ba abun da ya same shi kin ji ko ? " RIANNA ta fada cikin sigar rarrashi

a hankali Inaya ta mike zaune ta na kokarin tashi ta ce " Aunty RIANNA zan je na gan shi " ta kai karshen ta na kokarin sauko kafafun ta kassa

da sauri RIANNA ta ce mata " no baby kar ki sauko " ta fada saboda raunin da ta samu a kafa , kar ta ji zafi idan ta taka

ko sauraron ta Inaya ba ta yi ba ta sauko da kafafun ta , ta mike tsaye ta na fadin " Aunty RIANNA ni zan je na ga yaya Zayd di na "

da sauri RIANNA ta taro ta ta na fadin " Baby yi a hankali , akwai zafi ? "

a hankali Inaya ta fara takawa ta na fadin " Aunty RIANNA don Allah ki kai ni wajen yaya Zayd di na "

" baby don Allah dawo ki zauna , ba ki jin zafi a kafafun ki " ta fada cikin sanyin murya

girgiza kai Inaya ta yi ta na cewa " Aunty RIANNA ni babu abun da na ke ji , ni kawai ni kai ni wajen yaya Zayd di na , ni kai ni wajen yaya Zayd di na " ta kai karshen ta na sakin kuka

ajiyar zuciya RIANNA ta sauke ta na kallon Inaya da ke faman kuka , ta rasa abun da za ta yi , ba ta tunanin Inaya za ta iya jure ganin Halin da Malik ke ciki , ko ita kassa jurewa ta yi bare Inaya

babu yadda ta iya haka ta mike ta riko hannun ta , su ka baro dakin , kai tsaye room din da a ka kontar da Malik su ka nufa

da Sallama a bakin RIANNA ta shiga cikin room din ta na rike da hannun Inaya

a hankali MALIKAT INAS ta dago kai ta kali saitin kofar ta na amsa mata sallamar

ta na ganin ta tare da Inaya ta saki wani dan karamin murmushin karfin hali ta ce " baby har kin tashi ? "

gyada mata kai kawai Inaya ta yi ta na dan karamin murmushi kafin ta tako a hankali ta karaso bakin gadon da Malik ke konce ta kai hannu ta taba kumatun shi

ba tare da ta janye hannun ta ba ta ce " Ammie , jikin shi ya yi sanyi sosai kamar ice "

Shiru MALIKAT INAS ta yi dan ba ta da abun da za ta fada mata ita kan ta ta rasa dalilin da ya sa jikin shi ya yi sanyi Haka bayan kuma doctor sun ce ya na raye bai mutu ba

su na a haka kawai su ka ga Inaya ta janyo chair a hankali ta zauna bakin gadon , ta riko hannun shi ta daura saman kumatun ta ta na wani dan karamin murmushi , kafin ta sauko shi ta kai bakin ta saitin kunnen shi ta ce mishi " kar ka damu baby na , ba abun da zai same ka in har ina raye , don Allah ka yi min magana mana " ta ke fada mishi cikin rada

da ga haka ta dago kai ta daura forehead din ta saman nashi , ta lumshe idanun ta

kamar da ga sama su ka jiyo Muryar MALIKAT AL'UMU ta na fadin " Nawfel ! " da dan karfi

a razane MALIKAT INAS da RIANNA su ka kali saitin kofar dakin , nan su ka gan ta tsaye ta na faman Zaro idanu ta na kallon Malik

da sauri ta karaso cikin ta nufe shi

a hankali Inaya ta janye forehead din ta da ga saman nashi ta mike ta ja da baya sannan ta juya ta fara takawa za ta fice dakin

ta na fita ko ta ci karo da Diya ya na tafe kamar an koro shi

a rude ya tunkaro Inaya ya na fadin " baby , ina Malik ya ke ? "

a hankali ta ce mishi " yaya Moussa ina son na yi magana da kai "

" Baby , ki fada min Ina ya ke , ba abun da ya same shi dai ko ? "

" Yaya Moussa don Allah mu tafi , ina son na yi magana da kai " ta fada cikin sanyin murya

babu yadda ya iya haka ya bi bayan ta su ka fito Hospital din

su na tafiya ta ce mishi " yaya Moussa , don Allah ka sa a fara bincike a kamo wanda ya yi wa yaya Zayd di na wannan abun " ta kai karshen ta yi kuka

cikin rudu Moussa ya ce mata " baby wai me ya same shi ne , ni fa ina zaune kawai a ka ce min an kawo Malik Hospital kuma da allamun ba ya cikin hayacin shi "

" Poison ya ci "

" inallillahi wa'ina illaihi raji'un , baby garin yaya haka ta faru ? " Diya ya fada da dan karfi

marairaice mishi fuska ta yi kamar za ta yi kuka ta ce " yaya Moussa ni ma ban sani ba , kawai mu na shan fruits ne , sai da na ce mishi kar ya hadiye amma bai saurare ni ba , gashi yanzu su na neman su raba ni da shi , yaya Moussa don Allah ka sa a kamo wanda ya yi mishi haka " ta kai karshen hawaye na zubo mata

bayan salati ba abun da Diya ke yi , ya ma rasa abun da zai ce , ya za a ce da ga fitowar shi da ga fada har sun samu damar iya kashe shi

cak ya tsaya ya na zaro idanu ya ce " kenan bayan Miram da Mohammed akwai wanda ke son ganin bayan Malik ? "

ya tambayi kan shi cikin zuciyar shi , Miram da Mohammed da su ka kashe yanzu ya a ka yi su ka samu damar shirya wannan abun dole akwai wasu kenan

ya na dawowa da ga duniyar tunanin shi kawai ya ga Inaya har ta bar wajen ta nufi part din MALIKAT INAS

bai yi kokarin tseda ta ba , sai ma juyawa da ya yi ya nufi Hospital ya koma dan ya ga Malik







ROUKSAR

tsaye ta gaban Damba da ke faman dariya , sai matse fuska ta ke da allamun ba ta jin dadin dariyar shi

sai da ta gaji da sauraron shi sannan ta ja tsaki ta nan kauda kai ta ce " don Allah dariyar nan ta isa haka , na ce maka mu na cikin matsala kai k..... "

ba ta kai karshen maganar ta ba ya katse ta da cewa " ki bar ni na yi dariya ta mana , wannan shi ne a ke kira ka kashe maciji ba ka sare kan shi ba , Malik ya na konce rai hannun Allah , amma kin yi mistake guda , da ba ki kashe yarinyar nan ba , amma duk da hakan ba mu fadi ba , in dai Malik ya mutu kafin aljanun ta su Ankara ba abun da za su iya yi "

" Damba ban gane abun da ka ke nufi ba , ni plan din na ka ne duk ba na ganewa , ka ce ka na son zama Malik , amma ka ce na kashe yarinyar nan , ko na kashe ta ba za ka iya hawa mulkin ba saboda ba ita ce Malik "

" Rouksar , ba za ki gane ba , zomo me wayo ta kunnuwa a ke kama shi , wannan yarinyar da ki ke gani , ita ce garkuwar Malik in dai ta na raye ba abun da zai iya samun shi , ko so nawa za a yi kokarin kashe shi ko da kuwa rayuwar shi na tsakiyar gadar Siraji sai yarinyar nan ta medo shi duniya , in har ya tsalaka ta kuma shikenan ba abun da za iya yi "

cikin rudu Rouksar ta ce mishi " ban gane abun da ka ke nufi ba "

wani dan karamin tsaki ya yi kafin ya ce " ina nufi wannan damar mu ce , indai ya mutu ba za ta iya medo shi ba , ba abun da za ta iya yi "

wani dan karamin murmushi Rouksar ta saki kafin ta ce " in dai haka ne to ka kontar da hankalin ka , cikin daren nan Malik zai mutu , dan babu mutuman da zai iya shan poison di na , kuma ya yi rai "

cikin nitsuwa Damba ya katse ta da cewa " ko da kuwa poison din ki bai cika shi ba , ni zan je na Kamala shi , yanzu abu guda na ke bukata wajen ki , wanda zai tabbatar min hawa Mulkin Saudiya babu tangarda "

da murmushi a fuskar ta ta ce mishi " ina sauraron ka "

da hannu ya mata allamun ta matso , ba musu ta karaso dab da shi ta tsaya

a hankali ya dan sunkuyar da kan shi ya kai bakin shi saitin kunnen ta ya yi mata rada

a dubu dari Rouksar ta ja da baya ta na zaro idanu ta na wani nunfashi sama sama

" Yadda kowa zai yi tunanin halin da Malik ke ciki ne ya sa zuciyar ta bugawa har ta shiga doguwar suma " Damba ya fada da dan karfi saboda bayan da Rouksar ta yi

girgiza mishi kai ta yi a tsorace ta ke ce mishi " Aymane ba zan iya ba , Da ni da ita duk mutuwa za mu yi "

TO FA

🤔🤔🤔🤔

WANE AYMANE DIN ? BA DAI WANDA KE SHIRIN AUREN RIANNA BA ?

wani dan karamin tsaki ya yi kafin ya sa hannu ya zame haramin da ya rufe face din shi

😱😱

WLH AYMANE NE , WAIT KENAN TUN FARKO SHI YA YI KOKARIN KASHE MALIK TUN YA NA AMIR

🤔🤔🤔

NI FA KAI NA YA FARA RUFEWA KAMAR DAI BA NA NAN A KA YI WANI CHAPITER DIN LABARIN NAN , BARI DAI MU CI GABA

cikin wata murya cike da isa ya ce mata " ba abun da zai same ki matsoraciya kawai " a hankali ya juya ya daura hannu saman bishiyar bayan shi ya ce mata " cikin nan za ki boye shi , babu wanda ya taba zuwa wajen bishiyar nan tsawan shekaru sama da dari , tun Malik Zayd bin Saud na raye bishiyar nan ke cikin masarautar nan kuma babu wanda ya taba tunanin bishiyar micece bare har su ce a fitar da ita , duk wani sihiri da na yi cikin masarautar nan cikin wannan bishiyar na ke boye shi , kuma a ciki za ki boye ruhin MALIKAT AL'UMU "

girgiza mishi kai Rouksar ta yi da sauri kamar za ta yi kuka ta yi taku guda baya ta na fadin " a'a Aymane , ba dan ka na son zama Malik za ka saka rayuwa ta cikin hatsari , Damba in kuma a ka je wani ya fitar da ruhin ta da ga cikin bishiyar nan ka fi kowa sanin abun da zai faru da ni "

wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce mata " ba shawara na ke ba ki , umarni na ke ba ki , ba shawara ba "

da sauri ta ce mishi " Aymane son da ka ke yi wa kujerar Malik yanzu har ya kai za ka iya saka rayuwa ta cikin hatsari , I'm your little sister "

ba ta gama rufe bakin ta ba ya kai hannu ya damko wuyan ta ya matse da karfi ya na zaro idanun nan na shi da kyau ya ce mata " tun lokacin da na shigo duniya , da wannan kudirin na shigo ta , kalma ta farko da ta fara fitowa da ga baki na shi ne zai na zama Shugaban Saudiya baki dayan ta , wlh ba ke ba ko da sarki Abdoul Mujeeb ne zai fito da ka cikin kassa dan dakatar da ni wlh sai na meda shi inda ya fito , da tun farko ba ki bata min shiri na ba da yanzu ni ne zaune saman kujerar Malik , in ki ka ce ba za ki yi abun da na saka ki wlh da hannu na zan kashe ki , ban damu ba da ke yar uwa ta ce " ya na gama fadar haka ya tura ta gefe ta fadi wanwar a kassa ta jan nunfashi da karfi

ta na faduwa ya koma kassan bishiyar nan ya zauna ya ja haramin shi ya rufe fuskar shi , ya ce mata " na ba ki nan da kwana uku "

da sauri ta dago kai ta mike zaune , idanun ta sun koma jazir , cikin disashashiyar murya ta ce mishi " Damba , ba zan iya ba , tsawan shekaru nawa yanzu ban yi irin wannan aikin ba , kai ma ka sani idan a ka samu matsala da ni da MALIKAT AL'UMU tare za mu mutu "

" to ku mutu mana , sai me ? Zan kawo miki duk wani abu da za ki bukata for catching her soul , da ga shi na yi miki alkawari zan mayar da ke Daular Ottoman " ya na gama fadar haka ya bace bat a wajen ya bar ta nan zaune

ya na barin wajen ta saki wani dan karamin kukan kura ta na fadin " why ? gaskiya ba zan iya ba , ban shirya mutuwa ba , wlh yanzu zan yi wa Diya magana ya sa a mayar da ni gida "

ba ta gama rufe bakin ta ba ta jiyo Muryar Aymane ya na fadin " in dai ba ki yi abun da na saka ki ba , ko kin koma sai na medo ki "

Dum ta ji zuciyar ta ta buga ta zaro idanu ta na kallon wajen , babu shi kuma a wajen Muryar shi ce kawai

yau ta tabbata duk abun da ta ke tunani kan Aymane ya wuce haka , ai ba shiri ta tashi da gudu ta bar wajen







INAYA

zaune ta ke cikin parlourn MALIKAT INAS ta yi zugum waje guda sai ruwan hawaye ta ke yi

kamar da ga sama ta ji an dafa shoulder din ta

a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta juya ta ga wanene ya dafa shoulder din ta

nan take ta saki kuka ta fada jikin Nesrine ta rungume ta

a hankali Nesrine ta zauna geffen ta , ta rungume ta tsam a jikin ta ba tare da ta ce mata komai ba

sai da ta gaji da kukan ta sannan ta dago da ga jikin Nesrine ta na cewa " Nesi , yanzu ma su na neman su na raba ni da shi "

cikin sigar rarrashi Nesrine ta ce mata " Ki yi hakuri kin ji Auta ? in sha Allah mutuwa ce kadai za ta raba ki da yaya Zayd ba dai mutum ba "

ba ta ce mata komai ba ta ci gaba da kukan ta kamar baby

a hankali Nesrine ta kai hannu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login