Showing 42001 words to 45000 words out of 135778 words
shagwabe fuska ta ce " baby ni fa ba abun da na ke sha , kai ne kawai ke ganin na yi haske "
" da gaske na ke fa , har wata yar kiba ki ka yi na ga kayana suk kara cika" ya fada ya daga mata gera guda
kukan shagwaba ta sakin mishi ta na bubuga kafafun ta a kassa kamar wata karamar yarinya ta na cewa " ka daina cewa na yi kiba , ni babu abun da na yin "
shi dai'dai kawai ya tsaya ya tsare ta da wadanan hazel eyes din na shi , kamar ya tashi ya cinye ya ke ji
ai ko ba ta gama rufe bakin ta ba kawai ta ga ya tashi a hankali ya tunkaro ta
a hankali ya zagayo da hannun shi a kugun ta , ya matso ta jikin shi murya kassa kassa ya ce mata " wai ke me ya sa rigimar ki ta fi ki yawa "
turo dan bakin nan nata ta yi ta na dan sunkuyar da cikin gunguni ta ce mishi " ni ba rigimamiya ba ce "
daga mata gera guda ya yi ya na cewa " da gaske ? "
a hankali ta gyada mishi kai ta na turo dan bakin nan nata
" okay , you wanna dance with me ? "
a hankali ta dago kan ta ta kale shi cikin rudu ta ce mishi " dance kuma ? "
gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya saki kugun ta , ya juya ya nufi sofar da ya taso ya kai hannu ya dauki wayar shi , ya fara dannawa sannan ya ajiye ta ya dawo gaban ta ya tsaya ya mika mata hannu ba tare da ya ce komai ba
a hankali ta dago hannun ta ta daura saman nashi dai'dai lokacin da Music ta fara tashi a wajen wakar nan ta CKAY LOVE MWANTITI
wani cool murmushi ta sakin mishi ta na fadin " Baby , yaushe ka fara sauraron Music kuma ? "
bai ce mata komai ya riko dayan hannun nata , ya daura saman shoulder din shi
sannan ya zagayo da hannun a kugun ta , ya daga ta a hankali ta , ya daura kafafun ta saman nashi , dan ya san da wuya a ce ta iya rawar
a hankali ya fara yin rawa da ita ya na juyawa
ita dai ta na kallon shi ta na yar karamar dariya har dimple din ta ya lotsa
ba karamin burge shi ta ke ba idan ta na wannan murmushin , specially idan Dimple din ta ya lotsa
A hankali ya matso da face din shi saitin ta ta , ya hade forehead din su ya na kallon cikin idanun ta ,
murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta lumshe idanun ta
Ta na a haka kawai ta ji saukar lips din shi saman nata , ya fara kissing din ta cikin konciyar hankali
wata nanauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta cabko lips din shi na kassa ta fara mayar mishi da martani
kamar da ga sama ya jiyo Muryar Mohammed da ga bayan su ya na sallama
cak ya tsaya ya zaro idanu , a hankali ya zame bakin shi da ga cikin nata , Cikin bacin rai ya juya ya kali Mohammed tsaye bakin kofar lift ya tsare su da idanu
nan take yanayin face din shi ya sauya , ya tsuke gera ya ce " What are you doing here ! "
murya na kerma ya ce mishi " Ran ka shi dade dama........ dama m...maga........"
bai kai karshen maganar shi ba Malik ya katse shi da cewa " Get out ! " ya fada da karfi har sai da Inaya ta tsorata ta shige jikin shi
ba shiri Mohammed ya juya ya bar ya shiga lift ya bar wajen , dama ya zo yi mishi magana a kan Miram ne , ya ga bai je mosque ba yin sallat , kuma ya je gidan shi an ce ba ya nan , shine ya taho yi wa Malik magana , kawai ya tardo su su na rawa nan take ya tsargu da kallon su
A hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya , ya dan sunkuyar da kai ya ce mata " Sorry my Cutie "
ajiyar zuciya ta sauke ita ma , ta na a haka kawai ta ji ya sake ta , ya sauke kafafun ta kassa , ya juya cikin nitsuwa ya dauki wayar shi ya fara latsawa
bai yi one minute ba da tsayuwar shi , kofar lift ta bude Azim ya fito
taku uku kawai ya yi ya Zube saman guyiwowin shi cikin girmamawa ya shiga gaishe da shi tare da Inaya cikin girmamawa
bai bi ta kan gaisuwar shi Malik ya ce " Da ga yanzu duk wanda ke nema na ya tsaya a iya floor na biyu , idan kuma maganar mai mahimanci ce ka fara zuwa ka sanar min ba ka bar shi kai tsaye ya shigo min parlour ba "
cikin girmamawa Azim ya ce mishi " Afuwa ya shugaba na , Allah ya huci zuciyar Adalin shugaba na , in sha Allah za a kiyaye "
Gyada mishi kai Malik ya yi kafin ya saka wayar shi cikin aljihun wandon shi , a hankali ya juyo ya ce mishi " za ka iya tafiya "
" Godiya na ke ya shugaba na " Fadin Azim kafin ya mike kai a sunkuye ya juya ya koma cikin lift din ya bar wajen
a hankali ya tako ya Nufe ta ya tsaya gaban ta murya kassa kassa ya ce mata " Mu je na ba ki Sweet "
noke mishi kafada ta yi ta shagwabe fuska ta na cewa " baby ni barci na ke ji " ta kai karshen ta na turo dan bakin nan nata
bai ce mata komai ba ya sa hannayan shi biyu ya dauke ta cak , ya fara takawa ya na fadin " Kin san wani abu ? "
girgiza mishi kai ta yi ta na murmushi ta ce " sai ka fada "
a hankali ya matso da face din shi ya ce mata " Wlh babu barcin da za ki dan yunwa na ke ji "
dan zaro idanu ta yi da sauri ta yi kokarin sauka ta na fadin " don Allah baby ka kyale ni , wlh barci na ke ji , wlh sai na fadawa Ammie ...... "
cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " uhm me za ki fada mata ? " ya tambaye ta dai'dai lokacin da ya sauke ta saman gadon su , a hankali ya komo bakin gadon ya zauna ya kai hannu cikin aljihun ya ciro wayar shi ya fara latsawa
cikin shagwaba ta ce mishi " sai na ce mata ba ka bari na huta , ni gaskia yaya Zayd ka kyale ni na yi barci "
cen sai ta ga ya dago wayar ya kai ta a kunne ya yi sallama cen kassan makoshi sannan ya ce " Barka da wannan lokacin Ammie "
Inaya na jin ya ce Ammie ta zaro idanu ta na kallon shi
ta na haka ta jiyo Muryar shi ya na cewa " Fine Ammie , dama akwai wanda ke son magana da ke ne " ya na gama fadar haka ya sauko wayar
ya mika mata ya na cewa " karbi Ammie ce "
da sauri ta girgiza mishi ta na marairaice fuska
matse gera ya yi allamun babu wassa ya ce mata " karbi na ce ! "
wasu yawu ta hadiye kafin ta dago hannun a hankali ta karbi wayar , ta kai a kunne Murya na kerma ta ce " Hello Ammie "
a daya bangaran cikin fara'a MALIKAT INAS ta ce " Baby ya ki ke ? fatan ki na lafiya ? "
cikin sanyin murya Inaya ta ce mata " Ina lafiya Ammie , ya ku ke , da Aunty RIANNA ? "
" Alhamdoulilah baby , Allah ya sa dai lafiya mijin ki ya ce ki na son magana da ni "
a hankali Inaya ta dago kai ta ga shi ma ita ya ke kallo
" Oya , fada mata " ta fada ya na daga mata gera guda
" babu komai Ammie " ta fada da sauri ta sauko da wayar ta mika mishi
ba musu ya kai hannu ya karbi wayar ya kai a kunne ya ce " ta ce ne ta na kewar ki , shi ya sa na kira ki "
" kai dai Nawfel , na san Halin ka , anya ba takurawa yarinyar mutane ka ke ba "
" Ammie na takura mata ba matata ba ce ? " ya fada da larabci
wata yar karamar dariya MALIKAT INAS ta yi kafin ta ce " Allah ya huci zuciyar ka , ka dai yi mata a hankali na san halinka ba karamin jarabbabe ba ne , ka na gani fa yarinya ce , ba dan ta dauke ka sau guda za ka ci gaba da takura mata , ka dinga bari ta na hutawa kar ka ji mata ciwo "
shiru ya yi ya na sauraron ta , kenan ta gane maganar me Inaya ta so yi mata kenan ?
a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce " Shikenan Ammie "
" yawwa dan Albarka , ka kula min da ita ka ji ? "
cikin sanyin murya ya ce " In sha Allah Ammie , ki kula min da kan ki " ya na gama fadar haka ya sauko wayar ya katse kiran sannan ya kai hannu saman bedside drawer ya ajiye ta
ya na ajiye wayar ya dawo da kallon shi kan Inaya ya ce mata " I love you "
wani kyawatencen murmushi ta sakin mishi har da sauke ajiyar zuciya , da sauri ta fada jikin shi ta rungume shi
A hankali ya zagayo da hannayan shi a bayan ta ya rungume ta tsam , kafin ya Haye saman gadon ya konta da ita a jikin shi , a haka har barci ya yi gaba da su
▪
WASHE GARI
misalin karfe 8 na safe , fadar masarautar cike ta ke da mutane dan yau Malik zai yanke wa Hakim Hukuncin , musaman MALIKAT AL'UMU da MALIKAT INAS sai da su ka halar ta bisa Umarnin Malik
su na a haka General Abdallah ya ce wa daya da ga cikin sojojin shi ya je ya taho da Hakim
ba musu ya fice da gudu ya bar fadar
ya na fita Inaya ta matso kussan Malik ta ce mishi " Baby ciki na ciwo ya ke min " ta fada ta na marairaice fuska
slowly ya juyo ya kale ta , ya ce mata " Sorry my Cutie , da na Kamala za mu tafi "
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta gyada mishi kai ta gyara zaman ta
su na a haka sojoji Biyar su ka shigo , biyu na rike da Hakim
biyu na rike da Miram da ke daure kamar goro , fuskar shi duk ta yi ja allamun ya sha bugu dan bakin shi har ya fashe
mutanan wajen na ganin Miram duk su ka shiga kananan magaganu
da sauri Diya ya ce musu " please keep quiet ! "
ba musu kowane ya yi tsit ya na kallon abun da ke faruwa
sai da sojojin nan su ka kawo su tsakiyar fadar , sannan su ka zubar da su saman guyiwowin su , su na fuskantar Malik
cikin nitsuwa Diya ya ce musu " Kamar yadda ku ka sani wannan shi ne Sniper din da ya harbe marigayi Malik , a yau mun dawo ne gaban Malik domin yanke mishi hukunci dai'dai abun da ya aikata , na san kowa zai yi mamakin ganin Miram a wannan yanayin , duk za ku samu amsar ku nan gaba "
Wani dan karamin murmushi Diya ya saki ya na kallon Miram ya ce " Miram , ba za ka gaishe da Mai martaba ba ? "
ya fada dan su na son Miram ya yi magana Hakim ya ji yadda zai iya gane Muryar shi
wasu yawu Miral ya hadiye kafin ya bude baki a hankali ya ce " Barka da Safiya ranka shi dade mai girma Malik "
ko sannu Malik bai ce mishi ba da allamun yau na mulkin su na sama
gyada kan shi Diya ya yi kafin ya ce " Hakim , ka gane Muryar nan ? "
a hankali Hakim ya gyada mishi kai dan har yanzu bai samu karfin jikin shi ba
wani dan karamin murmushi Diya ya saki kafin ya ce " Hakim ina son ka fadawa mutanan wajen nan abun da ya faru tsakanin ka da wannan mutum "
ba musu Hakim ya ba su labarin da ya ba wa Malik a prison , sannan ya daura cewa " wannan shi ne wanda ya saka ni yin aikin , shi ne ya saka ni kashe Malik , sannan ya sace min matata , day BEFORE yesterday , ya tarda ni a cikin cell di ta ya yi kokarin kashe ni , ko da bai yi magana ba zan iya gane face din shi , saboda a ranar bai boye fuskar shi ba ya zo ya kashe ni , a tunanin shi ba zan yi rai ba " ya kai karshen ya na jan wani dogon nunfashi
nan take fadar kowa ya shiga fadin inallillahi wa'ina illaihi raji'un kowa da abun da ya ke fada
abun mamaki Malik kuwa ya tsare Mohammed da idanu , sai wani kauda kai ya ke , har wata zufa ke karayo mishi duk da ac din wajen ya na hadiye yawu
a hankali Malik ya furza iska da ga bakin shi kafin ya kali Diya murya kassa kassa ya ce " je ka taho da ita "
gyada mishi kai Diya ya yi kafin ya fara takawa da sauri sauri ya fice fadar
kowa ya na kallon shi har sai da ya fita sannan Rafik ya ce " Amma Miram ba ka kyautawa kan ka ba , me Malik ya yi maka ? tamkar dan uwa ya dauke ka am....... "
bai kai karshen maganar shi ba ya jiyo Muryar General ya na cewa " mai girma Rafik , please ka danne zuciyar ka , mu ji abun da Malik zai fada , da ga baya kowa ya yi maganar shi "
ba musu Rafik ya ja bakin shi ya yi shiru fadar ta yi tsit kowa ya na sake saken qui cikin zuciyar shi amma duk sai da su ka yi wa Miram tir da hali irin na shi
❤⚘
E
X
I
L
E
D
P
R
I
N
C
E
⚘❤
(LOVE
MEETS
POWER
)
👑🔥
(
A
heart
touching
love
story
,
Romance
,
injustice
&
destiny
)
STORY
&
WRITTEN
BY
:
MEERAH
⚘
🕊
BOOK
________3
👑
✌
P
A
G
E
6
🌹🕊
jim kadan bayan fitar Diya ya dawo cikin fadar , kai tsaye geffen Malik ya koma ya tsaya sannan ya daga murya ya ce " za ki iya shigowa "
ya na gama fadar haka Wata kyakyawar budurwa ta shigo fadar ta na sanye da wata Abaya blue color ta yi Rowling veil din ta , da ga gani ciki ne da ita , dan ga shi nan ya fito at least zai kai 5 to 6 months , kai a sunkuye ta shigo fadar , hannayan ta saman cikin jikin ta , ta na taku a hankali
kai tsaye Geffen Hakim ta karaso ta tsaya cikin girmamawa ta ce " ina mika sakon gaisuwa ta ga shugaba "
gyada mata kai kawai Malik ya yi ba tare da ya ce komai ba
Hakim na jin Muryar ta ya ji zuciyar shi ta yi mugun bugawa , a hankali ya dago da kan shi dan a sunkuye ya ke tun lokacin da ya Kamala maganar shi
ya na ganin ta , Ya dan zaro idanu , ya ma manta da mutanan da ke wajen ya tashi da sauri ya rungume ta