Showing 120001 words to 123000 words out of 135778 words

Chapter 41 - Exiled Prince Book Three Complete Hausa Novel

Meerah   

24 Oct 2025

318

ta , ya sauke forehead din shi saman nata murya kassa kassa ya ce " okay , zan kirga zuwa uku , da ga nan ki ka dogon nunfashi ki sauke , kin ji ko ? "

a hankali ta gyada mishi kai allamun Eh

" Okay , one , two , three let's go "

wani dogon nunfashi ta na sakin wata siririyar kara karfin ta sauke wata nanauyar ajiyar dai'dai lokacin da kukan baby ya gauraye wajen

wata nanauyar ajiyar zuciya Malik ya sauke ya na fadin " Alhamdoulilah " cikin zuciyar shi har lumshe idanunshi ya yi ya na sakin murmushi kamar shi ya yi aikin

ya na bude idanunshi ya ga Inaya ta yi tsit kamar an yi ruwa an dauke

Dum ya ji zuciyar shi ta buga da karfi , a dubu dari ya kai hannu ya fara jijiga ta ya na fadin " Cuti , Cutie , please ki bude idanunki , Cutie , please ki bude kar ki min haka mana "

da sauri Doctor da ke rike da babynsu ta karaso wajen ta na fadin " ka kontar da hankalinka , ba mutuwa ta yi ba , suma ce ta yi " ta na gama fadar haka

ya ga ta sauke babyn hannun ta saman kirjin Inaya ta kontar da kan shi saitin zuciyarta

wani irin sanyi ne ya ji lokacin da idanunshi su ka sauka saman babyn , kyakyawa da shi fari kal kamar ka taba jini ya fito har wani ja ya yi , ya na kama tak da Malik kamar an tsaga kara , sai dai idanun shi a rufe su ke sai in ya bude mu ga kalar su

kawai sai ya ga babyn ya rage kukan da ya ke yi , doctor na ganin haka ta dauke shi ta mikawa Malik ta na fadin " za ka rike shi , ko mu tafi ? "

bai ce mata komai ba ya dago hannayan shi a hankali ya mika mata

ba musu ta daura mishi babyn a sama

nan take ya kara sautin kukan shi ya na wuntsila Kafafu kadan ya kubcewa Malik

da sauri Doctor ta karbe shi ta na fadin " Nurse , ku je a yi wa mai martaba dress , ya samu rauni a jikin shi ta fada ta na juyawa da babyn

sai da ya sunkuyo ya mannawa Inaya kiss a saman forehead din ta , sannan ya kai bakin shi saitin kunnen ta ya yi mata rada kafin ya mike ya juya

ya bi bayan nurse din nan su ka baro dakin

su na fitowa kawai ta ga Malik ya yi gaba abun shi , ya nufi su MALIKAT AL'UMU da ke zazzaune sun yi zugum

su na ganin shi su ka mike a tare su na tambayar ta sauka lafiya

gyada musu kai kawai ya yi kafin ya ce " za ku iya komawa part din ku , doctor ta ce ta na bukatar hutu " ya kai karshen ya na shirin takawa

da sauri MALIKAT AL'UMU ta taro shi ta na fadin " me ta samu ? mace ko namiji ? "

slowly ya juya ya kalli MALIKAT INAS , cikin sanyin murya ya ce " Nayel ne "

wani kyawatencen murmushi MALIKAT INAS ta saki har hawaye na zubo mata

a hankali Malik ya juya ya fice word room din ran shi fari tas kamar an yi mishi albishir da gidan Aljanna

a haka su ma su MALIKAT INAS su ka baro Word room din , kowace ta nufi part din ta na asali

shi ma Diya da Nesrine su ka koma part din su , haka Abdoul da Tesnim

Rafik kuma ya nufi fada ya bude ta , ya kira duk wani na fadar ya fada mishi ya dawo Ranar Friday za a sake nada Malik Nawfel Hicham Bin Jaabar

bangaran Malik kuwa kai tsaye part din MALIKAT HOUDA ya koma ,

babu ko sallama ya shigo parlourn , nan ya tardo ta zaune , sai faman addu'a ta ke yi

ta na ganin shi ta sauke ajiyar zuciya ta tashi da sauri ta nufe shi ta na fadin " masoyina , ba abun da ya same ka dai ko ? Allah na gode maka "

wani dan karamin murmushin geffen fuska ya sakin mata kafin ya ce " kin ga , ki daina kira na da masoyinki , so ki ke papi ya tardo ni , ya ce na kwace mishi matar shi "

wata yar karamar dariya ta saki ta na fadin " kai dai ka sani , mara kunya kawai "

" shikenan , bari na yi wanka , zan yi miki albishir me dadi "

" shikenan , ina jiran ka , mai martaba " ta fada cikin zolaya

bai ce mata komai ba ya nufi corridor ya shige bedroom din Inaya ke ciki , kai tsaye toilet ya wuce

โคโš˜



EXILED



PRINCE



โš˜โค



(



LOVE



MEETS



POWER



)



๐Ÿ‘‘๐Ÿ”ฅ



(



A



heart



touching



love



story



,



Romance



,



injustice



&



destiny



)





STORY



&



WRITTEN



BY



:



MEERAH



โš˜

๐Ÿ•Š



ใ€

THE



ROYALTY



LOVE



โค๐ŸŒนใ€‘

ใ€



BOOK



________3



๐Ÿ“š

โœ๐Ÿ’Œ



ใ€‘

_______________________

โ™กโ™กโ™กโ™กโ™กโ™กโ™กโ™กโ™กโ™กโ™กโ™ก

___

___________________



๏ฝ›



P



A



G



E



________





28

โœ

๐Ÿ’•๐Ÿ”ฅ

๏ฝ

bai



ce



mata



komai



ba



ya



nufi



corridor



ya



shige



bedroom



din



Inaya



ke



ciki



,



kai



tsaye



toilet



ya



wuce

dan ya yi wanka

jim kadan ya fito sanye da bathrobe

bed din ya nufo ya zauna , ya zauna a baki ya kai hannu ya bude bedside drawer ya fido A box

sannan ya ajiye a sama , sannan ya bude ya fiddo wata yar takarda

hannu ya sa ya rabata gida biyu , ya fido wata yar karamar allura irin ta dinki ta na da wani siririn zare blue

a hankali ya kai allurar nan wajen yankar da Aymane ya yi mishi , ya fara yi wa kanshi dinki , ya na lumshe idanunshi , ya na cije lips din shi na kassa dan ba karamin zafi a dakwai ba

amma a haka ya yi wa kan shi dinki , ya yi dressing wajen , sannan ya tashi ya nufi dressing room

jim kadan ya fito sanye da Trouser black color , da T-shirt sky blue , sai wasu sneakers farare a kafafun shi , ya daure wanan smooth hai din nashi a baya , sai tashin qamshi ya ke , sannan ya nufi kofar fita bedroom din ya fito

kai tsaye part din ya baki daya ya baro , ya nufi hanyar Fada

bakinshi da sallama cen kassan makoshi ya shigo Fadar , nan ya tardo duk mutanan fadar shi , su na zaune

su na ganin shi kowane ya saki murmushi ya na mikewa tsaye su na gaishe shi cike girmamawa

sai da ya karaso tsakiyar fada sannan ya juya ya kalli side din su

tsayawa ya yi ya kare musu kallo na dan lokaci kafin ya ce " na ji dadin ganin ku cikin koshin lafiya "

a tare duk su ka saki wani kyawatencen murmushi su na fadin suma sun ji dadin ganin shi a raye

dan sunkuyar da kai ya yi kafin ya dago ya ce " okay , zan so ku fara shirye shiryen nada sabon Malik ranar Friday , sannan Dalil ( sabon Sarkin bayi ) zan so ka mayar da bayan ki part din su , sannan gobe ka sa su je part din Malik su kwashe duk kayan da ke ciki za a zuba sabi , duk wani abu da ke bukatar gyara a cikin masarautar nan har ma wajen ta kawai ku aiwatar , kar ku damu da adadin kudin za a kashe , Idris ( shi ne sabon me kula da dukiyar Daular ) ka bude bankin masarautar , na ba da dama a fitar da kudin da su ka dace dan ganin an kyara masarautar , amma abu na farko da na ke son ku fara shi ne cire min wadanacen banzan status da a ka kafa min bakin Daula , General Abdallah , duk mutanan Fadar Aymane da ke hannun jami'an ka , ku yi executed din su kawai , ita kuma Hafsat a mayar da ita wajen mahaifiyar ta , sannan ku shirya min zama da yan JARIDA a matsayin Mr president ba Malik ba ran monday "

( Idan ba ku manta ba tun farko na ce muku Malik shi ne shugaban kassar Saudiya , kuma duk wata maganar administration a hannun shi ta ke , hakan na nufin shi ne sarki kuma president din kassar Saudiya , mutanan Fadar shi kuma duk yawwancin su ministers ne )

" an gama ya shugaba " su ke fada a tare sannan su ka shiga jero mishi addu'a

cikin zuciyarshi ya ke amsa musu da Ameen kafin ya juya ya sa kafa ya baro fadar

tafiyar shi ya ke cikin konciyar hankali ya na bin Daular da kallo , a haka har ya karaso cikin word room

kai tsaye dakin da ya kai Inaya da farko ya nufa , kawai sai ya ga babu kowa a ciki

da sauri ya juya ya koma reception ya na tambayar matar shi

cikin nitsuwa Wata nurse ta ce mishi " an sauya musu daki , su na cikin room 5 "

bai bata amsa ba ya juya ya nufi room 5 , babu ko sallama ya tura kofar ya shiga

ya na idanunshi su ka sauka saman ta , ta na konce saman gado ta na sanye da wata gown blue irin ta ma su jinya , idanunta a lumshe da allamun barci ta ke ko har yanzu ba ta farka da ga sumar ta ba

kusan gadon ya ga wani dan cradle tsayin shi daya da gadon Inaya

a ciki ya hango babyn su konce a ciki , an dunkule shi cikin wani farin towel idanunshi na bude ya na kallon ceiling , idanunshi Tak tak irin na Malik wato hazel

wata nanauyar ajiyar zuciya Malik ya sauke kafin ya tako a hankali kamar barawo ya karaso gaban su

tsayawa ya yi ya na bin babynshi da kallo

ya na a haka kawai ya ga idanun babyn sun juye kamar yadda a ke juya PAGE din littafi su ka koma farare kal kafin su dawo dai'dai

wani dan karamin murmushin geffen fuska ya yi murya cen kassan makoshi ya ce " idanun momynka ka dauko "

ya na gama fadar haka ya tako a hankali wajen shi , har kai hannu zai daukar babyn ya tsaya cak ya na kallon Tambarin masarautar a wuyan babynshi

lokaci guda kawai ya ji ranshi ya baci

da sauri ya janye hannunshi ya juya da sauri ya fice dakin

kai tsaye office din doctor din da ta karbi haihuwar Inaya ya wuce

babu ko sallama ya tura kofar office din ya shigo ya na fadin " wa ya ba ku izinin yi wa babyna tambarin masarautar nan ? "

a hankali Doctor ta mike ta na fadin " ranka shi dade b..... "

ba ta kai karshen maganar ta ba ya katse ta da cewa " ki ba ni amsar tambaya ta kawai "

" MALIKAT AL'UMU " ta fada a takaice

bai ce mata komai ba kawai ya juya ya fice office din , kai tsaye word room din ya baro ya nufi part din MALIKAT AL'UMU ya na taku da sauri , duk yanayin face din shi ya sauya da allamun ranshi ya baci

babu ko sallama ya shigo parlourn MALIKAT AL'UMU ya na kiran " momy ! , momy ! momy ! " ya ke fada da karfi ya na tsaye tsakiyar parlourn

da sauri MALIKAT AL'UMU ta fito da ga corridor a rude ta ke fadin " lafiya ka ke min irin wannan kiran ? me ya faru ? "

cikin bacin rai ya ce mata " momy , why za ki ce a yi wa babyna tambarin masarauta ? , why ? "

" zo mare ni Nawfel , mare ni na ce don Allah " ta fada cikin tsare gida

wani dan karamin tsaki ya ja ya na kauda kai gefe kafin ya ce mata " momy , ni fa ban bada izinin yi wa babyna wannan abun ba , why za ki min haka ? "

" saboda yaron Malik ne , kuma dole a yi mishi tambarin masarauta , kar ka ce za ka goge shi , wlh za ka ji mishi ciwo ka ga har yanzu ba wani kwari ne da shi ba "

" momy ba na son abun da zai hada babyna da wannan masarautar , that's why na yanke shawarar komawa US da su bayan nadin Malik "

dan zaro idanu MALIKAT AL'UMU ta yi ta na fadin " what ? ban gane ba , kamar ya za ka koma US da su ? ka na nufin ba za ka zauna ba ? "

cikin sanyin murya ya ce mata " yeah , ba zan zauna ba , ni dama ban dawo da Niyar zama ba , kuma in sha ranar Next Friday zan koma US , dalilin da ya sa ban bada izinin yi mishi tambarin masarautar nan ba , amma kin je kin ce a yi mishi , gaskiya momy ban ji dadin haka ba "

a hankali MALIKAT AL'UMU ta nufi Sofa , ta zauna ta na kallon shi fuska a marairaice ta ce " yanzu tsakani da Allah Nawfel komawa za ka yi , tun da komai ya wuce ka zauna cikin familyn ka mana "

a hankali ya tako wajen sofar ya zauna geffen ta murya a sanyaye ya ce " momy , ba zan yi miki karya ba , these months that I spent there were the best of my entire life, I felt free, without any pressure, just her and me , na ji dadin zamana a cen fiye da komai , please kar ki ce za ki tsayar da ni , i promise duk bayan sallar Azumi za mu dinga dawowa mu yi babbar sallat a nan , just let me go please "

shiru MALIKAT AL'UMU ta yi ta rasa abun da za ta ce mishi , ita ta na farin cikin komai zai dawo dai'dai , amma ya ce zai koma , zai sake barin su

a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce " kujerar Malik kuma fa ? wa zai hau ta yanzu ? "

" Diya " ya fada a takaice

" ka sani Diya ba zai iya hawa kujerar nan ba , in da ma a ce Abdoul ne da zai iya hawa "

" na sani momy , amma shi za a nada , dan na san Bayan shi babu wanda zai iya rike min ahalina , na san zai kula da masarautar nan kamar yadda ni zan kula da ita , na yarda da Diya fiye da rayuwata , ba dan shi ba da yanzu ban san inda zan tsinci kai na ba , ba dan shi ba da ba zan taba haduwa uncle bare har ya ba ni auren Cutie , duk wani abun al'heri da ya same ni cikin rayuwata shi ne sila , shi ya sa na yarda da shi fiye da rayuwata , he is my best and ONLYfriend's , He is my Brother not my Cousin , dan haka ya na da ikon hawa kujerar Malik "

wani dan karamin murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta ce " ka tabbatar shi ne abun da ka ke so ? "

" na tabbatar momy " ya fada kai tsaye

" shikenan , amma kar ka fadawa kowa maganar nan , har ranar nadin "

" okay momy " ya fada ya na mikewa tsaye

da sauri MALIKAT AL'UMU ta ce mishi " ina kuma za ka tafi ? "

" ina son na ga babyna kafin mu tafi mosque lokacin sallat ya yi "

da to kawai ta amsa , da ga haka ya sa kafa ya fice part din

har ya nufi hanyar word room a ka fara kiran sallat , kawai sai ya juya ya nufi mosque dan ya yi sallat

bayan sun yi sallat , Diya ya ja hannunshi ya nufi part din shi da shi , sai tambayar shi Malik ya ke me ya faru , ya sake shi

amma ko sauraron shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login