Showing 114001 words to 117000 words out of 135778 words

Chapter 39 - Exiled Prince Book Three Complete Hausa Novel

Meerah   

24 Oct 2025

326

kin yi ke ma " ya fada ya na kai hannu ya dan zunguri kanta

wata yar karamar dariya ta yi ta na fadin " It's a problem to have a dream ? ni kawai abun da na ke so kenan " ta kai karshen ta na turo dan bakin nan nata

dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " okay , yanzu fada min , idan na cika mafarkin ki , me za ki ba ni ? "

cike da zumudi ta ce " duk abun da ka ke so "

" don't be sure , da gaske za ki iya ba ni abun da na ke so ? " " ya fada ya na daga mata gera guda

a hankali ta gyada mishi kai allamun Eh

" ko da kuwa ....... " ya rada mata karshen a kunne , ni dai ban ji abun da ya ce ba

da sauri ta girgiza kai ta na marairaice fuska ta ce " no gaskiya ba zan iya ba baby , wai har yanzu ba ka bar maganar nan ba ? "

" ta ya ki ke so na bari , idan kin shirya yi min zan saya miki Island din baki daya , na tafi na yi wanka "

ya kai karshen ya na mikewa ya nufi toilet ya shiga

jim kadan ya fito sanye da bathrobe , ya na fitowa ya wuce kai dressing room , kamar ko ya san kayan su na nan

jim kadan ya fito sanye da wani wando Jeans black color , da T-shirt black color ita ma

a hankali ya karaso wajen ta , kawai sai ya ga har ta yi barci

bai yi kokarin tashe ta ba , ya janyo duvet ya rufe ta har zuwa kirji sannan ya manna mata kiss saman forehead kafin ya juya ya nufi kofar fita dakin

security din ya cire sannan ya bude kofar ya fito kai tsaye parlour

nan ya tardo su zaune sun yi zugum kamar an aiko da mutuwa

cak ya tsaya ya na kallon su murya a sanyaye ya ce " lafiya ku ka zauna a haka ? mutuwa a ka yi ? "

a tare duk su ka dago kai su kalle shi , ya na tsaye ya rike hannayan shi a baya

a hankali ya bude hannayan shi ya na kallon RIANNA , da gudu su ka tasso ita da Tesnim su ka fada jikin shi , su na sakin kuka

cikin sigar rarrashi ya ce " wlh in ba ku yi min shiru ba sai na koma inda na fito "

da sauri RIANNA ta ce " shikenan , shikenan , mun yi shiru , ba kuka mu ke ba "

" that's good , yanzu ku sake ni , kar ku karaya min baya "

va musu su ka sake shi , su ka tsaya gabanshi har su na hada baki wajen cewa " i have really missed you "

" ni ma na yi kewar ku over " ya fada cikin sanyin murya

wata yar karamar dariya RIANNA ta yi ta na sakin kuka lokaci guda , na lura RIANNA kamar MALIKAT INAS ta ke , abu kadan sai ta saki kuka

a hankali ya raba jikin shi , ya raba ta geffensu ya nufi MALIKAT AL'UMU ya rungume ta

rungume shi tsam ta yi ta na fadin " na yi kewar ka sosai my baby "

a hankali ya raba jikin shi da nata sannan ya nufi MALIKAT INAS

tun kafin ya karaso ta nufe shi da sauri ta rungume shi ta na fadin " kar ka sake tafiya ka bar ni don Allah "

cikin sigar rarrashi ya ce mata " kar ki damu Ammie , ba zan sake rabuwa da ku ba "

wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke ta na murmushi

a hankali ya raba jikinshi da nata ya juya ya kalli MALIKAT HOUDA

cikin zolaya ya ce mata " wai ke tsohuwar nan har yanzu ba ki mutu ba ? "

" karbi nan dan rainin hankali kawai , don Allah zo kashe ni in ka gaji da gani na " ta fada ta na matse mishi fuska

dan tabe baki ya yi ya na kauda kai ya ce " ni tambaya ce kawai na yi "

wata yar karamar dariya MALIKAT INAS ta yi ta na fadin " kai dai ka na son takurawa mamie , me ta yi maka ? ko dan ta na son ka shi ne za ka yi mata wannan shegantakar ? "

" ai ni ban ce ta so ni ba " ya fada ya na kara shan tsami

da ga haka ya ce musu " kun ci abinci ? ko ba ku jin yunwa ? "

" Yanzu mu ke wa Inas mu koma part din mu , mu shirya muku abinci " fadin MALIKAT AL'UMU

cikin nitsuwa ya ce mata " No , ba na son kowa ya bar part din nan , mamie bedroom nawa ne a part din ki ? " ya kai karshen ya na dawo da kallon shi kan MALIKAT HOUDA

kai tsaye ta ce " bedroom takwas ne a ciki "

gyada kan shi ya yi a hankali ya na fadin " okay , ba damuwa na san za su ishe ku kafin a gyara masarautar , ba na son ku fita bayan wannan azzalumin ya na cikin masarautar , duk wani abu da za ku bukata zan kawo muku "

da sauri RIANNA ta ce " kai kuma fa Akhie ? "

dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya ce " kar ku damu a kai na , kawai ina son na tabbatar ku na cikin koshin lafiya "

" wacen Azzalumin kuma fa ? ya ce zau sauka da ga saman kujerar ? " MALIKAT INAS ta fada

" Yeah , nan da Friday za mu sani " ya na gama fadar haka ya nufi hanyar fita parlourn ya fice

da kallo su ka raka shi har sai da ya fita sannan MALIKAT INAS ta tasso ta riko hannun RIANNA ta na fadin " mu je ki sauya kayan nan "

ba musu RIANNA ta bi bayan ta su ka shiga corridor

bangaran Malik kuwa ya na baro part din ya shiga motar shi kai tsaye ya fice masarautar





AFTER SOME HOURS

bai dawo masarautar ba sai karfe goma sha biyu na dare , ko ina ya tafi ? oho

bakin shi da sallama cen kassan makoshi ya shigo parlourn MALIKAT HOUDA

kamar aljana ta na zaune ita kadai cikin parlourn , ta na kallon waje guda

a hankali ya karaso geffen ta ya zauna ya na fadin " me ki ke yi a nan ke daya ? "

ba tare da ta kalle shi ba ta ce " nothing , kawai na kassa barci ne "

" Da gaske , me ya faru ? tunanin me ki ke ? ko cikinki ke ciwo ? "

a hankali ta girgiza mishi kai ta na dan karamin murmushi ta ce " uncle ne ya tsayar da ni , wai ya na son magana da kai "

cikin rudu ya ce mata " ban gane ba ? "



a hankali ta sauke nunfashi , ta lumshe idanunta kafin ta sake bude su , sun koma farare kal

a hankali ta juyo ta kalle shi cikin a hankali ta bude baki ta ce " wai kai komai sai an kwatanta maka ne ? " ta fada da murya tak tak irin ta Malik HICHAM

ba karamar razana Malik ya yi ba har sai da ya yi baya ya na zaro idanu ya na karanto kalmar shahada cikin zuciyar shi

bushewa da dariya ta yi ta na fadin " wlh kai da momyn ka duk matsorata ne , dubi kamar ka ga wani aljani , ko da ya ke na mutu ashe dole ka ji tsoro , ba ni da isashen lokaci , kawai na zo na fada maka a kan ka yi hankali lokacin duel din ku , Aymane ba abun da ka ke tunani ba ne , ya ma wuce tunanin mutum , ba za ka iya kashe shi ba kai tsaye , dole ka fara kawo karshen sihirin shi , Idan ba haka ba ba zai mutu ba , ni kai na ban san inda ya boye karfin sihirin shi ba , da na je na kawo karshen shi , zabi guda gare ka , da ka samu dama ka cire mishi kai kawai ta haka ne kawai zai mutu idan ba haka ba tashin hankali da za ka gani da ga baya ya karfin tunanin mai tunani "

ta na gama fadar haka ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya , ta ja wani dogon nunfashi kafin ta lumshe idanunta , ta sake bude su a hankali ya ga sun koma dai

²

a hankali ta juyo ta kalle shi ta ce " baby me ya faru ? "

wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce " ba komai "

wani dan karamin murmushi ta saki sai kuma ta tsuke fuska lokaci guda ta na fadin " sai yanzu ka dawo , ni na yi fushi ma da kai " ta kai karshen ta na kauda kai

" sorry Cutie , na tafi yin wani aiki ne " ya fada cikin sanyin murya

turo dan bakin nan nata ta yi ta na fadin " baby yunwa na ke ji , tun tafiyar ka ban ci komai ba "

" shikenan , me ki ke ki ci ? "

da sauri ta ce mishi " irin abincin da ka ke min a US " ta fada ta na sakin wani dan karamin murmushi

gyada mata kai ya yi kafin ya ce " okay , jira ni ina zuwa "

da to kawai ta amsa mishi , da ga haka ya tashi ya nufi kitchen ya shiga

da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta saki wani dan karamin murmushi

sai da ya dauki one hour a cikin kitchen din kafin ya fito ya na rike da wani tray

kai tsaye gabanta ya karaso ya zauna a kassa saman carpet , sannan ya ajiye tray din a gaban shi ya na ce mata ta sauko

ba musu ta sauko kassa su na fuskantar juna , ya fara ba ta abincin da kan shi

sai da ta kammala sannan ya dauki tray din ya mayar da su kitchen sannan ya dawo parlourn

ta na zaune saman sofa ya tardo ta , ta shafar cikin ta

a hankali ya karaso wajen ta ya zauna ya na fadin " yanzu tashi ki je ki konta "

shagwabe mishi fuska ta yi ta na fadin " ba tare za mu kwana ba ? "

a hankali ya girgiza mata kai allamun a'a

shiru ta yi ta na kallon shi babu ko kiftawa

sai da ta dauki lokaci kafin ta ce " baby , amma akwai abun da ke damun ka ko ? "

" me ki ka gani ? " ya fada a sanyaye

" kawai na ga yanayin face din ka ya sauya ne "

" ba zan miki karya ba , ina cikin damuwa , ba kadan ba , amma duk lokacin da na tare da ke na kan ji damuwata ta tafi , please don't leave me , kar ki tafi ki bar ni "

wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta rungume shi ta na fadin " mutuwa ce kadai za ta raba ni da kai "

a hankali ya zagayo da hannayanshi a bayanta ya rungume ya na sauke ajiyar zuciya a hankali





AFTER TWO DAYS

🤧🔥

yau ta kama ranar Friday , tun karfe 6 a ka fara shirye

²

n duel din Malik da Aymane

misalin karfe 8 kowa ya hallaci wajen da za a gabatar da duel din , a cikin garden a ka shirya yin duel din

kowa na cikin masarautar sai da ya hallaci wajen , da mutanan fadar Malik , da kuma na fadar Aymane , har da su MALIKAT INAS , da Inaya ba rokon da su mama ba su yi mata ba a kan ta zauna , amma fir ta ki ta ce sai ta je

a tsaye Malik da Aymane su ke tsakiyar garden din , su na fuskantar juna , Rafik na tsaye da ga tsakiyar su a gefe

cikin nitsuwa ya fara magana ya na fadin " kun san yadda tsarin fada da takobi ya ke , ban da zalinci "

cikin nitsuwa Aymane ya katse shi da cewa " ka ga don Allah ka ba mu waje mu yi mu wuce wajen , a sani na ka kashe ko a kashe ka shi ne tsarin wannan fadan , dan haka ka wuce ka ba mu waje "

" za ka iya tafiya Rafik " Malik ya fada cikin sanyin murya

gyada mishi kai Rafik ya yi kafin ya juya ya karbi Sword din da ke hannayan Azim da ke tsaye bayan shi

ya mikawa Aymane guda , sannan ya mikawa Malik guda ya na fadin " Allah ya ba mai rabo sa'a " amma cikin zuciyar shi Malik kawai ya ke yi wa addu'ar samun nassara , da ga haka ya bar wajen ya koma wajen da a ka shiryawa ma su kallo

ya zauna saman chair din shi geffen MALIKAT AL'UMU , ya na zama ko Aymane da Malik su ka fara fadan su

a hankali MALIKAT AL'UMU ta juyo ta kalli Rafik ta ce " Rafik , wai fadan minene su ke yi ? "

wani dan karamin murmushi Rafik ya yi ya na fadin " ranki shi dade , wanda ya yi nassara shi zai hau kujerar Malik "

" Wanda bai yi nassara kuma fa ? " MALIKAT INAS ta fada

dan jinkirtawa Rafik ya yi kafin ya ce " mutuwa zai yi "

a tare su ka ce " inallillahi wa'ina illaihi raji'un , ka na nufin idan Malik bai yi nassara ba kashe shi Aymane zai yi ? "

a hankali ya gyada mishi kai ya na fadin " ina jin tsoron hakan ranki shi dade , addu'a kawai za ku yi Allah ya ba shi sa'a , idan Aymane ya yi nassara za mu shiga babban tashin hankali dan babu wanda zai iya yin jayaya da shi a kan kujerar Malik "

kalmar shahada MALIKAT AL'UMU da INAS su ka shiga jerowa , kenan kashe musu yaron su za a yi in dai bai yi nassara ba , nan take zuciyoyinsu su ka fara bugawa da karfi

a hankali MALIKAT INAS ta juya ta kalli su Malik dai'dai lokacin da Aymane ya samu Malik a damtsen shi na dama ya yanke shi nan take ya fara zubar da jini har ya gangaro saman takobin hannunshi

da sauri Inaya ta rumtse idanunta , ta na kauda kai gefe

a hankali RIANNA ta riko ta , ta na fadin " ko mu koma ciki ? "

girgiza mata kai Inaya ta yi ta na fadin " a'a Aunty RIANNA "

da to kawai RIANNA ta amsa mata kafin su ci gaba da kallon su Malik

wata yar karamar dariya Aymane ya yi lokacin da ya ji wa Malik ciwo a hannu ya na fadin " ya ,har ka gaji ? still yanzu ma mu ka fara "

a hankali ya kai hannun shi na hagu ya riko sword din , dan ba karamin rauni ya samu ba , ba zai iya ci gaba da fadan da hannun damar ba

wata yar karamar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya nufi Aymane , shi ma Aymane da gudu ya nufo Malik

sai dai kafin ya kai ga daga takobin shi , Malik ya juya ya ba shi baya ya caka mishi sword din shi a ciki har sai da ta fito mishi ta baya

da sauri Malik ya juyo ya yi baya ya na kallon Aymane da ke zubar da jini ta bakinshi

wata nanauyar ajiyar zuciya duk mutanan Malik su ka sauke MALIKAT AL'UMU da INAS su na yi wa Allah godiya cikin zuciyoyinsu

da sauri Inaya ta mike tsaye ta na kallon Malik ta ce " ka cire mishi kai ! " ta fada da karfi har sai da hankalin kowa ya dawo gare ta

Malik na jin hakan ya tuno abun da ta tabba fada mishi lokacin da ya ce wa Aymane su yi duel din na ya cire mishi kai ta haka ne kawai zai mutu

tuno hakan ne ya sa shi nufar Aymane da sauri zai zame takobin shi

sai dai kafin ya karaso ya ga Aymane ya zare takobin da kan shi ya tilla gefe ya na sakin murmushi

" ka kashe ni , amma ba za ka iya ja da shi ba " Aymane ya fada jini na fitowa da ga bakin shi

kafin Malik ya yi taku biyu , kawai ya ga skin din Aymane ta koma green scales na fito

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login