Showing 129001 words to 132000 words out of 135778 words
/>
ya na sanye da wandon Jeans white color , da T-shirt blue color , ya daura wata jacket a sama White color , kafafun shi na cikin wasu sneakers Navy blue , da gani renon madara da ice cream
da gudu ya ke sauko stair din ya na wata yar karamar dariya
ya na gama sauko stair din Malik ya shigo parlourn ya na sallama
yaron nan na ganin shi ya nufe shi da gudu ya na fadin " Daddy , tun dazu fa na ke jiran ka , har na yi fushi " ya fada cike da shagwaba
a hankali Malik ya sa hannu ya dauki yaron nan ya na fadin " I'm sorry my Prince , tell me kun gama shiryawa mu tafi ? "
da sauri Prince ya ce " yeah , kai kadai mu ke jira , na matsu na ga Ammie , da mamie , da mama , da Uncle " ya fada cike da shagwaba
( hmmm , ko da ga ina ya dauko wannan shagwabar ?
🤔🤔
)
" okay , where is your mom ? " Malik ya fada
" wait " Prince ya fada kafin ya juya ya kalli Stair ya ce " Momyyyyyyyyy ! " ya fada da mugun karfi sai da Malik ya lumshe idanunshi ya na fadin " Prince slowly mana , ka fasa min kunne "
ya na gama fadar haka Inaya ta fara sauko stair ta na sanye da wata Abaya fara kal mai mugun kyau an yi mata zanen flower kamar rainbow , ta yafa veil din ta fari shi ma , ta na sanye da wasu sneakers pink color a kafa , ta na rataye da wata yar bag pink color ita ma
ta cika ta yi bul bul abunta , da ga gani ta samu hutu , har wani haske ta yi kumatu sun fito , gaskiya US ta zauna mata
tun da ta fara sauko stair Malik ya tsare ta da ido babu ko kiftawa , sai magana prince ke yi mishi amma ba ya jin shi
a hankali Prince ya kai hannu saitin fuskar Malik ya kyasta mishi yatsu ya na fadin " Daddy , tun dazu ina maka magana ka kyale ni , sai kallon momy ka ke kamar ba ka san ta ba "
a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya dai'dai lokacin da Inaya ta karaso gaban shi ta na fadin " mu tafi ko ? "
gyada mata kai Malik ya yi a hankali ya na murmushi kafin ya riko hannunta , ya juya su ka fita parlourn , su ka fito harabar gidan ,
su na fitowa sai saman motar Malik , kai tsaye ya budewa Inaya wajen mai zaman banza , ta shiga sannan ya rufe kofar
ya zagayo ya bude wajen driver ya shiga tare da Prince ya zaunar da shi saman cinyoyinshi ya yi tukin a haka har su ka bar gidan su ka nufi hanyar Airport
â–ª
DAULAR SAUDIYA
👑🔥
zaune MALIKAT AL'UMU ta ke cikin parlourn tare da MALIKAT INAS sai murmushi su ke saki
su na a haka RIANNA ta shigo ta na sallama ta na fadin " Ammie , momy mu tafi sauran ten minutes jirgin su ya sauka " ba ta jira amsar su ba ta juya ta fice da sauri ta na sakin murmushi
a tare MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU su ka fito part din , su na fitowa sai saman wasu motoci a jere bakin part din , a tare su ka shiga motar da ke gaban su , su na shiga motocin su ka tada su ka bar masarautar da mugun gudu su ka nufi airport
a jere motocin su ka shiga airport , kai tsaye wajen saukar jirgi su ka nufa , sannan su ka yi parking ,
daya bayan daya su ka fara sauko motocin , Diya da Nesrine su ka fito da ga cikin motar su tare da Junior din su
RIANNA kuma ta fito da ga cikin motarta tare da mama da MALIKAT HOUDA
MALIKAT AL'UMU da MALIKAT INAS kuma cikin mota guda
sannan Abdoul da Tesnim su ka fito cikin mota guda tare da wata kyakyawar yarinya a shekaru ba za ta wuce 3 or 4 years ba , kyakyawa ce gaskiya kamar an tsaga kara da Abdoul dan ta na kama tak da shi , sai dai ta dauko farin Tesnim dan kamar ka taba jini ya fito ta ke har wani ja ta yi
ta na ganin MALIKAT AL'UMU ta nufe ta da gudu
wani cool murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta durkusa ta dauki yarinyar nan ,
a hankali duk su ka karaso wajen motar su MALIKAT AL'UMU su ka tsaya
da sauri MALIKAT HOUDA ta ce " wai har yanzu ba su iso ba ? "
wata yar karamar dariya duk mutanan wajen su ka yi kafin Diya ya ce " mamie , mu ma duk mun matsu mu gan su "
har ta bude baki za ta yi magana su ka jiyo karar jirgi
a tare su ka kai kallon su wajen da su ka jiyo sautin su na fadin Alhamdoulilah cikin zuciyoyinsu
a hankali jirgin nan ya sauka , ya tsaya ya na fuskantar motocin su
sai da ya yi two minutes a haka kafin kofar jirgin ta bude a hankali
a tare Malik da Inaya su ka fito da ga cikin jirgin Malik ya na dauke da Prince duk jikin shi ya yi sanyi allamun barci ya ke
a tare duk su ka nufe su su na yi musu barka da zuwa , da sauri MALIKAT INAS ta kai ta karbe shi nan ta ga ashe barci ya ke , amma duk da haka sai da karbe shi
da ga haka su ka shiga rungumar juna , specially Diya , da ya rike Malik sai da RIANNA ta shiga ce mishi ya sake mata dan uwa ita ma ta rungume shi , ita dai Inaya tun da ta rungume mama ba ta sake ta ba har kowa ya hakura ya bar ta dan sun San yadda kewar uwa ta ke
da ga su ka shiga motocinsu su ka bar airport din su ka kama hanyar Daular Saudiya
ko da su ka isa kai tsaye Diya ya wuce da Malik building din shi tare da Abdoul
MALIKAT INAS kuma ta tafi part din su da Prince tare da MALIKAT AL'UMU da RIANNA da Tesnim
Inaya kuma ta bi mama tare da Nesrine su ka nufi part din MALIKAT HOUDA tare da Junior
â–ª
MALIK
tsaye ya ke a cikin parlourn part din shi a floor na uku sai bin wajen ya ke da kallo kamar bakwon shi
ya na a haka ya jiyo Muryar Diya a bayan shi ya na fadin " mu tafi ka yi wanka , ka huta , amma gaskiya abokina US ta zauna maka , ka na cen ka na shan dadinka ka kyale ni nan da aiki "
wani dan karamin murmushi Malik ya yi ya na fadin " ai ni zuwan tsaye na muku , dan gobe zan yi gaba da Cutie " ya kai karshen ya na fara takawa ya nufi corridor
cikin rudu Diya ke ce mishi " ban gane ? "
ko sannu Malik bai ce mishi ba ya shige corridor
sai da ya shiga sannan Diya ya juyo ya kalli Abdoul da ke tsaye gefe ya ce " har yanzu dai na miskilancin nan su na nan "
wata yar karamar dariya Abdoul ya yi ya na fadin " ai miskilanci a jininshi ya ke , ba zai taba fita ba , ba banza Allah ya hada shi da wadda ba ta iya rufe bakin ta ba "
" hmmmm , mu tafi mu ba shi wuri " Diya ya fada ya na nufar lift
ba musu Abdoul ya bi bayan shi su ka baro part din , dan Diya nashi part din daban ya ke , ko so guda bayan tafiyar Malik bai taba shiga building din ba , saboda wannan building musaman na Malik nz , shi ya sa ya yi nashi part din daban , amma mai floor biyu , sai in Malik na shirin zuwa sannan ya ke sa a bude shi a gyara part din , amma floor na hudu sai Malik ya zo da kan shi ya bude shi dan babu wanda ya san ya ma a ka rufe shi bare a bude sai Malik , dan a ganin shi sirrin da ke cikin wannan floor na nashi ne shi kadai , saboda a nan ne ya ga dare mafi mahimanci a rayuwar shi , a nan ne ya zama cikaken mutum dan haka ba wanda ke da damar shiga floor din , idan kuma za su koma US ya sake rufe shi , bayan shi da Inaya ba wanda ya taba hayo shi , har prince
kai tsaye Malik kuwa bedroom din shi ya nufa , ya na isa ya wuce kai tsaye Toilet
sai da ya share good one hour a ciki kafin ya fito daure da towel a kugunshi
ya na fitowa idanun shi su ka sauka saman ta , ta na zaune tsakiyar gado , ta jingina bayan ta a forehead din gadon ta na rike da wayar shi ta na latsawa
wani cool murmushi ya saki kafin ya karaso wajen gadon , ya zauna a baki ya kai hannu ya kwace wayar shi ya na fadin " ta ya a ka yi ki ka san ina nan ? " ya kai karshen ya na ajiye wayar shi saman bedside drawer
wani kyawatencen murmushi ta sakin mishi ta na fadin " tracker na saka maka a jiki, ba ka sani ba ? "
daga mata gera guda ya yi ya na fadin " Oh , da gaske ? "
" sosai ma kuwa " ta fada ta na kauda kai gefe
a hankali ya matso , ya kai hannu ya janyo ta a hankali jikinshi , murya kassa kassa ya ce mata " kin zo ko a dai'dai lokacin da ya dace "
" wane lokaci kuma ? " ta fada cike da shagwaba har da turo dan bakin nan nata
a hankali ya kai bakin shi saitin kunnen ta ya yi mata rada
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta zagayo da hannayan ta a kugunshi ta kara shigewa jikinshi ta na fadin " kai dai ba ka gajiya baby , yanzu fa mu ka zo ka bari mu huta mana "
" idan mun je cen mun huta " ya fada ya na yin kassa da zip din abayar ta
cikin rudu ta ce mishi " ina kuma za mu je baby ? "
" Honey Moon " ya fada a takaice ya na cire mata Abayar jikinta ya ajiye gefe
a rude ta ke ce mishi " Honey Moon kuma baby ? ka manta da Prince ko ? "
a hankali ya kai hannu ya balle mata bra din ta ya na fadin " ina tune da shi , wajen Ammie da RIANNA zai zauna , mu kuma , mu tafi inda za mu huta , na kula da Big babyna "
turo dan bakin nan nata ta yi ta na fadin " ni ka daina kira na da big baby , kuma ba ka fada min inda za mu je ba "
bai ce mata komai ba har sai da ya raba ta da bra din ta ya ajiye gefe sannan ya ce " it's a surprise "
har ta bude baki za ta yi magana kawai ta ji ya sauke lips din shi saman nata
a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta lumshe idanunta ta fara biye mishi ita ma
â–ª
AFTER SOME HOURS
a zaune duk su ke a dining room din part din Malik su na yin diner , MALIKAT AL'UMU , MALIKAT INAS , mama , Diya , RIANNA , Tesnim , Nesrine , Junior , Inaya , Abdoul , Yarinyar wajen Tesnim da shi kan shi Malik duk su na zaune saman dining room sai cin abincin su su ke su na hira su na dariya gwanin burgewa
cen na hango Prince konce saman Sofa , ya na rike da phone din Inaya ya na latsawa
a hankali ya sauko da kafafun shi ya mike tsaye ya fara takawa cike da izza ya karaso wajen Malik , ya kai hannu ya dan bubuga cinyar shi
a hankali Malik ya juyo ya kalle shi ya na fadin " what happening my Prince ? "
" Daddy , wannan lion na ke son ka saya min " ya fada ya na nuna mishi screen din wayar hannunshi
da murmushi a face din ta MALIKAT INAS ta ce " My prince , me za ka yi da lion kuma ? ba ka tsoron ya ji maka ciwo ? ko dai Teddy ne ? "
tsuke fuska Prince ya yi cike da dakiya ya ce " ba Teddy ne ba , Lion din gaske ne kuma sai an saya min "
a hankali Inaya ta daura hannun saman kan shi ta na fadin " Prince , ba fa lion din gaske ba ne Teddy ne , ba ka gani da kyau ba "
" to momy ai ni lion din gaske na ce ina so , ba Teddy ba , Daddy ka fada mata mana " ya kai karshen ya na dawo da kallon shi kan Malik
da sauri yarinyar da ke zaune saman cinyar Tesnim ta ce " Uncle , ni ina son Teddyn "
wata yar karamar dariya MALIKAT AL'UMU ta yi ta na fadin " ke dai princess , duk Teddyn da gare ki ba su ishe ki ba "
ta na gama rufe bakin ta Prince ya marairaice fuska kamar zai yi kuka ya na kallon Malik ya ce " Daddy "
a hankali Malik ya kai hannu ya dauki Prince ya daura saman cinyar shi , ya na fadin " da ka tashi dauko rigimar momynka sai da ka fita , me za ka yi da lion don Allah ? kuma lion ba ya cikin dabobin cikin gida , bari zan sayo maka Dog or cat wane ka fi so ? "
" Lion " ya fada a takaice
" ya salam " Malik ya furta a hankali cikin zuciyar shi kafin ya ce " okay , zan siya maka , kafin mu koma US , shikenan ? "
da sauri Prince ya girgiza mishi kai ya na fadin " Yeah , that's why i love you more than momy "
da sauri Malik ya rufe mishi baki ya na fadin " yi shiru kar ta ji "
ya na gama fadar haka ya jiyo Muryar Inaya ta na fadin " na ji ai , kuma na yi fushi da kai kar ka sake min magana " ta na gama fadar haka ta tashi ta nufi corridor
sai da ta shiga sannan Malik ya bude bakin Prince ya na fadin " ka gani ko ? to ai yanzu sai ka tashi ka je ka bata hakuri tun da ka bata rai "
ba musu prince ya sauko ya bi bayan momyn shi
da ga haka su ka ci gaba da cin abincinsu , su na hira har sai da su ka kammala sannan kowa ya tashi ya nufi part din shi
Malik da Diya kuma su ka zauna a parlour
sai da Diya ya tashi ya na yi wa Malik sai da safe ya tsayar da shi ya na cewa " please ka sa a shirya min Helicopter gobe wajen karfe 10 ko 12 haka "
cikin rudu Diya ya ce mishi " Helicopter kuma ? akwai inda za ka je ne ? wai kai ba ka iya zama waje guda ? ka san sunan da a ke kiran ka da shi ? THE EXILED PRINCE , babu wanda bai san wannan sunnan ba cikin Saudiya "
" yeah I'M AN EXILED PRINCE , I bought the island of Palawan in the Philippines three years ago , ina son mu tafi ni da ita , ta ga gidan da na yi mana a cen "
dan zaro idanu Diya ya yi ya na fadin " noooo , you're serious , yanzu Islande guda sukutum ka saya ? "
gyada mishi kai Malik ya yi ya na fadin " yeah , har da gidaje ma a sama dan yanzu haka a na cikin gina na ukun , ni dai ka yi abun da na sa ka please , kar ya wuce kar ya wuce karfe 12 please "
" nawa ka saye ta ? a sani na Island din Palawan ita ce No 1 a cikin jerin wajajen Tourism , ta ya a ka yi ka saye ta ? "
" five hundred millions of American dollars na yi cinikin ta , that's why su ka yarda , akwai kuma wata private Island a Thailand cikin archipelago din Koh Samui da a ka saka a kasuwa last year , ita ma na saye ta "
shi dai Diya ya tsaya kawai ya na kallon shi , ya ma rasa abun da zai ce wa Malik
" okay , zan sa a shirya muku duk abun da ya dace , Allah ya kiyaye hanya , Hope dai ba za ku jima