Showing 99001 words to 102000 words out of 135778 words

Chapter 34 - Exiled Prince Book Three Complete Hausa Novel

Meerah   

24 Oct 2025

345

ce ka na tare da ita a wannan lokacin , ko da shi ne last time din ta a duniya , ku yi shi a tare , yanzu ka sa kan ka cikin damuwa , ka saka ta cikin damuwa , hakan ko ba karamin hatsari ba ne ga mace mai karamin ciki , ka na neman ka kashe ta da kanka , shawara guda zan ba ka , ka je ka rungumi matar ka da babynku , why za ka juya mata baya a lokacin da ta fi bukatar ka a kusa da ita ? kai a ganin ka ka yi mata adalci ? kar ka bari son zuciya ya raba ka da ita tun kafin mutuwa ta raba ku "

slowly Malik ya dago kai ya kalle shi , cikin sanyin murya ya ce " i'm afraid , ba zan so na rasa ta ba , ita kadai ta yi min saura a duniya "

" in sha Allah ba abun da zai faru da ita , kamar dai ba ka san ikon Allah ba , ka kai kukanka gare shi , in sha Allah zai warware maka matsalar ka , bare kuma wannan dan karamin abu , mata nawa ne ke rasa rayukan su wajen haihuwa without her pregnancy was dared ? kawai lokacin su ne ya yi , idan lokacin ka bai yi ba ko cikin bakin lion ka ke ba za ka mutu ba , may be ita ma nata lokacin ba wajen haihuwa zai zo ba , kawai ka sakawa kan ka tsoro ne "

a hankali Malik ya sunkuyar da kai ya na kallon hannayanshi

murmushi mai dan sauti Aylan ya yi ya na fadin " na cika surutu ko ? "

" hmmmm , ai kai na ba ka ce komai ba , idan Cutie na magana sai ka ce an kunna radio sam ba ta gajiya da surutu "

wata yar karamar dariya ya yi ya na fadin " haka matan nan su ke da mugun surutu , ga shi yanzu ta koya min har ya kai ba na iya rufe baki na " ya kai karshen ya na wani dan karamin tsaki ya kauda kai gefe

shi dai Malik bai ce mishi komai ba ya tafi duniyar tunanin shi , har sai da Aylan ya tashi ya bar wajen bai sani ba

sai da ya share wajen ten minutes a haka kafin ya dago kan shi , ya na shirin magana ya ga wajen babu kowa

ya kalli dama ya kalli hagu , amma bai gan shi ba

kawai ya tambayi kanshi ko dai da aljani ne ya yi magana bai sani ba

a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya jingina bayan shi a jikin bancin ya daga kai sama ya lumshe idanu , har ga Allah ya na matukar kewar Cutie din shi , specially wannan yar shagwabar ta , da wannan dan bakin surutun nata , ya na kewar komai nata , wajen two months ya kwaurace mata baki daya , sai yanzu ya ke nadamar biyewa son zuciyar shi , da yanzu tare da ita zai zowa park din nan , shi ma katari ne a ka yi ya zo wucewa kawai ya ga wajen ya burge shi shi ne ya shigo , ya San ita ma zai mugun burge ta , gaskiya zuciya ba ta yi mishi adalci ba , gashi yanzu ta na neman ta raba shi da abun kaunar shi guda , shi kan shi bai san ya a ka yi ya jure tsawan watanni ba ta kusan shi , bare kuma ita da ta fi bukatar shi fiye da komai , bisa hallacin da ta yi mishi , ta so shi a lokacin da ba shi da komai , kowa na yi mishi kallon makaho da kurma amma a haka ta so ta zauna tare da shi gaskiya bai kyauta mata ba

❀⚘



EXILED



PRINCE



⚘❀



(



LOVE



MEETS



POWER



)



πŸ‘‘πŸ”₯



(



A



heart



touching



love



story



,



Romance



,



injustice



&



destiny



)





STORY



&



WRITTEN



BY



:



MEERAH



⚘

πŸ•Š



【

THE



ROYALTY



LOVE



β€πŸŒΉγ€‘

【



BOOK



________3



πŸ“š

βœπŸ’Œ



】

______________________

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

___________________



ο½›



P



A



G



E



β™‘β™‘β™‘



22

πŸŒΉπŸ•Š

}



β–ͺ

MISALIN KARFE 1 NA DARE

a hankali ya ke haura stair jiki a mace , ya sunkuyar da kai hannun shi rike da wata yar leda kamar ta restaurant

kai tsaye bedroom din shi ya nufa

har zai shiga ya jiyo Muryar ta kassa kassa kamar ta na gama

a hankali ya juya ya nufi bakin kofar bedroom din ta ya tsaya ya na sauraron abun da ta ke fada

zaune ta ke tsakiyar gadon ta yi irin zaman cin ruwa , ta na rike da waya a kunne ta na hawaye

sai da ya yi wajen one minute a haka kafin ya jiyo Muryarta ta na fadin " shikenan Ammie zan yi yadda ya ke so "

dan jinkirtawa ta yi kafin ta ce " sai da safe Ammie " ta na gama fadar haka ta sauko wayar ta ajiye gaban ta , ta saki kuka kamar ran ta zai fita

har cikin zuciyar shi ba ya jin dadin wannan kukan nata , yau ga shi kuma ta kuka saboda shi gaskiya bai ji dadin haka ba

ta na tsaka da kukan nata ta ji cikin ta ya murda

a hankali ta ce " Ashhhhhh , za ka fara ko ? "

a rude Ya tsaya ya na tambayar kanshi da wa kuma ta ke magana

ya na a haka ya sake jiyo Muryar ta ta na fadin " ka yi hakuri babyna , amma ba yadda zan yi dole na rabu da kai , ba dan Daddyn ka ba ya son ka ba , kawai bai shirya haihuwa yanzu ba , amma ya na son ka , sosai ma fiye da yadda na ke son ka , ba zan iya jure ganin fushin shi ba ko wace safiya , ka na gani ya daina min magana , ko kallo na ba ya yi , hakan ya na min zafi , ka yi hakuri amma ba za ka ci gaba da zama ba , Washhhh " ta fada da dan karfi ta na komawa ta konta ta takure waje guda ta rungume pillow ta na kuka kassa kassa

duk abun da ta fada ya ji ta , ya na jin ta fara yin kuka ya juya ya shiga bedroom din shi

jim kadan ya fito sanye da kayan barcin shi ya na rike da ledar da ya shigo da ita

a hankali ya tura kofar bedroom din ta , ya shigo ya na sallama cen kassan makoshi sautin ma bai fito ba

bed din ya nufa ya zauna bakin shi , sannan ya kai hannu ya na neman fido abun da ke cikin ledar ya na fadin " Cutie , za ki sha ice cream ? "

wata irin muguwar bugawa zuciyar ta ta yi har sai da idanunta su ka ciko da ruwa lokaci guda , wajen two months yanzu rabon da ta ji ya kira ta da wannan sunnan

a hankali ta mike zaune ta jingina bayan ta a forehead din gadon ba tare da ta dago kai ba

a hankali ya mika mata bowl din ice cream da wata yar karamar spoon

ba musu ta kai hannu ta karba ta bude bowl din ta fara sha

nan take ta ji ice cream din ta yi mata mugun dadi , sai da ta shanye ice cream din ba ta sani ba

ya na ganin ta shanye ya kai hannu ya karbi bowl din ya na fadin " me ki ke son ci yanzu ? "

" ba komai " ta fada a sanyaye ba tare da ta dago kan ta ba

bai ce mata komai ba ya mike tsaye ya tsaya gaban bedside drawer

da sauri ta riko hannun shi ta na tunanin fita zai yi , ta saki kuka ta na fadin " yaya Zayd kar ka tafi don Allah , na yarda mu zubar da cikin amma kar ka tafi ka bar ni don Allah "

a hankali ya ajiye ledar hannun shi saman bedside drawer din

sannan ya zauna saman gadon shi ma jingina bayan shi a jikin forehead din gadon ya zagayo da hannunshi a bayan ta ya rungume ta

nan take ta kara kankame shi ta na kara sautin kukan ta

murya kassa kassa ya ce mata " i'm sorry my Cutie , na bar ki a lokacin da ki ka fi bukatar kulawa ta , na san ban yi miki dai

Β²

ba , ban rike amanar da ki ka ba ni ba , ki yi hakuri please kar ki ce kin tsane ni " ya kai karshen ya na zagaye da dayan hannunshi a bayan ta

wani dan karamin murmushi ta saki cikin kukan nata

da sauri ya ce mata " shikenan ya isa haka ki daina kukan nan ko sai kin janyo wa kan illa ? "

a hankali ta girgiza mishi kai ta na fara rage sautin kukanta

bai ce mata komai ba ya konta da ita a jikin shi , ya janyo duvet ya rufe kafafun su har zuwa kugu

cikin sanyin murya ya ce " Cutie ! "

" uhm " ta fada ba tare da ta bude idanunta ba

sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " bude ido ki kalle ni "

ba musu ta fara bude idanun ta a hankali , ba su sauka ko ina ba sai cikin nashi

ya na ganin ta bude idanunta ya ce mata " i'm sorry my Cutie "

wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta gyada mishi kai a hankali ba tare da ta ce komai ba

a hankali ya matso ya daura forehead din shi saman nata murya cen kassan makoshi ya ce mata " I Love you "

wannan karan sai da ta yi murmushi mai dan sauti kafin ta ce " i love you too "

" shikenan yanzu fada min , ki na son cin wani abu , ? "

a hankali ta girgiza mishi kai allamun a'a

cikin sanyin murya ya ce " okay , rufe ido ki yi barci yanzu "

ba musu ta lumshe idanunta , ta na sakin murmushi , shi kuwa ya tsare ta da wadanan hazel eyes din nashi , ya rasa wace irin zuciya ce da ita , da a ce wata matar ce daban ya yi wa wannan abun , ko mutuwa zai yi ya na ba ta hakuri ba za ta yarda ba , amma sai ga shi ko bata lokaci ba su yi ba har ta hakura

a hankali ya fara karanto musu addu'ar barci sannan ya lumshe idanunshi , ba jimawa barci ya yi gaba da su



β–ͺ

WASHE GARI

β›…

a hankali lips din shi su ka motsi allamun ya na karanto addu'ar tashi da ga barci , sannan ya ware idanunshi a hankali

ba su sauka ko ina ba sai saman face din ta

har yanzu sai sharar barci ta ke cikin konciyar hankali , shi kan shi bai san abun da ya tada shi ba saboda ya jima bai yi irin wannan barcin mai dadi bare kuma ita

a hankali ya raba jikin shi da nata , sannan ya sauko da kafafun shi kassa ya mike zaune ya sauke wata yar karamar ajiyar zuciya

sai da ya dauki two minutes a haka kafin ya juya a hankali ya kalle ta , rigar barcin ta ta nade ta yi sama , cikin ta ya fito waje bare ko ya kara girma ya fito sosai

a hankali ya juya kafin ya mike ya fara takawa a hankali ya fito dakin maimakon ya shiga nashi bedroom sai na ga ya nufi stair ya sauko , kai tsaye ya shiga kitchen

nan ya tardo wasu maid guda biyu su na shirya musu breakfast

cikin girmamawa su ka gaishe shi

cen kassan makoshi ya amsa musu sannan ya ce su ba shi waje zai shirya breakfast din da kan shi

ba musu su ka baro kitchen din

su na fita ya fara shirya musu breakfast

sai da ya share good one hour a kitchen ya na shirya musu lafiyayen breakfast , ni kai na sai da na yi mamakin yadda ya iya girki haka

sai da ya shirya musu komai saman sannan ya fito ya daura saman dining table sannan ya nufi stair ya haye ya koma bedroom din ta

ya na shiga kawai ya ga ba ta saman gadon , amma ya ji kamar ruwa na zuba da ga cikin toilet kenan ta na wanka

jin hakan ne ya sa shi juyawa ya shiga bedroom din nashi shi ma dan ya yi wanka

bai fi ten minutes da fita ba ta fito da ga cikin toilet din , ta na sanye da bathrobe , kai tsaye ta wuce dressing room

jim kadan ta fito sanye da wando palazzo pink color da wata t-shirt white color , ta daure gashin kan ta a baya ta na takowa a hankali

kai tsaye bed din ta ta nufa ta haye ta konta , ta lumshe idanunta

a hankali ya turo kofar dakin ya shigo ya na sallama cen kassan makoshi hannun rike da tray din breakfast din da ya shirya

kai tsaye Sofas din da ke dayan geffen dakin ya nufa

ya ajiye tray din a saman table ta tsakiya

sannan ya juya ya nufi bed din , ya zauna a baki , ya kai hannu saman kumatun ta ya na fadin " sai a tashi safiya ta yi "

wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ware idanunta , a sanyaye ta ke kallon shi

" tashi mu yi breakfast " ya fada ya na janye hannunshi da ga saman kumatun ta , ya mike tsaye bakin gadon ya na kallon ta

a hankali ta sauko da kafafun ta kassa kafin ta mike tsaye , amma kawai sai ta yi baya kamar za ta faduwa

duk da ya san saman gadon za ta koma hakan bai hana shi kai hannu ya taro ta ya na fadin " are you okay ? "

gyada mishi kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba

shi ma bai ce mata komai ba ya ja hannun ta , su ka nufi wajen sofas din nan , ya zaunar da ita saman three seaters sannan ya zauna geffen ta , ya kara janyo table din gaban su

hannu ya kai ya dauki wani Dewar flask , sannan ya dauki wani Mug da ke geffen shi , ya bude flask din nan , coffee a ciki sai tiriri a ya ke

cikin Mug din nan ya zuba , sannan ya meda flask din ya ajiye ya mika mata Mug din

a hankali ta girgiza mishi kai ta na fadin " yaya Zayd , ni ba na iya shan wannan abun "

" coffee ne fa ? " ya fada cikin sanyin murya

girgiza mishi kai ta yi allamun ba ta so

" please my Cutie , ki sha mana , ki fara shan coffee idan ya so ki sha fruits da ga baya "

sai da ta dan jinkirta kafin ta kai hannu ta karbi Mug din

a hankali ta kai shi a baki ta dan surba

da sauri ta mika mishi Mug din ta na fadin " umm ba dadi , amshi kayan ka "

dan zaro idanu ya yi ya na kallon ta ya ce " kamar ya ba dadi ? No , wassa haba ki ke min kawai dan ba ki son sha , wlh sai kin shanye shi "

marairaice mishi fuska ta yi ta na fadin " yaya Zayd , ba na so please "

" Cutie , ina wassa da ke ? " ya fada ya na matse gera

a hankali ta girgiza mishi kai allamun a'a

" okay , shanye coffeen nan tun kafin rai na ya bacci "

turo dan bakin nan nata ta yi kafin ta kai mug din a baki ta ci gaba da sha

sai da ta shanye coffeen tas sannan ta sauko mug din ita kanta ba ta sani ba

kawai sai jiyo Muryar shi ta yi ya na fadin " ki ka ce ba shi dadi "

shagwabe mishi fuska ta yi ta na fadin " ni ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login