Showing 54001 words to 57000 words out of 135778 words

Chapter 19 - Exiled Prince Book Three Complete Hausa Novel

Meerah   

24 Oct 2025

319

saman face din Inaya ta fara goge mata hawayen ta ta na fadin "idan ba ki daina kukan nan ba , ba zan fada miki abun da ya kawo ni ba "

a hankali Inaya ta rage sautin kukan ta , ta na fadin " Fada min to ina sauraron ki "

wani kyawatencen murmushi Nesrine ta saki kafin ta ce " I think i'm pregnant , kin kusa zama Aunty "

cak Inaya ta tsaya da kukan ta , ta na zaro idanu ta na kallon Nesrine

nan take ta saki wani kyawatencen murmushi har da wata yar karamar dariya ta rungume Nesrine da sauri ta na yar karamar dariya , kamar ba ita ba ce yanzu ke kuka

wata yar karamar dariya Nesrine ta yi kafin ta ce mata " ke malama sake ni , ban tabbatar ba , yanzu na ke shirin yin test din "

da sauri Inaya ta sake ta ta na cewa "Tashi tom mu je likita mu yi test din "

a hankali Nesrine ta juya ta kai hannu bayan ta ta dauki pregnancy Test din da ta shigo da shi , ta nunawa Inaya ta na cewa " kin ga ba sai mun je likita ba , two minutes kadai sun isa mu yi Test din "

da sauri Inaya ta ce mata " To ya a ke yin wannan shi kuma ? "

daga mata gera guda Nesrine ta yi ta na cewa " tasso mu je ki ka gani " ta kai karshen ta na mikewa tsaye

da sauri Inaya ta mike su ka fara takawa a tare su ka nufi corridor su ka shiga bedroom din Inaya

su na shiga Nesrine ta ce wa Inaya ta jira ta za ta shiga toilet yanzu ta fito

ba musu Inaya ta nufi bakin gadon ta , ta zauna Nesrine kuma ta nufi toilet ta shiga

ta na Shiga Inaya ta kai duban ta saman bedside drawer , nan ta ga Wayar ta ajiye saman bedside drawer

a hankali ta kai hannu ta dauki wayar , ta kunna ta

nan ta ga ruwan Text din a ka turo mata kuma duk Malik ya turo mata su

a hankali ta shiga karanto Text din daya bayan daya , duk kalaman Soyayya ne ya ke zaune ya turo mata wasu kawai I love you ne a ka turo , duk da su na tare a part din shi amma da ya dauki wayar shi first thing da ya ke yi shi ne ya tura mata Text

a haka har Text din su ka tafi dan sun kai hundred , kuma duk kalaman soyayya ne ya ke ta zuba mata , ni dai ba zan iya karanto muku text din ba sirrin su ba ruwa na

kawai sai ta tsinci kan ta da sakin wani cool murmushi ta na ci gaba da karanta text din

ta na a haka ta ji Nesrine ta fito da ga cikin toilet , a hankali ta kashe wayar ta ajiye saman bedside drawer sannan ta mike ta nufi Nesrine ta na fadin " Ya ne ? me ya ba da ? "

marairaice fuska Nesrine ta yi kamar za ta yi kuka ta karaso cikin dakin ta na dan karamin tsaki

da sauri Inaya ta ce mata " Nesi ki fada min mana , wlh har na kagu na ji "

" to malama sai ki daina kaguwa "

" shikenan shikenan na ji , yanzu ki ka fada min " Inaya cike da shagwaba

wani karamin murmushin geffen fuska Nesrine ta yi , ta na cewa " it's positif "

❤⚘





E



X



I



L



E



D



⚘❤



P



R



I



N



C



E



⚘❤







(LOVE



MEETS



POWER



)



👑🔥





(



A



heart



touching



love



story



,



Romance



,



injustice



&



destiny



)







STORY



&



WRITTEN



BY



:



MEERAH





🕊

BOOK



________3



👑







P



A



G



E

9

🌹🕊

wata irin kara Inaya ta saki har da tsale , ta na nufi Nesrine da gudu ta rungume ta ta na dariya kamar wata mahaukaciya

da sauri Nesrine ta ce mata " ke malama yi a hankali kar ki ji min ciwo "

a hankali Inaya ta sake ta , ta na fadin " Sorry , sorry , sai na fadawa Mama , mu je mu fada mata don Allah " Inaya ta fada cike da zumudi

noke mata kafada Nesrine ta yi ta na fadin " sai na fara fadawa Sweetheart kafin kowa ya sani " ta kai karshen ta na kauda kai

dan tabe baki Inaya ta yi ta na kallon ta ta ce " sannu ma su sweetheart , to sai ki yi sauri ki fada mishi , dan na samu na yi wa mama Albishir , da yaya Abdoul "

" yawwa Auta , wai ina yaya Abdoul ya ke , na yi wajen one week ban gan shi ba , kuma part guda mu ke "

" ban gane ba , part guda ku ke , kuma ki ce kin yi wajen one week ba ki gan shi ba "

" No ba ki gane ba , kamar part biyu ne a cikin bangaran namu , so shi ya na cikin part daya , mu kuma cikin gudan , ban san in da ya ke tafiya ba ko na je neman shi ba ya nan "

wani dan karamin murmushi Inaya ta saki kafin ta ce " Nesi , ina ga yaya Abdoul din mu ya fara soyayya shi ma "

hararrar ta Nesrine ta yi ta na fadin " ke ba na son shirme , yaya Abdoul din ne ki ke cewa ya fada soyayya , da wa kuma ? "

daga mata kafadu Inaya ta yi ta na turo dan bakin nan nata allamun ba ta sani ba

wani dan karamin tsaki Nesrine ta yi kafin ta kai hannu ta zungure ta a kai ta na cewa " ke dai wlh Allah ya shirya ki "

" Ameen " ta fada ta na yar karamar dariya

🤔🤔

BARI DAI MU LEKO ABDOUL NA JI SHIRU KWANA BIYU







ABDOUL

konce ya ke saman bed din shi , ya na sanye da short da Singlet Sky blue dukkan su

ya na rike da wani book a hannayan shi ya na karantawa , ya saka earpieces a kunnuwan shi , da ga gani ka san hankalin shi na cikin book din hannun shi

ya dan dauki lokaci a haka kawai ya ji an kwace mishi book din hannun shi

a razane ya juya ya kali saitin da ya ga an kwace mishi book din

Wata muguwar faduwa gaban shi ya yi , da sauri ya mike zaune ya na zaro idanu ya na kallon ta ya ce " ke , ke me ki ke yi nan " ya kai karshen ya na jan Duvet ya rufe kafafun shi har zuwa kugu

zaune ta ke bakin gadon nashi , ta na sanye da wata Abaya fara kal mai mugun kyau , ta sha wasu stone golden color , ta yafa veil din ta a kai ba ta yi Rowling din shi ba

kallon book din Tesnim ta na fadin " me ka ke karantawa "

" ba ki ba ni amsar tambaya ta ba , me ki ke yi a nan "

a hankali ta ajiye book din saman bedside drawer ta juyo ta kalle shi ta saki wani kyawatencen murmushi ta ce " ba ka ji dadin gani na ba ? "

" Tesnim please tashi fice min da ga daki , ba za ki iya jira na a parlour ba " ya fada ya na nuna mata kofar fita dakin

turo mishi dan bakin nan nata ta shagwabe fuska ta ce " haba ni da na zo yi maka Surprise shi ne za ka ce na tashi na fita "

a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " shikenan , tafi parlour ki jira ni na saka kayana "

noke mishi kafada ta yi ta na cewa " uhm ni a nan za mu yi hira " ta kai karshen ta na daura dan yatsar ta saman hannun shi ta fara yi mishi tafiyar tsutsa

da sauri ya riko hannun ta ya na zaro idanu ya ce " Ke lafiyar kuwa , kin san haka ba dai'dai ba ne , please tashi ki fita "

" okay " ta fada a takaice kafin ta tashi a hankali ta nufi kofar fita

ya na ganin ta mike ya sauke ajiyar zuciya kafin ya janye duvet din jikin shi ya sauko da kafafun shi kassa ya na shirin mikewa ya ga ta tura kofar dakin ta saka mata security

wani dan karamin tsaki Abdoul ya ja , ya na marairaice murya ya ce mata " Tesnim , what are you doing ? "

a hankali ta juyo ta fara takawa ta dawo gaban shi ta tsaya ta na murmushi

wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya kauda kai ya na fadin " shikenan , zauna ke ki ka sani " ya kai karshen ya na kokarin tashi

da sauri ta kai hannu ta tura shi ya koma ya zauna

a dubu dari ya dago kai ya na kallon ta a razane , " ke wai lafiyar ki kuwa ? " ya tambaye ta

" ban sani ba , me ka ce min ah ? wai ba na cikin ajin matan da za ka bude baki ka furta musu kalmar soyayya "

da sauri ya ce mata " i'm sorry , ni fa wassa na ke yi miki "

noke mishi kafada ta yi ta na cewa " ni ban yarda ba , yau sai ka fada min dalilin da ba za ka iya bude baki ka ce ka na so na ba "

marairaice mata fuska ya yi ya na cewa " please Tesnim , wlh ba na jin dadin yanayin nan da mu ke ciki , in magana ki ke son mu yi ki bari na saka kayana mu tafi garden "

noke mishi kafada ta yi ta na turo dan bakin nan nata

a hankali ya furza iska da ga bakin shi ya dafe kan shi da hannu guda murya cen kassan makoshi ya ce " na shiga uku yau ni Abdoul , yarinyar nan ta na neman ta kashe ni " ya kai karshen ya na jan tsaki kafin ya yi kokarin tashi

da sauri ta sa hannu ta tura shi ta na fadin " ba bu in da za ka je yau , sai ka ba ki amsar tambaya ta "

shiru ya yi ya na kallon ta , ya ma rasa abun da zai ce mata dan fa hakurin nashi ya kusa karewa

cikin zafin nama ya mike tsaye lokaci guda , ya riko hannun ta ya na kallon ta cikin ido ya ce " Get out ! "

marairaice mishi fuska ta yi ta na sakin kukan shagwaba kamar Inaya har da bubuga kafafu a kassa , har da wasu hawaye ke zubo mata

da sauri ya sake ta ya na fadin " please stop , wai me na yi miki ne ki na son ki takurawa nitsuwa ta wlh " ya fada ya na marairaice mata murya

a hankali ta daina kukan shagwabar ta , ta na turo mishi baki ta ce " kenan da gaske ba ka so na ? "

a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce mata " Tesnim Ina son ki mana , ki na son takura min dayawa , dubi cikin halin da ki ka saka ni yanzu , duk duniyar nan bayan Inaya da Nesrine ba taba kai hannu na taba wata macen ba , yanzu ga shi sai da ki ka sa na taba ki , why za ki min haka "

da sauri ta katse shi da cewa " because you are mine , and I love you "

a hankali ya koma ya zauna ya dafe kan shi da hannu ya ma rasa abun da zai ce mata wlh

ya na a haka kawai ya ji ta zauna geffen shi

slowly ya juyo ya kale ta cikin sanyin murya ya ce mata " Tesnim , wlh ba na jin dadin zaman ki a nan , dubi ko kaya ba bu a jikina "

cikin nitsuwa ta katse shi da cewa " so when we'll get marry ba za ka iya zama kusa na ba bare har " ta kai karshen ta na daga mishi gera guda

wani cool murmushi ya sakin mata kafin ya ce " ke dai wlh so ki ke ki kashe ni yau , na ji shikenan mu zauna a hakan amma wlh kar ki taba ni , in kuma ki ka taba ni sai na yi miki ihu kwartuwa "

bai gama rufe bakin shi ba Tesnim ta bushe mishi da dariya har da tapi

sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta ce " hayya bismillah yi mu gani , Ka ce fyade na zo yi maka "

hararrar wassa ya wurga mata ya na tsuke fuska ya ce " Lafiyar ki kuwa ? "

hararrar wassa ita ma ta yi mishi kafin ta ce " me ka gani ? "

daga mata kafadu ya yi allamun bai sani ba

wani dan karamin murmushi ta sakin mishi kafin ta mike ta dawo gaban shi ta tsaya sannan ta mika mishi hannun ta

kallon hannun nata ya yi na dan lokaci kafin ya dago nashi a hankali ya riko nata ya na kallon cikin idanun ta

" Na tafi , amma fa zan dawo , dan ban gama da kai ba " ta kai karshen ta na janye hannun ta ta juya a hankali ta fara takawa ta nufi kofar ta cire security , sannan ta bude ta

har ta daga kafa za ta fita ta jiyo Muryar shi ya na kiran sunan ta

a hankali ta juyo ta na murmushi ta daga mishi gera guda allamun minene

wani dan karamin murmushi shi ma ya sakin mata kafin ya ce " murmushi na yi miki kyau "

kara fadada murmushin ta ta yi sannan ta ce mishi " kai ma haka " ta na gama fadar hakan ta juya ta fice abun ta

wani kyawatencen murmushi ya saki ya na kallon har ta fita sannan ya kai hannu saman bedside drawer ya dauki book din shi , ya koma ya konta ya ci gaba da karatun shi





AFTER SOME HOURS





INAYA

a hankali ta turo kofar dakin da a ka kontar da Malik ta shigo ta na sallama

dakin babu kowa sai wasu sojoji guda Shidda ko wane rike da gun su na tsare da shi

su na ganin ta duk su ka shiga sara mata cikin girmamawa , sannan daya bayan daya su ka fara takawa su ka fice dakin , su ka tsaya a bakin kofar dakin

su na fita Inaya ta karaso a hankali ta janyo Chair ta zauna bakin gadon Malik , ta kai hannu a hankali ta riko nashi hannun

har yanzu dai jikinshi da sanyi , abun kamar kara sanyi ma ya ke yi

wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " Baby , na fada maka wani abu ? " Sai ta yi shiru na dan dakikai kamar ya amsa ta

a hankali ta matso da bakin ta wajen kunnen shi ta ce mishi " ka kusa zama uncle , Nesi is Pregnant " ta kai karshen ta na wata yar karamar dariya

da ga haka ta turo dan bakin nan nata ta na cewa " uhm ni ma ina son mu samu baby , kyakyawan baby boy or baby Girl , mai kama da kai , har wadanan idanun naka , na san ba karamin kyau zai yi ba , na ga Text din da ka tura a waya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login