Showing 60001 words to 63000 words out of 135778 words

Chapter 21 - Exiled Prince Book Three Complete Hausa Novel

Meerah   

24 Oct 2025

346

da farko ya saki wata yar karamar dariya ya ce " ko ni sai da ka ban tsoro wlh "

" na ga kamar ta na son ta raina min hankali , da tun farko tsawar ka yi mata da ba ta bata mana lokaci ba haka " ya fada ya na kauda kai

murmushi mai dan sauti Sojan ya yi kafin ya kauda kanshi shi ma

bangaran Nurse din nan kuma , kai tsaye Hospital din ta fito , amma ta kofar baya ta fito , babu kowa a wajen ko haske sosai ma ba bu

ta na fitowa ta tila box din hannun ta gefe cen cikin ciyayi

ta ja tsaki ta na fadin " why za su hana ni shiga ? gaskiya sai na zage damtse dan ganin na kashe Malik , dole na san abun yi game da wannan lamarin tun kafin ya tashi da ga saman gadon nan , ko kuma wacen sakarar yarinyar ta riga ni aiwatarwa , You just won a battle but the war has just begun "

ta na gama fadar haka ta ja wani siririn tsaki ta bace bat a wajen





WASHE GARI

⛅⛅⛅

a hankali Inaya ta ke tafiya cikin likita , ta na rike da wani basket a hannun ta , ta na sakin wani cool murmushi

ta na karasowa bakin dakin da Malik ke ciki duk sojojin da ke tsaye bakin kofar sai da su ka sara mata

da fara'a a fuskar ta ta ce musu " zan iya shiga ? "

a hankali guda cikin su ya kai hannu ya bude mata kofar ba tare da ya ce komai

wani dan karamin murmushi ta sakin mishi ta na yi mishi godiya kafin ta daga kafa a hankali ta shiga dakin ta na sallama

yanzu ma sai da sojojin wajen su ka sara mata cikin girmamawa sannan daya bayan daya su ka fice dakin

su na fita ta karaso a hankali bakin gadon shi ta janyo chair ta zauna bakin gadon ta na bin shi da kallo ta na murmushi , yanayin Skin din shi ya koma kamar yadda ya ke , ta rage wannan farin

a hankali ta dago hannun ta ta daura saman face din shi , nan ta ji jikinshi ya rage sanyin da gareshi jiya

wani kyawatencen murmushi ta saki ta na janye hannun ta ta ce " Baby , da ga gani ka na samun sauki , na fada maka wani abu ? Gaskiya ba na jin dadin kwana idan ba ka nan " ta kai karshen ta na turo dan bakin nan nata

a hankali ta juya ta kai hannu ta bude basket din da ke geffen ta , ta ciro wani dan karamin bowl da spoon , sannan ta cire Plate din da ke rufe da bowl din ta meda cikin basket din kafin ta juyo ta na kallon shi ta fara shan Fruit salad din da ke cikin bowl din , ta na ci ta na yi mishi hira , har wani dan jinkirtawa ta ke kamar ya na amsa mata

sannu sannu sai da ta share yinin ranar a cikin dakin shi ta na zuba mishi surutu , sai wajen kiran sallar Azahar sannan ta tashi ta ce mishi za ta dawo da yamma sannan ta baro dakin





ROUKSAR

zaune ta ke kassan bishiyar nan , Aymane na zaune geffen ta wannan karan bai rufe fuskar shi ba

ta yi irin zaman bokaye , ta na sanye da wasu kaya bakake da veil baki ta rufe fuskar ta shi

ga wasu kwallaye gaban ta sai hayaki ke fitowa da ga cikin su

a hankali wani wata guguwa ta fara tashi ta mamaye ta , har veil din ta ya fadi gashin ta ya fara tashi sama

sai motsa lips din ta ke yi da sauri sauri idanun ta sun koma farare kal

a hankali ta daga hannu sama , ta na haka kawai wata ball fara kal kamar lamps ta fado cikin hannun ta

lokaci guda ta juya da hannun ta daura shi saman bishiyar bayan ta , nan take Ball din nan ta shige cikin bishiyar

da sauri Rouksar janye hannun ta , ta yi baya ta na sauke nunfashi da karfi har da dafe saitin zuciyar ta da hannu guda

wata yar iskar dariya Aymane ya bushe da ita ya na fadin " Good job , kin yi aiki mai kyau "

wata nanauyar ajiyar zuciya Rouksar ta sauke kafin ta ce " Aymane , wlh idan wani abu ya same ni ba zan yahe maka ba , maci amana kawai "

" za ki iya fadin duk abun da ki ke so , ni dai ba zan ja da baya ba a kan kudiri na , na gode da taimakon ni , idan kuma ki ka ce za ki yi wani abu against me , kar ki manta da hannu kadai zan iya kawo karshen ki " ya kai karshen ya na dafe bishiyar bayan shi da hannu ya na sakin mata wani makirin murmushi kafin ya bace ya bar ta a wajen

wata yar karamar kara Rouksar ta saki kamar za ta yi kuka kafin ta bace ita ma , dama an ce macuci shi ya san makontar macuci , yanzu Aymane ya saka rayuwar Rouksar a hatsari , dan ko da kuwa branch guda ce ta bishiyar nan ta fado , to sai Rouksar ta ji a jikin ta bare a ce za a cire bishiyar baki daya , Allah ne kadai ya san abun da zai faru , amma ni dai na san ba al'heri ne su ka aikata ba





BAYAN SALLAR ISHA

a hankali Inaya ta ke fitowa da ga cikin corridor ta na sanye da wata Abaya Pink color me mugun kyau , ta yafa veil din a kai ba ta yi Rowling din shi ba ,

❤⚘





E



X



I



L



E



D



⚘❤



P



R



I



N



C



E



⚘❤







(LOVE



MEETS



POWER



)



👑🔥



(



A



heart



touching



love



story



,



Romance



,



injustice



&



destiny



)







STORY



&



WRITTEN



BY



:



MEERAH





🕊

BOOK



________3



👑







P



A



G



E



11

🌹🕊

ta na tafiyar ta cikin konciyar hankali da murmushi a fuskar ta

bakin ta da sallama ta shigo parlourn nan ta tardo RIANNA rungume da Tesnim da ke kuka kassa kassa

a rude Inaya ta karaso wajen ta na fadin " Aunty Tesnim me ya faru ki ke kuka ? "

cikin nitsuwa RIANNA ta ce mata " kar ki damu baby , momy ce a ka kai likita jinin ta ya hau saboda halin da Malik ke ciki , amma kar ki damu za ki iya tafiya wajen Malik "

a hankali Inaya ta karaso ta dafa shoulder din Tesnim ta na cewa " ki yi hakuri kin ji Aunty Tesnim ? ba abun da zai samu momy in sha Allah "

wani murmushin karfin hali ta na gyada mata kai ba tare da ta ce komai ba

kamar da ga sama su ka jiyo Muryar Abdoul ya shigo wajen ya na sallama

Tesnim na ganin shi ta tashi da gudu ta nufe shi ta fada jikin shi ta na sauke ajiyar zuciya

a tare Inaya da RIANNA su ka saki wani dan karamin murmushi , kafin Inaya ta tako a hankali ta raba ta geffen Abdoul ba tare da ta ce komai ba ta fice abun ta dan ita ma yanzu ta na da burin kasancewa da nata masoyin

a haka ita ma RIANNA ta mike ta bi bayan Inaya amma ita wajen MALIKAT AL'UMU za ta je

su na fita Abdoul ya dago Tesnim da ga jikin shi ya ce " To rigimamiya , sake ni kare ki karaya min baya "

noke mishi kafada ta yi ta na turo dan bakin nan nata ba tare da ta ce komai ba

a hankali ya rage sautin Muryar shi ya ce mata " mu tafi garden to ? "

da sauri ta gyada mishi kai kafin ta sake shi a hankali ta na sunkuyar da kai

hannu ya kai ya riko hannun ta kafin ya juya su ka bar part din a tare

😂😂😂✌

KU BARI NA BI BAYAN SU TUKUNNA , MUN NEMI INAYA DA GA BAYA

🤣🤣🤣

a tare su ka baro part din MALIKAT INAS su ka nufi garden

su na shigowa ya ce mata " me ya faru ki ka ce ki na son ganina ? " ya fada ba tare da ya kale ta ba su na ci gaba da tafiyar su

cikin sanyin murya ta ce mishi " kawai ina son kasancewa tare da kai "

wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " hmmm fada min gaskiya dai , da ga gani akwai abun da ke damun ki , za ki iya fadamin kin sani ko ? "

dan jinkirtawa ta yi kafin ta ce mishi " ban san abun mu ka yi musu , sun raba ni da Abbi , ga Malik cen konce rai a hannu Allah , yanzu kuma sun komo kan momy , yanzu da jimawa a ka tafi da ita likita ni na san doctor karya kawai ya ke mana , ba wani jini ta da ya hau , yanzu ga ta cen konce ko motsi ba ta yi " ta kai karshen kuka na kubce mata

shiru Abdoul ya yi ya na kallon ta ta na kukan ta , gwara ya bar ta ta gama kukan ta ta fitar da abun da ke cikin zuciyar ta da ga baya ya shiga rarrashin ta

sai da ta gama kukan ta kafin ta juyo ta wurga mishi hararra ta na fadin " ba za ka rarrashe ni ba sai ka kyale ni na yi ta kuka "

wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " to ba ga shi yanzu kin yi shiru da kan ki ba , ni fa ban iya rarrashi ba , bayan auta ba na jin zan iya rarrashin wata macen a duniya "

" Har ni kenan ba za ka iya rarrashina ba ? " ta fada ta na marairaice mishi fuska kamar za ta yi kuka

wani dan karamin murmushin geffen fuska ya yi mata kafin ya ce " zan iya mana , amma ba kamar yadda na ke rarrashin auta ba "

" kamar ya kenan ? "

a hankali ya juya ya kali dama , ya kalli hagu ya ga babu kowa sai su kadai sai kuma guards din da ke tsaron wajen amma hankalin su ba ya saman su

a hankali ya juyo ya kalle ta , ya sakin mata wani cool murmushi kafin ya tako ya matso dab da ita , ya na kallon cikin idanun ta ya zagayo da hannun shi a hankali a kugun ta ya janyo ta jikin shi , ya matso da face din shi dab da ta/ta yadda su na iya jiyo nunfashi juna

a hankali ta bude baki a tsorace ta ce mishi " me ka ke shirin yi ? "

daga mata gera guda ya yi ya na cewa " rarrashin ki zan yi mana , ko ba ki so ? "

" haka a le rarrashin mutum ? ni ka sake ni tun wani bai gan mu "

noke mata kafada ya yi ya na fadin " sai da nace miki ni fa ban iya rarrashi ba , ke ce ki ka matsa , dan haka yanzu ki bari na yi rarrashin ki yadda na iya "

har ta bude baki za ta yi magana ta ji ya cabko lips din ta na kassa ya fara kissing din ta

dum ta ji zuciyar ta ta buga da mugun karfi har wani zaro idanu ta ke ta na kallon shi , shi ko bai ma san ta na yi ba dan ya lumshe idanun shi

(

🤣🤣😂😂

wayyo na so malam na nan ya ga aikin yaron shi )

a hankali ya zame bakin shi da ga cikin nata , ya bude idanun shi

ba su sauka ko ina ba sai cikin nata , ganin irin da kallon da ta ke yi mishi ya sa shi tunanin ko ba ta ji dadin abun da ya yi mata

a hankali ya saki kugun ta ya ja baya kadan murya kassa kassa ya ce " I'm so so sorry , ban yi dan na bata miki rai ba "

a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta gyada mishi kai allamun shikenan

ya na ganin haka ya juya ya fara takawa zai bar wajen

da sauri ta rigo hannun shi ta na cewa " ina kuma za ka je ? "

ba tare da ya juyo ba ya ce mata " ina ga ya kamata na tafi "

" why ? please ba na so ka tafi " ta fada ta na marairaice mishi murya

slowly ya juyo ya sakin mata wani dan karamin murmushi ya ce mata " ki yi hakuri , akwai wani aiki da na ke son na yi yanzu , kuma kin ga dare ya yi ya kamata ki je ki konta ki huta., gobe zan dawo "

a hankali ta sake mishi hannu kafin ta ce " shikenan , amma sai ka meda ni in da mu ka fito " ta kai karshen cikin shagwaba

wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce mata " an gama ranki shi dade "

yar karamar dariya ta yi mishi ita ma kafin su juya a tare su ka koma part din MALIKAT INAS





AFTER SOME DAYS







INAYA

a hankali ta turo kofar dakin da Malik ke konce ta na sallama kassa kassa

ta na shigowa sojojin nan su ka nufi hanyar fita su ka fice

a hankali ta karaso bakin gadon shi ta tsaya ta na ci gaba da kallon shi

nan take idanun ta su ka ciko da ruwa kamar za ta yi kuka ta ke ce mishi " baby , wai me ya sa har yanzu ba ka tashi ba ? don Allah ka tashi mana , ina kewar ka over , ko barci na kassa yi saboda yawan tunanin ka da na ke , don Allah ka tashi ko dan saboda ni " ta kai karshen hawaye na zubo mata



a hankali ta lumshe idanun ta , ta kai hannu ta fara goge hawayen ta

cak ta tsaya ta kassa yin wani kwakwaran motsi

a hankali ta sauko da hannun ta , kafin ta bude idanun ta lokaci guda sun koma farare kal ko digon baki babu a ciki har wani haske su ke yi kamar lamps

a hankali ta ja wani irin dogon nunfashi kafin ta yi gaba kadan kamar an ingiza ta

nan take Kayan jikin ta su ka koma farare kal , veil din ta ya fado kassa , a hankali jelar gashin ta ta fara komawa white ta tashi sama kamar ana busar da ita

a hankali ta bude baki ta yi magana cikin wani harshen da ban taba ji ba , da ga ji kuma ba na mutane ba ne

slowly ta dago hannu ta daura saman forehead din Malik , ta fara motsa lips din ta a hankali kamar ta na karanto wani abu

lokaci guda wata guguwa ta tashi cikin dakin fara kal ta zagaye su ita da Malik

sai da ta dauki wajen good two minutes a haka kafin Malik ya ja wani dogon nunfashi har sai da kirjin shi ya yi sama

a dubu dari ya ware idanun shi dai'dai lokacin da ya furzo jini da ga cikin bakin shi da wasu kananan ball guda biyu green color , nan take su ka yi cikin guguwar ta bace bat lokaci guda

ta na bacewa kowa lamps din dakin su ka fara mutuwa su na kunna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login