Showing 108001 words to 111000 words out of 135778 words
hannayanshi a baya a Azim ya rungumeshi , da a ce zai iya yin kuka da ya yi shima
sai da Azim ya gaji da kukan nashi sannan ya dago da ga jikin Malik ya na fadin " Ina ka shiga ranka shi dade ? ina ka tafi ka bar mu ? kai da kanka ka ce mu ne ahalinka amma shi ne ka tafi ka bar mu ? ba ka san irin kangin da mu ka shiga bayan tafiyar ka ba , na godewa Allah da ba abun da ya same ka , don Allah kar ka tafi ka sake barin mu a hannun wacen azzalumin mutum " ya fada ya na hawaye bibiyu
a hankali Malik ya mike tsaye , sannan ya taimakawa Azim ya mike tsaye shi ma
hannu ya kai ya fara gogewa Azim hawayen shi ya na fadin " kar ka damu Azim , in sha Allah babu inda zan je , ko zan tafi sai na cire ou da ga hannun wacen azzalumin "
a hankali Azim ya gyada mishi kai ya na sakin wani dan karamin murmushin da har ya manta rabon shi da ya yi murmushi
a hankali Malik ya juya ya nufi motar shi da sauri Azim ya mara mishi baya , su na isa
ya bude gidan baya ya fiddo trolley din su
Malik kuwa ya nufi geffen Inaya , ya bude mata kofar , sannan ya mika mata hannu
ba musu ta daura hannun ta saman nashi , sannan ta sauko a hankali
Azim na ganin cikin Inaya ya saki wani kyawatencen murmushi ya na yi wa Allah godiya cikin zuciyar
cikin sanyin murya ya ce mata " ki shiga ina zuwa , su Ammie duk su na ciki "
gyada mishi kai kawai ta yi , da ga haka ya manna mata kiss saman forehead ya raba ta geffen ta ya shiga cikin motar shi
A hankali ta daga kafa ta fara takawa ta shiga part din MALIKAT HOUDA , Azim na biye da bayan ta janye da trolley
bakin ta da Sallama ta shigo parlourn MALIKAT HOUDA , nan ta tardo MALIKAT INAS , MALIKAT AL'UMU , mama , Tesnim , Nesrine , har ita kan ta MALIKAT HOUDA
Nesrine da mama na ganin ta su ka tashi da gudu su ka nufe ta , su ka rungume , su na sakin kuka
wata yar karamar dariya Inaya ta yi ta na fadin " Ashhhhhh , kar ka ku ji wa babyna , ciwo "
a tare mama da Nesrine su ka daga da ga jikin Inaya su na kallon katon cikinta
Godiya mama ta shiga yi wa Allah cikin zuciyar ta , Nesrine ma haka sai sakin murmushi ta ke
wani kyawatencen murmushi Inaya ta saki , ta nufi MALIKAT INAS da sauri ta na fadin " Ammie "
da sauri MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU su ka mike su na fadin " yi a hankali baby "
cak ta tsaya ta na murmushi har su ka karaso wajen ta , su ka rungume ta sannan su ka shiga tambayar ta ya jiki , ya hanya
gyada musu kai kawai ta ke ta na murmushi
cen cikin hannun MALIKAT HOUDA ta hango wani baby , ya na barci sai jijiga shi ta ki
washe baki Inaya ta yi ta nufi MALIKAT HOUDA ta na fadin " la mamie , baby ki ka samu ? "
a tare duk su ka yi wata yar karamar dariya sannan MALIKAT HOUDA ta ce mata " ba na son shirme , na Nesrine ne "
dan zaro idanu Ta yi kafin ta juya ta kali Nesrine , da ke tsaye ta na hawaye , irin kallon nan na tambaya
a hankali Nesrine ta gyada mata kai ta na murmushi allamun Eh
zama geffen MALIKAT HOUDA ta yi ta na fadin " mamie ba ni shi na rike " ta fada na mika mata hannu
cikin zolaya Tesnim ta ce mata " wannan katon cikin naki zai bari ki dauke shi ? "
" ni dai sai na dauki babyn Nesi " ta fada cike da shagwaba har da turo baki
" karbi , ba za mu iya rigimar ki ba , ai dama dole ta ce sai ta rike shi , ba mijin ta ba ne " MALIKAT HOUDA ta fada ta na daura Baby saman hannayan Inaya
da sauri Nesrine ta ce mata " yi a hankali kar ki murde min kan baby "
hararrar ta Inaya ta yi ta na fadin " to ina ruwan ki , ai ni ma na kusa samun nawa babyn " ta kai karshen ta na murguna mata baki
a hankali Nesrine ta karaso wajen ta , ta na fadin " ban babyna tun da haka ne " ta kai karshen ta na mika mata hannu
da sauri Mama ta ce mata " Nesrine wai biye mata za ki yi , kin fi san halin ta "
hararrar Inaya Nesrine ta yi kafin ta koma gefe ta zauna ta na tsuke fuska
a tare kowa ya koma ya zauna kafin MALIKAT INAS ta ce " baby , ina mijinki ya yi ? ba tare ku ka zo ba ? "
a hankali Inaya ta dago kai ta kalli MALIKAT INAS ta ce " a tare muku Ammie , ya ce akwai inda zai je yanzu ya dawo "
a tare duk su ka yi hamdallah , sannan MALIKAT AL'UMU ta ce " baby , ya kamata ki je ki huta ko ? "
noke mata kafada ta yi ta na fadin " ni tare da babyna zan tafi "
da sauri Nesrine ta ce mata " wane babyn ? kam , wlh tun wuri ki sauke idanun ki da ga saman babyna , in ba haka ba na yi miki duka kawo ruwa "
cikin nitsuwa Tesnim ta ce mata " Malik ko ya cire miki kai , gwara ki bi ta cikin ruwan sanyi ku rabu lafiya , dan ita ta na son babyn nan ko mutuwa za ki ba abun da zai raba ta da shi "
marairaice fuska Nesrine ta yi ta na shirin magana , ta ga Inaya ta miko mata babyn ta na fadin " amshi , barci na ke ji "
da sauri Nesrine ta kai hannu ta karbi babynta
ta na karba Inaya ta mike tsaye a hankali , ta na dafe da cikinta , ta ce " mama , barci na ke ji " ta kai karshen cike da shagwaba
wani dan karamin murmushi ta saki ta na kallon ta , yau dia ga autar ta da ciki har ya kai watan haihuwa , ga kuma Nesrine da babynta , saura na Abdoul kadai ta ga burin ta ya cika
a hankali ta mike ta nufi Inaya ta riko hannunta , ta na fadin " mu je ki yi wanka ki konta ki huta , Nesrine kawo kayanta bedroom di na "
" bari zan kai " Tesnim ta fada , ta na mikewa ta nufi trolley din da Azim ya ajiye a wajen ta bi bayan su mama da su ka shiga corridor
โคโ
EXILED
PRINCE
โโค
(
LOVE
MEETS
POWER
)
๐๐ฅ
(
A
heart
touching
love
story
,
Romance
,
injustice
&
destiny
)
STORY
&
WRITTEN
BY
:
MEERAH
โ
๐
ใ
THE
ROYALTY
LOVE
โค๐นใ
ใ
BOOK
________3
๐
โ๐
ใ
_______________________
โกโกโกโกโกโกโกโกโกโกโกโก
___
___________________
๏ฝ
P
A
G
E
________
25
โ
๐๐ฅ
๏ฝ
โช
MALIK AYMANE
zaune ya ke saman kujerar shi ta Gold
ya na rike da wayar shi ya na latsa , haka zalika duk mutanan wajen kowa na harkar gaban shi , sai hira su ke yi su na dariya
su na a haka Meli ya shigo da gudu babu ko sallama
ya nufi Aymane da gudu , kai tsaye wajen kunnen Aymane ya nufa ya yi mishi rada
a dubu dari Aymane ya mike tsaye har sai da ya saki wayar shi ta fadi kassa
a tare duk kowa ya juyo ya na kallon Aymane da ke faman zaro idanu baki sake har su na hada baki su na tambayar shi lafiya
ba su kai ga gama rufe bakunansu ba , su ka ga Aymane ya kai hannu ya damko wuyan Meli ya na fadin " karya ka ke , ba zai taba dawowa ba "
murya a disashe Meli ya ke fadin " ranka shi dade , ba karya na ke ba , da ido na na gan shi zai shiga part din MALIKAT HOUDA "
cikin bacin rai Aymane ya tura Meli baya har sai da ya fadi
ya na shirin magana idanun shi su ka sauka cikin na Malik , ya na tsaye bakin kofar shigowa Fadar ya rike hannayan shi a baya
a tare kowa ya mike tsaye ya na kallon Malik baki sake , wasu zuciyoyin su na bugawa
cikin bacin rai Aymane ya ce mishi " me ka ke yi a nan ? "
a hankali Malik ya daga kafa ya fara takawa ya karaso tsakiyar fadar ya na fadin " na zo karbar abu na , dama aro ne na ba ka "
wata shegiyar dariya Aymane ya yi kafin ya koma saman kujerar Malik ya zauna , irin zaman nan na qasaita ya ce " ko da HICHAM BIN JAABAR ne zai fito da ga cikin kassa , ba isa ya sauke ni da ga saman kujerar nan ba , bare kai ragon banza "
cikin bacin rai Malik ya ce mishi " kar ka kuskura ka kira sunan mahaifina "
" na kira , na kira me za ka yi ? ,ko ba ka son na fadi sunan wanda ya haifi lusarin namiji kamar ka ? tun kafin na sa a cire maka kai , ka fice min da ga fada "
a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " Aymane , tun ina yi maka cikin ruwan sanyi , ka sauka da ga kujerar nan "
wani makirin murmushin geffen fuska Aymane ya saki , kafin ya juya ya kalli wani dogari da ke tsaye bakin kofar fadar , da hannu ya mishi allamun ya cirewa Malik kai
ba musu dogarin nan ya tako gadan
ยฒ
ya na zaro takobi wai cire kan Malik
lokaci guda Malik ya kai hannu baya ya fido gun ya juya ya harbe dogarin nan tsakiyar kai , nan take ya fadi kassa matace
ba karamar razana Aymane da mutanan fadar su ka yi ba
a hankali Malik ya juyo , ya saita kan Aymane ya na fadin " idan na ga dama , move guda zan yi na aika inda ka aika mahaifina , amma zan ba ka damar ci gaba da rayuwa , ka sauka da ga kujerar nan "
cikin bacin rai Aymane ya mike tsaye ya na fadin " ba ka da ikon ce min na sauka da ga saman kujerar nan , kai da kanka ka bar ta , kowa ya na shaidar ka hakura da kujerar nan a bisa tsarin masarautar nan , duk Malik din da ya hakura da kujerar shi , ba shi da izinin komowa da sunnan zai koma saman kujerar shi , dan haka ba ka da ikon ce min na sauka "
ya na gama rufe bakin shi ya ga Rafik ya shigo cikin fadar ya na fadin " as a direct descendant of Malik HACHIM bin JAABAR, he has every right to claim the tron โโof his late father, even if he renounced him "
" Gaskiya Rafik ya fada , dan haka malam ka tattara kayanka ka yi gaba " Fadin Diya ya na karasowa geffen Malik ya tsaya ya na sakin murmushi
" No ! " Aymane ya fada da karfi ya na mikewa tsaye ya ci gaba da cewa " No , ba ka da izinin ce min na sauka , ba ka san irin famar da na sha kafin na hau saman kujerar nan , tun kafin ka shigo duniya na shirya hawa na kujerar nan ta Malik dan har yaron MALIKAT INAS na kashe , na kuma sace mahaifar ta dan kar ta samu wani babyn , amma wannan banzan uban naka ya auri kanwar Daddy , ta haife ka , tun ranar da ka shigo duniya , tawa duniyar ta ruguje , ni na sakawa part din Malik wuta shekara shidda baya kawai dan ka mutu na dawo na kashe Malik , amma wani ikon Allah dan banzan yaron nan ya rayu , okay na hakura , why za ka dawo ? me ya sa ba ka yi zaman ka a cen ba ? amma sai da ka dawo ka shiga tsakanina da burina , amma ban hakura ba ni na juya kwakwolwar Hakim ya harbi Malik saboda ya kassa kashe shi , ni na sa Rouksar zuba mata poison cikin abincinka , ni na saka ta sace ruhin MALIKAT AL'UMU , amma wacen banzar yarinyar ta ruguza shirina baki daya , why ba za ku bar ni na hau kujerar nan cikin konciyar hankali ba ? why ? , wlh ko da sama da kassa za ta nade , ba zan sauka da ga kan kujerar nan ba " ya fada cike da bacin rai da allamun fasuwar rai ta kama shi
duk mutanan wajen sai da su ka yi salati su na sauraron abun da Aymane ke fadi , bacon zai ya sa ya tonawa kan shi asiri da kan shi
shiru Malik ya yi ya na sauraron abun da Aymane ke fadi , dole ya yi mishi ta wayo dan ya samu ya sauka da ga kan kujerar nan , Idan ya ce zai ta karfi , ba zai yi nassara ba , dole shi ma ya yi tunani kamar na su na mugaye , dole ya meda kwakwolwar shi irin tasu kafin ya samu Aymane ya sauka da ga kujerar nan , dama an ce mugu shi ya san makwontar mugu , cuta ce za ta dau cuta
a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya , cike da nitsuwa ya ce "as the heir of Malik HICHAM bin JAABAR I have the right to claim the throne of my late father, but since you do not want to give in passively okay, Aymane Abdoul Mujeeb Me Nawfel HICHAM bin JAABAR I provoke you in a duel, the winner will ascend the throne of Saudiya and the loser will pay with his life "
a dubu dari Rafik da Diya su ka kalli Malik su na zaro idanu , har su na hada baki wajen cewa " ka na jin abun da ke fada kuwa , hakan na nufin idan ka fadi kashe ka zai yi "
cikin kwarin guyiwa Malik ya ce " Eh , na ji abun da na fada "
ya na gama fadar haka Aymane ya bushe da wata shegiyar dariya har da tapi ya dafe ciki
shiru kowa ya yi ya kallon shi kamar wani zarrare
sai da ya tsagaita dariyar shi sannan ya dago ya kalli Malik ya ce " kai a ganin za ka iya kashe ni ? , ko ka kashe ni kamar ka kashe maciji ba ka cire kai ba , Okay na yarda , wane irin duel ka ke so mu yi ? "
" Sword Duel " ya fada a takaice ya na kallon Aymane
sake bushewa da dariya Aymane ya yi ya fadin " okay , na yarda , in dai ta haka ne kawai zan zauna saman wannan kujerar , na yarda , kai kuma ka shirya tarda tsohon mahaifinka , dan har yanzu ba a yi wanda zai ga bayan Aymane bin Abdoul Mujeeb , ko mutuwa tsorona na ke , bare kai ragon banza "
" All right , tun da ka yarda fine , yau ranar monday , za mu yi shi a ranar Friday , amma kafin nan , da ga kai har wadanan mutanan fadar taka , ba ku da izinin shigowa fada da sunnan aiki , har sai mun kammala duel din mu , sannan da ga yanzu ka fita da ga Malik Aymane , ka koma Aymane , har zuwa lokacin da za mu kammala , a nada wanda ya yi nassara a matsayin sabon Malik "
" okay " Aymane ya fada a takaice kafin ya sa hannu ya cire Alkyabar Malik da ke jikin shi ya ajiye saman chair din bayan shi , ya cire Rawanin kan shi ya ajiye saman Alkyabar , sannan ya juyo ya fara takawa ya karaso gaban Malik ya tsaya
sai da ya kalle shi cikin ido sannan ya ce "