Showing 1 words to 3000 words out of 96493 words
*KANA NAKA..!*
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
_Saturday 10june_
*Time:12:00pm.*
*Wannan Labarin tundaga farkonsa Har zuwa K'arshen sa Sadaukarwa ne gareka MUHAMMAD KARIM(MK)*
*Labarin KANA NAKA,Tukwai ci ne tare da kyauta na musamman zuwa ga Antyna ANTY SIS♥️Ba rubutu na kike so ba*
*Ni kike so,yadda kika kaunace ni domin Allah kema Allah ya so ki ya kuma lullube rayuwarki da alheri Ameen*
*KIRKIRARREN LABARI NE DUK ABUNDA AKA GANI YA YI DAIDAI DA NA SUNA,KO HALLAYA,GARI KO DABI'A TO ARASHI NE,JUYA WANNAN LABARIN KO SARRAFA SHI TA HANYAR FILM KO D'ORASHI A YOUTUBE CHANNELS SABA'MA HAKKIN MALLAKATA NE*
_Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai_
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DWmMEYuvM0QH3eJh17wR4X
*🅿️01*
*Shimfid'a.*
Katsina.
Area:Layout.
Karfe Tara ya shigo gidan nasa kamar yadda ya saba duk da yau yayi dare agidan mama chan kofar soro tunda tachan ya fara sauka bayan isowarsa Dazu da mangariba dagachan inda yake aiki a birnin Abuja.
Da kansa ya Tuko kansa Daga Abuja wannan Satin sakamakon Direbansa mallan iliya,mahaifinsa ba Lafiya ya tafi garinsu ya Dubasa bayan ya mai izini..shiyasa gabadaya agajiye yake gabobinsa gabadaya sun sake suna Bukatar Ruwa mai zafi tare da Tattausan Hannun wajen kwantar dasu su koma Daidai kuma Gajiyarsa ta Hada harda Dadewar da yayi mai baiyi Dogon Tuki ba ko Chan karofi zai Tafi Mallam Iliya ke tukasa Abu ne mai Wahala ka gansa yana Tuki da karan kansa.
Cikin muryansa mai Cike da Zati kamar ko yaushe yayi sallama bayan ya shigo Kyakyawan falon gidan nasa,wanda yara duk sun bata Fentin da Rubutu da Maker da Pencil,sun gama Lalata kyakyawan fentin Dake cikin Falon da ba'a sabuntasu ba Sannan ga kujerun nan duk sun ji jiki,sun fara yagewa Kushin din zaman duk yayi kasa,ya yamushe,shi kanshi Cafet din Tsakar Dakin ya fita Hayyacinsa Duk yayi Wusu wusu sannan yayi Datti Sosai.
Sau tari irin wad'anan abubuwan ke saka yayi zamansa Abuja baya kaunar ya shigo Katsina ya Shigo Gidansa yaci karo da yanayin yadda MATAR gidan ta bar yara suka barnata komai na gidam kamar gidan wata mai Saida Kuli kuli Tsabar yadda gidan ya fita Hayyacinsa.
Cikin yanayin kallonsa ya kare ma Falon kallo karamin Tsaki yaja ganin harda Takardun yaran duk sun yaga sun gama Haukata Falon bai nemi kowa ba sanin ba Sautin dawowarsa zataji ba Wacce ko agabanta kake sai kayi mgana kana Faman maimaici take iya jinka.
Yana Sarsarfa zuwa Bangaransa,wanda ke Rufe sai in ya Dawo ne yake budesa da kansa kamar Daga sama yaji Daga bayansa ance"Sannu da zuwa Yaya ISHAQ.."
Cak ya tsaya kafin ya juyo lokaci D'aya yana kara rike yar Jakar Laptop din dake Hannunsa,Girman Idonsa ya kara na ganinta domin har ya koma wanchan Satin bata agidan kenan bayan Tafiyarsa ne tazo gidan kenan..?
Bai damu ba illah baki Daya mele kafin ya ce"Sannu da gida.."
Ta amsa mai tana kokarin Tattara kayan yaran da suka gama Bidirinsu yanzu afalon kafin Yaya Fa'iza ta ja su ciki Domin su yi Fitsari su kwanta.
Bata Damu da yanayin da ya amsa mata ba inda Sabo ta saba tun tasowarta bata Taba ganin Fara'ar Ya Ishaq acikin gidan yayarta ba sai dai in chan gidan Mama kofar soro ce ko kuma yana Tare da yan'uwansa su a Gare su mutum ne mai wahalan mu'amala.."
Agabanta ya Bude kofar Shashensa ya shige ya rufo kofa ta bisa da kallo ta jinjina kai Gaskiyan Anty Binta batagwara ce Data Dad'e tana Fadin ban da Kaddaran aure ta ina Yaya FA'IZA ta Dace da Ya Ishaq..?Ya Ishaq Dogo ne Farin Buzu tas dashi Domin Mama kofar soro Buzuwar Yamai ce,Sannan Baba Kabiru marigayi Cikakken batsine daya fito Daga Korofin katsina Sai dai kaf ya'yan mama ita suka Dauko Wajen kyau da Nasaba Domin har yau da shekaru suka ja kyanta bai Zube ba Tanan nan mai kyau da ita.
Kuma yanayin Tsahon sa ya biyo na Dangin su Baba ne dake Karofi suma Dagayen katsinawa ne marasa Lalaci sannnan sai ya Hada da Hancin Mama da Sirantar ka ta yasa Ishaq ya zama mai kyau kuma mai aji sannan mai Tarin Ilimi Addini dana Zamani Wanda Duniya ta san sa kuma take ji dashi,Ayanzu haka Babban ma'aikaci ne A Hukumar Tattara Haraji na kasa reshen Abuja(FIRS)Federal Inland revenue Services,Ya dade yana aiki a wajen shekaru hudu da suka gabata da farko a reshen su na Jahar katsina ya fara aiki da su shekara uku kafin ya samu karin matsayi sai aka yi Transfer dinsa ya koma babban Ofishin su na Abuja,sosai yake jin dadin aiki a abuja musamman ma da samun Adalin Shugaba irin Dr. Lawal bako da yakasance shine Shugaba a ofishin su na Abuja kuma Uba garesa ko nace wanda ke shirin zama Surukinsa nan da Lokaci kad'an.
Yaya FA'IZA kuwa iyakarta primary School,primary di'n ma ba ta gama ba,a karatun Boko kenan na addini kam Saukakkiyace ta wannan Fanni sannan ta karanci sauran littafan addini iya abunda ya sauwaka ammh Duba da wannan Zamanin da muke cike domin kina da karatun muhammadiya ke bakowan kowa bace in baki Hada Fukafukan Ilimin Boko ba,Bama wannan ba Yaya Fa'iza ba irin Zabin Ya Ishaq ba ce ba cin haka ma Tana dq Laluran rashin ji,Bata iya jin mgana ahankali sai an mata da karfi take ji Dashi aka Haifeta Laluran TaMADINA ce ya shafeta Tunda ita din BEBIYA ce da shi aka Haifeta ba ciwo bane.
Tana wannan Tunanin tana Faman gyara Falon acikin ranta Tana Tunanin Yaya Fa'iza batasan ya Ishaq zai dawo yau ba domim kwata kwata bataji tayi zencen ba sannan basu da abinci agidan Taliyace ta Dafa ma su AMIR da Daddaren nan kuma D'ayace duka suka cinyeta ba Saura.
Kayan yaran ta kwashe ta tattara Takardun da suka yanka suka Zubar ta kai waje ta kofar Kitchen ta fita ta zubar a Abunda suke tara shara kafin ta Dawo Cikin Falon Dakin yaran ta Nufa inda yayar tata take domin ta shaida mata Dawowar Mijinta nata.
Da sallama ta shiga duk tasan ba lalle ta jita ba Amir Dake kwance ne ya amsa mata,Anum kuma har tayi barci mustapah musty Tuni har yayi barci,Ahmad ne a Hannunta tana Faman kiciniyar sanya mai pampers alamun wanka ta sake mai.
Karisowa shigowa Dakin yaran tayi mai Dauke da ciki Daya da karamin Tiolet,Adakin akwai gado guda uku kanana na yara,Daya na babban yaya ne Amir D'aya na Anun ce sai d'ayan na Mustpaha ne Ahmad na shan Nono Fa'iza bata yayesa ba wajenta yake kwana
Akwai Drowers na yaran guda uku acikin Dakin,inda suke ijiye kayansu na makaranta Dana gida,Har HAFSATU ta kariso ta zauna gefen Gadon Amir Fa'iza bata san ta shigo ba Hankalinta na kan saka ma Ahmad pampers ganin haka yasa Hafsatun watsa ma Amir Harara tana Fadin"Wai sau nawa zan maka Fad'an watsar da kayan ku duk inda kuka samu ne.?
Cikin muryan yarinta yace"Na Dauke nawa nasu Anum ne fa.."
Kayan ta Daga tana Fadin"Ai kai ne babba in suka bata sai ka gyara Amir din Umma.."
Jin Abunda tace ne yasa yayi mirmishi kafin yace"To Anty Hafsatu.."
Yafada Lokaci Daya yana kallon Fa'iza wacce har alokacin bata san Hafsatu na Cikin Dakin ba,Har sai da ta mike ta Zube kayan cikin kwandon da yaran ke tara kayan wanki Amir D'an kimanin shekaru Shidda da wani abu aduniya yace"Anty Hafsatu..Umma fa bata san kin shigo ba, kiyi mata mgana."
Hafsatu tace"Zan mata ka kwanta kayi barci.."
Kai Tsaye yace"Umma nake jira ta gama shirya Ahmad ta mana Addu'an kwanciya barci.."
Hafsatu ta juyo Daidai Lokacin da Fa'iza ta Dago bayan ta gama saka ma Ahmad saukakkam kaya tunda zasu kwanta ne taci karo da idon kanwar nata akanta Cikin Sanyinta da yanayin mganarta Tace"Hafsatu..yau..she kika shigo..?
Ta Fada tana kokarin Daukan Ahmad.
Hafsatu ta zauna gefen gadon Amir tana Fadin"na da'n jima da shigowa.Amir oya bude Hannu muyi addu'an barci."
Ba musu ya Bude hannu itama ta Bude suna karanta addu'ar Barcin da Annabi ya koyar da karfi ita dashi zaku mamakin yadda yaron yake karantowa Tiryan Tiryan wannan kuma kokarin Fa'iza ne bata bari wannan Ilimin nata ya tashi a banza ba Tana kokarin Rabashi ita da ya'yanta.
Fa'iza kuma Ficewa tayi Daga Dakin ganin suna addu'ar Barci Bedroom din Dake kallon Shashen Ishaq ta Shiga ta Shimfide Ahmad a kan gadonta na Royal bed sai dai ya kwana Biyu duk yaji jiki.
Dakin shima dai kadahan kadahan,Wardrope ne babba adakin ssi kofar Tiolet,daga ganin yanayin Dakin shi kanshi Shirgi yayi masa yawa Sannan uwa uba Cafet din Daya malale bedroom din shima duk ya kode yaji Duniya Duk da karfinsa na Italiyan Cafet..
Ta kwantar da Ahmad din kenan zata Fito Daga Dakin suka kusa cin karo da Hafsatu daya sa ta koma da baya tana Fadin"Ban san zaki shigo ba.."
Hafsatu ta bi ta da kallon Tsausayi kafin tace"Yaya Fa'iza kinsan ya Ishaq zai dawo yau..?
Ta fada da dan karfi Saboda ta jita Da Sauri Fa'izan tace"Eh..Me kika ce..?
Tafada Cikin yanayin sanyinta da mganarta Hafsatu ta kara matsowa kusa da ita da dan karfi tace"Ya Ishaq ya dawo nace.."
Fa'iza ta zaro ido kafin tace"Yaushe..?
Wlh bansani ba..?
Hafsatu tace"Dazu ina falo kafin na shiga Dakin su Amir.."
Fa'iza ta kama Hanyar barin Dakin Tana Fadin"Yana bangaransa ne..?
Da karfi Hafsatu tace"Eh..!
Har ta fice tana binta da kallo ganin yadda take tafe tana kokarin Daidaita Hannun Rigar jikinta na Atamfa Daya dan mata yawa yana dan Fado mata.
Kitchen naa fara isa na Bude Fridge na Dauko mai lemu da ruwa na D'ora saman wani karamin Faranti na kuma Dora Kofuna guda biyu na fito lokaci d'aya na nufi bangaran Megidan.
Kofar shashen nashi yana Bude ne ta Tura ta shiga da sallamanta duk da tasan ba lalle yana Falon ba,Agidan kaf bangaransa ne ke da Falo da Bedroom har guda biyu ne,Kuma bangaransa ne yafi ko'ina kyau domin ayanzu ma kyakyawan Falo ne Dake Dauke da Manyan kujeru na alfarma masu ruwan zuma gabadaya Falon Ruwan zuma ne,harta da Labulayen kalansu ruwan zuma da Hadadden Tattausan Cafet din Dake Falon wani Sihirittacen kamshi na tashi na Irin Turaran da Ya Ishaq ke yawan amfani dashi ne..
Akan Center Table din dake falon na Sauke Farantin Hannuna kafin na karisa D'aya daga cikin Bedroom din Dake bangaran inda na san Ishaq din yana ciki.
Da sallama na Tura kofar na shiga yana Tsaye gaban madubi ya gama saka kayan barcinsa masu Taushi Farare,riga da wando,waya ce a Hannunsa yana mgana cikin Sanyi da Tattausawa.
Ganin haka yasa Fa'iza ta juya zata fita har ta kai jikin kofa Hannunta kan marikin kofar ba zato taji muryansa Cikin Kaushinsa akoda yaushe ya Kirata.
"FA'IZA.."
dayake da karfi yayi mganar na jisa Da Sauri nq juyo inaa gyara wuyar riga ta kallon da yake min ne ya sanyaya min Jiki D'aya sa na kariso gabansa Jikina na rawa ko kafin nq samu Zarafin mgana ya D'aga min hannu Cikin Fushi yana Fadin"Je ki ma kawai domin ganin ki karin Takaici ne a wajena.."
Yafada kai tsaye Lokaci D'aya yana kauda kai Dauke da matsanancin Takaicin daya Dade yana cinsa tun shekaru Takwas da suka gabata.
Duk da ba duka tna jisa ba nasan ransa ya baci sai na Durkusa kan gwiwiyoyina Cikin yanayina nace"Ka..kayi hakuri.."
Kamar na watsa ma Fushinsa Fetir haka ya taso min yana Fadin"An ki ayi Hakurin..?
Nace bazan hakuran ba..?
Aikin banza ni zaki raina haka Fa'iza..?In shigo gidan nan tund'azu kiyi banza Dani kamar wani kashi sannan kin ga Dama kin shigo bangarena kuma kin gan ina waya ki Tsaya in gama ki gaisheni ne ki ke ke jin asara ko..?
Har da juyawa ko kunya zaki Fice ga Dan iska ko..?
To tashi ki Ficemin Daga Daki bana son ganinki..Domin ganinki ba komai Cikin sa sai karin Takaici da bakinciki..wlh har gobe bazan Daina cewa Hajiyar Karofi da Baba sun cutar dani ba..Cuta ta har Abada da suka Hada aure na Dake FA'IZA.."
Ya karishe Fad'a yana nuna min babban yatsansa Lokaci Da'ya da wani banzan kallo dayake bina dashi kaina na kasa ko motsin kirkin na kasa yi daga inda nake durkushe Domin indai ana Sabo da Tozarci da Mganangun Cin mutimci to ni na gama Sabo indai Daga bangaran Yaya Ishaq ne.
Baya ya juya min yana Faman kokuwa da bacin ransa yana jina Cikin yanayin mganata ina kara Fadin.
"Kaayi hakuri don Allah..Ban ji shigowarka bane ina chan ina ma su Anum shirin barci sai yanzu Hafsatu ke shaidamin dawowarka..!
Sannu da zuwa.."
Kyaci yayi kamar wani maciji shifa ba Domin Ya Binta ta Kira sa akan yazo yaga kayan lefensa da ya bata kwangilar hadawa ba,da babu abunda zai kawosa katsina cikin wannan Satin ballatana har yazo ya shaki wannan Bakinciki.
Juyowa yayi yana kallona Lokaci d'aya kawai ya tsaya yana kara kare ma Fa'iza kallo akasan ransa yana kara Tambayan kansa da gaske FA'IZA matar sace?
Fuskarta ya kara kalla yana jin Shima Tunda yake bai taba ganin mai baki,bakin Fuska irin Fa'iza ba, zai iya Rantsuwa ga Allah kaf ajikinta banda Hakoranta ba inda yake da Haske bakace ta kwantance irin bakin nan mai Duhu da Dususu,Sannan mummuna ce bata da kyau a ganinsa sannan bata da Tsaho wanda Hausawa suke cewa mai cike Girman kyan y'a mace Gajera ce,da Fadin Fuskarta kamar Fanteka,Da guntun Hancinta da bakinta mai Fadi shima,Abu daya ne zai ce mai kyau a wajen Fa'iza shine tana da Kirar mata Wannan kam masha Allah Dirarriyace Kirjinta da kugunta suna cike da Fasali ya mace ko ayanzu Data Haifi ya'ya Hudu bata Sauya ba Ta na nan da Jikinta mai Fasali daidai misali bata da kiba sai dai Haihuwa ta d'an Budata.
Sai kuma bangaran Ni'imar jikinta ta wannan bangaran bai da ta cewa ya san Fa'iza fiye da yadda ya san kanshi Fa'iza bata shan kayan mata ko wani abun da zai kara mata Ni'ima duk abunda yaji in yazo tarayya da ita shine Hallitarta wanda Ubangiji ya yi mata,bazai kusheta ta wannan bangaran ba,abu daya ne ke masa cikas baya sonta sannan tun farko komai nata a wajensa bamai kyau ba ne shiyasa ta wannan bangaran ya gaza sakin jikinsa to ya saki jiki a wajen Fa'iza yaji me..?Matar da bata iya komai ba,Shiyasa ba kasafai ya cika Raba'arta ba.
Kayan jikinta ya kara bi da kallo,sai da Ransa ya baci har gobe yana jin Mamakin yadda Fa'iza bata taba saka kayan da yayi mata Daidai ba ko Rigar da hannu yayi yawa ko Sikat kagansa kamar Buhu in yayi mata mgana sai tace itake son haka kada watarana su mata Kad'an,Yau ma din riga da Zani ne ajikinta Rigar Hannun dai bai zama ya na yi ya na Sabule mata Jan Bra dinta Data sanya tana bayyana Saman kafad'anta.
Wani mololoon abu ya tsaya mai yaki wucewa a makogwaronsa Saboda Bakinciki kamar shi ISHAQ KABIR KAROFI kamar shi Ace wannan abar ce Matarsa Uwar ya'yansa..?
In ya kalli FA'IZA sai yaji Fiye da madaukacin Takaicin daya ke ji in ya tuna itace yau MATAR SA..Fa"iza ba mafarkin sa bace a irin Rayuwar ISHAQ KABIR KARAFI..Sam Fa'iza bata dace ko kadan da Tsarin Rayuwarsa ba kowa yasan Ishaq dan gayu ne mai ilimi ne,kyakyawa ne dan Fafane d'an Alfahari ne Duniya tasan da zamansa mai Burin Auran mace FARA mai kyau mai Tarin kwalayen matakan karatun Zamani SAI DAI KASH"
Hakan bai samu ba..Sakamakon kutse da Fa'iza tayi cikin Rayuwarsa ta Ruguza Mafarkinsa har Abada bazai daina Hango FA'IZA a matsayin Nakasun Mafarkinsa ba.
Sannan karin bakin cikinsa yana da Burin kullum in ya Dawo aiki kyakyawan matarsa ta tarbesa ita da yan Gudi gudin ya'yansu Farare masu kyau kamar ya'yan Turaawa tun yana yaronsa yasha yin wannan mafarkin sai dai ina Hajiyar Karofi da Baba sun Saka almakashi sun Datse wannan Mafarkin nashi,Gabadaya ya'yan da suka Haifa da Fa'iza Shekara Takwas da auransu duka ita suka Biyo acikin su ba wanda ya Dauko ko da Hasken Fatansa ne sai Baki irin na uwarsu,Yana Tsananin kaunar yaransa ammh wani Lokacin yana kunyar nuna su ga Duniya Saboda a yanayin Tsarin Rayuwarsa bai kamata Tsarin Iyalansa su zama haka ba.
Duk da irin barnan kudin dayake yi a kansu Fa'iza bata da wannan Tattalin komai sai ta barshi su lalata shiyasa ya gaji ya barta ta karaci muguntarta sai dai yaci ta ita kadai.
Gefen gadon Dake Dakin nasa ya koma ya zauna yana Kad'a Fararan kafafunsa masu cike da gargasa yana kara kallon Fa'iza Dake duke har Lokacin kanta na kasa kamar tamai Sujjada,Kai ya girgiza yana Tunanin yadda yaso ya Dakile ma Fa'iza Haihuwa sai dai ina kana naka ne Allah na nashi,Kowani Tsarin iyali bai karbeta ba,da an saka mata lokaci kadan' sai ya bata matsala na karshe ma da aka saka mata yar Ashanan da jini ya Tsinke mata Dakyar ta sha Ashe Rabon Ahmad ne,Haihuwa take yi akai akai ita ko gajiya batayi da Hidiman yara da Haihuwa kamar akuya..?
Tsakani ga Allah ya'ya indai ta Bangaran Fa'iza ne shifa ya kai makuran Hakura da hakan.
Shi kadai kawai ya saki Tsaki"Mtsewww.."
Kallonta ya sake yi kai Tsaye kafin yace"Where is my Childreen.?
Yafada da dan karfi ta Dago tana Kallonsa Kafin tace"Eh me kace..?
Wani Tsakin yaja Kafin yace"Na manta ba Turanci..Ina yarana na nace..?
Mutum yayi ta wage baki yana mgana har sai makota sun gama jinsa ke ko Sirri ne bamai yi Dake domin kafin ki gama gane abunda mutum ke nufi Duniya ta gama jin Halin Dayake ciki..Mtswwwsss.."
Yana gama Fadin haka ya mike ya Tsallaketa ya fice Daga Dakin,Kaina na kasa na saka hannuna na share guntun Hawayena kafin na mike Salau Salau nabi bayansa saman D'aya Daga Cikin kujerun falon na samesa ya kunna kallo remot a Hannunsa yana Sarrafawa.
Jikina na rawa na karisa inda na ijiye Farantin dana shigo dashi na Tsiyaya mai ruwa mai sanyi nataso nazo gabansa na Duka ina Fadin"Kayi hakuri..Ga ruwa kasha.."
Sai da ya ga Dama sannan ya kalleni kafin ya amshi ruwan kadan yasha ya maida mata yana Fadin"Da ruwa kadai kika iya tarban mijin ki da yayi kwana Goma baya nan..?
Ya fada yana mai Tsurata mata ido Fa"iza bata ji farkon mganarsa ba sai karshe yasa tace"Kwana goma..?
Tafada Cikin alamun Tambaya kai kawai ya Dafe kafin yace"Innalillahi..Gaskiya an gama Dani..Ishaq ka gama aiki kawai.."
Yafada kamar yayi kuka kafin ya kalleta yana Fadin"Ahmad yayi barci ne..?
Tana kallonsa ya kara ware murya yana Fadin"Eh nace Ahmad yayi barci ne..?
Da Sauri tace"Dukaa sun yi barci.."
Kai ya girgiza kafin