Showing 69001 words to 72000 words out of 96493 words
gane me take nufi ba da Sauri tace"Hoto karami nake mgana wanda za'a lika acikin Form din sauran kuma za'a kai musu"
Ta fada tana nuna min inda za'a saka Hoton sai na gane nace mata bani da shi sai tace"Bakomai in mun gama zan Dauke ki Hoto a wayata in na fita sai na Biya shagon Hoto a Wanke min a maida shi karami yau nake so naje na kai ma Hajiyar, Mama ma karya nayi mata da zan yi subbmitting wani aiki a makaranta"
Kusa da ita na matsa ta sauka kasa saboda yadda zataji dadin Rubutu ta dago tana fadin"da Farko a jikin Form d'in sunanki ake tambaya"
Kai tsaye nace"Fa'iza Sidi karofi"
Ina kallo ta Rubuta sannan tace shekaru na gayamata sai kuma ina da aure..?ta saka eh ya'yana na wa..?
Ta saka,sannan yaushe Mahaifina ya rasu na ce ta saka shekaru goma sha da Rasuwarsa ta saka,sai ina da Mahaifiya..?
Nace ta saka eh,Sai ina da Sana'a ?in akwai wata sana'a nake yi acikin gida? nace ta saka Babu,Sannan matakin karatuna nace itama ta sani ko Takardan gama primary ai ban da ita Saboda ban gama ba sai Badariya ta saka matakin karatu na addini Saukakkiya a Qur'ani da Sauran Littafai.
Na kalleta cikin wani yanayi kafin nace"Kada su k'i daukata Badariya kila sun fi son masu takardan ko Sakandiri ne ko Hafsatu zan bar mawa..?
Badariya tace"Zasu Dauke ki in sha Allahu ai ba da Takarda zasu amfani ba, da Kwarewa ce ke kuma ai bana jin ki ta wannan bangaran"
Ni dai duk sai naji jikina yayi sanyi ta cigaba da karantomin ko'ina tana Fassaramim yadda zan gane tace ance in da wata matsala ta fanni hallita ko wani ciwo..?
Nace ta saka ina da matsalan ji,ta saka Hearing problem,Sai adireshin gida nace ta saka na gidan yayanta
Daga karshe sai jerin abubuwan da zasu koyar akwai girken girken zamani da na gargajiya nace ta cike min shi saboda na kara kwarewa, sai Gyaran jiki dilka da Halawa nace shima ta Cikemin,sai kuma koyan yadda ake had'a lemuka kala kala nace shima ta cikemin akwai koyar da Kunshi Fulawa,koyar da manshafawa da su sabulan wanka da na kamahi sai koyar da su yaji kori da kayan kamshin Girki sai koyar da Turaran kamshi na Itace da kwallacha
suma nace ta cikemin duk zan koya Badariya na Dariya tace"Anty Fa"iza duk ke kad'ai an ya zaki iya..?.
Ina da yakini acikin raina nace"In sha Allahu ai basu da wahalan dauk'a zan iya da amincewar Allah"
Ta amsa min da in Allah ya yarda sannan daga karshe akace in mutum nason a bashi tallafi yace eh ta sakamin eh sannan da kuma abunda zakayi da tallafin in an baka
Na kalli Badariya ina fadin"Kice ina son a bani tallafi nan saboda na kama sana'a daga cikin sana'o'in da suka koyar damu..Sannan saboda na rike kaina na kuma tallafama rayuwar ya'yana saboda inganta goben su watarana"
Haka kuma ta rubuta sai lambar waya nace ta saka min nata tunda ni bani da waya sai ko ta saka lambar wayarta.
Daga karshen karshen sai saka hannuna ta bani na jagwalgwala hakanan,Kafin ta tafi sai da ta D'auki Hotona a wayarta bayan na saka Hijabi tace zataje a fito mata dashi a gyara muka yi sallama zuciyata ta cika da murna ammh ban daina saka Allah cikin lamarina ba adaran nayi salla sannan nayi addu'an Allah yasa mafitan nan ta zame min mafitan alheri a rayuwata gabad'aya.
Ni dai ina ta addu'a ko da naji shuru ban damu ba daman nace in mafitan ta alheri ne Allah ya tabbatar min in kuma ba alheri aciki Allah ya kawo min wata mafitar ta alheri Ameen.
Kafin kayan abincin da Sa'adatu ta kawo mana ya kare ta kawo min Dankali hausa da yawa tace itama daga gida aka aiko mata dashi,Babansu ne ya noma na karb'a na saka albarka shi nakan soya ma yara da Safe su tafi makaranta,Wata rana ma har da rana ina soya mana muci mu sha ruwa,kuma dayake na koyama yarana cin komai duk abunda suka samu zasu ci basa zabar abinci shiyasa sai rayuwar tazo min da Sauki.
An yi wata da cike Form din da mukayi ni da Badariya tazo sau d'aya mukayi mgana tace Raliya tace an Tura Tarkadun namu chan kaduna inda Babbar Jibiyar kungiyar take da su zabi wad'anda zasu dauka za'a turo ma kowa ta sakon waya da lambar da ya saka Badariya ta tabbatar min da Hajiyar su Raliya tace ba matsala sai na saka raina asalama araina nace bakin Da Allah ya tsaga bazai taba hanasa abinci ba.
Ana haka kwatsam sai ga Ya Ishaq ya Dawo ranar wata asabar da azahar Lokacin bana gida na shiga wajen sa'adatu muna hira to yara in sun tafi makaranta sai ni kadai kamar mayya na da zauna tunani ya kasheni sai nake shiga muna hira tana Debemin kewa rashin dangina akusa dani.
Get din a bude na barsa saboda ban yi nisa ba yagaji da Hon ya fita ya Bude ma kansa ya shigar da Motarsa sai da ya shiga gidan ya tabbatar da ba na gidan mamaki ya kamasa ya D'aga waya ya Kira Mama ko nazo Mama tace tafi wata biyu ban zo inda take ba.
Ransa ya baci nan da nan ya fara Tunanin haka nake fita ina barin masa gida a bude ina tafiyata gantalin da baisan yaushe na iya ba,Ni kuma ban san ya dawo ba sai biyu da rabi na Dawo gida domin yi ma yara girki,sannan nazo da Guzurin Dambun Dankalin da Sa'adatu ta zubamin mafarin zamana ma yau saboda na koya ne ina so nima watarana nayi lokacin da na shigo Haraban gidan naga Motarsa ban ji tsoro ko fargaba ba Allah na Tuba in da sabo ai yaci na saba da Tozarcin sa a gareni.
Kaina Tsaye na shiga cikin gida kamar daman yana jira na ne sai yau ya gwada kiran wayata a kashe duk tsawon Lokacin da ta lalace bai sani ba.
Yana ta Safa da marwa a falon ya kasa zama na shigo bayana goye da Ahmad Hannuna Dauke da kwanon Silba da Sa'adatu ta zubomin dambun aciki.
1do hudu muka had'a dashi Sanda na shigo yana bi na da wani kallo na raini kamar yadda ya saba ni kuwa sai na Dauke kaina ina fadin"Sannu da zuwa.."
Nafada ina nufar Hanyar Kitchen nasan yayi mamakin yadda nayi mai shiyasa ko taku uku ban yi ba yasha gabana cikin bacin rai yana fadin"Ni kika gani kika dauke kai kamar kin ga Dan'iska Fa"iza?
A gajiye na kallesa cikin yanayina nace"Nayi maka sannu da zuwa..ina so na shiga kitchen na sauke abun hanuna ne"
Kallo hannuna nawa ya shiga yi Lokaci daya yana fadin"Miye wannan kuma..?
Sai na Bude masa ina fadin"Dambun Dankalin Hausa ne na shiga ta koyamin ne saboda ina so nima nayi ma yara"
Yamutsa fuska yake yi kamar yaga kashi kafin yace"Wannan bakin abun ne zaki yi ma yarana su ci..?Shiyasa kika bar min gida a bude kika fita yawonki me na sha fada miki..?
Ban ce ban amince ki rika fita ko na nan da chan ba indai ba gidan Mama ba..?shine kike so ki nuna min kin isa har kina shigowa kina ganina kika Dauke kai kamar kin ga sa'an ki ko..?
Na kallesa da Idanuwana da suka yi ciki ciki ban iya rashin kunya ba Saboda ba Halina ba ne ammh dai naji Tsoro nan nasa da nake ji a baya ya gushe araina na kasa ce mai komai kawai sai na rabasa na wuce kitchen na sauke kayan hannuna a zafafe ya biyo ni yana fadin"Fa'iza ina miki mgana kina wucewa yaushe kika raina ni haka ban sani ba..?
Ko tankasa ban yi na sauke kwanon Hannuna ya shigo Kitchen din yana Fadin"Daga gidan uban wa kike..?rokon abinci kika fara na salon zubar min.."
Bai karisa mganarsa ba yayi shuru ganin Dankalin hausa zube a kitchen din sannan na bude karamar kular dake saman wajen wanda na soya ma su da Safe ne na rage ma Ahmad in ya tashi daga barci yaci,na dauko na barsa akitchen din yana Dube dube cike da mamaki..
Afalo na zauna akasa na kwanto Ahmad daga bayana da naji motsin tashin sa kamar walkiya sai ga shi a gabana yana fadin"Fa'iza wannan dankalin fa..?sannan naga store ba komai wannan watan mama bata aiko da kayan abincin ku ba ne..?
Ahmad na kallonsa ammh sai ya lafe ajikina ba irin zumudin daya saba yi mai a baya ni kuma ban kallesa ba nace"Wannan dankalin shi kad'ai garemu shima daga gidan haruna aka bani kyautarsa kayan abinci kuma ba'a kawo ba"
Daga haka na tsuke bakina daga alamu jikinsa yayi sanyi sai ya fara Fadan meyasa ban kirasa na gayamai ba cikin gajiya da korafinsa nace"A ina zan ganka ballatana na fad'a maka..?
Kai tsaye yace"Ina wayarki fa ?ko bata da amfani ne da bazaki kirani ba..?
Ina bama Ahmad Dankali nace"Bani da waya ta lalace tuntuni"
Sai kuma ya kasa mgana,Daganan ya shige bangaransa bansan ko ya kiran Maman ne me tace mai oho yadai fita sai chan kuma ga shi da Cefanen kayan abinci masu yawa wani Lokacin Ya Ishaq bai da matsala ta bangaran hakkin iyalansa da ya'yansa sai dai Mama itace tafi matssala ta wannan bangaran
Daga karshe yace na kwashe Dankalin nan na fitar mai dashi nace tab wlh bazan kwashe ba,Kafin yazo ai shine ya Rufamana asiri sai ya kasa mgana nasan yana ta mamakin yadda wannan karon nake iya maida masa mganarsa kai tsaye ni ko gani nayi tunda alfarma yake min nima sai na fara mai alfarma saboda ya'yan da suka hadamu tsakanina da shi ba Domin zumunci da baisan Darajansa ba.
Yaran ma da suka dawo ko da suka gansa ba su yi wani D'oki kamar baya ba, shine daya lura da haka ya rika jansu ajiki washegari kuma yace bazasu je hadda ba ya daukesu suka tafi yawo ya siyo musu kayan kwalama da duk abunda suke so,Daganan ya sauke su gidan Mama sai Dare suka dawo ashe sallama yazo yi ma su mama zasu tafi india inda Mahaifin zainab ya dauki nauyin su Saboda aduba lafiyar Farhan sai a daran da suka dawo ya fadamin ban san Dalili ba sai naji ban damu ba nayi masa fatan isa lafiya da kuma samun abunda akaje nema.
Washegari Litini ya koma ban ma sani ba ashe ya biya Haruna kudadensa har da na wata biyu anan gaba yana ta basa Hakuri,Harunan ya ke shaidamin washegarin talata da na rako su Amir kofar gida araina sai naji sanyi,in zan fadi gaskiya Yaya Ishaq baya so na ammh kuma yana son ya'yansa kuma bai hadasu da komai ba, sai dai sabon iyalansa sun Dauke masa hankali har akan yara sannan da karin muguntar Mama acikin lamarin tunda ita ake barin ma komai.
Ina nan bansan abunda ke faruwa ba Ba mai nema na kuma nima bani da Hanyar neman kowa ashe Tamadina bata da lafiya ta fito daga bandaki ta zame ta fad'i shikenan jikinta yayi nauyi tun tana gida har an kaita asibitin general na bakin asibiti,Har Yaya Asiya dake kano ta sani tazo ammh ni da nake kusa ban sani ba Goggo ganin ba'a samu inda zan ji ba sai ta Kira Mama a waya tace ta fadamin Lokacin Hafsatu suna Jarabawa,bata samun zama shiyasa ma Goggon tace bari ta kira Maman,Tunda Har Yaya mariya sai da tace tazo ta fad'amin tace ma Goggo sai dai tayi Hakuri bazata iya zuwa ba jin haka yasa Goggo bata matsa mata ba.
Ita kuma Mama da aka fad'amata washegari yamai ta tafi, diyar Kanwarta ta haihu,kuma abun bai Dameta ba shiyasa sai ta sha'afa.
Sai da jikin Tamadina ya kara rikicewa Goggo ta tada Ya Isa tace yazo ya fad'amin nazo in muna da Rabon ganawa da tamadina tana asibiti bata da lafiya.
*Littafin KANA NAKA book2,3.paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*
*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*
*Janafty*
*KANA NAKA..!*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWAR ZAKI YI AMFANI DA ITA SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*..
*🅿️16*
Na gigice tare da Dimaucewa lokacin da Yaya Isa yake shaidamin Tamadina bata da lafiya ta kwana uku a asibiti bayan tayi sati a gida ba yadda take.
Sai naji na rasa hankalina na wani lokaci, na koma nayi yaraf saman d'aya daga cikin tsofaffin kujerun falona kamar wata kayan wanki.
Hawaye nan da nan suka fara sintiri a saman fuskana kamar an bud'e famfo sai yau na kara tabbatar da cewa Mama bata kauna ta kuma har abada baza ta taba so na ba,Uwa ai ta wuce wasa ace a fad'amata rashin lafiya ammh ta gagara aiko ko Badariya ta shaidamin sai da aka gaji da jirana akaji shuru Goggo ta tado mutum tun daga karofi akazo aka fad'amin, kawai tuna hakan da nayi sai naji raunina ya karu na Fashe da kuka Yaya Isa ya zauna gefena yana fadin"Ki daina kuka Fa'iza jikin da sauki sosai.."
Na dago idanuwana sharkaf da kuka ina fadin"Wa ke zama da ita..?
Kai tsaye yace"Mariya ce..Asiya tazo ta kwana biyu ta koma to bata ma nan aka kai ta asibitin ammh naji Goggo tana fad'amin itama gobe tana Hanya"
Jin haka sai na kara saka kuka ina fadin"Allah ya tada kafad'un ki Tamadina Allah ya baki lafiya"
Ya amsa min da Ameen yana fadin"Ki tashi ki shirya sai na sauke ki a asibitin"
Da sauri na mike jikina yana faman bari har na shiga d'aki na Sunkunci Ahmad dake barci na goya na zura Hijabi sai kamar an tuna min na tuna da su Amir sai jikina yayi sanyi na fito ina Raba ido na neman mafita yanzu in na tafi ina su Amir zasu zauna..?
Ko gidan su Sa'adatu zan ce su zauna kafin na dawo..?Sai dai akwai D'awainiya acikin lamarin yara ba d'aya ba,ba kuma biyu ba har guda Hudu ganin yadda jikina ya kara Sanyi ne yasa yace min"Muje ko..?
Ya fada Lokaci daya yana mikewa sai yaga kuma ban biyosa ba sai ya juyo yana kallona kafin yayi mgana na taresa da fadin"Ya Isa yara na..Su Amir bansan inda zasu zauna ba, in suka dawo daga makaranta ba"
Kai tsaye yace"Su zauna gidan kakaninsu mana"
Sai kawai na koma na zauna ina sharan kwallah Lokaci d'aya ina fadin"Ya isa kaje kawai sai gobe da Sassafe zan taho in sha Allahu"
Shima kansa nasan mamaki yaji da mganata saboda yadda ya ke kallona sai na sake sadda kaina ina jan majina.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Shikenan ki tabbata goben kin taho kin ji ko..?
Yafad'a cikin alamun Tausayawa acikin lamarinsa na gyad'a mai kai sai ya kara kallona yana fadin"Kina da kudin mota ne..?
Sai na kasa mgana shi kuma ganin haka sai ya cire dubu uku yan Dubu Sabbi ya bani yace nayi na mota na karb'a ina godiya na mike shi kuma ya wuce da sauri nace"Wani ma asibiti kace..?
Bai juyo ba yace"Asibitin general da ke bakin asibiti Dutsenmah"
Na gyada kaina ina fadin"Ka gaisheta ka fad'ama Goggo gobe da Safe ina tafe..Allah ya tashi kafad'an Tamadina"
Ya amsa da Ameen ya fice bayan ya kare ma falon kallo lokaci da'ya yana girgiza kansa.
Komawa nayi na zauna in da na tashi na Rushe da kukan,kukan bakinciki da takaiici ace Tamadina ta kwanta jinya tafi sati ban sani ba to ni a wani bingire zan saka rayuwata ne..?
Ahmad da yaji ina kuka shima ya fara Rigimansa na kwantosa na Rumgumesa na cigaba da kuka sai kawai ya rika bi na da kallo.
Haka na yini cikin wani yanayi motsi kad'an sai na daga hannuna sama ina fadin"Ya Allah ga baiwarka chan tamadina kafini sanin Halin da take ciki..Allah ka bata lafiya ka tashi kafadarta"
Ko abinci da na kan yi ma yara da wuri ranar sai da suna gabda dawowa na dora musu farar taliya nace sa ci da mai da yaji,Domin bani da natsuwar yin wani abincin da zai bani wahala su kansu da suka Dawo sun ganni duk a sanyaye sannan fuskata da Idanuwana sun kumbura hatta Ahmad rigimamme yau bai yi min rigima ba kamar yasan bana cikin yanayi mai dadi.
Sun dawo suna murnan an basu resit a makaranta na shedar sun biya kudin makaranta har na Team biyu,Alfarma akayi musu saboda naje wajen sau biyu ina basu hakuri sai wannan lekowar tasa ne yaran suka mai mgana inaga yaje ya biya musu, ko kuma ya tura musu.
Ni dai da yake ba wannan ne a gabana ba ko duba Takardan ban yi ba,nace su adana cikin Littafansu.
Amir ne mai wayau cikin su shi ne ya tambayeni Umma baki da lafiya ne..?
Na kallesa cikin wani yanayi sai na kasa basa amsa,sai da daddare bayan mun idar da sallar Isha'i dukkanmu muna zaune sai na kallesu ina fad'in"Kowanne ku ya d'aga hannu ya ce Allah ka bama tamadina lafiya.."
Sai suka tsaya suna kallona Anum ce tace"Umma wace ce?
Da sauri nace"Ina wannan da ta taba kawo muku gyad'a da su masara har nace muku mamana ne kakarku.?
Suka gyad'amin gabad'ayan da sauri nace"To mahaifiyata ce, bata da lafiya ku yi mata addu'a in dai kuka yi sallah"
Fuskarsu ta nuna jimami Amir yace"Allah ya bata lafiya Umma"
Na amsa mai da Ameen atare muka daga hannu muka yi addu'a da Fatan Allah ya bama Tamadina lafiya.
Saboda tafiyata Dutsenma agobe da wuri nace su kwanta ko karatun Dare basu yi ba na kwana ina Tunanin inda zan kai su Amir su zauna kafin na Dawo na duba na hango ba su da inda yafi gidan Mama dole dai ko naki ko