Showing 36001 words to 39000 words out of 96493 words
kawai ina kallonta a kasan raina naji bacin rai kawai yana taso min daman ina jin Haushi yadda Anum ta koyi shagwabar banza abu kadan za'ayi mata sai kawai ta fashe da kuka wani Lokacin har da birgima.
Mikewa nayi dakyar bata sani ba sai dai kawai taji saukan mari sai tayi tsit na kalleta raina a bace cikin fada nace"Ki ka ka..ra..min kukan banza anan sai nayi miki dukan tsiya zan baki Babu ne Saudatu..?.
Na kirata da ainihin sunanta sai ta kasa mgana ta koma ta zauna ana son kara fashewa da kuka tana jin tsoro Amir da Musty sai suka tsorata suka koma suka lafe a zaune idanuwansu ya ciko da kwallah ganin yanayin su sai Tausayin su da tausayin kaina ya kamani na koma na zauna na jawo Anum jikina na Rumgume ina share mata Hawaye.
Ta lafe ajikina tana sauke numfashi sai na Fahimci yara irin su Anum basa bukatar tsawa ko fad'a ko Duka a jasu ajiki sannan a lallashe su cikin yanayin mganata na fara lallashin ta ina fadin"Anum biskit din ku ya kare da lemu kuma bani da kudi ki yi hakuri ku tafi in na samu zan siya muku."
Ta dago idanuwanta da alamun kuka tace"Umma Daada fa ya na ina..?
Sai na kasa bata amsa Amir ne yace"Daada na Abuja"
Mamakin sa ya kamani a ina yaji Babansu na Abuja wata zuciyar ta fadamin zai iya sani ai baban nasu na zauna yayi hira da su kamar manyan yara.
Ni dai na samu na Lallashe su suka tafi hakanan na dawo na zauna tayi Tagumi ina tunanin in yau sun hakura gobe fa..?
Ko Badariya da kan lekomu lokaci bayan Lokaci itama shuru naji ta ni ba kudi a waya ba ballatana na kirata,Ina gane lambar kowa saboda da ajami na Rubuta na iya rubutu da Ajamin labarci tunda Hausan ban iya ta sosai ba, ba komai nake ganewa ba.
Haka washegari ma Dakyar Anum da Musty suka yarda suka tafi a makaranta ba biskit ba Lemu,na rasa yadda zan yi da su,kuma ko giyan wake na sha bazan taba kiran ya Ishaq nasan sauran abunda zai biyo baya shi da ya ijiyemu bai Tuna damu ba sai nice zan neme sa,ai ko bai neme ni ba sai ya Tuna da ya'yansa ya Tuna da Hakkin kula da komai nasu yana wuyansa ne ammh bai iya tunawa da wannan ba Tunda ya samu Cikar Burinsa bai damu da komai da kowa ba ni tunda ya jingine ni sai ya tuna da ya'yansa tunda su bai jingine su ba.
Hakanan na cigaba da lallab'a rayuwata yadda Allah ya tsaramin Tun su Anum na rigima har suka zo suka Hakura,Sai kuma suka fara Damuwa da ina Daada bai taba Sati Hudu bai zo gida ba sai wannan karon in suka tambayeni ina Daada kasa mgana nake yi in suka Dameni sai nace ya kusa dawowa aiki ne yayi masa yawa Ranar da Dadaddare bayan mun gama sallar isha'i suna zaune suna aikin makaranta da aka basu Amir na taya mutsy nayi na shi Dayake shi yana primary 1 ne Anum Nursey 2 take Musty kuma Nursey 1 ni ban yi boko ba,ban san komai a bangaran su ba sai dai ina gane wasu abubuwa na y'an Nursey,iyakata da su bangaran islamiya da Hadda da karatun Qur'ani da azkar wannan bangaran ban yi waasa da shi ba,shi na iya shi kuma zan koyama ya'yana.
Anum ce ta kara tambayata Daada sai nace mata ya kusa Dawowa Amir ya Dago kansa yana fadin"Umma Daada wata Umman ya samo mana achan Abuja..?
Mamakin sa ya karamani na kallesa na kasa mgana Amir tun yana Shekara Biyu da wattani ya fara mgana yaro me mai wayau sosai cikin Mganata nace'wa..ya fada maka..?
Kai tsaye yace min"Uncle Jamal..Ba mun je har chan ba..Umma naga Daada yaci gayu sosai"
Daganan ban kara mgana ba ina jin Anum na girgizani tana fadin"Umma da gaske ne..?
Musty na tayata da gwarancinsa,Dakyar na iya bude baki na amsa musu da hakane sai kawai suka fara Murna Anum kenan Amir kuma bai tashi ba Musty kuma ganin ta mike tana Tsalle shima ya mike yana Tayata Ahmad na jikina ya lafe ba barci yake yi jikinsa ne ba Dad'i zawon hakori sannan ba kudi ballatana na kaishi asibiti.
Amir ne ya kalkeni kafin yace"Umma to ta na ina ita Sabuwar Umman tamu..?
Kai tsaye nace"Tana tare da Daadan ku achan Amir"
Cikin mganarsa ta kuruciya yace"Umma to me yasa Muma Daada bai tafi damu dake gabad'aya mu zauna achan ba?
Mirmishi nayi wanda yafi kuka ciwo kafin nace"Watarana zamu je Amir in sha Allahu"
Zai kara mgana nace su cigaba da aikin da aka basu a makaranta Anum kuma sai ta koma wasa da musty ni kuma sai na zurfafa cikin Tunanin haka rayuwa zata cigaba da tafiya har yara sun fara gane wani abum..?.akwai nan gaba akwai matsala in dai abubuwa suka cigaba da Tafiya a yadda suka faro.
Ranar da Ya Ishaq ya cika kwana Talatin a abuja,ranar jumma'a da yammh sai ga Anty Binta batagwara tazo nayi mamakin zuwanta ammh ban nuna ba naje na Debo mata ruwa mai sanyi da nakan diba na saka a fridge saboda ruwan ledan ya kare na famfo muke sha.
A wani karamin jug na dibo mata na Hado mata da karamin kofi na koma ma zauna a kasa ina gaisheta Amir da Anum suna Haraba suna wasa Musty kuma ya kwanta Ahmad ne ke goye a bayana.
Ina gaisheta a wulakance ta amsa tana kallona da ni da Falon sama da kasa tana wani yamutsan fuska kamar taga kashi ruwan da na kawo mata ta kallah kafin tace"Wannan ruwan fa..?ba ku da na Gora ne..?
Cikin Ladabi nace"Ya kare wannan na famfo ne nake sakawa a Firij Saboda yayi sanyi"
Baki ta tabe kafin tace"Shi ne kuma D'an pure water bazaki iya siya ba komai kina jiran sai bawan ki yazo ya siya miki,ko ke irin Dubarun nan na mata da suke yi na taimakon mazajen su baki iya ba sai dai komai ki kwanta Shi d'an wahalan yayi miki ko..?
Na kasa Dagowa ma in kalleta da karfi take mganar shiyasa na ji ta sosai duk da ba duka ba.
ina jin ta har ta gama cin mutumcinta ban iya Dagowa ba,Sai chan ta mike tana zagayen falon tana leka Dakunan ta Dawo tana fadin"Gaskiyan Ishaq ne da yace gwara nazo na duba kada ya kawo Amaryansa yaji kunya..Ji yadda kika lalata ko'ina na gidan nan Fa'iza..?
Tsiyan a kawo wacce bata dace da irin gidan nan ba kenan ba sanin Darajan sa kika yi ballatana ki Lura da shi"
Taja karamin tsaki kafin ta koma ta zauna kafa kan d'aya ta Dauko Jakarta ta Ciro wayarta ta yi Danne danne ta kara kunne ina ji tana mgana ban ji me take fadi ba Daga karshe dai naji tace"kada ka damu ai zan ja mata kunne in ta yi ba Daidai ka dauki mataki a kanta"
Daga haka ta Datse kiran ta kuramin ido kafin ta daga murya tana fadin"Ke wai baki da aiki sai goye ne..?
Kaina na kasa nace"Ba ba shi da lafiya ne..".
Baki ta tabe kafin tace"Uhm..Kina ji..?
Tafada har da rike kunnewanta na Dago kaina ina kallonta na gyada mata Tsawa ta dakamin tsawa tana fadin"Matso kusa dani domin bazan iya Ihu ba ina mgana"
Dole na ja jikina kusa da ita kunnena ta kama guda d'aya ta rike tana fadin"Abunda nake so na gaya miki shi ne..Gobe Ishaq zai zo shi da Zainab kuma nan zai sauketa da farko yace gidan Mama saboda yasan Halin ki kada ki basa kunya ni nace nan zai sauketa tunda tasan yana da gida har da Mata da ya'ya Saboda haka gargad'i na Farko shine zaki gyara gidan ko'ina yayi fes sannan ki shiga shashensa ki gyara ko"ina nan Zainab zata sauka har ta gama kwanakinta ta koma"
Ta fada cikin daga murya Lokaci d'aya tana kara jan kunnina zafi nake ji ammh na Daure na kasa nuna mata Raunina cikin kara rike kunnina tace"gargadi na gaba shine ki kama kanki kin dai san ba D'aya kuke ba..Zainab yar boko ce sannan yar gatace gaba da baya ki kula sosai ki Tsaya iya matsayinki ki karbeta hannun Biyu ki mata Hidima duk abunda tace tana so ki yi mata kada kice zaki yi gaddama zaman ki lafiya shine Zainab ta koma Abuja ba bu abunda ya faru Ishaq yace na Fad'a miki kada ki kunyata sa agabanta yasan Halin ki baki da Tunani wani Lokacin kina jina ko..?
Idanuwa sun kawo ruwa ammh sai na maida su cikin Rawan murya nace"Eh..e..Naji"
Sannan ta saki kunnena tana fadin"Sannan ki yi wanka ki d'an gyara jikin ki in tazo ta ganki wannan yarkace yarkacen shi zai kunyata sannan yaran nan suma ki yi musu wanka ki sanya musu kaya masu kyau kina jina ko..?
Nan ma kai na gyada mata key din Shashen nasa ta ciro a jaka ta bani na saka Hannun Biyu na karba sannan ta kara da cewa"Zaki yi musu girken girken Tarba sosai yace tana son Sakwara da miyar agusi,Sannan ki yi mata kunun aya da Ferfesun kayan ciki,ki soya mata Naman kaza ki yi pepe dashi"
Kaina na kasa ban dago ba nace"kayan abincin mu duka ya kare shinkafa kadai garemu"
Bata Damu ba ta mike tana fadin"Daman ai kamar ya san zaki kawo korafin babu komai anjuma Jamal zai kawo miki Cefane..Wlh Tallahi Fa'iza in kika kuskuere mganata ki ka bamu kunya gaban Zainab sai kin Raina kanki ki kuma sani ki kara Sani matsayin ku ba D'aya ba Zainab yar gatace gaba da baya sannan yar boko ce mai kyau yar babban gida"
Har Haraban gidan na rakata tana kara ja min kunni da kara Jaddamin matsayina sai naji ban damu ba Domin ko bata fada ba ban isa na Hada kaina da wacce suke kira da Zainab ba,na ganta a hoto na kuma san ruwa ai ba'asan kwando ba ne.
Nayi kokarin yakice duk wani abu dake cikin raina Hankalina ya tafi kan Ahmad da Zazzabin jikinsa yayi zafi panadol na ruwa nake basa shima Sauran na Musty ne da yayi zazzabi kwanaki Ya Ishaq ya siyomin Hankalina duk ya tashi,ga shi yana ta zawo bani da pampers sai napkin nake yi mai kafin Safe ya bata kaya da yawa ina tashi da wankin na tashi,Sai da na gama tsabtace sa sannan na yi musu shirin Tafiya Hadda.
Saboda bani da masaniyar sanda Bakin da zasu iso,Bayan tafiyar su sai ga Jamal ya kawo min cefane nake tambayansa ashe bai koma ba..?
Sai yace min bai koma ba sai sati na sama shima ko zama bai yi ba yayi min sallama ya tafi.
Sai da na fara zagewa na gyara Shashensa,tas na turara turaren wuta mai kamshi sannan na gyara Falon da Sauran Dakunan daidai yadda zan iya sannan na Fad'a Kichen Hankalina ya kwanta Ganin jikin Ahmad yayi sauki har ya samu barci.
Cefane ne da yawa saboda bakuwa zata zo shiyasa aka siyo aka kawo har da Lemuka da ruwa kwai,Dankali Doya,Kayan lambu taliya macaroni da Buhun Shinkafa sai Couscouss,na Sauke komai a muhallinsa har da aya nagani Saboda ai Anty Binta tace Zainab nasan kunun aya.
Banji kyashi ko mugunta ba na zage na fara aiki kan jiki kan karfi miyar Sakwaran na fara yi sannan nayi ferfesun kayan cikin araina ina jin Dadin Dalilinta yara ma zasu samu chanjin abinci.
Na zuba a kololi na rufe naje nayi sallar azahar na zauna na Huta saboda ina Tunanin sai yammh zasu shigo,ashe ma sun zo garin gidan Mama suka fara sauka Badariya ta shiga makaranta sai ta Biyo ta iskeni ina makarda ayan a blander dina wacce Dakyar ma take yi tana yi ta na mutuwa ta tsufa duk taji jiki.
Tana ta fadamin uban kayan da Zainab din ta kawo ma su Mama har da ita an zo mata da abaya ni dai sai dai yake na kasa cewa komai.
Bata jima ba ban yi sakwara ba Ferfesun ta Diba taci sannan tayi sallah Tatafi jin sun iso yasa na mike na Cigaba da aikina kafin La'asar na gama komai hatta dakan sakwaran,nasha wahala sosai ga Ahmad a baya na ya tashi ya saka Rigima Dole na goyasa haka na yi ina yi ina Hutawa ina Haki,Kazan a karshe na Soyata kamar guda biyu ce ta Turawa sannan nayi pepe chicken na shirya komai na ijiye anan kichen din sannan naje nayi wanka na Sauya kaya na saka Atamfa ta riga da Sikat,ko Hoda ban shafa ba domin bani da ita,ban kuma ji ina son na Burge kowa ba sanin ko nayi bazan burge kowa ba.
Karfe hudu daman nace Haruna yaje ya Dauko min su Amir,Shima din yana da Hakuri da Darajan makota wajen wata biyu Ya ishaq bai basa kudin sa,ina Tunanin ranar da yagaji ya daina kai su sai dai na kai su a kafa kuma akwai tazara mai yawa Tsakanin gidanmu da makarantar tasu.
Suna Dawo na taya su suka cire kayan makaranta ko alama ban gaya musu Babansu zai dawo ba Na riga daman na Dibar musu sakwaran ni dai ko ban ci ba,su dai su samu su ci,daki na jasu sukaci achan kada su ci afalo su lalata Su shigo fada'n komai ya Dawo kaina na shiga uku.
Bayan sun gama Daman sun yi sallar su a makaranta,Sai na saka musu Sabbin kayan su Anum nata Murna Amir ne yace"Umma anguwa zamu?
Sai nayi masa shuru ban ce komai ba sai na Tuna naji wani malami yana mgana kan tarbiya yara yace kada yaro ya jefa miki tambaya ki yi shuru to a ransa zai saka wani abu.
Sai nayi saurin cewa"Sabuwar Umman ku ne zata zo Amir"
Dukkansu suka bini da kallo ban damu ba na cigaba da fadin"Tare da Daadan ku zasu zo in kuka ganta ku je ku gaisheta itama Umman ku ce"
Anum da Amir suka Dagamin kai Musty na chan na wasa da kwalliyar jikin Yan kantin da na sakamai riga da wando.
Hatta Ahmad da bai jin Dadi na sakamai yan kati riga da wando,nayi mai Napkin duk da zawon yayi sauki ba kamar jiya ba na goyasa Tunda baya jin dadin jikinsa har alokacin.
Su dai yaran suna ta Tsalle tsalen wasan su ni kuma ina zaune nayi jugum ina Tunanin wani irin Tarba amaryan Ishaaq zatayi min..?
Sannan wani zama zamu yi da ita acikin gidan nan..?
Nayi zurfi cikin Tunanina naji Amir a saman kaina yana fadin"Umma wayarki umma."
Nayi firgigit na kallesa wayatace a Hannunsa ana ta kira ya mika na karba sai da gabana ya fadi da naga Sunan Ya Ishaq na kirana cikin Rawan jiki na Daga kiran tun kafin nayi sallama naji muryansa cikin Kaushi yana fadin"Ina kika kuma jefar da wayar ina ta kiran ki baki D'auka ba..?
Cikin yanayina nace"Ban ji ba ne.."
Karamin tsaki yaja kafin yace"Ina fatan kin gyara ko'ina..?
Yanzu zamu baro gidan Mama"
Kamar yana ganina na gyada kai sannan nace Allah ya kawo ku lafiya
Bai ko amsamin ba ya katse kiran ya barni da waya a hannu ina Tunanin mafita da farko wlh jikina bai saki ba sai da ya kirani yace gasunan zuwa naji gabbaina sun saki jikina ya fara rawa ina nan zaune ina fama da Faduwar gaba naji kamar ana taba Kofar falo ko Hon dinsa banji ba ballatana Shigowar Mota,to ina ma nake da karfin jin ballatana,yadda hankalina ya bar jikina raunannun kunnuwan nawa ba su saka naji ko motsin shigowarsu ba.
Sai da naji Sallamarsa da mganarsa Su Amir na dago na kalla basu bi ta kaina ba suka fice da gudu suna kiran sunansa Daada kamar yadda suke kiransa.
Ni kuma ina zaune na kasa tashi Jikina gab gab yake yi kamar mazari gabana ya fara Dif Dif kamar an sakamin Wutar lantarki ji na nayi na kasa motsi sai yanzu nake jin yanayi na ba Dad'i ina Tunanin da wani irin kallo Amaryan tasa zata karbeni,?Kamar acikin kaina naji yana Kiran sunana a kausashe kamar yadda ya Saba.
Sai na zabura na mike da Hanzari Daidai Anum na shigowa Dakin ta fara jan Hannuna tana fadin"Umma Daada na kiran ki"
Kamar rakuma da akala haka Anum ta rika jan Hannuna har Tsakiyar Falo inda Ishaq da amaryan suka samu mazauni saman kujera mai zaman mutun biyu Amir na jikin Babansa Musty na Dauke ajikin wata Farar mace Doguwa Lalle tsarki ya tabbata ga Allah shugaban Hallitun Duniya.
Lalle gaskiyan su Anty Binta ne kada na Had'a kaina da zainab,tazaran kamar sama da kasa ne a wajen nisa ashe a Hoto ma an rage mata kyau da Haske kamar balarabiya tana sanye da Wani leshi daga ganinsa mai Tsada ne doguwar riga taci Daurinta gashinta ya zubo har gadon baya Fuskata Dauke da kwalliya mai kyatarwa kafafunta da Hannayenta Sun ci kunshi Lalle baki da Fari kamar don ita ma akayi zanen Saboda yadda kunshin ya haskata kafarta da Takalmi daga ita har Ya Ishaq basu cire takalmansu ba har zuwa Tsakiyar Falon.
Kanta na kasa tana ma Musty wasa yana mata gauranci bata san da ni a Falon ba ni kuma kawai ita nake kallon Sakin Hannuna Anum tayi ta nufi Babanta tana fadin"Daada Umma"
Shima sai Lokacin ya Dago yana kallona ina ganin sanda Fara'arsa ta Dauke kamar yaga mutuwarsa hararata yake yi kasa kasa ni kuma Chanzawarsa nake gani yayi kiba kamar bashi ba Daga gani ya samu kwanciyar Hankali sosai.
Na kasa gaba ballatana baya sannan bakina yayi nauyi shine da yaga haka ya D'aga baki yana fadin"Haka ake tarban baki a karofi ko Fa'iza..?
Sai alokacin ta Dago kanta muka Hada ido hudu da ita ni dai a bangarena sai naji na muzanta ni bansan yanayinta a bagaranta ba sai dai ban gane yanayin da take ciki a Fuskarta ba.
Tayi saurin Shanye mamakin ganina ta kallesa tana fadin"Maman su Amir right..?
Tafada tana bin sa da wani irin kallon da Sai da na kauda kaina kai ya gyad'a mata yana fadin"Yes Fa'iza"
Dukkansu a tare suka sakarmin ido sai naji kafufuwana na rawa lojaci d'aya sun kasa D'aukana sai na bi ra'ayin su na Durkusa kaina na kasa cikin yanayina nake fadin"Sannun..Sannun ku da zuwa an zo lafiya..?
Bakina har rawa yakeyi Ta kalleni ta kara kallona sannan ta kallesa ya gyada mata kai Cikin Zakin muryanta da ta karye da Turanci tace"Hy Am Zainab Nice to mee