Showing 75001 words to 78000 words out of 96493 words

Chapter 26 - Kana Naka Book 1 Hausa Novel Complete

Janafty   

07 Dec 2024

214

baya da wani Dand'ano ballatana na iya cin wani abu,sai Ranar Biyu da rasuwa na samu nasha Fura ya zauna acikina Mutane Dabam dabam sun zo gaisuwa Dangin mazajen su Yaya mariya da mazajen kansu,suna nan da su ake zaman gaisuwa hatta da yan makarantar su Hafsatu sun mata kara na zuwa da kuma kololin abincin su,Hatta da sauran dangin mu ta bangaran uwa suna nan tare damu,ammh ni ba Mijina ba Ahalinsa sai ranar uku sai ga Mama da Anty Binta sun zo da rana suna ta wani jin kai,ko awa d'aya basu yi ba sukace zasu tafi,Muna zaune adakin Tamadina dukkanmu,ni ina gefe kaina a jikin bango ina bin kowa da kallo Carbi ne a hannuna inaja Hijabin Yaya Asiya ne ajikina da shi nake kwana nake tashi wanka kuma tun da nazo ko sau daya ban yi ba.
Mama ta isa kusa dani tana fadin"Ai ya kamata ki koma gida hakanan saboda karatun yara sannan ki bar gida ba kowa kada a haura ayi sata."
Bata bani mamaki da kalamaanta ba, sai na kalleta da Jajayen idanuwana kafin nace"Aka rasa rai ma aka Hakura ballatana abun duniya..?
Na tsareta da idanuwana cikin wani yanayin da na tabbata bata ganina aciki ba.sai ta mike tana fadin"Rai ai da'ya ne, shi kuma asara ai suna da yawa"
Ban ce mata komai ba Anty Binta kuma ko ya Hakuri bata iya ce min ba nima ko ban gaisheta ba,sai dai naji tana Tambayan ina yaran..?
Naji Yaya Asiya na gaya musu Hafsatu ta shiga makota dasu tayi musu wanka,Da zasu tafi Mama bataji kunya ba tace Ishaq na yi mana gaisuwa Dayake basa kasar shi da Zainab.
sun je india a Duba Farhan Saboda Haushi Goggo ce kad'ai tayi fatan su dawo lafiya ni kuwa Idanuwana na Rufe naji wani Tiriri na fitowa daga
k'asan raina,kaina ciwo yake yi har na bala'i ga jiri,nasan bani da lafiya. ammh halin da nake ciki ban ki nima ace na Mutum ba,da dai irin rayuwar da nike ciki wacce bata da wani amfani.


*Littafin KANA NAKA book2,3.paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*
*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*




*Janafty*
*KANA NAKA..!*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*Ina gaida Matar Abba,Maryam jumare.*
*Madalla da ke Hauwa'u(Real smasher)Fa'iza ta ce na gaishe ki*
*Fa'iza na gaida mai sunan k'anwarta Hafsah Hafnan,(Sahibatu) tace sannu da Himma.*
*Fa'iza ta ce na isar da sakon gaisuwarta ga uwar Dakin Gudayo da Yabi,tace madallah da kawar kirki irin ki Surayya Dahiru gwaram.*

*Ishaq na gaida Ahalin Masoyansa gabad'aya,yace na Fada muku. ya ji duk zagin sa da kuke yi groups groups,Har da masu sauya masa suna wai Isiya,Yace kwa yi ku gama shi da Fa'iza mutu ka raba takalmin kaza.*

*JANAFTY NA GAIDA MASOYANTA
MASU AIKO MIN DA SAKO GA FA'IZA DUK NA ISAR DA SAKON KU,TAJI KUMA TACE TA D'AUKA IN SHA ALLAHU ZATA MIKE TA TAIMAKI KANTA*

        *🅿️17*

Ranar da akayi addu'ar bakwai da Daddare,aka taramu saboda washegari zamu watse. kowacce zata koma gidan mijinta,Cikin taron har da Megidan Tamadina da abokan zamanta. sai manyan ya'yan gidan maza,sai mu sai Goggo da Baba Ati kamar kaka take wajen Tamadina ita kad'ai ta rage acikin dangin mahaifinsu da na mahaifiya tunda daman auran zumunci ne tsakanin iyayan nasu..
Bayan bude taro da addu'a da yi ma Mamaciyar addu'a sai d'an nasiha garemu na hakuri da rayuwa,duk yadda tazo ma bawa sai kuma aka gangarowa mgana kan abunda ta bari na magada.mu kenan to da yake bata bar wani abu ba,sai yan kayanta da gado da Sauran tarkace nan take kuma mukace mun yafe a raba ma bakuta,suka shiga saka mana albarka Megidan su ya ce Tamadina tun iya zaman da yayi da ita, bata taba sab'a mai da gangan ba,saboda haka ya yafe mata duniya da Lahira,haka Sauran abokan zamanta suke ta fad'in alherinta suna fadi'n bata yi musu komai ba mace mai kirki da son zaman  lafiya,Daga karshe Yaya mariya ta muskuta tana kallo Goggo Lokaci d'aya tana fadin"Goggo ya mganar bashi.shin ko sun san ana binta a bashi Saboda a biya a sauke mata nauyi..?
Maman isuhu ta kad'a baki tun kafin Goggo tace wani abu tace'"Allah ya jikan Tamadina ba mace bace mai cin bashi ba,ga yara nan duk sai su tsallakemu su kawo mata ajiyan kudadensu,wlh yadda suka bata haka suke karb'an su ko chanzasu batayi.bata taba cin bashi ba,macece mai godiyar Allah da Wadatar zucci"
Gabad'ayan mu dad'in wannan yabon mukaji,har sai da hakan ya nuna a saman fuskar mu,an tashi taron cike godiya da fatan Allah ya jikan Tamadina bayan Goggo ta sanar da Mutan gidan gobe zamu koma gidajenmu suka nuna alhininsu.
Bayan mutan gidan sun fice suka bar mu, mu kadai Ni ina gefe nayi tagumi bana mgana Amir ne kadai bai yi barci ba yana jikin Hafsatu,Yaya mariya ce da Yaya Asiya ke ta zencen su da Goggo da Baba Ati acikin Hiran ne Yaya Asiya tace"Baba Ati wai har yanzu ba'a samu labarin inda Dan'uwan Tamadina yake ba..?
Baba Ati ta sauke Numfashi kafin tace"Ke dai bari Asiya wlh ba'a samu ba.Kwanaki har chan karayen naje da muka kai yar gidan mallam Akilu aure chan. aka tabbatar min sun tashi sun koma cikin garin kano hannun wani Dan'uwan ita Zuwairan"
Yaya mariya tace"kuma babu lambar waya Baba Ati..?
Ta jinjina kai kafin tace"Gaskiya babu..Ai tun lokacin zamanta a korafi batayi dogon Huld'a da kowa ba Zaman nasu ma da mahaifiyar Tamadina kakar ku kenan ba dadi gaskiya har da shi Mallam din saboda bata so auran ba,mahaifinta ya had'a abun akwai wanda take so shiyasa sanda aka kawota batayi huld'a da kowa ba,ko Haihuwar Usman din Rabo ne kawai da ya rantse yasa aka samar dashi.
Sai kuma mallam din yazo ya rasu.to bayan ta fita Takaba,Danginta suka zo tafiya da ita.sai ta nuna zata tafi dashi to rayuwar nan ba wanda ya damu da rikon D'an da ba nasa ba, saboda ganin Nauyi ne in ma ta barsa anan d'in shiyasa ba Gaddama akace zata iya tafiya da shi Har ga Allah na zata zata rika kawosa ko don yar'uwansa da suka Had'a uba sai kuma gashi Tunda ta saka kafa ta bar Karofi yau shekaru sama da Arba'in da Doriya bata Dawo ba.sannan shima Usman din bai nemi Dangim mahaifinsa ba har yau din nan kuwa"
Ba kuma wanda yasan inda suke ahalin yanzu"
Gabad'ayan mu muka sauke Numfashi Yaya Asiya tace"To Allah yasa yana raye"
Yaya mariya tace"In sha Allahu ma yana Raye kuma in dai da rai da rabo watarana zamu had'u da shi"
Muka amsa gabadayan mu da Allah yasa Goggo ta gyara zama tana fadin"Duk inda yake in dai jinin ku ne zai nemeku jini ai ba karya ba ne".
Muka jinjina mata kai alamun gamsuwa ni ko araina sai na samu kaina da addu'an Allah yasa yana raye domin shi kad'ai ne shakikin Tamadina anan duniya mu kuma kawun mu Namiji kwara d'aya tak da yau zamu bugi kirji muce muna da shi acikin raina ina addu'an in dai yana raye Allah ya bayyana sa da gaggawa.
Washegari da shirin tafiya muka tashi. kowa kagani da Kuzarinsa ban da ni,kwata kwata kamar an zaremin lakkan jikina,Goggo sai fad'a take min wai na kwazzabi kaina bana cin abinci Yaya mariya na wajen tace"Kuma zama da yunwa bazai taba Sauya komai ba..Tamadina ta rasu sai dai mu yi fatan Allah yasa tana kyakyawan karshe"
Sai hawaye ya kecemin suka shiga tsere bisa kumatuna, bayan mutuwar da ta dake ni,yayi sanadiyar tasomin da ciwona da daman kamar jira yake na shiga hali makamancin sa,Mun had'a duka kayanmu na yara Hafsatu ta wanke musu ta had'a musu ta musu wanka,ta shiryasu haka ma su Yaya mariya sai kuma sabon kuka ya tashi muka zauna mu hud'u muka ci kukan mu muka koshi,muka share Hawayen mu. Goggo tagaji da bamu baki ta Hakura ta koma gefe ta zuba mana ido bayan ta kira Yaya Isa tace yazo ya Dauketa ita da Hafsatu da mariya da Baba Ati, Yaya Asiya kano zata wuce nima kuma gidana zan koma.
Da azahar sai ga Hajiyar Dala,mun dauka ma bazata zo ba ne ahalin taji Rasuwar. tunda Goggo da kanta ta kira wayar ta,ta fad'a mata,Tazo tayi mana gaisuwa ta bama Yaya Asiya dubu goma Sadaka batayi awa d'aya ba,Ta ce zata tafi, nan take zencen zata karisa katsina Tare da Direba take jin Haka yasa Goggo ta kalleni tana fadin"Fa'iza tunda kun gama shiri,sai ki bi goggon taki tunda katsinar zata shiga"
Da Sauri tace"Aa ba gidan Saudatu zani fa gidan Wani abokin Major ne. mahaifiyarsa ta rasu zan biya nayi musu gaisuwa suma na wuce"
Ina jin haka nima murya a sanyaye nace"Ki bari kawai Goggo zan tafi da kaina"
Sai goggo ta jinjina kai kafin tace"Shikenan"
Daga haka tayi mana Sallama tatafi Goggo ce ta rakata har Dakunan matan gidan tayi musu gaisuwa, kafin Tafiyarta sai da ta dawo sannan Yaya Asiya ta bata kudin da Hajiyar Dala ta bata Goggo ta karb'a tana fadin"Kudin ku ne ai Asiya ba ni aka bawa ba"
Yaya Asiya tace"Goggo mu bama bukata ayi sadaka Allah ya kai Haske kabarin mahaifiyarmu"
Goggo ta amsa da Ameen itama fita tayi da kudin Dakin Maman isuhu ta shiga ta bata kudin Dakyar ta karba, Goggo tace kun yi wahala damu wajen kwana takwas ku karba ku kara Allah ya Rufa asiri .sannan ta karb'a tana sharan kwallah da kara fadin Allah ya jikan Tamadina.
Yaya Isa ya kira yace gashi nan zuwa,Shinkafa suka dafa mutam gidan suka zubo mana yaran aka zuba mawa suna ci ni dai bakina yayi nauyin  bana jin Dad'in komai kaina wani Dum dum kawai yake yi duniyar ma ba daidai nake jinta ba.
Kwatsam sai gasu Sa'adatu da Habiba sun zo min gaisuwa nayi mamakin zuwan su sai da aka gama gaisawa sannan na kalle su ina fadin"A ina kukaji rasuwar sannan waya kwatanta muku gidan nan..?
Sa'adatu tace"Ai tun da naga an kwana biyu baki dawo ba nace ba Lafiya Megidan ma nata jimamin abun.  yace haka kurum bazaki je ki zauna ba ko don makaranta yara da muka ga an yi kwana biyu sai yace bari yaje gidan kakaninsu su Amir yaji ko Lafiya. to chan yaji abunda ya faru wajen kanwar Baban su Amir ce domin ina ganinta tana zuwa itace ta fad'amai mahaifiyarki ta rasu sai ya Nemi ta kwantatamai gidan nan sai ta mai kwantance mun d'an sha wuya kafin mu gane,sai dai kinsan gidan mutuwa baya boyuwa balle da naga ba'a gane ba sai na rika kwantance da cewa Bebiya bata mgana sai ko gashi an kawo mu"
Na jinjina kaina,kwallah na Taruwa acikin idona makota na ne da ban had'a komai da su ba,Ammh sun nemi inda nake sun zo min gaisuwa Su mama kuwa tun ranar uku basu dawo ba,bana saka ma Yaya Ishaq a lissafi bai Dauke ni da Daraja ba,ballataana ya Dauki dangina da iyayena abun Daraja Har afili na nuna musu jin Dadi'na na nuna su ga sauran yan'uwana da Goggo suka dinga saka albarka har da gurasa Habiba tazo da shi ita kuma Sa'adatu sai ta Dafo Dambun Shinkafa da yaji Zogale Goggo ta karba ta kai ma Mutun gidan suna fad'in Allah ya bada Lada
A nan suka yi sallar La'asar sannan suka yi shirin tafiya sai nace su jirani mu wuce tare Lokacin Yaya Isa ya iso ya tafi masallaci ne,na mike na shiga uwar Dakin Tamadina na Dauko jakar kayan mu da Hijabina.da Yaya Asiya ta wankemim Goggo ta matsamin nayi wanka da Safe na fito falo na ce Hafsatu tazo ta sakamin Ahmad a bayana na goyasa ta sakamin shi har na saka zani na goyasa irin na D'ago kaina sai Duhu ya mamaye ganina na fara Laluban bangon gabana na rasa sai nayi luu ta baya zan fad'i sai  naji an tareni ana salati kuma hannuwana ne da yawa suka rikeni,Sama sama nake jinsu jiri ya rikeni da kaina da ya dauki wani irin azaban ciwo,Kamani sukayi na zauna Yaya mariya ta kwanto goyon Bayana Goggo fad'i take"Daman ni nasan yarinyar nan bata da lafiya, shigen zurfin cikinta yasa taki mgana"
Asiya kira min Isa yayi maza yazo in asibiti zai kaita ya kaita kada ta yi ma kanta Lahani bamu sani ba"
Ina nan zaune Dafe da kaina ina jin Sannu sannu na tashi Daga bangarori Dadama, chan jimawa na zame na kwanta naji shigowar Yaya Isa da Bayanin da Goggo take yi masa,sai yace a kamo ni muje asibiti a dubani.
Yaya mariya ta kamani muka fita mutan gidan na tambayan lafiya tace jiri ne ya kwasheni Maman isuhu tace"Daman daga ganinta bata cika lafiya ba itama"
Ni dai ina jinsu har muka fice muka shiga mota wani asibitin kud'i acikin gari ya kaimu shi ya shiga ya fita muka ga likita akan Lokaci gwajin Farko sai ga jini na ya yi sama Dari Biyu da Doriya sai ucler likitan nata fada ina so na kashe kaina da na fadi zan iya kamuwa da Ciwon barin jiki, ko jini ya haye yayi sama na mutu mgunguna ya bani bayan yayi min alluran jijiya ta ucler sannan yace na rika cin abinci sosai saboda kiyaye lafiyata.
Muna hanyar Dawowa Yaya Isa sai fad'a yake yi,Yaya mariya bata mgana sai dai kawai ta sauke numfashi tace"Uhm" abun yafi karfin ta wannan karon ko da muka koma makotana sun tafi sun so su jira dawowarmu Goggo tace su tafi Saboda Dare sannan sun bar iyalansu agida to sanadin haka komawa Katsina bata yuyu ba da Goggo ta kawo mganar Yaya isa ya maidani sai yace"Haba Goggo kalli Halin da take ciki fa..?,jininta yafi dari biyu a yadda take nan ko kanta bazata iya mora ba ballatana ga yara tare da ita,kawai mu wuce da ita gida in taji sauki sai ta koma"
Sai Goggo ta kasa musamai saboda taga Halin da nake ciki,Ni a motar Yaya isa muka tafi ni da Goggo da Baba Ati da yara su Yaya mariya da yaya Asiya da itama tafiya kano tasha ruwa suka hau ta haya mun yi sallama da mutanen gida muka rabu suna Hawaye muma muna yi.
Sai dare muka isa karofi ni dai abinci suka matsamin naci, nasha mgani na kwanta barci. Salolli na ma sai da asuba na rama su na ji saukin Jirin sai dai ciwon kan ne,Washegari Yaya Asiya ta koma kano Yaya mariya daman muna isowa ta wuce gidanta
Wasa wasa jikina ya ki dad'i har sai da na kara Sati a karofi Goggo na kula da ni,tare da su Amir kamar kada na koma inda na fito sai dai ba Dama ranar da nake da kwana bakwai a karofi Goggo ta saka Yaya isa ya maidani da Yammah bayan taga naji sauki,Tare da sha tara na arziki komai ta had'amin su garin kunu,garin Danwake,Wake,Tsaki,rama bushasshiya da Zogale sai Taliya yar Hausa da yara suke so sai ta saka aka Murzamin ta samin a kwali saboda kada ta karye hatta kayan maggi sai ta siyamin,da kayan miya mai yawa sannan ta saka Yaya isa ya kaini har gida ni da yara ina ta masa godiya shima da ya saukeni ya bani dubi biyar yace na rike sannan ya Jadaddamin naa kula da lafiyata na amsa mai da in sha Allahu.
Gyaran gidan na fara ko'ina duk yayi kura,Amir na tayani da kwashe kaya su Anum kuma sai dai su kara batawa,Adaran Taliya yar murji na Dafa mana na manja mai ruwa ruwa muka ci tare a faranti daya muma Santi muna gamawa bayan mun yi sallah na saka suka kwaso littafan makarantansu nace su duba tunda gobe zasu koma makaranta.
Wasahegari Laraba da wuri na shiryasu na kuma fita da su da kaina,Haruna da Sa'adatu da na leka gidan suka karamin gaisuwa da tambayan ya karfin jikina..?nace naji sauki sai hamdalar ubangiji.
Makota na dake kusa dani wad'anda ban taba ma shiga gidajen su ba sun shigo sun min gaisuwa daga suce Sa'adatu ta fad'a musu ko Habiba naji Dadi Sosai domin ba karamin masoyin ka ba ne zakayi rashin uwa yazo yace maka Allah ya kara hakuri kuma bazaka manta da wannan mutumin ba, wanda kuma bai ce maka Allah ya kara Hakuri ba,shima girman abunda ya aikata yana nan acikin ranka bazaka taba mantawa dashi ba.
Na dawo da kwana Biyu Anty Mamah tazo min gaisuwa tace ta zo sau biyu bana nan,nace mata eh nayi rashin lafiya ne tayi min gaisuwa ta kuma bani Hakurin sun yi tafiya ne chan dangin megidanta Kumo dake jahar Gombe ta jima muna ta Hira sai la'asar tatafi bayan nayi mana Danwake da manja da yaji taci ta koshi,sannan mukayi sallama washegari kuma daga makaranta Sai ga Badariya tazo min gaisuwa itama da ban hakura Mama bata nan bikin D'iyar Hajiya Barira k'awarta tatafi wajen satin ta daya Abuja aka kai Amarya, dagachan ta biya gidan su Zainab ta kwana biyu.
Sai kawai na samu kaina da cema Badariya"Sun dawo ne..?ya mai jiki..?
Badariya tace"Basu dawo ba suna chan jikin Farhan da sauki sun dai Tsaya Hutawar su kawai"
A fili nace"Allah ya dawo da su lafiya"
Daganan ban kara tofawa ba,Bata jima ba ta tafi tace saboda Mama yanzu in taga ta Dad'e sai ta fara fada, nace gaskiya kam ya kamata ta tafin kada dare yayi mata.
Mutuwar Tamadina ta Dakeni matuka,sai dai na zauna nayi Tagumi ina sharan kwallah in Amir yaga nayi Tagumi sai ya cire tagumin yana fadin"Umma ki daina tagumi ummanki zata dawo"
Sai ya bani dariya na jawosa jikina ina fadin"Aa bazata dawo ba Amir..Ai kasan mutuwa ko.?kuma a makaranta an fad'a muku duk wanda ya mutu ai baya Dawowa a rami za'a ha'ka a binnesa shikenan bazamu kara ganinsa ba"
Cikin yanayin mganar sa yace"Ita Umman ki a rami aka sakata..?
Sai na gyad'a mai kai Lokaci d'aya ina fadin"Eh mana..kowa zai mutu muma watarana zamu mutu a hak'a rami a binne mu baza'a sake ganinmu.Mu yi ma wadan'da suka rigamu mutuwa addu'a muma in mun mutu sai mu samu masu yi mana addu'a"
Ya gyad'a min kai kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login