Showing 78001 words to 81000 words out of 96493 words

Chapter 27 - Kana Naka Book 1 Hausa Novel Complete

Janafty   

07 Dec 2024

217

yace"To Umma zan rika yi ma umman ki addu'a"
Daman kuma ina yawan fad'a musu in sukayi sallan su rika cewa Allah ya gafartama iyayanmu da magabatanmu da yan'uwanmu,kuma suna yi,Har su Anum haka na koya musu nima in dai na yi sallah sai na Roki Allah ya jikan dukkan yan'uwa musulmai da suka rigamu gidan gaskiya mu kuma Allah yasa in tamu tazo mu samu cikawa dakyau da imani.
An yi addu'ar Arba'in Tamadina,Ni ban je ba Hakama Yaya Asiya su Goggo ne da Yaya mariya suka koma sai dai daga gida nayi mata addu'a da Sadakan Allah yakai haske kabarinta na Rokar mata salama da amimci a wajen Ubangiji a kabarinta,Ni tunda Tamadina ta rasu komai ya fita kaina naji bakowani wani abu ne zai rika batamin rai ba,Na riga nasan na rasa dukkan wani bangare na jin Dadi, Dariyata kadai ya'yana ke gan. sune kad'ai yasa har yau nake tsaye kan kafafuwana,Saboda hakane yasa na Dage da shan mgunguna saboda in nazo na kasa ko nayi Rauni ya'yana baza su iya d'aukan maraici tun suna da kananun shekaru ba. shiyasa karfina da Kuzarina duk Ta dalilinsu ne shiyasa ita uwa ya'yanta kan zama gwarin gwiwanta sau da dama.
Kwata kwata nama manta da mganar Form din da na cike na koyan sana'o'i da bada tallafi,na mikama Allah duka al'amarina,sai kwatsam Badariya tazomin da labarin an Turo mata sako Daga Kungiyar Women charity Foundation kan zasu tantancemu ranar asabar karfe goma na Safe a wata makarantar yan mata Dake cikin gari sai na rud'e na fara rawan jiki ina fadin"Bada..riya..To ni ya zan yi..?bansan ko'ina ba fa..?
Sai tayi Dariya tace"Sha kurum ki zan yi ma Mama karyan makaranta sai nazo na rakaki"
Sai da ta fad'i haka sai hankalina ya kwanta, tun daga ranar ko dayaushe addu'ata d'ayane in da alheri acikin wannan mafitan. Allah ya tabbatar min in ba alheri Allah ya musanya min da mafi alheri.
Sai naji zuciyata ta natsu da al'amarin,Ranar jumma'a Dakyar na iya barci Saboda Zullumin abunda zai faru gobe,Da sassaafe na shirya yara suka wuce Tahfeez nima ban zauna ba na shirya tara da wani abu Badariya tazo na goya Ahmad na saka Dogon hijiba na mai ruwan kasa duk yasha ruwa na rufe gida muka tafi,Ita ta biya kudin adaidaita gaskiya akwai tafiya ba kad'an ba tsakanin gidana da Makarantar mun isa goma saura Haraban makarantar cike da manyan motoci daga gani abun na manyan mata ne.
A wani babban hall na makaranta ake taruwa kai tsaye muka nufi chan mun shiga mun tarar da mata da yawa duk sunzo,muka samu waje muka zauna ina ta raba ido sai da goman tayi sannan Manya mata masu nasaba da ilimi da zati suka rika shigowa suka tsaya a gabanmu, ina ji Badariya namin Rad'a mai bakin mayafi mai jikan nan Hajiyar su Raliya ce na jinjina kaina daga gani kudi da isa sun zauna ajikinsu
A she mu Talatin suka Dauka,Bayan sun kira sunayen kowa da kowa muka mike gabad'ayamu akwai yan rakiya ire iren Badariya,Wata Hajiya ce mai glass take kiran sunaayenmu,na kasa Raunanun kunnuwa a ina jin sunana na mike bayan Badariya ta rike hannuna muka mike tare sannan ta koma ta zauna, ashe Wani kati zasu raba na na shedar Training d'in da zamu yi sannan da wasu bayanan da suka danganci abunda za'a koyar damu.
D'aya bayan d'aya aka rika kiranmu ana bamu wani karamin kati mai dan Fad'i.sannan akwai hoton kowacce ajikin katin har akazo kaina,na mike na kwanto ma Badariya Ahmad dake bayana na fita ina raba ido har gaban Babban ajin na mika hannu na karb'a ta kara kallona sama da kasa har na juya sai ta kirani da fadin sunana"Fa'iza Sidi karofi'
Sai na juyo da Sauri saboda ina gabda ita naji ta fad'i sunana yasa Hajiyar su Raliya ta D'ago tana kallona sai na rankwafa na gaisheta da girmamawa sai ta amsa itama cikin sakewa Lokaci daya tana fadin"Kece matar Brother din Badar..?
Sai na gyad'a mata kai cikin yanayi mganata nace"Eh hajiya tare..tare ma muke da ita"
Sai na juya ina nuna mata Badariya ashe har tataso dauke da Ahmad tazo wajen mu,Ta duka ta gaida Hajiyar Raliya ta amsa tana tambayanta Mama tace tana lafiya sai ta kara kallona tana fadin"Ashe tare kuka zo..?
Badariya tace"Na rakota ne Hajiya"
Kai ta jinjina tana kara kallona nasan har da mamakin ganin yanayina sai matar nan mai glass ta duko tana mata mgana naga tana nuna mata Takardan hannunta sai ta amsa tana Dubawa kafin tace"Fa'iza abu hud'u zaki koya..?kuma a ka'ida biyu ne kina ganin zaki iya..?
Da Sauri nace"Eh zan iya Hajiya.."
Sai dayan Matar tace"Hajiya kinsan dokace Biyu ne ai hudu yayi mata yawa da wanne zataji..?
Sai naga ta duka daidai kunnenta tana yi mata mgana sannan ta jinjina kai,Itama kuma Hajiyar Raliya sai tace muje mu zauna.
Komawa mukayi muka zauna ina ta Raba ido,naga mata kala kala ire irena masu fama da rayuwa da zamantakewar aure,ni dai akasan raina ina jin yakinin zan koyi duka abunda za'a koyamin Saboda shi kad'ai nake ganin gatana a wannan duniyan.
Bayan an gama bawa kowacce Katin ta, sannan suka fara mana bayanin yadda abubuwa zasu kasance zamu fara koyan abubuwan da zasu koyamana nan da sati d'aya zasu raba abun gida Biyu Mrning da Aftternoom,Da Safe za'a koyar da abubuwa Biyar da yammah ma biyar daman goma ne,Da Safe za'a koyar da girke girke da Had'a lemuka,Da yammah akwai koyan yadda ake hada halawa da dilka,Da yadda ake yinta,Da had'a Turaren wuta na Icce da Humra da su Kwallaca,sai na fara nazarin ya abubuwa na zasu kasance..?kenan sai dai na rika zuwa safe da yammah kenan..?
Sannan sun yi mana bayanin awa Bibbiyu ne da Safe tara zuwa sha Daya da Yammah D'aya na rana zuwa uku na yammah,sannan sun bamu shawaran mu natsu zamu iya duka abunda za'a koyar damu tunda na wata uku ne tsawon sati goma sha Biyu ina jin duk abunda suke fad'i Saboda da karfi suke mgana kamar su san da masu Laluran rashin karfi ji irina.
Sun tabbatar mana da cewa acikin mu za'a dibi mutane goma masu hazaka da aka ga sun chanchanta ranar da zamu gama za'a basu Jarin su a Hannunsu,sannan sun horemu da mu maida hankali komai daki Daki zasu koyamana duk abunda bamu gane ba mu yi tambaya. kada mu zama masu duhun kai,Sannan daga karshe sun ce zamu rika zuwa da Littafi da biro mu rika rubuta sunayen abubuwan da za'a koyamana saboda in mun koma gida mu yi bita,Sannan zamu rika rubuta sunanmu kullum inda muka zo da Turanci wato Attendence.
Sannan ko da wani lokaci zamu rik'a zuwa da wannan katin shine shaidar an tantance mu sai mun nunasa za'a barmu mu shiga, zuciyata na cika da Farinciki har na fara tunanin ma na iya duka abunda nasaka raina zan koya,ajikin katina  an saka Abunda nake son koya kamar yadda Badariya ta Rubuta, shi zai nuna inda ya kamata na tsaya sai Sha biyu  na rana aka tashi sun tabbatar mana da cewa kwararun ma'aikata ne zasu jagoranci wannan tafiya tamu mun yi godiya sosai sukace mu yi ma shugabar wannan kungiyar addu'a da fatan nasara Rayuwa, ni ko araina nace duk Sallah sai na sakata nace Allah ya yi mata gatan Duniya da lahira kamar yadda itama tayi mana gata a duniya.
Daga nan muka rabu da Badariya ta taremin adaidaita na Dawo gida zuciya ta cike da Farinciki,Sai dai na Fara Tunanin inda Zan rika kai Ahmad Saboda sun ce ban da yara saboda ba wajen da yara zasu zo ba ne,akwai abubuwan da bai kamata yara su shakesa ba yayin had'asa.
Sa'adatu ta fadomin rai nako shiga na gayamata ta tayani murna ta kuma tabbatar min na rika barin mata Ahmad zata kular min da shi sai naji Sauki na Dauki damaran maida Hankalina kan damar da Allah ya aramin,Naji dadi tun Sha daya zan dawo gida nayi ma yara girki ko na kimtsa gida da la'asar kuma in na Dawo sai naji da girkin su kafin su dawo makaranta.
Har wankin yaran sai da na kwashe na wanke na goge tare da nawa tunda zan fara fita ba lalle na rika samun Lokaci ba,Ranar Alhamis saura kwana biyu a fara koyar damu Yaya Ishaq ya dawo da Safe na sallami yara sun tafi makaranta kenan ina zaune afalo ina bama Ahmad kuninsa ya shigo ban ko ji sallamansa ba ina chan ina Lissafin duniya.
Sai da ya kariso cikin falon ya kara yin sallama sannan na jisa,na d'ago na kallesa,kamar ba shi ba ya kara Kiba har da karin Saje da gemu ga Tumbi alamun yana samun hutu da jin Dadi.
Kamar bakina na ciwo nayi mai sannu da zuwa bayan na kauda kaina.
Ahmad kuma sai ya fara dagamai hannu yana gaurancinsa.
Bakinsa na gogemai da Kyallen dake gefena shi kuma sai ya Duka ya Dagasa sama bayan ya sauke jakar Hannunsa, mikewa nayi ina kakkabe jikina zan wuce dakina araina ina fadin ka dawo adaidai kuwa.
Sai dai ban karisa ba ya D'aga murya kirani na juyo cikin mganarsa yace"Kin yi min sannu da zuwa baki dauki kayana kin kai min ciki ba.kuma zaki wuce ni kamar kin ga wani banza Fa'iza..?
Sai ban damu da kalamansa ba na koma na Dauki Jakar ya mike ina gaba yana baya ya bude shashen nasa. muka shiga a tsakiyar falon na Dire masa jakarsa na juya naji ajikina ya Juyo yana kallona ammh ban tsaya ba,Sai dai kuma har na fice bai yi mgana ba,dakina na koma na shiga kakkabewa ina gyarawa da na gama na koma Dakin yaran ina tattara kayansu da suka zubar ni kad'ai a araina ina auna abunda zan fad'a ma Yaya Ishaq akan fitar da zan rikayi araina naji wannan karon bazan iya Laushin da na saba yi mai ba.
Ina da Dakin yara naji yana ta kiran sunana da karfi na fito na iskesa zaune afalo Ahmad na jikinsa yayi barci a bakin kofa na tsaya ina jiran cewarsa sai ya kalleni cikin mamaki yana fadin"Kika tsaya min a nan kuma..?
Sai na kariso tsakiyar falon na Tsaya sai da yaga dama sannan yace"Ba wani abu ne agidan..?
Sai kai tsaye nace"Kamar na me..?
Da mamaki ya D'ago yana kallona cikin Hargaginsa yace"Ban sani ba..Wannan wani irin tambaya ne? tunda kikaji nace wani abu ina mgana kan abin ci ne"
Ni kaina bansan meyasa yanzu shakkanan da tsoron Yaya Ishaq suka Fita daga raina ba ,cikin Yanayina nace"Oh gaskiya bakomai sai ruwa Danwake nayi ma yara suka tafi makaranta dashi"
Wani kallon mamaki yake bi na da shi, mamakina ya hanasa mgana ni ko na shiga kitchen na Zubo masa Ruwan Famfom da ya bar mu muna sha,Na kawo mai a karamin jug da kofin Roba duk yaji jiki shi gareni saboda aciki zan basa araina kuma nace bazan Dafa maka komai ba domin bansan da zuwan ka ba.
Gabansa na duka na Sauke ruwan na kuma tsiyayamai na mikamasa sai yaki karba ya bini da kallo kafin yace"wannan ruwan fa..?
Ba na gora ba pure water ne..?
Kai tsaye nace"Babu muma wannan muke sha tun ba yau ba"
Sai jikinsa yayi sanyi cikin wani yanayi yace"Acikin Cefane babu ruwa ne yanzu..?
Nace "Babu.." daganan na sauke Kofin hannuna ganin yaki karb'a ina shirin tashi naji yace"Ashe Kuma Babarku ta rasu..?muna chan Mama ke fadamim..?
Kallon da nayi masa zan iya rantsuwa da Allah ban taba masa makwancinsa ba,da muka kusa shekara goma da Aure,Idanuwana na tsaida a kansa bako kyaftawa cikin wani irin amo nace"au ashe ne ma..?baka tabbatar ba kenan..?
Sai yayi saurin cewa"Kinga ba na son korafi Allah ya jikanta da rahma"
Da karfi na amsa da ameen Ameen Saboda addu'a yayi a gaban idonsa na Dauke Ahmad na shige da shi na Shimfidar na koma na zauna a gefensa ina auna waye yaya ishaq a wajena a tsawon wad'anan shekarun da muka dauka tare..?abu daya ya taba bani da zan kallah naji dad'i shine ya maidani Uwa ya bani ya'ya bayan wannan sai Tarin Tozarci cin mutumci kaskanci da Sauke Daraja da na Fuskanta a zama na dashi.
Ishaq shine sanadiyar da aure ya gama fita daga raina kwata kwata.



*Littafin KANA NAKA book2,3.paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*
*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*



*Janafty*
*KANA NAKA..!*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*

*Gaisuwar Fatan alheri ga iyayen Janafty*

*Anty Habiba Abubakar Imam ikra*
*Anty Summayyah Abdulkadir(Takori)*
*Hajiya Hadiza Mahe muhammad(Mama)*
*Hajiya Halima Dalha Shehu(Umma)*
*Hajiya Hauwa Maman unwas(Mommah)*
*Na gaishe ku,Madallah da iyaye kamar ku,Allah yasa a gama da duniya lafiya Ameen*



         *🅿️18*

Na dauki tsawon lokaci aciki kafin na fito,domin nima sama sama barcin ne ya fara fizgata.ko da na fito falo baya nan, da na leka haraban gidan ba motarsa. sai hakan ya bani tabbacin fitarsa kenan ya tafi gidan Mama. domin ba inda yake zuwa da wuce wajenta,ko Anty Binta sun fi mgana ta waya ko su hadu gidan Maman.
Ban damu ba na cigaba da Harkokina, na riga na saka ma kaina yak'inin Tunda har ya zab'i iyalan zainab sama da nawa iyalan nima zan zab'i ra'ayina da ya'yana sama da shi mu ma Ture mganar aure a tsakanin mu sai dai a duba zumuncin da Allah ya riga ya had'a ,kuma shi sada zumunci Umarnin Ubangijine kuma shi Umarnin Ubangiji sab'a masa babban Laifi ne.
Haka kurum naji ina sha'awar shan Faten Rama ina da sauran tsaki tun wanda na dawo dashi daga Karofi shi na Tankad'e na wanke na d'ora sannan na Jika bushasshiyar Rama nayi amfani Dashi bani da nama ko kifi sai nayi amfani da wake na watsa musu aciki,sai Faten yayi dad'i yana tashin kamshin kayan miya da Daddawa da su Citta,na juye a kula ni saboda bazan iya jiran yaran ba, sai da na Dib'i nawa muka sha ni da Ahmad sannan na sake yi mai wanka nima nayi muka sauya kaya shidda Saura yaran suka Dawo daga makaranta suka cire Kayan makaranta, suka sauya na gida sannan na zubo musu faten a faranti suka na suna santi,bayan sun gama Anum ta fara min labarin makaranta Musty kuma sai wasan zagayen falon yake yi Amir kuma kan kujera ya hau yana Duba Littafansa.
Anum wasa da kaina take yi,kalaba ne daman har ya kusa warware kansa ma, domin ni nayi ma kaina.Ahmad kuma na daka Tsalle saman jikina Amir yace"Umma ki dubamin aikin nan ban gane ba..?
Ya fad'a yana mikomin littafin rubutun sa  na karb'a nayi gefe da kaina Ahmad nata mika hannu da Sauri Amir yace"Umma karki basa zai ya ga min"
Cikin yanayi na nace"Bazan basa ba.Arabiya ne zan koya maka kabari ayi sallah mu natsa tukunna"
Ya amsa min da Toh ya karb'i Littafinsa Kiran sallar mangariba ya tadamu mukaje mukayi alwala mukayi jam'i gabad'ayanmu afalo bayan mun idar na d'aga hannuwana Ina addu'a Sai suma suka d'aga sai da na shafa sannan suka shafa na kalle su ina Fadin"me kuka rokar mana acikin addu'an..?
Amir ne yace"Umma a makaranta an ce mu rika ma iyayan mu addu'a"
Kai na jinjina masa ina fadin"Yauwa to ina so in dai kuka yi sallah ku rika rokar ma Umma Sa'a da nasara a abunda zata yi kun ji ko..?
Da Sauri Anum tace"Umma me zaki yi..?
Kanta na shafa ina fadin"Ba'a fada ma yara sai abun ya tabbata ke dai ki rika yi ma Umma addu'a ai zaki yi ko..?
Da Sauri ta d'agamin kai sai na Shafa kumatun ta ina saka musu albarkar acikin raina Musty da Anum har sun fara wasa na dakatar da su nace su karanta azkar din su,shiyasa suka natsu,Kiran sallar isha'i ya tadamu muka yi sallar tare sannan muka zauna mukayi addu'o'i Anum da karfi ta rika fadin"Allah ka bama Umma sa'a Allah ya bata gida da mota"
Sai ta bani Dariya Amir ya kwab'e ta da Fadi'n"Aljannah ake cewa"
Da sauri tace"Eh Allah ka ba ma Umma Aljannah "
Ba zato kawai Musty yace"Allah ka sa Umma ya hau jigi"
Gabad'ayanmu muka kwashe mai da Dariya idona ya ciko da kwallah na kama Musty na rumgume ina fadin"Ameen Ameen Allah yasa amsa bakin ku ya'yan albarka kuma Allah ya baku duk abunda kuke so duniya da lahira"
Anum ce ke gyara ma Musty sunan Jirgin da bai iya fada ba sai nanata mai take yi yana fadin Jigi sai suka sanyani Nishadi ina ta Dariya Tuni na manta da duk wani bakincikin dake Damuna. zuciyata ta dawo fara tas kamar farar takardan da ba'a taba yi mata wani Dameji ba.
Falo na tattara su muka koma na hana wasan nace mza a dauko Littafan makaranta a duba sukaje suka Dauko na shiga Tsakiyar su,su kuma sun Zagaye Ahmad ne ya fara kiriniya zai yaga musu littafai sai na Daukesa na goya a baya na ammh duk da haka sai uban zillo yake yi shi sai ya sauka naki ko sauke sa.
Na Amir guda biyu ne Arabiya da na English na Arabiyan na koya masa,Sai na Anum littafin koyon bakake ne da aka saka su,siya itama na nuna mata yadda zata yi na Musty kuma na turanci ne sai Littafin da na saka ya Rubuta Huruful Hija'iya na Damki hannunsa ina koya mai rubutawa da Fadin su a baki, muna rubutawa muna fad'in su d'aya bayan da'ya sauran na turancin da ban iya ba nace Amir ya taimaka musu tunda shi yana primary 3 ne zai je hud'u Anum na 2, Musty kuma 1,Ahmad ne ya rage shima in da ina da kud'i saka shi zan yi, bakinsa ya bude achan kamar yadda Babansu yayi ma Anum da Musty.
Sai da suka gama duka aikin makarantan nasaka suka kwashe Littafan suka maida jaka suka maida su dakin su,sannan na zubo mana Faten nan a katon faranti muka Had'u muna ta sha Ahmad na kan jikina ina basa a baki Musty ma yasa ka rigima sai na rika basa Anum na ganin haka ta kwabe fuska zatayi kuka tace"Ni fa Umma"
Sai itama na riga bata a baki Amir ne kad'ai ke shan abunsa da kansa muna cikin haka sai ga Yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login