Showing 45001 words to 48000 words out of 96493 words

Chapter 16 - Kana Naka Book 1 Hausa Novel Complete

Janafty   

07 Dec 2024

204

in basu ji dasu ba da waye zasu ji..?Dole ne su ji da su tunda basu da kamar su,In tace hakan bai kamata ba sai yace duk wanda kika ga bai sakar ma ya'yan sa Gata ba bai da shi ne sannan bai san Darajan ya'yan ba ne.
Daga karshe sai ta koma bangaran yaran sai ta Fahimci suma sun fi jin mganar Uban su fiye da ita tun suna yara sun Fahimci mahaifiyarsu kamar Hoto take sai Uban yayi shawara da su,ammh ita bai neme ta ba ko wani abu yace in suka ce Daddy mommy fa..?Sai yace su kyaleta kawai mommy bata san komai a wannan zamanin ba to har suka girma da wannan Tunanin aransu Daddyn su shine nasu uwar su kuma ta nan a matsayin Mahaifiyar su ammh bata da wani Say a gidan da Rayuwar su gabadaya.
Sun taso da Yare guda biyu a bakin su Turanci da Fullanci saboda Daga Uban har uwar basu yarda Yaren su ba In dai suna gida daga Fillaci sai Turanci suke yi Hausa kuma sai dai a waje ko a makaranta,Sannan in sukaje ziyara chan Rugga basa wani yare sai Fillanci sai yaren ya zauna Sosai a bakinsu..
Zainab da Zuzu kyakyawan yan mata ne na gani na fada kamar su, sukayi kan su Saboda kyau da zati to bangaran Uwa da uba duk kyawawa shiyasa suke jajir kamar a taba jini ya fito sannan sun tashi cikin gata da jin Dadi,Zainab ta gama junior secondary dinta suka koma Abuja da zama anan ta ida karatunta ta fada Universty of Abuja ta karanta Chemisty,Gatan duniya ba wanda basu samu ba komai suke nema kafin su yi mgana sun same shi Tun suna kanana komai yan aiki ke yi musu shiyasa su Rayuwar Hutu suka sani da jin Dadin.
Dr.Lawal bako Rauninsa Daya ne ya'yansa yana tsananin kaunar su,Zai iya batawa da duk wanda ya nemi ya tabasu sannan zai iya karta ma kowa rashin mutumci a kan wadanan ya"yan nasa,Yana nuna musu kauna a fili har tana wuce misali Hajiya Halima da suke kira Mommy ko tayi mai mgana sai yace me ta sani kan wannan zamanin tayi mai shuru kawai shiyasa ita nata ido ne sai dai tana addu'an Allah yasa kada su zame mai Raunin da zai zame masa Lalura watarana.
Ishaq kabir karofi ba Zainab ya fara sani ba,Dr.Lawal bako ya fara sani Lokacin da aka mai karin girma da sauyin wajen aiki ya koma Abuja shine ke rike da babban Ofishin su na Abuja,Haka kurum Ishaq yaji Dr.Lawal na Burgesa saboda he is Educated and Innocent,sannan jajirtattace ne kan aikinsa,Shi kuma Ishaq yana da Ladabi da Biyayya ga manyan sa shiyasa suka Saba da Dr.Lawal,Kuma karin ma abun yana ganinsa Farin namiji gaye kyakyawa mai ilimi da sanin ya kamata Dr.Lawal na son harka da mutane masu kyau da wad'anda suka san abunda suke yi,Dalilin Sabawar su yasa Ishaq bai iya kiran sunansa Sai dai yace Daddy kafin shekaru su ja su san komai na juna har gida Daddy kan gayyace sa gidaansa yaje yaci abinci anan yaga Zainab ya nuna yana sonta lokacin tana shekarar karshe a jami'a tana masters d'inta lokacin daya ganta yaji aransa mafarkin daya Dade yana yi ne Allah zai tabbatar masa bai nemi zainab  kai  Tsaye ba sai da ya fara Tuntubar Daddy shi kuma yace ya bashi lokaci ya kara Bincika Ishaq din kuma ya Samu komai yadda ya sanar da shi Cikin Lokaci ya amince batare da Shawara da Hajiya Halima ba Ya'yansa kawai yayi shawara da su,Daman kuma achan Rugga an saka ido kan rashin auran su zainab din,Shi daman baya so ya aurar da su in da zasu sha wahala ne ya fi son ya aurar da su inda yake da Mgana a wajen zai iya kula da ya'yansa ya kuma Tofa komai a lokacin da yaso a kan Rayuwar ya'yansa.
Zainab bata isa tace taki Ishaq ba ganin Farko da tayi mai taji ya shiga ranta suka fara soyayya sai dai da Farko taso ta Damu da taji yana da mata sai ya nuna mata kada ta Damu Fa'iza ba komai bace a rayuwarsa face Uwar ya'yansa ita ce First love dinsa da ta fadama Dr.Lawal Dariya yayi yaji Dadin da yarsa zata kasance Zara Cikin wata Hajiya Halima nata sai dai ido kawai har gwara ma Zuzu bata kai zainab rawan kai da Daukan duka Hallayar mahaifinsa nasu ba ita ta kan tsawarta mata taji,Ita ma tana nan tana karatu a Nile University of Abuja,zainab kuma tana gama karatu tayi Services a wani kamfani karafuna bayan ta gama kuma suka Riketa aiki a wajen,Batare da Ishaq din ya sani ba kuma Lokacin har an yi mgana ta iyaye lokaci kawai za'a sanya har zuwa Lokacin da akayi auran Ishaq bai fahimci bai da wani iko akan Zainab ba sai abunda Mahaifinta yace da shi ta ke amfani.
Shi ya gina auransa kan Soyayya da kyau nasaba kudi da nagartan ilimin zamani,ita kuma ta auresa ne Saboda kyansa da kudinsa sannan saboda Mahaifinta,shi kuma Dr.Lawal bako ya amince da auran ne saboda yana Tunanin Daga Ishaq har Zainab suna karkarshinsa ne zai iya yanke kowani irin Hukunci kan yarsa batare da ya D'aga ido yayi mgana ba.

Muje zuwa..!

****

*Katsina..*
Bayan wata daya.

Mutanen Umra sun dawo an kawo Tsarabobi kala kala nima Badariya ta kawo ma su Amir nasu,abakin ta nake jin Tsaraban ma aiko da shi sukayi ta Abuja suka sauka,Ya Ishaq din kuma bai zo ba,an kawo ma yaran Jallabiya Amir da Musty,Anum kuma Riga da wando,Ahmad kuma kaya riga da wando masu kyau da yarari,Sai Dabino da ruwan zamzam na amsa nayi godiya Daman ni ban saka aka ba ballata don ba'a bani ba na Damu Badariya ta fadamin har Hajiyar Dala an aika mata Da Tsaraba to daman ai ya kamata a aika mata ta chanchanta.

Damuwa ta daya ne yanzu yadda komai ya ke kara lalacewa,Ni ba na jin kaina sai ya'yana sune a gaba,Ko Haruna ni da kaina na shirya na shiga har gidansa Daman makota muke bamu da nisa,Na taba shiga sau biyu tun Fara kai su Amir makaranta,Sunan matarsa Sa'adatu,dayake bana harka da kowa sau daya ta taba shigomin gidan daganan bata kara ba Ishaq bayan Yan'uwana da Dangina har da Mutane ma ya rabani da su Ahalin kuma an ce Mutane Rahma ne.
Naje na same sa na bashi Hakuri akan rashin Biyan sa kudin sa wajen wata uku sai ya nuna min bakomai an zama D'aya tunda Hakkin makota ya hadamu matarsa Sa'adatu ta karbe ni Hannun Bibbiyu,Na isketa tana ta Saida Saide kayan miya da su maggi da gishiri kayan dai kulle kulle na gida na mata sai kuma zuwa ake yi ana siya sai abunda ya bani sha'awa naji Dama ni ce ban iya shuru ba har sai da nayi mata mgana nace dama nice ita ina son nima na Fara sana'ar cikin gida na mata, bata ji ba sai da na kara maimaita mata sannan taji ni Dariya tayi kafin tace"Haba Hajiya kamar ki ina ke ina wata sana'a..?kuna da Rufin asirin ku..Sana"a ai sai irin mu matan talakawa mu samu na Rufa ma kanmu asiri damu da mazajen mu"
Naji mamakin mganarta ni kuma sai nace mata"ai sana'a bata ga Talaka  bata ga mai kudi..Muna yin sana'a ne Domin dogaro da kanmu da kuma ya'yanmu sannan ita mace da neman na kanta a kasanta saboda kada gazawa ya zame mata nakasu watarana"
Sai ta jinjina kai kafin tace"Kuma hakane Hajiya"
Ina kallonta kai tsaye nace"Ba sunana Hajiya ba..Sunana Fa'iza ko ki kirani maman Amir"
Daganan tayi dariya muka cigaba da Hira sama sama,Ban jima ba na koma gida tundaga Lokacin araina na saka ma raina bazan zauna na mutu ni kad'ai acikin wannan gidan da bama ceto sai Allah ba nima zan rika fita na shiga jama'a domin su din Rahma ne.
Muna cikin Haka aka kore su Amir daga makaranta suna dawowa suka fadamin suna zuwa aka koresu kudin makaranta acikin makarantar suka zauna har sai da aka tashi Haruna yaje ya Daukosu hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi na so na kira Ya Ishaq na fadamai sai kuma bani da kati ko na flashing kuma bani da ko asi a hannuna sai na koma na Rumgume hannunawana kawai na rasa mafita,kawai sai nace su dakata da zuwa makarantar sai an biya a baya duk Lalacewa yana biyan musu kudin makaranta akan Lokaci basai ta kai ga an koresu ba,ganin sun kwarari sati a agida ba bokon ba islamiyan sai dai nayi musu na Islamiyan agida,Sai suka fara Damuwa suna ta tambaya na Umma meyasa muka Daina zuwa makaranta..?Anum da Musty kenan Amir shi yafi su wayau da sanin me ake ciki,gabadaya na rasa mafita Kwana takwas da Faruwar haka Ranar da yammah sai ga Jamal yazo shima k'wallo suka zo yi anguwan ya shigo gidan ya iske su a bakin Anum yaji basa zuwa makaranta da ya ce meyasa yau basu je ba..?Shine daya tambayeni nace an koresu ne basu biyu kudin makaranta ba yana ta mamaki ya tambayeni ko na fadama Ya Ishaq sai nace mai A'a.
A gabana ya Daga waya ya Kirasa yana fadamai abunda ke faruwa duk da bana jin me yake fada nasan Fada yake yi kuma duk a kaina,Sai da suka gama mgana yace min Ya Ishaq yayi fada kan meyasa ban kirasa na fadamai ba..?
Har Jamal din na fadin"Anty Fa'iza kema da kin kirasa kin fadamai Halin da ake ciki.."
Kallonsa kawai nayi ban yi mgana me zan ce..?ko na fadamai ba ganewa zai yi ba shurun yafi alheri.
Labari har kunnen Mama da Anty Binta na kuma san nasha Zagi da cin mutumci washegari Jamal din yazo ya Dauke su ya kaisu makarantar ya biya komai,Sannan da yammah ya kawo min 20k a bama Haruna kafin ya Dawo na karba nayi godiya da Safe kuma da kaina na shiga na kai mai yana ta godiya nima inayi sai naga ai ni ce da Godiya domin ni yake yi ma alfarma.
Haka rayuwar ta cigaba da gangarawa masu jin dadi suna ji masu jin akasin haka ma sun cigaba da ji,Har azumi ya karato Ya Ishaq bai waiwayo mu ba abun na bani mamaki ace in shi ya manta damu su Mama ai basu manta yana da mata da ya'ya ba ammh sai naga suma basu damu ba kamar hakan ma yafi ye musu,Kayan abinci ko wani sako sai dai ta Hannun Mama ko Anty Binta batagwara,Ni bani da wata Daraja ko kima sai ta zaman ya'yansa kamar yadda yace din.
Tuni yara har sun saba tafiya makaranta ba biskit ba Lemo saboda babu Daga shinkafa sai taliya ake kawo min sai man girki da kayan maggi,duk abunda bazai zama Dole ba ba'a kawo mana shi,Nama ko mun manta rabon mu da shi,ni bana ma jin kaina yaran nake ji sun gaji da Rigima sun Hakura tunda babu sannan Tun suna Zencen Daada har suka hakura suka Dangana ni ce karfin gwiwan su shiyasa bana yarda na Sare ko Raunina ya bayyana agabansu
Ahaka muka fara azumin watan Ramadana,Har kuma muka fara shi muka sauke Ya ishaq bai zo ba,kuma bai taba nema na ba,Ni ma sai na kama kaina sai dai da watan nan mai albarka ban yi barci ba nayi addu'an Allah ya sama min mafita domin ya'yana domin goben su,Kayan sallar yara Sai ana gobe sallah Jamal ya kawo musu Amir da Musty shadda guda biyu sai yan kanti kowanne D'aya d'aya Ahmad ma shadda guda daya sai sauran yan kanti Anum kuma Atamfa da leshi dinkakku sai Doguwar riga guda daya,sai takalma su sai nawa kala daya jal na wata Bakar atamfa,ko araina ban ji zan sakaba sai dai in na zauna ba kaya ammh in dai suturan Ya ishaq ne na hakura da su har abada Tsoffin dai zan cigaba da sawa Tunda  bani da zabi ammh bayan ya jingine aure na dashi na cire ma raina kara Daura wani abu daya fito daga Hannunsa..
Ganin yadda ya kwarari wata Hudu bai zo ya ganmu ba nasan da gaske yake yi ya zabi Zainab a kaina sai ban ji komai ba sai dai naji Bakinciki har da ya'yan sa suma ya jingine su..?
Ban damu ba ni kawai Fafutaka nake yi har akayi azumi akaga gama bamu ci ko tsokar nama ba ballatana su Dankali da kwai sai tsurar abinci kawai nice nake Sarrafa nau'in abincin Tunda Allah yasa na iya sai Wahalan bata mana yawa sosai ba.
Naman Sa da naman kaza Jamal ya kawo min ranar idi da Safe na gyara na soya su Anum nata murna zasu ci Nama sai da nayi musu kwallah ina Tunanin tun yanzu kenan to nan gaba bansan wani Hali ni da ya'yana zamu shiga in dai na zauna ahaka ba,
Allah Sarki Goggo washegarin Sallah sai ga Hafsatu ta aiko da sakon Nama da Cincin da Cake,Naman soyayye da Danye,Sannan da sakon Hijabi Sabo da Anty mariya ta dinkamin da takalmi na karba na rumgume kayan ina kwallah Allah Sarki yan'uwana basu manta dani ba duk da ni ma ban manta da su ba yanayi ne yasa nayi nesa da su ba acikin son raina ba
Ta fadamin daga gidan Tamadina take jiya taje chan ta kwana ta kai mata kaya daga kano Anty Asiya ta aiko dashi sai naman sallah Daga Goggo sai na wajen Ya mariya naji dadin jin Tamadina tana lafiya,Naji takaici bani da abunda zan daga na bama mahaifiyata nima nema nake yi.
Zuwan Hafsah ne ya Debemin kewa Dani da yara Ranar sallah ta uku gidan Mama muka yini sai Dare Ya Ishaq ya sauka shi da Zainab,Anty Binta da Mama suka rasa ina zasu saka su saboda murna mun gaisa da ita sai mamakin ganin chanzawarta nake yi ta zama wata katuwa ta kara gogewa shima gogan ya Sauya kamar ba shi ba har da Tumbi ya sauke.
Darajan zainab yasa da ni da yara da Hafsah ya kwaso mu muka koma gida,Wannan karon ma Shashen sa ta sauka kuma ni na rika wahala da ita da shi,Dalilinta yasa yayo mana Cafane mai rai da lafiya Saboda sai abun take so ake ci acikin gidan,Da kuma zabinta ake amfani..
Hafsah ita kanta da take yarinya sai da ta ga abun bai dace ba ranar da zasu fita yace na shiga na gyara Bangaransa nasa,Suna fita ta kalleni kafin tace"Yanzu Anty Fa'iza bayan Girkin da kike musu har da gyaran inda suka kwana kamar wata yar aiki..?
Ban ce mata komai ba sai ma Dariya kawai da nayi to ai batayi karya ba kamar yar aiki nake agidan nan,Sati Daya suka yi mana suka koma inda suka fito,Hafsah dai ana jibi Tafiyarsu ta koma Karofi Saboda an koma makaranta..
Bayan tafiyar su muka koma Gidan Jiya kamar yadda muka Saba dai,Allah ya taimake ni Matar Ya Isa wajen Goggo ta haihu,yan biyu Dalilin dayasa Mama tace na shirya aje suna Dani,Murna kamar an biyamun aikin Hajji,Dukkamu muka tafi har da Anty Mahma da Halisa da yara,Nima tare da su Amir muka tafi chan na hadu da Ya Mariya,Yaya asiya dai bata samu zuwa ba,naji dadin zuwana karofi Allah yasa kuma Lokacin Tamadina tazo gida na kai mata su Amir ta gansu sai mamakin girman su take yi shi da Anum,Koda wani Lokaci in naga Tamadina sai na tuna da Dan'uwan  ta da akace sun hada Uba,Wanda tunda mahaifiyarsa da Danginsa suka tafi dashi ba"a kara jin Labarinsu ba sai ina Tunanin ko yana Raye..?ina fatan yana Raye domin shi kadai ne shakikin Mahaifiyarmu.
Hajiyar Dala tazo anan take kara Fadin Bikin Diyarta Suwaiba nan da wata Daya,ban saka raina ba Saboda nasan ba barina ma za'ayi naje ba.
Kwananmu biyu muka Dawo gida Mama kuma Yamai tatafi kanwarta Hure mijinta ya rasu ta tafi gaisuwa ta jima tafi Sati biyu Sai Badariya ta Dawo gidana tana kwana in gari ya waye tayi wanka ta shiga makaranta in kuma tana gida mu shiga kitchen tare tana ganin girki Saboda bata iya Sosai ba Tunda bata zaman gidan.
Ita kanta sai da tayi mgana ganin Daga Shinkafa sai Taliya kawai muke da shi tace ban gayama Ya ishaq cefane ya kare ba ne. ?Sai nace ban fada masa ba ashe da ta koma gida Mama ta dawo sai ta fada mata shikenan Cibi ya zama kari wai ina yawo ina fadin Ishaq ya barni da yunwa Mama musamman tazo gidan Har Store ta shiga taga shinkafa ta fara Masifa tana zagina wai wannan abincin dake gidan gidan uban wa zan kai da zan ce ba kayan abinci..?
Har tana fadin nama samu ne mata dadama suna neman irin Damata basu samu ba,Har jamin kunnen tayi kan wai ina albuzuranci da kayan abinci,bai isa ace sun kare ba ko dai ina Saidawa ko kuma ina kyauta dashi Ina mata rantsuwa da abunda zai kasheni ban taba Saida abinci ko nayi kyauta da shi ba,Tace bata yarda dani ba ni bakar Munafukace ni.
Haka tatafi ta barni ina kuka kamar raina zai fita abun ya koma har da kazafin Satan abinci wlh ban taba ba,Ba Halina ba ne sai dai nasan ko zan shekara ina Rantsuwa Mama bazata yarda dani ba.
Sai nayi kuka na ni kad'ai na Share hawayena na riga na yardan ma kaina Allah kadai ke da mafita sannan garesa nake neman mafitana,Acikin wannan tsukin Bikin Diyar Hajiyar Dala ya taso har ga Allah ban sa araina zan je ba sai ga Mama ta aiko Badariya akan na shirya dani za'a tafi kano yara kuna gidan Anty Binta zasu zauna tare da Halisa suna Exams bazata samu zuwa ba.
Ashe ashe da walakin goro a miya,Hajiyar Dala tace azo dani Saboda aikin abinci Shiyasa Mama ta ce na shirya ana gobe biki muka tafi dani da Mama da Anty Binta da Badariya,Su Amir kuma na bar su wajen Halinsa.
Chan muka iske Goggo da Anty Nasara Da Hafsatu Yaya mariya sai adaran da muka isa ta iso,Yaya Asiya kuma ace ciki gareta har ya fito sai korafin na Rame na lalace suke yi  sannan na kara baki na zama kamar tsohuwa ni dai bana cewa komai Saboda bani da tacewa,Tunda muka isa Hajiyar Dala ta Turani Dakin girki,Da Goggo tayi mgana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login