Showing 27001 words to 30000 words out of 96493 words
kai na cikin Yanayin mganata na yi mata tsawa ina Fadin"Anum zan saba miki fa yaushe kika koyi rigiman ban..za.?
Kuka take neman ta sakamin sai na ware mata idanuwana na Daga Hannu kamar zan daketa sai ta yi shuru tana kallon Uban nata nima nasan ni yake kallo sai naki yarda na kallesa kada tsoron sa yayi tasiri a kaina.
Cikin Fadansa yace"Ammh kina ji na fada ma kanwarki bana son ana dukamin ya'ya shine zaki kwantata agabana ko Fa'iza...?
Kaina na kasa kawai sai nace"Ka..kayi hakuri"
Sai na koma na zauna,Kallona yayi kafin yace"Meyasa ba Biskit ba lemu a basket din nasu..?
Kai tsaye nace"Babu sun kare gabadaya"
Cikin Fad'a ya fara fadin"Gaskiya kina da matsala..Ke shikenan kamar ba mace ba..?komai na Dubaran mata baki iya ba..?to sun kare da kika yi shuru da bakin ki baki fadamin ba ke zaki siyo ki kawo..?
Ya karishe fad'a cikin hayaniyar mganar dayace saboda yanayina ya koya kaina na kasa na kasa mgana suma yaran sai suka yi shuru duk sun yi tsuru tsuru.
Fad'a ya cigaba da yayi yana fadar duk mganar da tazo bakinsa ya karishe da Fadin"Ya'yanki ma baki san yadda zaki kula da su ba Fa'iza to meye amfaninki..?
Komai naki zero ne baki da wani amfani wlh aikin banza kawai"
Dagowa nayi ina kallonsa Hawaye sun cikamin ido bana so su zubo saboda yaran duk sun kuramana ido Kama hannun Anum da Musty yayi yana Fadin"Muje zan siya muku a hanya ku jira anan bari na dauko key din mota dina"
Kai suka gyada mai ya juya ya koma Shashensa yana ta tsaki yana shigewa hawayena suka kawo sai na kauda kaina ina kokarin sharewa sai jin Hannun nayi a kan fuskata ina dagowa naga Amir cikin Wani yanayi da Sauri na kakaro mirmishi ina Fadin"Amir..kwaro ne ya fada min a ido"
Bai ce komai ba yasa Hannu ya Sharemin hawayena Lokaci daya yana fadin"Kiyi hakuri Umma"
Kawai sai naji wani Dum acikin kaina jikina yayi sanyi nabi Yaron da kallon Duka duka shekarun Amir bakwai ne ammh yasan ya ganni ina kuka ya sharemin hawaye ya bani Hakuri kawai sai naji wani abu ya tasomin daga kasan raina bansan Lokacin da na kamasa na Rumgumesa ba da dubara ina Dauke Hawayen idanuwana.
Mganar Ya ishaq kawai naji a tsakar kaina yana fadin"In bazaki barsa yaje makarantar ba ne sai ki gayamin na tafi na kai masu zuwa"
Da Sauri na sake sa ina shafa kansa a sannu nace"Kada ku manta ku yi addu'a"
Suka gyadamin kai,Gabadayan su suka dagamin hannu kafin ya tasasu su fice,bayan fitan su na Dade zaune ina Tunanin rayuwa kafin na mike Dakin Hafsah na shiga na isketa ta shimfidar da Ahmad nata barci ita kuma tana Hada kayanta a karamar Jakar gabanta na tsaya ina Fadin"Yau zaki tafi.?
Mganata yasa tasan na shigo ta Dago tana fadin"Eh Yau goggo tace na dawo gobe muna da makaranta"
Gefenta na zauna na Dafa kafadarta ina fadin"Kiyi hakuri kin ji Hafsatu.."
Mirmishin da yafi kuka ciwo tamin kafin ta kalleni Lokaci d'aya tace"Ni mai sauki ne Anty Fa'iza kece za'a bama Hakuri..Allah ya kara miki Hakuri"
Ban ce komai ba sai mirmishi da nayi shuru mukayi na wani Lokaci kafin tace"Zan biya ta Dutsenmah na Duba Tamadina na riga na fadama Goggo zan biya tachan"
Kai na gyada mata kafin nace"Kice ina gaisheta nima in sha..Allahu zan..zan zo na Dubata"
Da kai ta amsa min kafin tace"Allah yasa"
Bamu cigaba da Hira ba na mike na koma kitchen na dora ma Ya Ishaq ruwan tea bayan ya tafasa na juye mai a falas ba komai na cefane har kwai ya kare wani sauran dankali ne bashi da yawa na fere na soyamai sai namai miyar albasa,na tattara komai na kai Shashensa na shiryamai afalonsa na fice Ganin Hafsa ta karbi gyaran gidan ni kuma sai na kwashi wankin yaran da suka taru naje bayan inda tankin ruwa da famfo yake yi na Fara wanki Uniform na fara wanke musu da Hafsah ta gama sai tazo ta sameni tana tayani sama sama muna Hira,Saboda yanayina Allah yasa bani kuma da yawan mgana sosai
Muna cikin wankin Ya Ishaq ya Leko dauke da Ahmad a Hannunsa yana fadin"Sai ku bar Cikin gida ba kowa sannan ku bar yaro shi kadai adaki..?
Wannan wani irin rashin Hankali ne..?
Da Sauri na tsame Hannuna a ruwan Sabulu na karisa wajensa na karbi Ahmad ya juya batare da yayi min mgana ba sai nabi bayansa muna zuwa Falo ya tssya ya juyo yana kallona Lokaci daya yana fadin"Ga cefane nan..Ki lallaba kinsan ina da Hidima yanzu haka wajen Milyan daya zan yi ma Anty Binta ciko na Hidiman bikin nan sannan ba Lalle na kara miki wani cefane ba sai karshen wata"
Da kai na amsa mai kafin a Sannu nace"Angode Allah ya saka da alheri"
Ko amsa ni bai yi ba yayi gaba daidai Lokacin da wayarsa tayi kara kafin ya shiga ya Daga wayar kasa kasa yayi mganarsa ban ji ba.
Zama nayi na bama Ahmad Nono na maidasa baya na kwantar Domin bazai yarda na ijiyesa ba.
Na dauki Ledojin na shiga da su Kitchen Katan din Bobo ne sai na maltina sai Biskit kwali biyu sai Na ruwa faro sai kwai da doya sai Dankalin Turawa sai kayan miya,na Zazzage komai na jera a muhallinsa
Sannan na koma muka cigaba da wanki ni da Hafsah duka sai da muka wanke har da nawa muna bayan Ya Ishaq ya fice daga gidan bamu sani ba fitowa kawai nayi naga bayanan sannan ba Motarsa nasan bazai wuce gidan Mama ba..ga Hafsah zata tafi bani ko da naira Biyar balle na bata na Mota.
Ina so na bata wani abu ta kaima Tamadina bani da komai sai na Dibar mata Sabulin wanka da na wanki muna da Sauran su bai kare ba, nace ta kai mata,mganar kudin mota kuma tace min kada na Damu goggo ta bata 3k da zata taho zasu isheta ta koma Gida ina ji ina gani Hafsah ta tafi ni na rakata har kofar gida muna Daga ma juna Hannu.
Na dawo cikin gida Nepa sun kawo wuta na zauna na fara gugan kayan Su Amir saboda sai yammah zasu dawo,haka ma Ya ishaq sai da yammah sai nayi Tunanin sai da yamah nayi girkin ni kuma Daman cikina ya cushe hafsah kad'ai taci taliyan nan na Safe ni kuma sai na barta sai an juma.
Ban tashi Daga wajen nan ba sai da na goge rabi da kwatan kayan nan tas sai wad'anda basu bushe ba kawai Sallah kawai ke tadani sai bayan Sallar la'asar na tashi daga wajen shima Saboda girki ne.
Sai alokacin nayi wanka na saka wata bubar doguwar rigar wata atamfa da Yaya Asiya ta dinka mana mu hudu har da ita.
Na shiga kitchen na fara Tunanin me zan sarrafa sai kawai nace bari nayi jallop din shinkafa tunda ina da Sauran kayan lambu sai na Hada da su,Naso na hada ko lemu ne to bani da kankana ba aya ba abarba ba Sinadrin hadawa kayan zobo kuma Daman Badariya ke siyon irin wad'anan abubuwan duk Ya Ishaq baya siyan su sai abunda ya zama Dole.
Sai da na gama komai naje nayi sallar mangariba Allah ya taimake ni Ahmad yau barci ya yini yi bai yi rigima ba Tunda naji su Anum shuru nayi Tunanin Babansu ya Dauko su suna gidan Mama.
Shiyasa na idar da sallah sai na fara jera ma kowanne kayan sa a dirowansa ina Dakin wayata na kara ammh ban ji ba sai chan sama sama naji karan a cikin kaina.
Na daukota na Duba Goggon Karofi ce Ina hada Hausa Ina karantawa wanda bai da wahala sosai in dai kamar na sune ko mgana wacce ba'a rubuta tayi tsawo ba.
Ina Daukan kiran na sakata a speaker Hafsah ce muka gaisa tace ta Sauka lafiya taje wajen Tamadina taji sauki tana ta godiya Daganan ta bama Goggo muka gaisa ta yi tamin nasiha daman ita nata kenan Fadi take yi "Fa'iza ki yi hakuri kin ji ko..?Allah bai manta dake ba..In sha Allahu zaki ci Ribar wannan biyayyar taki"
Shuru nayi ban ce komai ba ta yi ta bani Misalai da matan da suka yi Biyayya agidan aure sannan suka Rabuta ranar Lahira hawaye suka kawo Cikin idanuwana ina tuna Baba a mganarta shima duka kalamansa ne..daga karshe tace min"Naji Isahaq zai kara aure ko..?to sai kin kara Hakuri Fa'iza daman abunda Saudatu take nema ne ya samu ki koma gefe ki rumgumi ya'yanki Allah yayi albarka Allah ya baki Dangana"
Ina share hawayena nace"Ameen Goggo ammh dai zaki zo ko..?
Goggo tace"To sai nagani in zan samu zuwa ammh yara zasu zo su zauna Dake"
Daga haka mukayi sallama na koma na cigaba da aikina naki bari Tunanin auran nan ya shiga zuciyata.
Tun ina saka ran dawowar su da wuri har na sare gani har Tara tayi nayi sallar isha'i nayi ma Ahmad wanka har yayi barci nima wanka na Sake yi na saka Riga da wando masu taushi na barci Diyar Goggon karofi Anty Nasara ta kawo min su Tsaraban Umra.
Ina zaune afalo ni kad'ai kamar mayya naji Hayaniyar yaran da shigowar su dukkansu jikina suka fado suna murna nima na rike su ina Mirmishi Tun kafin nayi mgan Amun tace"Umma Gidan Mama fa Daada ya kaimu"
To daman yana da inda yafi gidan Maman ne..?
Suka fara gwadamin Tsaraban Kayan lashe lashen da ya siya musu sai ga shi ya shigo yana shigowa da sallama bai ko bari na amsa ba ya fara fada yana fadin"Don iskanci kina ji ina ta Hon bazaki iya fitowa ki budemin get ba..?
Ni wlh har ga Allah ban ji ba cikin sanyina nace"Ban ban ji ba wlh..kayi hakuri"
Tsaki kawai yaja ya wuce Shashensa yana fadin"duk kin ji..ai ba hayaniya a inda kike balle ki fake da Lalurarki"
Ina jinsa ban ce komai ba sai ma kirkiri mirmishi Saboda yaran kada su Fahimci wani abu,ni ke kokarin kauce ma wasu abubuwan ammh yadda Ya ishaq baya jin kunyar tozartani gaban ya'yana in da ina Biyesa da tuni yaran tun tashi da shi a ransu,sai dai in dai suna wajen da ya fara fadansa zan yi saurin ba shi hakuri na nuna komai ba komai ba ne.
Kayan makarantan su nace suje su cire kafin su ci abinci sukace min sun sha tea agidan Mama.
Suna shigewa d'aki ni kuma nabi Ya Ishaq Shashensa kada yace ya dawo nayi banza dashi daman na hada mai abincin sa tuni na kai mai shashensa.
Koda na shiga yana Cire kayan jikinsa sallamanta ma aciki ya amsa min na Rankwafa ina mai Sannu da zuwa ya amsa sau d'aya ya dauke kai ya Tura kofar Tiolet ya shige ni kuma sai na karisa cikin bedroom din na Tattara kayan daya cire na ninke mai na bude Wardrope dinsa na sakamai na gyara mai Dakin Dazu daman saboda bai bar key din bane shiyasa.
Ina Dakin ya fito yana Digan ruwa da Sauri na Dauko mai Towel na basa ya amsa yana Goge jikinsa Lokaci d'aya yana kallon kayan jikina ni kuma ban ma Lura ba wardrope dinsa na Bude ina Fadin"Jallbiya zan dauko maka..?
Kai tsaye yace"Bar shi kawai"
Ban damu ba na rufe na koma gefe na Tsaya kaina na kasa kamar Daga sama naji yace"Ina kika samu wad'anan kayan barcin kuma..?
Shuru nayi kafin nace"Anty..Na..Nasara ta kawo min Tsaraban Um umra."
Tabe baki yayi kafin yace"Shi yasa da zata baki sai da ta zabo kalan da zai yi daidai da yanayin ki.. Green wannan kayan ba su yi ba ammh ke kin ga abun sawa da sunan ki yi ma mijinki kwalliya dashi.."
Sai naji na muzanta duk da ya saba kusheni ammh na yau sai yafi Dafani barin ma da ya kara fadin"Kwata kwata na rasa wani abu ne zaki saka ya Dace dake Fa'iza..Alhamdulillah da Allah ya bani Zeey yarinyar mayar dressing ne komai tasa ajikinta sai kin ga kamar don ita aka Hallici kayan zata zo kuga juna don Allah in kun had'u ki fara D'aukan gyara daga kanta"
Kaina sai da ya yi Dum jikina sai yayi min ba Dadi ammh ban nuna ba kayan jikina na kallah har ga Allah ni ban ga Aibun su ba kore ai kalan yan aljannah ne sai dai daman shi tozarcin sa ba inda baya tashi.
Da naga zai saka kaya sai na fice abuna na zauna afalo ina jiransa haka ya fito yazo ya zauna ya fara cin abinci sai da ya gama sannan na kwashe komai na kai kitchen na koma nayi mai sai da Safe naga yana waya da Hannu kawai yayi alamun naje ni kuma na fice na koma Dakin yarana na iske Amir na koyama Anun aikin da aka bata a makaranta Musty har yayi barci na gyaramai kwanciya na mai addu'a na koma cikin su Anum na zauna ina ganin abunda suke yi ina mirmishi sai da suka gama na saka Amir yaje yayi fitsari shi da Anum suka kwanta muka karanta addu'an barci atare suka Shafa na gyara musu kwanciya na rage musu fanka na kashe musu wutar Dakin na fita zuwa D'akina na gyarama Ahmad kwanciya nima na kwanta agefensa ina addu'an barci.
Karfe uku na dare yau na tashi nayi Nafilfiluna sannan na fita naje na tashi su Amir,sai ga Baban su ya fito suka tafi masallaci ni kuma muka yi tamu ni da Anum agida.
Kamar yadda n Saba kafin bakwai din Safe sun shirya cikin kayan makarantar su Ahmad na bayana sai rigima yake yi,Ba ya ishaq zai kai su ba Haruna mai adaidaita ne wanda ya saba kai su baban nasu yau zai koma Abuja.
Shashen shi suka je suka mai sallama sannan suka fito ni na saka Hijabi na rakasu har waje muka gaisa da Haruna sannan suka shiga suka wuce ina Dawowa a gurguje na had'a ma Ya Ishaq abun karinsa buredi da kwai na Soyamai sai ruwan tea na kai mai Shashensa ya fito cikin shirin Tafiya sanye da Suit bakake ya tsuke kamar ba shi ba har da wani damfararen bakin glass na ba mutumci.
Yana zaune yana karyawa ina Gabansa Ahmad na Hannuna ina Lallashinsa sai da ya gama sannan ya mike yana fadin"Fa'iza zan tafi kuma kila sai satin biki zan shigo.karbi ki ga."
Kudi ya miko min yan Dubu na saka Hannun na karba ina godiya Karamar Jakarsa ya Dauka na mike ina Sabe da Ahmad zan karb'a da Sauri yace"Kada ki damu da wannan..Ki kularmin da yarana in akwai wani abu ki kirani a waya..koda yake nasan zaki kira indai kina da bukatar wani abun"
Nidai ina biye dashi har Haraban gidan Ahmad ya karba yayi masa sumba kafin ya miko min shi Sai da ya shiga mota sannan ya Leko yana fadin"Anty Binta zata aiko miki da kayan fitan biki da wasu kaya da ta matsa sai na siya miki in ma da wani abu zaki ji wajen su Mama na tafi..Ban da yawo..Fa'iza gidan Mama da Gidan Anty binta kad'ai kike da izinin zuwa ki Kiyaye"
Daga haka ya rufe motarsa lokaci daya yana fadin"Ki budemin get"
Haka na tafi zugwi zugwai ga goyo a bayana,na saka karfina na bude mai get ya fice na bisa da Allah ya kiyaye hanya na maida get din na Rufe ina Haki sai da na koma falo sannan na Kirga kudi Naira dubu biyar itama nasan Saboda matsalan yara ne daman duk sati in yazo haka ya ke bar min.
Kuma kafin ya Dawo ta kare ko Kudin motar da nake zuwa gidan Mama ko Anty Binta sannan ga Dawaniyar yara yau Anun tace bata da pensil gobe Amir yace zai siya Drowing duk anan kudin ke tafiya.
Tunda ya tafi sai na maida Hankalina wajen kula da ya'yana Kwana Hudu Tsakani da Tafiyar Ya Ishaq Anty Binta ta kirani a waya mu hadu agidan Mama ranar jumma'a da Safe bayan su Anum sun tafi makaranta na shirya na tafi bayan nace ma Haruna gidan Mama zai kawo su Anum in ya Dauko su daga makaranta.
Naje na iske gida cike da kawayen Mama ana ganin kayan lefen da za"a tafi dasu Abuja agobe.
Akwatuna goma shake da kayan alfarma ni ko Aleda Anty Binta ta bani nawa Less d'aya atamfa biyu sai takalmi sai Hijabi na karba da Hannun Biyu ammh sai Mama ta harareni tana fadin"Naga kin karba a wulakance kin raina ne..?
Kaina na kasa na kasa mgana Hajiya Barira aminiyar Mama tace"To ina Laifi wannan kayan Hajiya Saudatu..?ai wlh naga kokarin Ishaq ma matar farko ai ba kowa ke wani wahalar da kai akan su ba"
Mama ta tabe baki kafin tace"Matar ma irin wannan abar ba.."
Suka kwashe da Dariya suna nuna ni, Anty Binta ta kyabe fuska tana Fadin"In ma ta raina ita ta sani..Kila wad'anan take kalla ai inda suka dace za'a kai su Yarinya ba inda basu dace ba"
Ni dai kazil ban ce ba Saboda suna so naji cin mutumcin su da karfi suke mganar su,Haka suka sallameni na kwashi kayana zuwa Dakin Badariya bata nan tana makaranta.
Ba domin nace Haruna ya wuto da su Anun nan ba da gida zan koma saboda su yasa na jira sai da suka Dawo nazo musu da kaya suka sauya ni nayi girki daman indai nazo to kamar jaka haka take komawa agidan Mama.
Sai La'asar na koma gida ni da ya'yana da kayan da Anty Binta ta bani duka an dinka su daman,Washegari kuma Badariya tazo take gayamin an tafi kai lefe har da Hajiyar Dala da Anty Binta da Hajiya Barira kawayen Mama.
Sai fada take wai ba su sanar da Goggon karofi ba araina nace ita din banza ai in dai su Hajiyar Dala na waje kowa ma bai da kima a wajen Mama.
*Littafin KANA NAKA Book 2,3paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.*
*Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223*
*Janafty*
*KANA NAKA..!*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
*Book 1*
*ASSALAMU ALAIKUM*
*KAYA SUN SAKE SAUKA*.
*INGANTATTUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*.
*ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA*.
*KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI