Showing 81001 words to 84000 words out of 96493 words
ishaq ya shigo da Leda sai dai yaran suka juya suka gansa kwatsam ni nama manta ko alama ban ce musu Daada ya dawo ba.
Haka suka tsallakeni suka nufesa Har da Ahmad,Amir ne kawai ya tsaya a tsaye sauran kuma jikinsa suka fad'a ya tarbesu yana fadin"Oyoyo ya'yan Daada"Anum sarkin Karad'i ta ce"Daada yaushe ka dawo..?mun daina ganinka ko da yaushe muna tambayan Umma sai tace baka nan".
Ina jinsu sai ya kasa bata amsa sai da ya kai ga zaune sannan ya Dauketa ita da Musty da Ahmad ya Dora zaman jikinsa Amir ya zauna agefensa yana fadin"Umman ku bata gaya muku nayi tafiya ba ne..?Kanin ku bai da lafiya jaririn Antynku muka kai Asibiti"
Da Sauri Anum tace"Jaririn Anty mai kyau"?
Sai ya gyad'a mata kai,sai suka nuna tausayawar su Ledar hannunsa ya warware ya fito musu da Minti da Biskit wajen rabasu musu ne yaga Hannun Anum duk maiko ya shinshina sai yaji warin Daddawa da Sauri ya Dago kansa yana kallona ni kuma shan Fate na, na cigaba da yi kallo basu isheni ba.
Sai ya kalli Anum yana fadin"Me ye a Hannun ki Mamana..?
Da Sauri ta ce"Daada Fatee ne Umma tayi mana dad'i"
Sai ya k'ara kallona ya kuma kalli Farantin gabana cikin yamutsa Fuaka yace"Fa'iza meye wannan..?
Naji sa ammh sai nayi kamar ban jiba. sai da ya kara Daga murya yana fadin"Nace meye wannan kika bama ya'yana Fa'iza..?
Na dago kaina ido cikin ido nace"Fate ne"
Saboda naga abun na sa kuma ya fara zama renin wayau faten ne bai sani ba..?
Ya maimaita sunan fate a ransa da Fili kafin yace"Me kenan..?ina mikewa nace"Abinci ne shima.."
Su Anum na kallah ina fadin"Kun koshi ne..?dukkan su suka d'agamin kai sai na nufi kitchen da shi nasan ya bini da kallo ammh ban ko waigo ba sai da na shiga na sauke abun hannuna na wanke hannuna na fito ina Fadin"kuje ku wanke hannuwan ku"
Kamar suna jirana suka sauka da gudu zuwa Daki har da Ahmad shi kuma sai ya kalleni yana fadin"Ina miki mgana kina basar dani Fa'iza?
A kaikace nace"na baka amsarka nace maka abinci ne"
Sai ya kasa mgana sai chan yace"Baku da abinci ne a gidan sai kin basu wannan abun sun ci hannunsu sai wari yake yi"
Sai ma ya bani Dariya na murmusa na gyara zama na akasan cafet din Falon ban yi mgana ba da kansa ya mike ya shiga kitchen din yaga bakomai Sai Dubaruna irin na mace mai ya'ya Shinkafa kad'ai ta rage mana itama ko Tiya bata kai ba,ba domin Goggo ta taimakeni ba da Tuni asirina ya Dad'e da Tonuwa a idon duniya domin tun da na dawo daga Rasuwar Tamadina k'waran abincin ban gani ba.tun Cefanen da yayi mana kafin ya tafi shima bamai yawa ba ne,ina jin ba shi da kudi a tare da shi ne lokacin.
Ina ganinsa ya fito cikin wani yanayi ya kuma daga waya ya kira Mama naji yana mgana ammh Dayake ban maida Hankalina akansa ba ban ji me yake fad'i ba.tunanina na chan inda mafita ta take, da Tunanin yadda komai zai faru jibi,Har na kosa ma jibin yayi mu fara kamar na matso da jibin gobe haka nakeji zumud'i kawai nake ji akasan raina kamar nama iya komai haka nake ji.
Sunana naji yana kira da karfi sannan na Dago ina kallonsa cikin Mganarsa yace"Wani banzar Dabi'a kika samu ina mgana kina ji na,kina yi min banza..?
Kai tsaye nace"Kayi hakuri abun ka ga mara karjin ji sai hakuri"
Sai ya kasa mgana,Bata rai yayi yana Hararata kafin yace"Na rasa wata irin mace ce ke Fa'iza..?
Yanzu kayan abincin ku ya kare bazaki iya kiran Mama ki fad'a mata ba..?jamal baya gida yana makaranta ita nake turo ma kudin cefanan ku duk wata da kudin bukatun yara, ammh yanzu da nayi mata mgana tace bata zauna ba sannan bata san cefanen ya kare ba"
Kallonsa kawai nayi na kasa mgana shi kuma sai ya cigaba da fad'a yana fadin"Badar na zuwa gidan nan fa ko ita bazaki aika wajen maman ba..?Ko ke bazaki shirya ki je ki gayamata ba..?
Sai kawai nace"Kayi hakuri.."
Saboda na datse mganar ganin yaran sun fito kowanne da Biskit da minti a Hannunsu,Shima jin abunda nace ne yasa sai ya kasa cigaba da tijararsa,Daganan sai hankalinsa ya koma kan yaran yana ta tambayan su abunda suke so suna fad'amai da labarin makaranta ni ko araina ina kara jinjina kaifin ikon Mama akan komai shi kayan abincin sai naje na Fad'amata ya kare kenan zata fidda kudin da ya turo mata ta siyan mana kenan..?kamar tana yi mana alfarma a raina daman na Guduri niyar ko zamu mutu da yunwa na gwammace duk mu mace da naje wajen Mama nace mata bamu da abinci.
Tara nayi na tattara yaran suka je suka yi shirin barci suka kwanta Anum ma da Ahmad na kwantar da su akan gadona,Na fito falo zan d'an gyarasa tunda yaran duk sun zubar da Ledojin Biskit din a tsakar falon na iske sa Lafe kan kujera yana waya a hankali yake yi shiyasa ban jisa ba sai na shiga abunda ya fito dani bayan na gama zan koma Daki sai ya kwalamin kira na Dakata na juyo ina kallonsa a kishingid'e yake sai ya Dago yana fadin"Naga zaki shige ciki ni me zan ci..?
Sai nayi shuru ban ce komai ba ya kara maimaita mganarsa ya karishe da fadin"ina jin yunwa kuma ban tsaya gidan mama naci abinci ba'
Cikin yanayin mgana tace"Sai Faten in zaka sha..?
Yadda yayi da fuska ne sai da naji kamar nayi dariya sai dai na kanne cikin kaushinsa yace"ki sama min wani abu"
Ko bakomai yaci darajan Zumunci da ya'yan da suka had'amu sai na juya zuwa Kitchen ina fadin"Sai dai shinkafa ita kad'ai garemu"
Ina jinsa ya mike yana fadin"Dafamin ki yi min source din miya tunda naga akwai kayan miya dare yayi ba na son na sake fita ne"
A daran nan ma dafamai Shinkafa araina ina kallon gas d'ina ina godema Wutar nepa ba domin anguwar da muke ana barin wuta ba, da tuni na raina kaina Gas ne mai shidda,wanda ke amfani da
Gas da Electric,basan shekara nawa na kwashe ina amfani da shi da wuta ba, tun Auran Ya Ishaq da Tarewansa a Abuja komai ya sauya,a baya yana mana Refliing ko ya aiko Jamal ya yi mana, ammh daga baya komai ya sauya sai da nayi da mai wuta,shi kuma baya da saurin girki,tunda bani da wata mafita hakanan nake hakuri da shi,Daman gas din Yaya Ishaq ya siya san da zamu dawo gidan.
Har goma da wani abu sannan na gama na had'a komai na kai masa shashensa a falo na sauke mai komai yana ciki ko bari ya fito ban yi ba na koma Dakina nayi shirin kwanciya,na kwanta sai barci ban farka ba sai asuba,bayan na idar da sallah nayi ma yara shirin tafiya makaranta saboda yau Jumm'a ne basa dad'ewa sai basu je da Kwandon abinci ba sai ruwa da na Dura musu suna shirin fita su yi ma Haruna mgana sai ga shi ya fito yace zai kaisu suna ta tsallen murna.
Shi ya kwashe shi suka fita ya kai su sai wajen goma ya shigo gidan,da amajirai guda biyu suna ta shigowa da kaya,kayan abinci ne ya siyo masu yawa har da Biskit din yara da Lemun su da ruwa har da kayan Tea wanda har yaran sun manta da shi sun saba da kunu har da su kwai kayan miya da kayan lambu,Dankalin Turawa da yawa haka ya siyo ina zaune ina karishe ma yaran guga afalo sannu da zuwa kawai nayi mai na juya na cigaba da aikin gabana har ya sallami yaran ya shige shashensa ya sake fitowa kayan na nan zube afalo ban kauda su ba cikin fad'a da bacin rai yace"Wai fa'iza wani salon iskanci kuma kika samo..?
Na dago ina kallonsa ya cigaba da Fadin"nine kike nufin zan kwashe wad'anan kayan ko me kike nufi..?
Ban ce komai ba na kashe soket din Abun gugan, na wuce na fara Daukan kayan ina shiga dasu ni ko na daina rawan jikin kan abunda bazai D'ore ba
Sai da na kwashe duka na shirya komai a muhallinsa ina shirin na koma na cigaba da aikin gabana yace"ki sama min abunda zan ci"
Kamar nace zainab bata aiko maka dashi ba ne..?
Sai na fasa rashin kunya ba Halina ba ne sai na Tashi na shiga kitchen dafamai mai Dankalin Turawa nayi,sai nayi mai miyar kabeji da taji albasa sai na Dafa mai ruwan tea na Dafa mai kwai guda biyu kuma duka na Tattaramai ko abakina domin na koshi Faten jiya na dumama nasha abuna yaran, kuma Farar shinkafa na Dafamusu da Mai da yaji sukaci kafin su tafi makaranta.
Yana zaune afalon na kawo mai ya kalli Filet da jug din da na sanya mai Ruwan zafin kai tsaye yace"Gabad'aya komai naki ya tsufa Fa'iza..Ji kwanukan cin abinci sun fita Hayyacin su mtswww.."
Ya saki tsaki daga karshe ina jinsa ban ce masa komai ba na koma na cigaba da aikin gabana,sai da na gama na kashe komai na kwashe zan koma Daki naji ya daga murya yana fadin"Ki shirya in yara suka dawo makaranta zamu je gidan Mama a gabanta sai ki fad'amata in ni nayi miki iyaka da zuwa gaisheta"
Sai abun ya bani mamaki.matar nan Kwata kwata bata kaunar ganin kwanciyar Hankalina, burinta ta samo hanyar da za'a tozartani, to da ikon Allah kanta zai koma ni dai ina Daraja ta ko ban auri Yaya Ishaq ba. kamar uwa take gareni, tunda ta rikeni bata barni na yi rayuwa a titi ba sannan duk tsananin wuya da Dadi ta killaceni acikin gida rayuwata bata shiga tsaka mai wuya kamar na sauran matan da rashin gata da mafita yasa suka fada harkan banza ba,ballatana ina auran Abunda ta Haifa har abada bazan ki Darajata ba.
D'aya saura na rana yaran suka Dawo shi yaje ya Dauko su da kansa masallaci jumma'a ya tafi da mazan har da Ahmad ni da Anum mukayi tamu a gida,Shinkafa da miya Da salat nayi mana ni da Anum muka fara cin namu kafin su dawo suna Dawowa na zubo mai yaci tare da yaran,Suna ta Murnan tunda na saka musu sabbin kaya nace gidan mama zamu je.
Wajen uku saura na rana muka isa gidan Mama,Mun iske gidan cike Anty Binta,da su Halisa da Anty mahma da ya'yanta kamar ana biki yaran muna zuwa suka had'u da abokan wasa suka tafi suna ta wasan su.
Afalon kowacce tayi shigar alfarma har ta da Mama ko da taga jiya taga yau da na gaishesu dakyar suka amsa min gwara ma Anty mahma Halisa daman ita ta gaisheni har tana min gaisuwa,Ni da Badariya ne muke mgana kasa kasa kan gobe Badariya tace"Kin fad'a ma Yaya ishaq dai ko..?
Na girgizamata kai kafin nace"Ban fada masa ba ammh zan shaida masa yau in mun koma gida"
Badariya ta zaro ido kafin tace"in ya hana ki fa ?nasan Halin Yaya Ishaq barin ma in ya fad'ama Mama wlh bazaata bari ba"
Kai tsaye nace"Wannan karon bazai iya hana ni din ba"
Cikin mamaki take kallona bata samu zarafin mgana mukaji muryan Mama asama tana Sababi sai da na Saurara naji dani take tana cema Yaya Ishaq gatanan ka tambayeta yaushe rabon da kafarta tako gidan nan da sunan gaisheni.?
Anty Binta ta karbe da cewa"Ballatana ni banza abanza mama"
Shi kuma sai ya d'ago daga Danna wayarsa yana kallona Lokaci daya yana fadin"Shiyasa na kawo ta gata gani ta fad'a in ni nayi mata iyaka da gidan nan? Gata nan ni da kaina na yarje mata zuwa Gidajen ku duk sati ta gaisheku ita zaku Tuhuma me ke hanata zuwa"
Mama ta tabe baki tana fadin"Rashin mutumci ne ba wani abu ba.ko yaran nan bata kawo su, nace to in kai ne ma kake so ka raba su da nan gidan basu da inda yafi gidan nan a wajen su ta bangaran ta da take takama wa take dashi ?uwar tasu da ta rage itama Allah ya karbi a binsa sai naga karyan tsiya "
Idunuwana suka ciko da kwallah na kasa mgana zagi da cin mutumci ba wanda Mama batamin ba Anty Binta na tayata sai da Anty Mahma tace"Haba Mama ki barta hakanan mana ba ta baki hakuri ba"
Sai Mama tayi shuru tana Numfarfashi ni dai kaina na kasa ina bata Hakuri Saboda Yaya Ishaq yace na duka na basu hakuri in ba haka ba sai ya sabamin ban ki ba na Duka gwiwa Bibbiyu na basu hakuri dakyar suka Hakura.
Daganan suka yi kamar bana falon suka cigaba da Hiran su sai Badariya tajani Dakinta tana bani Hakuri na kalleta cikin wani yanayi kafin nace"Bakomai duk wanda yayi ma Aure bauta bazai taba tabewa ba..Sannan sakamakon sa na wajen Ubangiji"
Daga haka muka saki mganar mu kama wacce nake ganin zata Fisheni Badariya sai jinjina yadda zan rika zuwa sau biyu arana take yi.nace mata kada ta Damu zan iya ai nace Allah adakin ta nayi la'asar sannan Mama ta aiko wai nazo nayi musu abincin dare haka na kwabe Hijabi na shiga kitchen da Badariya ta shgo zata tayani Mama na ganin haka sai ta kirkiri aikenta sai bayan mangariba ta dawo Lokacin na gama Tuwon shinkafar har na kulle a leda Miya ce bata karisa ba.
Har ta Anty Binta sai da taci tayi guzuri Anty mahma dai da wuri ta koma gidanta mu kuma sai wajen goman Dare tuwon nan ko bakina ban ci ba,su Amir dai sun ci da Babansu duk na Takura na kosa na koma gida.
Kusan Lokaci d'aya muka fito da Anty Binta itama zasu wuce afalon Mama ta kalleni tana fadin"Wai ni kam fa'iza ina kayan ki da Ishaq yake miki ne..?bana ganin ki da su sai tsumma kike sawa"
Gabada'ya suka kalleni harda shi da Mama,Bai dai yi mgana ba sai Mama ce ta tabe baki kafin tace"Daman da Tsumman ta dace.aiko don yan'uwanta su zagesa zata rika mugun shigga alhalin daidai misali yana fita Hakkinta"
Har muka isa gida mganar Mama tamin Tsaye arai bayan wannan kayan Da Anty binta ta bani ko Hijabi Ya Ishaq bai kara dinkamin ba.ammh Mama ta iya bud'e baki ta fadi yana Fita Hakkina, Lalle gaakiyan masu iya mgana da sukace wata shari'ar sai Lahira.
Sai da duk nayi ma yaran shirin barcin daman ko da muka dawo su Anum duk sun fara barci,sannan na Dauki wannan Katin I.d card kenan na nufi bangaran Yaya Ishaq acikin raina ina jin cewa wannan karon bazan iya bin Umarninsa ko ya amince ko bai amince ba wannan karon ba gudu ba kuma ja da baya insha Allahu.
Na shiga na iske baya falo yana cikin Bedroom dinsa ba domin ni nake bukata ba,ba yadda zai sa na bisa ciki Tuni na kiyayewa kusantar inda yaya Ishaq yake saboda Dalilai masu karfi.
Bedroom din na shiga da sallama baya Dakin sai nayi mamakin to yana ina..?
Har na juya zan fita naji karan Bude kofa kii..Sai na juyo muka hada ido shima kallon da yayi min nasan na mamakin ganina ne.
Yana sanye da kayan barci riga da wando, masu taushi Farare na barci,Ya kariso tsakiyar dakin yana fadin"Lafiya..?
Har yana wani gimtse ransa kila yayi tunanin wani abu nazo nema sai yaga na mikamai abun hannuna ya karb'a yana zama gefen gado lokaci daya yana fadin"Wannan kuma na menene.?
Sai dai yayi mamakin ganin Hotona da sunana da dukkan bayanan abubuwana ajikin katin sai ya kara Dagowa yana kallona cikin mamaki ya kara fadin"Fa'iza duk wannan abun na menene..?
Sai na duka a gabansa na gyara zama na Dakyau kafin nace"Kune yan boko ka karanta Dakyau zaka fahimta"
Ya sake karantawa ya Dago cikin mamaki yana fadin"Naga Katin shaida ne na Training din da za'ayi na koyon sana'o'i daga karkashin kungiyar Women charity Foundation."
Shine nace ban gane ba naga hoton ki da sunanki shaidar katin naki ne"
Mirmishi nayi Cikin karfin gwiwa na fara mai bayani da yadda kawar Badariya da ita kanta suka samo min form din na cike,da kiran mu da akayi wanchan satin mukaje da bayanin komai na karishe mganata da fadin"Gobe zamu fara koyan abubuwa kuma na tsawon sati goma sha Biyu ne,Sannan sau biyu za'a je a rana ni kuma abubuwan da nake so na koya da Safe ake koyar da biyu da yammah biyu kenan kaga a rana sau biyu zan rika zuwa kenan safe da rana"
Har na gama bayanina yana kallona cikin mamakina daya nuna har a saman fuskarsa,Cikin kaushinsa yace"Duk a yaushe kika fara yanke ma kanki hukunci yin wani abu batare da sanina ba Fa'iza?
Nima kai tsaye nace masa"A ranar da ka zabi wata matar sama dani.Nima aranar na zab'i yanke ma kaina da Rayuwata komai batare da na saka ka aciki ba"
Maganata ta girgiza sa ya tsaya kawai yana kallona,ban damu ba sai ma naji kamar gwarin gwiwan. da na shigo da ita ta ninka wacce na samu yanzu tsoro ko fargaba sun fice daga raina kwata kwata.
Hanuna na saka na karbi katina daidai Lokacin da yace"Ni ki ke gayama wannan mganar Fa"iza..?Rashin kunya zaki yi min.?
Kai na girgiza kafin nace"Ko d'aya kada ma ka dauka ahakan Yaya Ishaq ai ko ba aure tsakaninmu kai yaya na ne,kuma babu rashin kunya har Abada tsakani na dakai.kawai akwai lokacin da in mgana tazo a muhallinta gwara a fad'eta kawai da a barta tayi ta zama a inda ba Muhallinta ba"
Sai ya kasa mgana sai kallona yake yi cikin mamaki nasan aransa mamakin ya akayi na samun bakin yi masa mgana yake yi ni ko araina nace daga yau bakunan fa'iza sun bud'e kenan Har Abada.
Cikin Ajiyar numfashi yace"Naji yanzu meyasa kika fad'amin..?
Na gyara zama na nace"Saboda ya dace ka sani ko ba komai ina gadin gidan ka.
da kuma kula da ya'yanka in fita ta kamani naa jera sati ba ma wata ba, yana da kyau ka sani d'in shiyasa nake shaida maka"
Kai tsayae yace"In kuma nace baza ki fita ko'ina ba na isa ko ban isa ba..?
Ya fada yana kallona cikin ido nima sai na Dago ina kallonsa bansan Lokacin da bakina ya furta"a wannar gabar Isar ka bata isa ba Yaya Ishaq.."
Sai ya zabura yana kallona cikin bacin rai ya nuna da hannu yana fadi"Ni kike cema isa ta bata isa ba Fa'iza"?
Sai