Showing 6001 words to 9000 words out of 96493 words
ya amsa yana Dubanta ganinta Dauke da Ahmad yasa yace"Ina zaki kaishi..?
Hafsah tace"Kuka yake yi zan kai shi ta bashi Nono ne."
Hannu ya mika mata yana Fadin"A kitchen din zaki kai mata shi..?
Wato salon ta jefa shi Cikin wani abu kin santa bata da kula."
Hafsah dai batace komai ba ta mikamai D'ansa ya Cafe shi yana Daga sa sama cikin Fara"a Hafsah bata damu ba ta karisa kitchen din Domin kama ma yayar nata aikin itama gobe zata koma Daman Hutun Midterm break Aka basu a makaranta yasa Goggo ta barta ta taho itama tana Karofi ne wajen Hajiya Indo da suke kira Goggon Karofi ita take rikonta tun bayan da ta karbota wajen mahaifiyarsu Ta madina.
Suna Kitchen din suna aiki Hafsah taji Sanda Anum ta fito ganin babanta yasa ta nufesa cikin murna tana Fadin"Daada yaushe ka dawo..?
Daman Anum akwai kirniya da Rashin jin mgana Yana ganinta itama ya Tarbeta yana Fadin"Anum dina jiya da Daddare na dawo kun yi barci."
Kai Tsaye tace mai ina Tsarabanta yace sai an juma in ya sake fita Hafsah ce ke Sauraran Hiransa da ya"yansa banda Fa'iza da baji take yi Sosai ba sannan Hankalinta na wajen Soya Doya bata ma san Abunda suke ciki ba.
Kafin bakwai na Safe tayi Fa'iza ta gama komai sai ta bar Hafsah a kitchen din tana karisawa,ni kuma sai naje na Shiryan yaran saboda suna da Hadda Tahfiz ne tun Safe sai shida suke Dawowa Allah ya taimake ni Ahmad na wajen Ya Ishaq ya shiga Dashi Shashensa.
Koda bakwai da Rabi tayi sun karya sun shirya Tsab Cikin kayan makarantarsu Ga Basket din kowanne an shiryamai da soyayyar doya da miyar kwai,Sai lemu da ruwa Fa'iza na kokarin Tura Hafsah ta leka tayi ma wani wani makotanci Haruna mgana mai Tuka adaidaita shi ke kai yaran makaramtar Hadda da Boko a wata Ya Ishaq na Biyansa Saboda abaya motace har da Direba ya Daukan musu tunda Anum ta taba koke motar Mama ta sa ya bama Jamal kaninsa motar tana chan gidanta Kofar soro in ya Dawo Hutu Daga Kano inda yake karatunsa na Engeering yake amfani da ita su kuma Ishaq ya Daukam ma yaran mai adaidaita a cewarsa Tunda bata iya Tattali ba shi ba asararrre bane sannan kuma yace Mota bata Dace da ni ba,irin mu yawo acikin Adaidatan yafi Dacewa damu,ni Dayake ban Damu ba, ba fita take yi sosai ba Daga Gidan Mama sai gidan Anty Binta shima na da'n Rage zuwa tunda ba maraba suke da zuwana ba Karofi kuma sai dai in an yi Rasuwa muje Gabadaya ammh ni kad'ai Ya Ishaq cewa yake bai yarda da ni ba zanje ne na Had'u da yan'uwana azagesa shiyasa ban ma Damu da Fitan ba nima.
Ina shirin aika Hafsah ne sai ga Ya Ishaq din ya fito yace shi zai kai su,jin Haka yaran suka fara Murna sosai,Tare da Ahmad suka tafi har Lokacin bai koma barci ba shima ai yasam Ishaq saboda gaskiya in yana Gida yana bama yaransa Lokacinsa nice dai bani da wannan matsayin.
Har sun fita naa bisu Haraban gidan ina kwalama Amir kira ya juyo yana Fadin"Umma menene..?
Ina Sosa gashin idona nace"Kada ku manta ku karanta addu'ar fita Daga gida."
Da Karfi Anum ta fara karantawa Amir na Binta shi da mustpaha suna gamawa nabisu da mirmishi ina Daga musu Hannu Ishaq dai Tuni ya Shige mota yana Dauke da Ahmad irin wad'anan Hallayar na Fa'iza ba wani Burgesa suke yi ba,Sai dai kuma a kasan Ranta yasan Tarbiya ce mai kyau shiyasa wani lokacin baya mgana.
Ganin ya shiga motar bai bude get ba yasa na karisa na Budemai motarsa ta Fice Daga gidan sannan na maida na Rufe,abaya munq da megadi wani Dattijo,Tunda lokacin da Yaya Ishaq yaga ina basa Abinci yace don me..?
Ai yana Biyansa duk wata ba wata mgana kawai sai ji nayi ya sallamesa Daganan kuma bai kara Daukan mana wani megadi ba yace Tunda Zan iya na yi Hidiman get din da kaina
Sai da suka tafi naje nayi wanka na Sauya kaya zuwa wata Doguwar Rigar Shadda Dinkin zamani kan na gama Shiryawa Hafsah ta gyara Falon ta share in da yaran suka bata sannan ta gyaro Dakin yaran suma ganin haka yasa nayi mata sannu da aiki ni sai na shiga Shashen Ishaq na gyara duk da ba sosai yayi Datti ba na Cika shi da Turaran kamshin Daki sanin sa mai son kamshi ne.
Kafin ya Dawo na jera mai kayan karinsa,na koma Falo muka karya ni da Hafsah muna yi muna Taba Hira duk da Hiran Daga Hafsah ne ita Fa'iza nata Eh ne ko A'a sai mganar da batayi Tsawo ba.
Har muka gama karyawan bai shigo ba,Hafsah tatafi tayi wanka ni kuma na kwashe komai nakai kitchen na Fara kimtsa wajen,Bayan na gama nayi wanke wanke,ina cikin goge gogen kitchen din naji Sallama atsakar Falon Sai na leko da Towel din gogogogen a Hannuna,Baki na washe ina fadin" BADARIYA.."
Cikin bayyana Murna ta ganin wacce aka Kira da Badariya na Tsaye da katuwar leda a Hannunta yar matashiya doguwa Fara Fuska kamar ta Ishaq sai dai ta fisa Haske saboda ita macece Autansu ce Badariya Kabir Karofi.
Karisowa tayi Cikin Falon Tana Fadin"Anty Fa'iza yunwa nake ji wlh..akwai sauran abun kari kuwa..?
Tafada tana wanchalar da gyalen Hannunta Lokaci Daya da ledan Data shigo da ita.
Bata ma saurari Fa'izan Dake faman mata gaisuwan yasu Mama ba
Ta Shiga kitchen din tana Dube Dube ta samu Doya a kula da Miyar Kwai ta Dauko ta Fito Tana Fadin"Anty Fa'iza adana gaisuwarki sai naci na koshi Tukunna."
Dariya nayi mata bance komai ba na koma kitchen din na Cigaba da goge gogen da na fara ina mai jin Dadin zuwan Badariya din duk cikin ya"yan Mama Ita kadai ce ke sona sai Jamal shi kuma bai da alkibla yau ya min Mutumci gobe kuma akasasin sa shidai baka gane ina ya Dosa,Ammh yana zuwa gidan nan wajen su Amir sannan yana zuwa cin abinci ba wacce tafi Tsanata Daman Tun zamana wajen Mama irin Anty Binta batagwara ita da Ya Ishaq daman basu so zamana agidansu ba Sun gama Dora min karan Tsana wanda har yafi ma wanda Mama take min tun ina da karanci shekaru kafin ma aure ya shiga tsakani da ya Ishaq
Sai da nagama aikin na Sannan ta sake Fitowa Falon na iske su Tare da Hafsah wacce tayi Rashe Rashe kasan Cafet tana Bude kayan da Badariya ta shigo Dasu ita kuma Badariya na kan kujera ta cin Doyarta suna mgana da Hafsah.
Ina Shigowa Hafsah tace"Anty Fa'iza kinga ankon Bikin ya Ishaq.."
Jin Shuru yasa Badariya tace"Bafa ta jiki ba..Anty Fa'iza ga ankon Ya Ishaq..kin gani..?
Sai alokacin najisu nabi Kayan Dake Hannun Hafsah da kallo sai na kasa mgana Badariya da Hafsah suka kalleni Cikin wani yanayi kafin Hafsah tace"Kilama bata san da ankon ba.."
Badariya tace"Anya..?Anty Binta ta Dauko fa..Ranar agabana da tazo gidan Mama ta Kira ya Ishaq din tace zata Daukan ma Anty Fa'iza ,Anum kuma zata Hadasu dasu Hibba ne.
Hafsah tace"To ba mamaki."
Badariya tace"Wannan da kike Dagawa naki D'aya nawa daya..Yanzu Daga wajen tela nake bai Dinka Less din ba.."
Hafsah ta zaro ido tana Fadin"Wai nawa..?
Badariya ta mata Dariya ai sai tatashi ta Daga Tsalle tana murna ta Rumgume Fa'iza Dake Tsaye tana kallonsu tana Mirmishi Cikin Fara"a tace"Kinga Anty Fa'iza Badariya ta Dinka mana..!"
Fa"iza ta karbi Atamfan tana gani kafin tace"Sun yi kyau.."
Hafsah ta isa ga Badariya ta Rumgumeta tana Fadin"Nagode sister..Allah ya bar zumumci."
Badariya tace"Ameen ammh bani Zaki ma Godiya ba Ya Ishaq ne shi ya siya mana.."
Hafsah bata wani ji mamaki ba,Saboda in yayi Niyya yana da Alheri sosai tana ta godiya tana Santin kayan.
Badariya tace"Za dai kizo bikin ko..?
Nima yanzu aBakin Ya Ishaq nake jin kinzo Daga kai yara makaranta wajen Mama ya biya."
Hafsah tace"Zan zo tunda weekend ne."
Badariya tace"in Goggon Korofin ta bar ki ba..Domin ita kanta ban Tabbatar da zata zo ba..Naji suna waya da Mama tana Fadan Ya Ishaq bai Fada musu zencen auran nasa ba"
Hafsah dai batace komai ba Badariya ce tacigaba da Fadin"To waya fadamawa..?
Daga shi sai Mama sai Anty Binta suke abinsu Amaryan ma suna waya da Anty Binta tunda ita ta Hada lefen.
Hafsah tace"To yaushe ne ma Bikin..?
Badariya ta tabe baki Tana kallon Fa"iza dake zaune gefe tana kallonsu kafin tace"Anty Fa"iza ta san Lokacin Bikin..?
Hafsah tace"Anya..? Batamin mgana ba."
Badariya tace"Karshen wata ne sauran Sati uku."
Hafsah tace"Allah ya kaimu nan za"a kawo Amaryan..?
Badariya tace"A"a chan Abuja zata zauna..Ai itama yar Abujan ce,mahaifinta shugaban ya ishaq ne a wajen aiki,Itama ai ma'aikaciya ce tana aiki da wani kamfani ban dai san ko na menene ba nima
Haka naji Anty Binta na fada ma mama cikin Hirarsu."
Hafsah tayi shuru jikinta yayi sanyi Tana kallon yar'uwanta wani Tsausayinta ya kamata sai taji Badariya na Fadin"Ya Ishaq ya samu Cikar Burinsa Mace mai kyau Fara Doguwa mai kwalayen zamani ga Kudi da Nasaba..Allah yasa a wanye Lafiya."
Hafsah ta amsa mata da Ameen kawai Domin bata da tacewa,Fa'iza ce ta dan Daga Sautinta tana Fadin"Badariya ya mama..?
Badariya tace da karfi"Tana lafiya..Tana chan tare da D'anta na barsu na fito amso dinki nan sanan kuma yunwa ce ta koroni."
Mirmishi kawai nayi ban ce komai ba ni kowa yasanni bani dayawan mgnaa Saboda yanayina
Sai Hirar ta koma Tsakanin Hafsah da Badariya da Daman kawaye ne suna Hirar Hajiya Fatima wacce suke kira da Hajiyar Dala tana chan kano tana auran wani Babba a soja.
Hafsah ke tambayan su Suwaiba sun san Bikin ya Ishaq din..?
Badariya ta tabe baki tace"Ke share su basa min mgana ko achart kuma suna da Layina..Naji dai mama na Fadin Hajiyar dalar bata nan ta Raka megidanta India Cheekup,Kinsan ta bata Damu da zumunci ba.
Hafsah tace"Haka naji Goggo na Korafi kinsan zuwanta na karshe kaca kaca suka Rabu da Goggon.."
Badariya ta tabe baki tace"Shiyasa sau Daya na taba zuwa gidanta.
Hafsah tace"Ni ai ban ma taba zuwa ba.Yaya Asiya da ta zauna awajenta in tanaa baki Labari sai kin sha mamakinta."
Badariya tace"Shiyasa tasu tazo daya da Mama fa."
Dariya kawai Hafsah tayi suna ma Hirar Fa'iza ta koma Dakinta tana gyarawa,Hankalinta na kan aikinta duk yadda Tunani ke mukurkusanna naki bashi muhalli,na gyara Dakin Tas sai dai abu daya ne Fa"iza bata iya gyarashi ba shirgi bata iya yadda Zata kakkanta ko'ina yayi kyau ba,Sai dai ta gyara ko'ina ta kuma ta maida shirgin waje D'aya.
Mata kala kala ne, kuma kowacce da yanayin yadda ta iya gyaran waje,Ita fa'iza haka Allah ya yi ta tana da Tsafta jiki da na zuciya sai dai bata san yadda zata gyara komai a bisa muhallinsa ba.
Tunani nake yi anjuma zan yi wanki kayan yaran hade da Uniform dinsu Tunda Anum ta lalata injimin wankin su na koma yi da kaina domin duk abunda yara suka Lalata Laifin a kai na Ishaq ke dorashi.
Kayan Ahmad masu Datti nake fitowa Dashi Sanda Hafsah ta shigo ta kawo min Ahmad,alokacin nasan ya Ishaq ya shigo gidan ganin na riga ta kai mai abun karinsa yasa na zauna ina Bashi Nono,ko kafin ya gama sha yayi barci naa koma na shimfidar dashi,na kwashe kayan Ahmad da na Anum data cire dasafe zuwa Dakin yaran na wuce Badariya da Hafsah a Falo suna Hira Dayake Tv Din dake falon yara sun Lalata kuma Ishaq bai Damu daya gyara ba.
Sai da na gama Hada kayan waje daya na kullesu cikin wani Dankwali Sannan na fito ta nufi Shashen Ishaq.
Afalo na sameshi zaune kan kujera mai zaman mutum Daya ya lafe ni ban ma san waya yake yi ba Saboda ba Karfin ji gareni baa.
Kayan daya gama kari dasu na kwashe na kai Kitchen kuma ban baro kitchen din ba sai da na wankesu,koda ma fito ta iske Badariya zata tafi mukayi sallama Hafsah ta fita domin ta taka mata...Shashen megidam na koma naji ko akwai abunda yake so saboda karamin abu laifi ne a wajensa..Ina Shiga Har Lokacin bai gama wayarsa Daga yanayin yadda yake mgana zaka san yana bama wayar Muhimmanci kayan Haushi Fa'iza bata ma jin me yake Fadi shi da Zeey tana mai shagwaban jiya Daga Tahowarsa har tayi kewarsa.
Ganin yadda Fa'iza tamai zaune agabansa ne yasa yace ma Zeey ta bashi Minti biyar sannan ya datse kiran..
Fa"iza ya kura ma ido yana kallonta hankalinta na ma kan Tv dake aiki afalon cikin Tashar Mbc3 cartoon suke yi Ahmad ya kunna ma D'azu da Safe kafin fitarsu.
Mirmishi takaici yayi kafin ya Kirani a Kaushashe kamar yadda ya Saba.
"FA'IZA..!"
Firgigit nayi na Dago ina kallonsa Lokaci daya ina amsawa da Na"am
Kallonta ya karayi yana Nazarina domin Idanuwanta sun kumbura sai kuma ya waske cikin yanayinsa yace"Kin tasani agaba ina waya wani abu ne..?
Dayake a sama yayi mganar na jisa sai nace da Sauri"Kayi hakuuri..Daman nazo naji ko kana Bukatar wani abu ne..?
Karamin Tsaki yaja kafin yace"In ma ina bukata ai zam miki mgana ko..?
Tashi kije abunki ban cika son kina yawan zama a inda nake ba Fa"iza Allah Nagani."
Tsam na mike zan fice dagaa Shashen nasa, lokaci daya kuma ina daga rigata Daga kasa saboda tsawon yamin yawa kallo ya Bini dashi To ai Daman yasan Tunda wuyan yayi mata Daidai Daga kasan Rigar sai ta bata mtsala.
Har zan fice ya Kira sunana da karfi na juyo ina amsawa da hannu yayi min alaman na Dawo da Hanzari na na Dawo na Duka agabansa sai da ya sha Iskarsa sannan ya Tashi ya shiga cikin Dakinsa minti kad'an ya fito Hannunsa Dauke da wani Hoto ya zauna Lokaci Daya yana mika min Hoton na sa ka Hannu biyu na karb'a Fuskata da mamaki da neman karin bayani.
Ya Dora kafa d'aya kan D'aya kafin ya kalleni yana Fadin"Duba ta da kyau ki gani Fa'iza.."
Sannan ki Fadamin ya kika ganta..?
Fa'iza tabi Hoton Dake hannunta da kallo Wata kyakyawan Hallita nagani kamar ita tayi kanta wajen kyau Doguwa mai Dogon Fuska da Hanci har Baka Farace tss mai ja ja ja,Sannan tana da lobawar Kumatu,Wato Dimple Gashinta Har gadon bayanta yake,ga Diri na Cikar ya mace duk da Abaya ne ajkinta Shape dinta ya bayyana sannan tana da Wushirya hakoranta data Bude sun bayyana Farare masu Tsari ga Kunshinta ja ne ya fito akan Fararan Hannayenta masu kyau da sheki Fa'iza tana ganin Ya Ishaq mai kyau ne sai dai dataga wannan sai taga ai shi bamai kyau bane.
Ganin yadda ta bada Zuciyarta wajen kallon Hoton yasa ya Karbe Hoton batare data shirya ba na Dago ina kallonsa ya Daga Hoton yana Fadin"Ya kika ganta..?
Fa'iza cikin yanayin mganarta tace"Tana da kyau..!"
Ishaq yace"Eh ban ji me kikace ba..?
Fa'iza tace"Tana..tana da kyau sosai.."
Ishaq yayi wani irin Dariya kafin yace"Bayan kyau fa..?
Baki Fahimci ta mallaki komai na Kyau da Zatin ya' mace ba..?
Fa'iza tayi shuru batayi mgana ba Ishaq ya kalli Hoton na wani Lokaci kafin yace"Kinsan wacece wannan..?
Fa'iza ta girgiza kai kafin Ishaq ya Cigaba da Fadin"Matar da zan aura ce..Zabi na ce Fa'iza Zainab lawal Bako kenan..Mace ce mai kyau Kamar yadda kika ganni Mai tarin ilimin Zamani Tana da Degree Biyu sannan tana Shirin komawa Phd dinta,Iyayanta masu Kudi ne da Nasaba ta mallaki Duka Burina na nan duniya nan da Sati uku zata zama matata zata cika min gurbin mafarkina da kika Tarwartsa Fa'iza.
Shiyasa na yanke shawaran zaki Dakatar da Haihuwa hakanan ki bar mai wuri tazo ta fara Haifamin kyawawan ya'yan da nike Mafarki.Yanzu ne zan san ni Ishaq nayi aure,abaya ina jin kunyar nuna ki a matsayin Matata ammh ayanzu banda Haufin Duniya taga Zeey a matsayin Matata ina Rokon ki Fa'iza nayi miki komai a Rayuwar ki yi Free d'ina ki barni naji D'adin Rayuwata ni da Matar data dace dani."
Ya karishe fada ya na kallon Fa'iza da kanta ke kasa ta kasa gane ina mganganunsa ya Dosa Cikin wani yanayi na Dago ina Fadin"Bangane ba..?
Kai Tsaye yace"Zamu jingine AURAN mu ne Fa'iza..Wlh in nace ashekara Takwas din da mukayi da aure ban cutu da auranki ba nayi karya kiyi ma kanki adalci kiyi min adalci nima"
Gaskiya ya Fada Tabbas gaskiya ya Fada Fa'iza ta fada acikin aranta.
Cikin wani karfin gwiwa na kallesa kafin nace"Jingina kamar ya..?
Kai Tsaye yace"Jingina ina nufin ba Saduwar aure tsskanimu a matsayin miji da mata ba wata mu'alama ta aure ba Raba kwana Tsakaninki da Zeey..Sai dai zan cigaba da kula Dake saboda Darajan ya'yan dake tsakanin mu Kada ki manta ba Mu'alaman miji da mata Tsakanina Dake..Kawai zan kula Dake ne Saboda ya'yana kawai"
Har ya gama mganansa kallonsa nake yi Hawaye sun gama wanke min Fuskata ga mamakinsa sai kawai yaga nayi Mirmishi,mirmishin da zai iya rantsuwa bai taba ganin Fa'iza tayi irin sa ba.
Cikin wata irin muryan da baisan ina da ita ba yaji nace
"Na Amince.."
Farinciki ya kamasa ya kalleni yana Fadin"Nagode Fa'iza ko bakomai kin yi sakayyah ga Alherin Baba agareki."
Ko kara Sauraransa ban yi ba na mike Zan fice ya Kira sunana na waigo Cikin Kaushinsa yace"I ya ni da ke..Ban yarda wani yaji wannan mganar ba kina jina..?
Kai na gyadamai ina sharan Hawaye, muryata na rawa nace"Insha Allahu ba wanda zai ji sai indan kai kaso hakan"
Daga haka na fice da Sauri Saura kadan Rigar jikina ta Hardeni na Fadi bai Damu ba Murna yake zai samu Salama Shekara Takwas yana cikin kurkuku sai yanzu yaji sa kamar yana Shakan iskar yanci.
Har na karisa Dakina kuka nakeyi bana ko ganin gabana sosai,kan gadona na Fad'a gefen Ahmad ina wani gunjin kuka Dake fitowa Daga kasan Raina Hasbunallahu wani'imal wakeel shin ni na Tsara ma kaina Rayuwata a haka..?
Allah ne yayi ni baka mummuna Allah ne ya so ya ganni afasalin daya ijiyeni meyasa ya Ishaq bazai gane haka ba..?
Yau ni Ya Ishaq ke mganar zai jingine auranmu Saboda wata.? Na tabbata ba Domin mganar Baba ba da tuni aurane da Ishaq ya kare to ai yanzu ma ba Maraba..?
Zai jingine ne kawai saboda mganar Baba ba Domin Ra'ayinsa ba,sai kuma domin kuma ya'yansa Ba laifi na bane domin na fito a mummuna ba, kuma ba Laifina bane domin na fito daga jikin Bebiya ba, ba Laifina bane domin na kasance an Haifeni da Laluran rashin ji sosai da yanayin mgana taba, ba Laifi na bane Allah ne ya Tsara min Rayuwata Daki Daki.
Sannan ba Laifi na bane