Showing 30001 words to 33000 words out of 96493 words
ZAKI YI GYARA?*
*INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*.
*GADALIN MATA AKWAI*.
*INA DA TABBACIN INGANCINSU*.
*SANNAN WACCE TAKE SON A DAFA MATA KAZAR, ZA'A DAFA*.
*TUARAREN WUTA NA ASALIN CHADI AKWIA SU AVAILABLE, SAI KIN GWADA ZAKI BADA LABARINSU*
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU DOMIN KARIN BAYANI*
*08032773332*.
*NATION WIDE DELIVERY*.
*SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*
🙏.
*🅿️07*
Bayan ta gama fad'an rashin gayama Goggon karofi sai ta koma fad'an kayan da aka bani bayan tace na dauko mata ta gani Badariya karama ce acikin ya'yan mama ammh da ace itace Babba da abubuwa da dama sun gyaru tana da kyakyawan zuciya da Hali mai kyau.
Ina kallonta ta d'aga kayan a rene tana tabe baki kafin tace"Yanzu Anty Fa'iza abunda suka baki kenan acikin Uban kayan akwati goma da suka tafi kaiwa Abuja..?
Duk da ba duka naji mganar ta ba,ammh na dauki wasu,Sannan ina Bin bakin wanda na saba mgana dashi na kan Fahimci abunda yace ko da ban ji ba.
Ban ce mata komai ba sai ma wani mirmishin takaici da nayi,na sani ko Lokacin aurena ya ishaq bai min lefe ba ballatana yanzu ba da bani zai aura ba,Daman a wanchan Lokacin Baba ne ya matsa masa akan sai yayin lefe ba Sadaka ya aura masa ni ba, awanchan Lokacin Mama ta shiga mganar tayi ruwa tayi tsaki akan ita da kanta zata had'amin lefe nagani na Fad'a da ya kara tambayata sai tace tuni ta bama ya ishaq ya kaimun kaya ahalin kaya ko kala goma basu kai ba sannan saukakku dai ba masu tsada ba daman tun a baya na fada muku Baba shi ba magidanci ba ne mai bin diddigin abunda ke faruwa a cikin gidansa ba shiyasa wani Lokacin Mama kan yi nasara a kansa da kuma kila an yi masa surkullen mutanen yamai.
Ni ban damu ba saboda ba kayan ba ne a gabana, ko su bani ko kar su bani bazai kankare yadda bani da Daraja a idanuwan ya ishaq da su kansu ba.
Har ta gama fadan ta ban bude baki nayi mata mgana ba to me zan ce..?duk abunda zan ce alokacin bashi da amfani Saboda ajiyan agaban Mutane Anty Binta ta kara maimaita Dakyar ta lallaahi Ya ishaq ya amince ya siyamin ma kala ukun da aka bani Domin da farko cewa yayi bazai siya ba Saboda ko ya siya zai yi asara ne ban san Darajan su ba sai da tayi ta basa baki sannan ya amince to saboda mene zan damu..? Awannan gabar da auran mu ya zama jingina ba lalle ne Hakkokina su rataya a wuyansa ba ni ba Dolen sa ba ne yanzu Saboda haka raina ya daina Damuwa kan duk Tozarcin da zai aikata agareni.
Kuma na kudiri araina bazan saka kayan sa ba,Akallah dai zan fara Dogara ga kaina ko Saboda ya'yana na fara Tunanin zamana ahaka bazai yuyumin ba in ya'yansa Dolensa ne,ni na tashi adolensa bazan bar gidansa yanzu ba Saboda lokaci bai yi ba ya'ya na suna Bukata ta, sosai in na tafi na bar su basu da wanda zai kula da su da Tarbiyan su ina tsoron su tashi Cikin maraicin uwa kamar yadda muma muka tashi cikin wannan maraicin muna da uwa a raye ammh kamar bataa raye ne a wajenmu.
Tattara komai nayi na tusa cikin Wardrope d'ina ban kuma yarda nayi mganar da kowa ba Daman Ya Asiya ce kadai take kirana kan Sha'anin Bikin Yaya mariya ko sau d'aya bata kirani ba ita ta na da Zafi ne Ko zuwa tayi had'uwa goma sai sun yi Cacan baki da Anty binta gata irin tanada Sauri Saurin mgana ne kafin Anty Binta ta fadi daya ta maida mata Biyar Shiyasa bata cika zuwa katsina ba sai da Dalili mai girma waya kuma bamu cika mgana ba Saboda abu kad'an zataji ranta ke baci kuma bata da Hakuri ko kada'n.
Biki nata karatowa barayin su Mama suna ta shirin su gayya Mama tayi bani da Gayya ba Domin tace sai yanzu ta san Ishaq zai yi aure ni ina gida bansan halin da suke ciki ba,bani cikin kwanciyar Hankali Saboda ina ta mafarkin Tamadina sai na tsorta kada tazo ta mutu itama bamu gana ba sai na fara Tunanin ya kamata naje na gaisheta na Dubata Saboda mahaifiyata ce in na rasata a wannan gabar sai nafi kowa kuka Saboda dani kad'ai ne bata gana ba.
Na fara Tunanin Tafiya sai dai matsaalan kudi ne Dubu daya da Dari Biyar suka Ragemin a hannuna cikin Dubu biyar din da Ya Ishaq ya barmun da zai tafi sannan Tunda ya tafi ko sau daya bai kirani yaji Halin da muke ciki ni da yara ba nima kuma ban kirasa ba Sai dai na riga na kuduru niyyar zuwa gaida Tamadina Cikin Satin nan da zai shiga kafin Lokacin Bikin yazo.
Na shirya tafiya ta Ranar asabar in su Amir sun tafi Hadda,Shiyasa Ranar jumma'a da Daddare na yi ma Ya Ishaq flashing Saboda wayata ba kati na ma manta Rabon da na saka mata kati ba na kira daman sai dai mai son mgana dani ya kirani bansan adadin Flashing din da nayi masa bai kira ba sai chan naga kiransa na dauka jikina na rawa na saka ta a amsa kuwwa na kara kunne tun kafin nayi mgana ya Dakamin Tsawar da sai da tasa na razana Cikin Fadansa yace"Haba don Allah wai meye haka Fa'iza..? Sai flashing kike yi min tunda kika ga ban kira ba ai kinsan ina wani abu mai muhimmanci ne ko ina tare da wani mutum mai muhimmanci ke duk abunda kika fara Hankali bai isa ya baki ki bar shi haka ba..?
Sai naji kwallh ta ciko cikin kwarmin Idanuwa na cikin rawan zuciya da na Murya nace"Kayi..ka..yi hakuri..Ban..Sani ba ne.."
Karamin tsaki yaja kafin yace"Zan kiraki in na koma gida ina tare da Zeey ne.."
Daga haka ya katse wayarsa ina jin muryanta kafin ya katse tana fadin"Honey kai da waye kake ta Ihu haka..?kamar a kusa da wayar tayi mganar shiyasa na ji ta.
Ban ji me yace mata ba ya katse kiran sai na Sulale gefen gadona na fashe da kuka Allah yasa yaran duk sun kwanta har ta Ahmad yayi barci kuka nayi wanda naji ya isheni nasan bani da wata Daraja a idanuwan Ishaq ammh ban dauka har agaban wacce zai aura ma bani Daraja ba ,Sai na fara tunanin wani irin karb'a amaryan sa zatayi min in muka fara Had'uwa sannan me ya fada mata akaina..?
Wata zuciya ta amsamin ya fad'amata ke bakomai bace face bebiya mummuna baka mara gata sannan mara ilimin zamani wacce bata da komai atare da ita tuna haka yasa kuka na ya karu bansan tsawon Lokacin da na Dauka ina kukana ba sai da nagaji sannan na tashi na Shiga Tiolet na wanke fuska ta na fito na k'i yi barci ina jiran kiransa na riga na sakama raina Gobe zan je na Duba Tamadina kuma ba yadda zan iya tafiya batare da izininsa ba..
Bai kira ba sai wajen sha d'aya da Rabi na Dare sannan ya kirani ina D'auka fada ya hauni da shi wai ni bai san me nake yi ba sannan bani da Hankali komai ba cikin lissafi nake yi ba ni dai Hakuri nayi ta basa sai da ya sha iska ya gama wulakacin nasa sannan yace"Ina yara na..? Ina fatan suna nan cikin koshin lafiya ko..?
Nayi saurin amsa mai da suna lafiya jin nayi shuru yasa yace"Fa'iza fadi abunda yasa kika addabeni da Flashing ina da shiga office da Safe zan kwanta akan Lokaci"
Cikin yanayin mganata nace"Da dama..Ina so ne gobe naje Dutsenmah na Duba Tamadina"
Cewa yayi bai ji ba na sake bud'e muryanta na kara gayamai sai kawai yace"wacece haka..?
Ban yi mamaki sanin Waye Ya ishaq kai tsaye nace"Babarmu.."
Karamin Tsaki yaja kafin yace"Daman nasan bana ganin kiranki sai wata Bukatarki ta taso miki Fa'iza baki da wani Amfani sai kina da bukatar wani abu..me akayi da kike son ki tafi..?
Kai tsaye nace"Tayi rashin lafiya ne ni kad'ai ne ban je na Dubata ba"
Kyafci yayi kafin yace"Kada nace bazaki je ba kice na hanaki ganin mahaifiyarki Allah ya kiyaye hanya..Sai dai kada ki kuskura ki tafin min da yara na gidan da ba wanda yasan su, salon suje suna Rab'e rab'e ke kanki ai araben zaki je Ahmad na amince kawai ki tafi dashi Shima Saboda yana shan Nono ne"
Ban damu ba nace"Eh daman suna Hadda haruna in ya Dauko su in ban dawo ba gidan mama zan ce ya kai su"
Da Sauri ya tasomin yana fadin"Au Dare ma zaki kai?ko nufin ki Daman chan zaki kwana..?
Cikin daburcewa nace"A"a..Dama..Dama ina so na Biya Karofi na gaida Goggo ne"
Kai tsaye cikin D'agawar Harshe yace"Ban amince ba..Ban kuma baki izinina ba..Dutsemah kadai zaki je shima Dubiya ce in kika Kai dare Fa'iza wlh sai ranki ya baci..Wato ki je a had'u ayi ta gulmana ana zagina nan Goggon karofi ta kirani tana min Fad'a duk akan ki wai in nayi aure kada na wulakantaki to in tana ganin ban taimake ki ba meyasa sanda Baba ya nuna zai Aura min ke bata famsheni ta aura miki Isa ba..?karewar tana kaunarki da Tausayin ba..bana son Rainin wayau kada ki sake naji kin taka Karofi in kuma naji wlh tallahi kin ji Rantsuwan musulmi Fa'iza zaki ga Other side of me da baki Taba gani ba.."
Hawaye wani na koran wani suke zuban min cikin wani yanayi nace"Ko gidan Ya..ya mariya..?
Dogon Tsaki yaja kafin yace"Ita kuma wannan na yi miki iyaka da ki kara Takawa gidanta tunda bata da mutumci bata da,kunya har ni nan zata rika gani na, tana min kallon banza kamar taga kashi..?,Sannan naji Labarin ta raina Mama ta kuma raina Anty Binta har sa'insa tana yi da ita in dai ni ke auran ki kin bar kara taka gidan da ake cin zarafin Uwa ta da yayata sannan itama ki gayamata kada ta kuskura na kara ganin kafarta agida na in kuma ta bari muka Hadu sai na Koreta wlh"
Daga haka kit ya kashe wayar sai nayi sororo da waya a Hannuna Hawayena suna D'iga a saman wayar gefen gado na koma na zauna kukana ya kasa Fitowa sai dai Hawayen kawai ina Tuna mganganunsa in ya zagi Yaya mariya bazan damu ba Tunda har Goggo bata tsira ba awajensa ni Ya ishaq daman ya saba kirana da duk sunan da yaga Dama,na yarda yace ban da amfani sannan bana Kiransa sai in ina da Bukata Saboda tun farkon fara aikinsa a abuja ina kiransa Ranar ya Dauka ya yi min fata fata yana min ihu akan me zan rika Damunsa na D'auka Abuja irin katsina ne..?
Abuja yana harka da Mutane Dabam Dabam bazai zo cikin jama'a yana wage baki da murya Saboda mgana dani ba kada na kara kiransa kada na kunyatasa watarana cikin jama'a Tunda ga ranar ban kara gigin kara kiransa ba kada na kunyatasa kamar yadda yace d'in sannan Halin ko in kula da ya nuna kan Tamadina bai Dameni ba Domin bashi ba ne na farko ba kuma Kila bazai zama na karshe ba.
Tunda ya ke aure na bai Taba taka gidan da Tamadina ke aure da,Niyyar gaida mahaifiyata ba akwai wani zuwan da mukayi karofi bayan Haihuwar Anum ne da Mama da shi a motar abokinsa Dakyar ya aminnce ya biya dani zan kai mata Anum saboda sanda aka haifeta bata zo ba Shima din Sai da na roki Mama ta saka baki ya Biya dani ammh K'iri k'iri yaki bari na shiga da Amir sannan Daga shi har Mama suka ki' shiga Gidan suka tsaya a mota ni kuma ya bani Minti goma.
Ina shiga ko zama ban yi da kyau ba ya fara Hon ta na rike da Anum a hannunta ni na fad'amata tare da su Mama muke bata damu ba tayi Lullubi ta fito har kofar gida suka gaisa Ya ishaq kuma ki'ri kiri yak'i fitowa Daga mota Mama ce ma ta fito suka gaisa duk yadda Tamadina taso ta Dauki Amir ya ishaq ya ki fitowa da shi yana rike dashi,Sannan ya hanani komawa cikin gidan ko cikakken gaisuwa bamu yi da ita ba yace na shigo mota mu tafi da nace bamu gaisa ba sai yace sai dai ko na san yadda zan yi na Dawo gida wlh in ya tafi bazai dawo ya Daukeni ba.
Ina ji ina gani na shiga mota bayan Tamadina ta bani Anum,Tana d'agamin hannun idanuwanta sun cika da kwallah,ni kaina kwallar ta kawo cikin Idanuwana da Dubara na share mun D'auki Hanya Ya Ishaq ya juyo yana fadin"Tab Mama ashe kice Allah ya Dubi Fa'iza da idon Rahma ana jin mganarta har ana gane me take fad'i naji Babarsu ba'a ko jin abunda take fadi sai uban Ihu kawai ake ji tana yi"
Da Dauri na Dago ina kallonsa shi kuma ko ajikinsa maimakon Mama ta kwab'amai a'a sai cewa ma tayi"Eh mana ai uwar su ce ainihin Bebiyan Sai dai kaji tashin Ihu nan kuma wai mgana take yi"
Ya Ishaq yayi dariya yana kallona kafin yace"Allah ya taimake ki Fa'iza da yanzu kema ihun kawai zamu rika ji"
Daga shi har Mama Dariya suka saka har muka iso gida ina kuka Tozarcin ya tashi daga kaina da yan'uwa ya koma Har kan mahaifiyata shiyasa abunda yayi yau ba zame min Sabo ba sai dai shi Tozarci baka Sabo da shi ko yau aka yi maka shi sai kaji ba Dad'i.
Ban karaya ba sannan na yi kudurin sai naje shiyasa da wuri na tashi na shirya yara suka tafi Hadda sannan na yi wanka na shirya Ahmad Na fara Tunanin me zan kai mata bani da komai ban ijiye ba sannan ban bama wani ajiya ba ina bakincikin wannan Rayuwar da nike ciki ko da bani da shi akwai Hakkin uwata a kaina sannan wazai amince bani da shi Tunda kowa yasan Ya Ishaq nada Rufin asiri sanna ba kowa yasan yanayin Rariyar ba ballatana yasan yanayin zubar ruwanta ba Nasan Su Yaya mariya suna iya bakin kokarin su ammh suma ai ya'yanta ne kamar yadda nake yarta akwai Hakkin kyautata mata a wuyana.
Da na rasa abunda zan kai mata sai na D'ibar mata garin rogo wanda Ya Ishaq kan siya saboda yara in yaga Dama sannan shima yana son gari da siga,sabulin wankan mu ya kusa karewa sai na Dibar mata na wanki da na Klin,sai na Daukan mata Maltina guda hudu na kulle aleda ina da Burin ko kaya na bata ammh bani Dashi sannan bazan iya bama mahaifiyata tsohon kayana ba kamar na ci mata mutumci ne.
Sai nayi Hakuri na Dauki iya abunda nake da shi koda goma tayi na isa Dutsemah sai dai Tamadina ta ganni kamar Daga sama Allah Sarki Uwa bakinta yaki Rufuwa ta rasa ina zata sakani Saboda Murna taji Sauki Sai dai kafafun sun kumbura abokan zamanta sun ce Daga dare zuwa Safe ta tashi da Kafafu a kumbure ana ta dai shafa mganin sanyi.
Tunda muka zo ta kama Ahmad ta goya ram a bayanta sai kallonta nake yi farinciki ya cikani ta tambayi su Amir nace suna makaranta tace meyasa ban kawo su ta ga yadda suka kara girma ba..? Idona ya ciko da kwallah ya'ya na ne suma ammh bani da iko da su ballatana mahaifiyata tayi iko dasu suma dai ce mata kawai nayi zan kawo su watarana.
Abokiyar zamanta Maman isuhu suke kiranta tayi danwake ta kawomin naci abuna muna ta Hira Da Tamadina duk da mganar nata sai a hankali ammh mu ya'yanta da ta zame mana Dole muna ganewa ni dai ban gayamata wani abu da zai tada mata Hankali ba ko mganar auran Ya ishaq ban mata karfe biyu nayi na tashi na fara shirin tafiya bayan nayi sallah na bata abunda nazo da shi ta Dafa kaina tana ta sakamin albarka.
Ta bani Ahmad na goya a baya na,na saka Hijabina nayi ma mutan gidan Sallama ta rakani har zaure tana D'ingisawa ina ta koma sai tace sai ta Rakani mun yi sallama kamar kar mu rabu har zan tafi ta riko Hannuna na Juyo ina kallonta ta kuramin ido sai naji jikina yayi sanyi cikin mamaki nace"Manene ke faruwa Tamadina..?
Kawai sai ta Dafa kaina ta jijjiga nata kafin tace"Kiii....yi....hakuri..Fa'iza..!
Sai naji raunina ya bayyana da Sauri na kauda kaina ina Boye hawaye na kafin na gyada kai ina fadin"In sha Allahu..Allah ya baki lafiya"
Daga haka muka yi sallama har na kule tana Dagamin Hannu.
Tunda bai amince na biya karofi ba Daganan ma hau motar katsina,na koma gida hud'u saura sallah kawai nayi na fara kokarin dora girki Saboda yan makaranta ammh gabadaya sai ina jin jikina duk yayi wani irin sanyi komai nawa yayi sanyi kamar an zare ma jikina lakka.
Ko su Amir da suka Dawo makaranta sai da suka ga yanayi na Amir mai wayon ciki ne ya dinga ce min"Baki da lafiya ne Umma..?
Sai nace mai a'a saboda kada na tayar musu da hankali sai na warware na shiga cikin su mukaci abinci bayan sun gama mukayi sallar isha'i tare bayan mun idar nayi musu karatun Qur'ani na kara ma kowannen su inda ya ke sannan nace su yi na makarantan bokon su da aka basu amatsayin aikin gida.
****
Tunda Ya ishaq ya tafi bai Dawo ba sai ana Saura kwana uku D'aurin auran sa,sannan ya Dawo shima din gidan Mama ya sauka sai Dare na gansa,gari kuma na wayewa ya kara fita Jamal ya Dawo tare naga suna ta zirga zirgan karbo dinkuna Gidan Mama kuma ya fara cika da baki Badariya ta fadamin Hajiyar Dala ta iso tun jiya sannan da yan'uwan Mama na yamai ni dai ta barayina bana wani shiri Saboda ban ga abunda zan shiryamawa ba.
Ana jibi Daurin aure da yammah sai ga Anty Mamah da Halisa sun zo gida na karb'e su hannun Biyu Saboda suna da kirki Har Halisa ba ta Dauko Halin Anty Binta ba.
Na kawo musu ruwa kenan na zauna muna gaisawa,ba islamiya Saboda alhamis ne Su Amir suna gidan Mama dazu da Jamal ya kawo wasu kayan Shahen Ya Ishaq ya tafi da su Ahmad ne kad'ai tare dani.
Bayan