Showing 54001 words to 57000 words out of 96493 words
daraja ni ba..Kamar ni zaki rika gani kina D'auke kai kamar kin ga kashi..?ai ba gaba da ni kike ba ko Yayarku Asiya ba Sana'ata bace ballatana ke karamar alhaki kin raina uwata da yayata suna fada kina fada sannan ki rika shigomin gida kina raina min wayau bazai sabu ba..Kada na kara ganin kafarki acikin gidana Daga yau sai yau..In yar'uwanki zata yi zumunci dake in kun had'u awani waje ban hanaku zumunci ba ammh ba acikin gidana ba"
Ya karishe fad'a cikin nuna cin mutumci har yana nuna ta da Hannu,Yaya mariya tayi dariyan takaici kafin tace"Shikenan sakon naka..?
Ya daga mata kai Lokaci d'aya yana fadin"eh shikenan"
Yaya mariya ta gyara tsayuwa kafin tace"To ai ba saboda kai ko dangin ka nake zuwa wajen Fa'iza ba..Ku ai baku isa ba wlh Fa'iza yar'uwata ce baka isa ka raba jinin dake Tsakanina da ita ba gida kuma bazan fita ba sai dai kayi abunda zakayi"
Tafad'a cikin Jaddada mganarta cikin mamakinta yace"Haka kika fad'a..?
Ta daga kai kafin tace"Kwarai haka nace in kuma kana da yadda zakayi dani Bismillah.."
Kawai sai ta koma ta zauna kafa d'aya kan d'aya tana latsa wayarta cikin Fushi ya juyo yana kallona cikin Tsawa yace"Wlh ki Fad'ama yar'uwanki ta fice ta barmin gida tun kafin raina ya baci na hadata da jami'an tsaro.."
Na zaro ido cikin rawan murya ina fadin"Yan sanda.."!
Ko kulani bai yi ba ya shige bangaransa da Sauri ni kuma sai kawai na fashe da kuka da Sauri na karisa gaban Yaya mariya zan yi mgana kenan ta Dakatar dani da Sauri kafin tace"Kada ki ce Tak in na isa dake fa'iza in sha Allahu yau zan kawo karshen duk zalunci da yake miki acikin gidan nan"
Cikin kuka nace"Yaya mariya yan Sanda fa yace zai kira miki"
Tayi wani mirmishi kafin tace"in shi takamar shi iskanci na shanyesa na Dokesa ya Dade bai kira yan Sanda ba in yaso ya Dauko gabad'aya police din kasar nan gabadaya yau ko ni ko shi acikin gidan nan"
Tafad'a tana mai kara tabbatar min da mganarta nasan Halinta tana da kafiya da Taurin kai ban kara mgana ba ammh na tsorata sanin Halin Ya Ishaq na kasa zaune na kasa tsaye,Kawai sai gashi ya fito yana waya kalmar da naji ita ta Razani Cikin Fushi yake fadin"Yallabai gida na zasu zo akwai wata matsala ne..Ok sai sun kariso.."
Nasan zai aikata ba ni da Daraja a idanuwansa,ballatana Dangina su yi Daraja a wajensa zai iya aikata duk abunda yaga dama bai damu ba,kuma nasan bazai taba Saurarata ba sai kawai na zube gaban Yaya mariya na Hada Hannayena duka Biyu cikin kuka na fara fadin"Don Allah..Don Allah..Yaya mariya ki tafi bana so ya Tozartaki bana so aci mutuncin ki"
Yaya mariya ta dakamin Tsawa cikin fada tana fadin"Bazan fita ba ina nan inajiran duk abunda zai yi"
Shi kuma yace"Zaki gani sai kin raina kanki yau d'in nan"
Bana so wani abu ya faru shiyasa nake rokonta tatafi cikin wata murya tace min"Ni kike roko na bar miki gidan ki fa'iza saboda wannan azzalumin mijin naki..?
Lokacin da ta fadi haka baya falon ya koma bangaransa ganin bazata Fahimci ba yasa na tashi zan koma Shashen nasa sai gashi mun ci karo da juna,cikin sauri na rikesa ina Fadin"Don Allah kayi hakuri..Kada ka kira mata yan sanda"
Ba laifinta ba ne Goggo ne da suka zo Dubani jiya tace ta zauna na kara jin Sauki shine..Shine ma.."
Sai na kasa karisawa Cikin Tsawa yace"Shine me..?
Cikin In ina nace"Ta tafi da Ahmad tunda..Tunda na ya ye..s.."
Tas..! Kake jin karan marin da ya yarfamin sai d na yi gefe dafe da kuncina cikin Bacin rai ya nuna ni da Hannu yana fadin"Wacece ke da zaki yanke hukunci kan ya'yana ba tare da kin Sanar dani ba..?uban wa yace ki kai min yaro na wani waje? Ban miki kashedi kan hakan ba..?.
Nace ban miki kashedi kan haka ba Fa'iza..?shine kika aikata gaban kanki saboda kin raina ni ko..?
Yana mgana yana nunani da yatsa cikin bacin rai sai kawai na koma na durkushe ina kuka yaya mariya ta mike cikin Takaici da bakin ciki kafin tace"Ba dai Ubanmu kake zagi ba ko..?
Sannan daman ai dabba shi ke dukan matarsa wannan abun da kayi ya tabbatar min da cewa kai Dabba ne acikin mutane"
Ya Ishaq ransa ya baci ya taso mata itama ta taso da Sauri na shiga Tsakaninsu na rike Yaya mariya ina wani irin kuka kamar zan shide cikin Shakewar murya nace"Ki tafi..Ki tafi don Allah yaya mariya ki tafi.."
Yaya mariya ta kalleni kafin tace"Zan tafi..ammh ba ni kadai ba tare da ke Fa'iza yau zaki bar ma wannan azzalumin gidansa in kina da amfani in kuma baki da shi zai sani"
Sai na Rud'e na kasa mgana ta ja Hannuna keey kamar rakumi da alaqa zuwa Dakina ta fara Hadamin kayana tana yi tana fadin"Kin gama zaman aure in da ba'a san Darajan ki ba..da ikon Allah hakkin ki bazai barsa ba sai Allah ya saka miki"
Ni dai na kasa mgana sai uban kuka nake yi,Ta gama had'a min kaya cikin karamar akwatin Amir itama ta Hada nata kayan ta zura hijabi,Nima tace na Dauko Hijabi na saka ganin na kasa tashi yasa ta dauko min ta sakamin tajani,har zuwa Falo yana Tsaye hannayensa goye a bayansa yana Safa da marwa acikin Falon.
Yana ganin mu ya saki mirmishi kafin yace"Better..Ni bazan hanaki tafiya da yar'uwanki ba ni dai ban ce ta tafi ba in kuma tabiki wannan ra'ayinta ne sai dai ta sani in dai ta saka ta bar gidan nan to ta Rubuta ta barsa har abada"
Yaya mariya tace"To sai me..?ai daman ta bar sa har abada kenan wannan bakin gidan da bakomai cikinsa sai zalunci da mugunta da ikon Allah sai Hakkin Fa'iza ya Bibiyeka"
Ya ishaq yace"Sai dai hakkin kashe aure ya Bibiye ki dai..Sakarya wacce bata san inda ke mata ciwo ba..Na dai gama mganata ni dai in dai ta Fita to a bakin auranta sannan har Abada bazata Dawo ba"
Yaya mariya ta fincikeni tana fadin"Zaka gani yau kam zaman Fa'iza da kadaddaran auran ku ya kare"
Bai damu ba ya koma ya zauna ya Dora kafa d'aya kan d'aya ko ajikinsa,Yaya mariya ta rika jana har kofar Falo cikin Dashewar murya nace"Ban saka takalmi ba yaya mariya"
Cikin Fada tace"in mun je tasha na siya miki"
Na kara turjewa ina fadin"Yara na..Yaya mariya su Amir fa..?in na tafi wazai kula da su..?
Ta juyo tana min wani kallo kafin tace"Ko mutuwa zasu yi sai dai su mutu nan d'in ne gidan Ubansu ke kuma ai ba gidan naki uban ba ne wuce muje.."
Ta kara jana naki yarda na Bita na Turje ta juyo ta kara kallona afusace kafim tace"Fa'iza kada ki bari na saka miki Hannu"
Na kasa mgana sai kuka ya'yana nake Tunani in na tafi basu da wani Sauran gata bani da mafita sai zabin Dawowa na cigaba da zama acikin yanayin da nake saboda ya'yana.
Yaya mariya mamaki ya kara kamata lokacin da na kwace hannuna daga gareta na juya baya ina kuka nace"Ki yi hakuri..Kiyi hakuri..Ki tafi don Allah..BAzan iya tafiya na bar ya'ya na ba"
Kiyi hakuri"
Sai kawai na kwashi gudu zuwa Cikin D'akina ina kuka kamar raina zai fita kaina har wani bugawa yake yi Dif dif,Yaya mariya ta kasa motsi saboda abunda nayi Ya Ishaq kuma na zaune yana Dariya kasa kasa kafin ya mike yana kallon Yaya mariya cikin gadara yace"Fita ki bar min gida bakar munafuka..Kin dai ji kunya wlh kin kuma yi asara..Yar'uwan naki da kike Hakilo a kanta ta nuna miki baki da wata Daraja sama dani..Sai ki fice min Daga gida kada na kara ganin siraran kafafunki acikin gidana.."
Yafad'a yana nuna mata hannun alamun ta fice ta bar mai gida Takaici da bakinciki yasa Yaya mariya Zubar kwallah ta kalle shi ta kara kallonsa kafin tace"Naji kayi nasara a kaina zan tafi..kamar yadda ka bukata bazan kara zuwa gidan ka ba..Sannan mganar Fa'iza karyan ka ta sha karya ai jini yafi ruwa kauri sannan wata kusan tafi wata..Zan cigaba da zumumci da yar'uwata domin ba kai ka Had'amu ba..Mgana ta karshe shine akwai Allah kuma yana nan a madakata Duk abunda kake aikata ma Fa'iza na sharri da zalunci kai da Mahaifiyarka da yayarka,Da ikon Allah sai kunga sakkaya tun a duniya sai Allah ya jarabceka da iftila'in da sai ka rasa ina zaka saka kanka in sha Allahu sai Allah ya saukar da aya akan maza ire iren ka da basu darajan matan su sannan basa adalci ya yin zamantakewar su,Kuma kada ka manta akwai Hakkin zumunci shima sai Allah ya tambaye ka, sannan hakkin Fa'iza bazai barka kayi rayuwar da kake Buri ba Ishaq Kabir karofi."
Tana gama fad'in haka ta Sauke karamin akwatin na data Dauka,ta juya ta fice tana zubar da hawayen bakinciki da takaici duk da kalamanta sun Dakesa ammh bai damu ba ya Bita har get yana gayamata bakaken mganganu sannan ya Dawo Cikin gida ya Iskoni har dak'i yana gayamin duk mganar da ta fito bakinsa har yana fadim Tunda ya aureni bai Huta ba yake cikin Matsala ni ba matar kirki bace ni matar Tsiya ce.
Nayi kuka,kukan da ban taba yi ba,kukan yadda ya tozarta yar'uwata ni ban damu da kaina ba Daman ni bani da wata Daraja ammh Yaya mariya fa..?yar'uwata ce bata chanchanci cin zarafi da tozarci ba.
In da nagode ma Allah Yaran basu dawo daga makaranta ba,da suna gidan nan ban san wani amsa zan basu ba ina kwance ina kuka suka Shigo,Ganin su yasa nayi saurin share hawayena kaina ciwo yake yi duk yadda yaran suka so su fahimci wani abu ban basu dama ba da Amir ya dameni da Umma baki da lafiya ne..?naga fuskarki ta kumbura ne"
Sai nace masa wani abu ne ya fadamin a ido,Nasan inda Ya Ishaq ya mareni ne ya tasa sannan ga kuma kukan da na sha.
Tuni Ya Ishaq ya fice daga gidan na rarrafa na shiga kitchen na Dafa ma su Amir Jallop din taliya,kunyar kaina nake ji da abunda ya faru ace mijina shi ya tozarta yar'uwata da muka fito ciki d'aya uwa daya uba daya,Abun sai ya tsayamin a cikin raina ya kasa wucewa su kansu yaran su san yanayina ya sauya,suna mgana sai dai na bisu da ido kawai da wuri nayi musu shirin kwanciya Saboda ban jin Dadin jikina,Kamar kazar da kwai ya fashe ma aciki haka jikina ya koma,Kayana da Yaya mariya ta hada ni na kwaso su na maida su muhallinsu araina ina Tunanin Lokaci bai yi ba.lokacin da zan bar Rayuwar Ishaq bai yi ba akwai sauran Lokaci.
Ina D'akina zaune ina kuka ni kadai ina sharan hawaye na Ya Ishaq ya shigo Fuskarsa ba Fara'a,Ina ganinsa na Dago kawai ina kallonsa ina jiran naji dame kazo Saboda nasan wani Sabon Tozarci ne ilai cewa yayi gobe geben nan nasan yadda zan yi na karbo masa D'ansa kafin raina ya baci.
Jikina na rawa cikin rawan murya nace"Goggo ce ta karb'esa fa..?Sai naje nace ta dawo dashi..?
Cikin Tsawa yace"Ina ruwana da wata Goggo..Mama ce..?nace Mama ce..?
In ba munafunci kika so ba, meyasa baki aika ma Mama shi ta yayesa ba..?
To wa ma yace ki yayesa batare da kin Fad'amin ba..?
Kaina na kasa nace"Saboda bani da lafiya ne ina asibiti da kuma na Dawo sai yak'i karb'an Nono sai na yayesa kuma Goggo Saboda Tausayina yasa ta tafi dashi fa"
Karamim Tsaki yaja yana fadin"Kedai kika sani na riga na gaama mgana wlh in gobe da yammah tayi Ahmad bai Dawo gida ba sai na Wulakantaki Fa'iza"
Haka ya fice ya barni ina kuka,ina jin wani daci na tasomin a kasan raina ciwo nayi ba sannu ba Tausasawa ba Lallabawa sai tozarci da cin mutumci ya Allah ga baiwar ka Fa'iza ka bata mafita D'aya daga cikin mafitan da ka ke bama Bayinka salihai.
Adaran nan barci sai dai barawo ya iya Sace ni da Safe kuma da zazzabi da ciwon kai na tashi su Amir na da Hadda Dakyar na iya musu shiri da abun karyawan su,To basu samu ma tafiya makarantar ba Haruna adaidatan sa ya samu matsala Babansu kuma ko motsinsa ban ji ba,Ballatana na saka ran zai kai su,Sai kawai nace su tube kaya su bari sai gobe sai fadi suke Daada bazai kai mu ba nayi musu shuru kawai ina ji Anum ta je tana ta Buga kofar Shashensa tana kiran sunansa Ammh har tagaji bai fito ba.
Sai daga baya da Amir yaja su suka fara wasa ita da Musty sai ta manta ammh da farko har ta fara kukan ta na rigima..
Ni ko kwata kwata hankalina baya jikina Tunani nake yadda Ahmad zai Dawo kafin yammah tayi nasan duk abunda yace zai aikata ammh na gwammace ni na tozarta da na iya cema Goggo ta Dawomin da Ahmad bazan iya ba Har abada bazan iya ba.
Ranar ko girkin rana ban yi ba gari na jika musu suka sha,Nima ba na wani jin Dadi sai da na sha Panadol cikin mganguna na hawan jini kuma yana da karfi sai Dare nake shan sa.
Bani da masaniyar Ya Ishaq na gidan ko baya gidan,Bayan la'asar ina Dakina na idar da sallah su Amir suna Haraban gida suna wasa dakyar na saka su suka dawo cikin gida suka yi sallah wasa na ransu suka koma suka cigaba da yi.
Tashin mgana na rika ji afalo lokaci d'aya da kiran sunana zubur na mike jin kiran sunana kuma Muryan Mama nake ji tana tsagamin kira da karfi kamar zata tsaga gidan.
Na fito da Sauri muka kusa cin karo da Anty Binta ina shirin gaisheta ta bangaje ni ta shige Mama na Tsaye tana Karkad'a jiki kamar wata mazari Cikin Daga murya tace"Shiga ki fito mata da kayanta jiya bata bi Yar'uwanta ba yau kuma zata bita Daga baya fito mata da kayanta yau in dai ba gidan Sidi da tamadina bane sai Fa"iza ta barmin gidan D'ana"
Hankalina ya tashi jikina ya fara rawa na karisa gaban Mama na zube ina gaisheta bata amsa ni ba ta fito da wayarta ta kira,naji dai tana fadin gasu sun kariso daganan ta kashe wayarta ta koma ta zauna tana kad'a kafa Anty Binta kuma ta rika kwasomin kayana ta na min watsi da su a tsakiyar falo na zama mutum mutum na kasa mgana har Ya Ishaq ya fito Daga bangaransa yana sanye da Jallabiya ko barayina bai kallah ba ya isa ga Mama suka gaisa.
Cikin ko in kula ya zauna gefenta yana fadin"Mama meke faruwa ne..?
Yafad'a yana bin kayan da Anty take watso kayana da kallo Cikin Daga murya Mama tace"Zaman fa'iza a gidan ya kare Daga yau..!
Cikin mamaki yace"Saboda me ne Mama..?
Mama ta mike tana nuna ni da yatsa tana fad'in"Har saboda wannan gayyar Tsiyar gayyar matsiyantan ne za'a zo har gida aci maka mutunci muma aci mana wace ce ita..?taimakon ta fa kayi ita har ta isa..?
Wlh sai ta bar min gidan D'a na damam Darajan mahaifin ku take ci dama ta kai iwar haka ammh Tunda daga ita har yan'uwanta matsiyata ne yau sai na muna musu nafi karfin su..Sakinta zakayi ta kara gaba nagaji da Fitina nagaji Tunda ka auri wannan yarinyar tsiya da Jafa'i basu bar Bibiyan rayuwarmu ba,meye amfanin Mata irin Fa'iza..?
Dangin Talauci Dangin kurame dangin tsiya da tsiyataku..?
Nace meye amfanin mace irin ta..?.
Ai tunda basu san an yi musu alfarma yau zasu sani"
Ta karishe fada tana kumfar baki Shuru yayi bai yi mgana ba, ni kuma kaina na kasa ina kuka,Mama ta cigaba da zagina ni da iyayena da yan'uwana tana aibatana Iyayena barin ma mahaifina da yake kwance a cikin kabarinsa naga bazan iya Jurewa ba na Dago kaina cikin kuka nace"Mama ni ki zageni ni ce nayi miki Laifi ammh me mahaifina yayi miki da kike aibatasa yana kwance acikin kabari..?
Sai mama ta saka salati ta Dire tana Fadin"Ishaq kana jinta ko..?
Sai nace ka sakete zaka saki wannan tsinanniyar bakar yarinyar nan kenan..?
Ya Ishaq ya kalleni alokacin nima ina kallonsa ne, ba kuma Saboda ya barni ba ne ina kallonsa ne domin nasan zai iya yanke duk hukunci da Mama tace ai bata san abunda ya faru ba jiya shi yaje ya fad'amata..
Cikin Karsashin muryan sa yace"Mama ni ba domin Sarkan da Mganar Baba ta sakani aciki ba da Tuni na Rabu da Fa'iza domin na Dad'e da sanin ita ba matar kwarai bace Matar Tsiya ce..Sai dai kalaman Baba su suke zaune da ita acikin gidan nan sannan su suka cece igiyan aure na dake tsakani da ita"
Mama tace"Kalamansa baza su yi wani Tasiri ba ai baya raye yanzu"
Kai ya girgiza mata kafin yace"A"a Mama ki yi mata kowani Hukunci ban da na saki..Ina tsoron kada bakin Baba ya kamani in na Saki Fa'iza"
Hawaye suka gocemin zuciyata naji tana wani irin Zafi shi ya D'aga murya yana fadin"Anty Binta bar watso kayan nan haka kiyi hakuri.."
Anty Binta ta fito tana faman Hararata a kaina ta Tsaya ta saka Hannu ta Dago habana ta kwasheni da mari mai kyau Mama tayi kyafci tana fadin"Kara mata tunda bata da mutumci"
Ta d'aga hannu da niyyar kara marina suka ji kukan su Anum acikin Falo sai ta Dakata,ta d'ago tana kallon su suna bakin kofa atsaye Amir na kuka ammh na hawaye,yana rumgume da Anum da Musty dake kuka share share ganinsu cikin wannan Halin sai naji Rauni ya kamani kawai sai na Bude murya na fashe da kuka
Mama da Anty Binta suka saki baki suna kallona Ya Ishaq kuma sai ya mike ya nufe su yana fadin"My Anum"
Ya saka hannu ya riko Anum dake jikin Amir ta ture hannunsa ta nufeni da gudu cikin kuka tana fadin"Umma..Umma"
Sauran ma sai suka mara mata baya na mike zaune na Bude hannayena na Tari ya'yana da silar su ne nake zaune cikin wannan kaskastaciyar rayuwar.
Rumgumesu nayi kam ina kuka da dukkan zuciyata Anum kuma Musty ma haka Amir ne ke faman gogemin Hawaye na shima kukan yake yi sai na Dago kaina nima na saka Hannuuwana ina share musu hawaye Bud'e bakin Amir sai cewa yayi"Umma ki daina kuka in na girma zan rama miki Dukan ki"
Sai wani kukan ya kwacemin na Rumgume sa ina fadin"Ka da ka zama mai Riko Amir..Ka zama mai yafiya saboda Allah ma gafurun Rahimun ne..Ba