Showing 72001 words to 75000 words out of 96493 words
naso chan din zan ce Haruna ya kai su in suka dawo ban dawo ba.
Da asuba da na tashi ban koma ba ina gama shirya su na tafiya makaranta na Dafa musu abunda zasu tafi dashi makaranta,Tunda bani da komai sai nayi Tunanin na Dafa wani abu na tafin ma tamadina dashi,Shiyasa da kaina na saka Hijabi na raka su Amir kofar gida muka gaisa da Haruna na fad'amai zai kai su gidan Mama in suka Dawo da yammah ban dawo gida ba,Mahaifiyatace ba lafiya zan je na Dubata ya yi min Fatan Allah ya bata lafiya.
Na duka ina kallon yaran kafin nace"Zaku zauna gidan mama kafin na Dawo kun ji ko..?
Amir ne ya gyadamin kai Anum ce ta kwabe fuska tana fadin"Umma ki tafi dani"Na shafa kumatunta ina fadin"Zaku je Anum insha Allahu ku dai ku yi ta mata addu'an Allah ya bata lafiya"
Da haka na lallabasu suka tafi da Anum ta fara rigiman kayan sawan su ni kuma naga suna da kaya agidan mama bazasu rasa na sawa ba,Suna wucewa na shiga gidan Sa'adatu muka gaisa na gayamata abunda ke faruwa cikin tausayawa tace"Allah sarki wannan da kika kawo min ita muka gaisa ko..?
Na gyada mai kai cikin wani yanayi cikin jimami ta yi min fatan Allah ya Tada Kafad'a,na amsa mata Daman Nama nake so na siya sai tace min sai karfe tara mai naman bakin titi yake fitowa, sai na zauna muka cigaba da Hira sama sama Ahmad na bayana yana barci,Taran nayi muka yi sallama Daga gidanta na gangara bakin titi daga cikin Dubu ukun da Yaya Isa ya bani na siya Naman dubu Daya na koma gida na Dora jallop din Shinkafa,da nama daman ina da Cabeji sai nayi amfani da shi kad'an sai da nagama komai,na samu wata Tsohuwar cooler dina na zuba abincin aciki,sannan na je nayi wanka nayi ma Ahmad muka shirya tare,Atamfa ta na saka wacce Yaya Asiya ta dinkamana mu hudu,na Zura Dogon Tsohon Hijabina da yasha ruwa,kan duk ya kod'e da Takalmina duk yaji duniya ya d'aga tun wani Takalmi da Anty Nasara ta taba bani ne, yafi shekara hudu ina moransa don ma ban cika yawan fita ba,ai da yanzu bani da nasawa.
Rufe get din nayi da key din gidam,Na rike Dubu biyun da suka yi saura da abincin da na Dafa na shiga nayi ma Sa'adatu sallama sha daya da wani na isa gidan Mama,adaidaita na hau na sallame shi na shiga gidan ba kowa ina ta sallama Ashe Mama na falo tana faman kirga kudi sai dai ta ganni na shigo kamar daga sama hankalinta yayi sama bata ji sallamata ba.
Tana ganina kamar taga mutuwarta ta wani zabura sannan ta saka kudin hannunta kasan cafet din datake zaune,Tana wani zare ido tun kafin na kariso ta tareni da fadin"Lafiya ke kuma daga ina yarkace yarkace kamar yar gudun hijira..?
Gabanta na Duka ina gaisheta ta amsa a gaggauce tana kara fadin"Lafiya..?
Kaina na kasa nace"Dama..dama zan je Dutsemah duba jikin Tamadina ne"
Sai Mama ta gyara zama tana fadin"To ashe jikin har yanzu..?ni Goggon taku ta kira ni tace a fad'a miki na sha'afa tafiya ta kamani zuwa Yamai"
Ina jinta ban ce komai ba sai ta cigaba da fadin"Allah ya bata lafiya"
Na amsa da Ameen shuru dai taga ban tashi ba sai ta fara fad'a tana fadin"Wai ni kam sintirman me kika zo kika min a gabana..?
Da Sauri nace"Dama ina so su Amir zasu zo nan su zauna ne in na Dawo da wuri to..inkuma naga jikin nata yayi tsanani zan kwana shine..Shine nace bari nazo na fad'a miki tunda Babansu baya nan"
Har na gama Mgana Mama na bina da wani kallon banza sai da na Dire sannan ta karbe da fad'in"Daman ai tunda na ganki nasan banza bata kawo ki..so kike bayan na gama wahala dake na kuma dawo na ya'yanki..?to baki isa ba malama kije ki Dubata la'asar nayi ki kamo Hanya,Gida ba kowa Badariya ta shiga makaranta Jamal baya garin nima yanzu da kika ganni Hajiya Barira nake jira zamu fita ban san da wa kike so su zauna ba..Kuma Allah na gani bazan soke fitata saboda ke ba"Ta karishe fada tana tabe baki daman ai nasan za'a rina sai kawai na mike ina yi mata sallama ta bi kulan Hannuna da kallo kafin tace"Ke ke..Wannan abun fa ina zaki kai shi..?
Sai nayi mata kamar ban ji ba kuma na jita naki juyowa ina ji tana fadin"Aikin kenan shiyasa kayan abinci ba sa wata suke karewa ga inda ake kwashewa ana kaiwa ashe "
Daganan na jita sauran mganganun nata ban ji ba Domin na fice daga Falon Idanuwana na kawo ruwa naji Nadaaman zuwa ma.
Sai dai na fita Hakkinsu daga ita har Yaya Ishaq din.
Ni da naso naje tun da Wuri sai gashi sai azahar na isa Karofi chan na fara zuwa saboda ban san d'akin da suke ba,Ina ko zuwa na iske Yaya Isa zai kai su Goggo da matarsa da Anty Nasara Goggo na ganina tace"Ga ma Fa'izan nan ta iso..Sai mu rankaya muma asibitin zamu"
Sama sama muka gaisa na shiga Mota sai asibitin General na Bakin asibiti Tamadina na Female ward ne babban Dakin Yaya mariya muka iske a wajenta da Maman isuhu sai matan ya'yan su.
Muka gaggaisa da tambayan mai jiki sukace da sauki na Ubangiji.
Na kara rud'ewa da naga Tamadina kwance bata motsi numfashinta na sama sama alamun dai tana jin jiki na karisa gaban gadon na tsaya ina kallonta sai kuka na dafa Hannunta da ba karin ruwa ina fadin"Allah ya baki lafiya ta madina"
Goggo ce ta fara bani Hakuri sai na bar gaban gado nayi baya sai yau muka had'u da Yaya mariya tun bayan Tozarcin da Yaya ishaq yayi mata, kaina na kasa cikin jin nauyinta na gaisheta da Tambayan ya mai jiki tace da Sauki sai na sauke kulan Hannuna a gabanta ina fadin"Ga abinci"
Bata kalleni ba tace"Allah ya ba da Lada"
Bamu dade da zuwa ba Nurses suka zo suka fitar damu waje,muka fito baranda d'akin inda mutane ke zama masu jinya da masu Dubiya muma Tabarma Yaya mariya ta shimfida mana muka zauna Yaya Isa ya wuce wajen aikinsa.
Haka na zauna jugun jugum,sai da Yaya mariya tamin mganar salla,Sannan na tuna ban yi salla ba, na mike tace zata rakani masallaci Ahmad ya tashi Lokacin sai Maman Isuhu ta karbesa tace muje mu yi sallan mu dawo su za su yi nasu anan Tunda ga ruwa.
Yaya mariya ta dauko kwanukan da sukayi amfani da shi zataje chan ta wanke sai nayi saurin karb'a muka tafi ,Sallar muka fara yi sannan na yi wanke wanken,muka Dawo muka iske Maman Isuhu na bama Ahmad abinci Goggo ta kalleni tana Fad'in"Yaron nan naki rigimamme ne kuna tafiya ya fara mana rigima"
Ina dariya nace"Goggo har yaye fa kin masa..?
Goggo tace"Nasha rigima dai,don ma yana ganin idon Hafsatu ne. ita ai ya saba ganinta a gidan su"
Sai alokacin na tuna da Hafsah da na tambayeta sai Yaya mariya tace min sai ta taso makaranta zata zo.
Muna zaune ana ta hira sama sama duk rabin hiran na ciwon tamadina ne Maman isuhu tana fadin yadda ciwon ya fara daga zamewarta shikenan abu kamar wasa bata ko iya tashi komai sai an yi mata, suna mganar ni kuma ina faman share kwallah
Goggo tace"Abun ba dadi..Allah dai ya bata lafiya.."aka amsa da Ameen Goggo ke tambayana ashe Mama bata sanar dani ba..?nace bata gayamin ba Goggo ta jinjina kai kafin tace"Allah ya shirya Saudatu"
Yaya mariya na gefe tace"Itama karamar waya ya kamata a nema mata Goggo ace sai arika yin abubuwa mutum bai sani ba, yana chan shi kadai kamar wani mara gata da galihu"
Goggo tace"Haka Isa yace.bari dai komai ya daidaita bazai gagara ba"
Ana cikin tattaunawar ne sai ga Yaya Asiya ta diro ita da mijinta Dauke da kayan Dubiya katan din maltina da Ruwan gora,Ya duba jikin Tamadina bai jima ba ya bama Goggo dubu goma sannan yayi mana sallama ya tafi yana min tsiya da na gaishesa ya rike baki yana fadin"Wa nake gani kamar Fa'iza Asiya?
Tana dariya tace"Itace mana"
Sai kawai yace"Ke kan Fa'iza bakya zuwa ziyaran kano yaushe rabo na da ganinki..?
Goggo tace"Ai in dai Fa'iza ne haka take gidan kowa bata zuwa"
Bai tsawaita zencen ba ya karbi Ahmad yayi masa wasa yana tambayana Sauran yan'uwansa nace suna makaranta Dubu d'aya ya sama Ahmad a hannu kafin ya tafi Ya Asiya ta tafi rakasa.
Ni dai sai duba yanayin Rana nake yi Saboda la'asar nake son na tafi sai na kalli Yaya Asiya da ta dawo daga Rakiyar ina fadin"Don Allah karfe nawa..?
Yaya Asiya ta duba agogon wayarta kafin tace"Uku da rabi"
Sai na jinjina kai ba wanda dai yace wani abu sai da aka kira sallah mukaje mukayi sallah su Goggo kuma anan sukayi nasu sanda muka dawo an fara barin yan dubiya suna shiga D'akin.dukkanmu muka shige muna kara Duba jikin Tamadina ta nan a yadda take sai dai Numfashi,Bata ma sanin wanda ke kanta Yaya Asiya ta kalli Goggo tana fadin"Anya goggo bazamu sauya ma Tamadina asibiti ba..?
Ko dazu da naje raka babansu Usaini sai da yayi min zencen"
Goggo tace"To nima Isa ya cemin haka ammh ku bari an juma in megidan nasu ya zo sai muji ra'ayin shi"
Mganar Goggo yasa ba wanda ya kara mgana ni sai na zauna wajen kanta na sunkuya na rika karanta mata Fatiha da Suratul yasin sai Arrahaman goman Farko da ayatul kursiyu ina Tofamata a kanta zuwa kirjinta na dauki Wani Lokaci sannan na mike na rike Hannunta ina fadin"Allah ya baki lafiya Tamadina.."
Gabad'aya suka amsa min da Ameen sannan na sauke hannunta na gyara mata kanta saman filo na koma baya ina sharan kwallah Maman Isuhu na fadin"Sai hakuri..Allah zai bata lafiya"
Yaya Asiya da Yaya mariya suka hada baki wajen fadin"In sha Allahu"
Ahmad dake hannun Goggo na karba na goya Yaya mariya na ganin haka ta kalleni cikin wani yanayi kafin tace"Ba dai tafiya zaki yi ba Fa'iza..?
Sai na kasa bata amsa kaina na kasa nace"Tafiya zan yi sai gobe zan dawo tare da yaran gabadaya in sha Allahu"
Yaya mariya tace"Haka zaki tafi ki bar Mahaifiyarki cikin wannan Halin..?
In kafin Goben baki Dawo kin Tarar da ita da rai ba fa..?
Sai naji hankalina ya tashi Yaya Asiya ta daka ma Yaya mariya tsawa tana fadin"Haba Mariya wannan mganar bai kamata acikin wannan yanayin ba"
Goggo tace"To ban da abun mariya in ta zauna ai ba sauki zata saka mata ba..Ki barta tafi Dakinta ta kula da ya'yanta tunda gobe tace zata dawo..'
Yaya mariya sai ta juyar dakai ta fice Daga Dakin Tana fadin"Ai shikenan ta tafi..In ta rasu zata fi kowa kuka na sani Saboda itace kad'ai ta zabi miji da Danginsa fiye damu Ahalinta"
Sai kawai na Fashe da kuka Yaya Asiya ta kamani tana fadin"Daina kuka Fa'i haba Fa'i kamar baki san Halin mariya ba share hawayen ki,Ki tafi goben in Allah ya kaimu sai ki Dawo"
Na kalleta hawaye jage jage ina fadin"Ammh Tamadina bazata mutu ba ko..?zan zo na ganta ko..?
Har suna had'a baki da Goggo da Maman Isuhu wajen fadin Insha Allah sai na share hawayena nayi musu sallama goggo tace ina da kudin mota nace mata eh,har zan tafi Goggo tace na dawo na Dauki kulata tunda an juye abincin na koma na Dauka sannan na fice ina kara waiwayan ta madina.
A baranda naga Yaya mariya nayi mata sallama tayi banza dani bata amsa ba sai kawai na girgiza kai na wuce a bakin asibitin na Hadu da Hafsatu da kawayenta,muka gaisa tace har zan tafi nace mata eh sai gobe zan dawo mukayi sallama suka shige ni kuma na hau adaidaita zuwa inda zan hau motar katsina shida saura na yammah na isa gida ina sauka daga adaidaita Haruna na karisowa da su Amir sai da na sallami mai adaidaitan sannan na isa wajen su yaran suka sauko suka zo suka Rumgumeni nima na rikesu muka karisa wajen Haruna bayan mun gaisa yace min daga gidan Mama suke gidan ba kowa shine ya Dawo da su in ban dawo ba su zauna wajen Sa'adatu zai koma tunda bai tashi aiki ba..nayi mai godiya na tara ya'yana na bude gida muka shiga,Allah yasa akwai sauran shinkafar da na Dafama Tamadina shi na basu suka fara ci kafin nayi musu girki..
Anum tace min"Umma kakanki ta warke..?
Sai ta bani Dariya na rikota jikina ina fadin"Ba kakata bace kakarku ce Anum ni mahaifiyata ce Mamana kum, kamar yadda kuke da Umma nima ina da Mama"
Sai tayi dariyan su na yara batayi mgana sai nice nace"Ta ji sauki gobe zan kai ku gaisheta kuna son zuwa.?
Suka amsa mim atare,nan dai nace musu gobe da su zan tafi Anum sarkin yawo tana ta murna ita da Musty Amir kuma daman bai da Hayaniya.
Taliya na yi mana mai miyar Jajjage mukaci da daddare kafin mu kwanta kamar yadda na sakama raina ban yi musu shirin makaranta ba Saboda na saka araina tare dasu zan tafi in ta kama na kwana ne bani da matsala.
Kafin takwas na safe duk mun shirya na Dibar musu kaya kala daya dukkansu Ahmad kuma Biyu a wata jaka da Babansu ya siya ma Amir mai girma kuma tana da Hannu aciki na Dura kayan,Buga get din haruna shi ya fitar dani na gayamasa bazasu samu zuwa makaranta ba Dutsemah zamu je tare yayi fatan samun sauki ga Tamadina ya wuce wajen sana'arsa.
Karfe tare muka fito na rufe gidan muka shiga nayi ma Sa'adatu sallama ta karbi address din asibitin tace zata yi ma Habiba mgana zasu zo in sha Allahu nace Allah ya yarda.
Ina da kudi dubu da wani abu a Hannuna zasu ishemu na Dawowa kuma bazasu gagaremu ba,Ni na zauna na dauki Anum da Musty a jikina Amir kuma nace ya zauna a inji saboda Saukin kud'in mota,goma da wani abu tama na a bakin asibiti ina Rike da Hannun Anum musty kuma Amir ne ya rikesa tunda d'ayan Hannuna na Riko Jaka muna tafe ruk'i ruk'i har Dakin da aka kwantar da Tamadina sai dai gabana yayi tsalle waje d'aya sanda naga ba itace bace akan gado sai ma wata mata da nagani.
Na rud'e dakyar na iya gaida gadon na kusa da Inda Tamadina ta kwanta. sannan na tambayesu mai gadon nan,Mara lafiyan na kwance bata mgana, masu jinyata ne guda biyu suka kalli juna in ban manta ba, jiya ma na gansu tare muka yi sallar La'asar da D'aya daga cikin su kamar daga sama mai kibar ciki tace"Ya ku ke da ita..?
Duk da sun ga kamannina da Tamadina cikin rawan baki nace"Ni yarta ce jiya ma ai nazo"
Kamar saukan aradu haka naji mganar"Ayya ai ta rasu yau da asuba kila ma an"
Bata karisa ba ta kusa da ita ta Rufe mata baki sai na kwalalo ido ina fadin"Eheee.."
Kamar ban ji ba sai naji lalurata tayi girma kunnuwana sun toshe bana jin komai Sama sama naji ana fadin"To ko ban gayamata ba,zata sani gwara taji tun yanzu"
Sai wata murya tana fadi'n"Ba haka ake fadin mutuwa ba sai ki barta in ta karisa gidan sai taji"
Ni dai bazan iya cewa ga yadda na iya fitowa daga asibitin nan ba, na dai tsinci kaina a bakin asibiti ina Shatatan Hawaye na manta da su Amir dake tare dani,Sai da naji muryan Amir yana fadin"Umma umma.."
Sannan na dawo hayyacina na juya ina kallon sun yi tsuru tsuru sai na Share hawayena na sunkunci musty na Saba ina rike da jakar kayanmu muryata shake nace"Amir rike ma Anum Hannu"
Gaba nayi ban tsaya bi ta kansu ba yau,ina dai jefa kafane kalaman Yaya mariya na dawomin da cewa in tamadina ta mutu sai nafi kowa kuka,Saboda Halin da nake ciki Tun daga Bakin asibiti har anguwan su Tamadina anguwan mallan yusuf Dutsemah a kasa muka je shi Anum ta gaji da kiran Umma ban ko amsa ta ba, nagaji bata kanta nake yi ba shi kanshi Amir din ya jigata ni kuma nafi su wahala ga Goyo da Musty ga Jaka ko da muka iso futu fitu kamar wad'anda suka fito daga Cirani kofar gidan cike da maza masu karban gaisuwa ni bana wani gani sosai ban iya gane kowa ba ina gaba su Amir na bin bayana har Cikin gidan da Mata suke cike Damkam ni dai so nake na isa Dakin Tamadina na tabbatar da ta rasu ne ko wasa ne..?
Ban san me matan da na wuce a tsakar gidan suke fad'i ba sai da na Dangana da Dakin Tamadina naga Mutane zazzaune suna ta kuka Goggo na fara Hangowa tana ganina ta Dago tana fadin"Ga fa'izan ta iso ma ba ma sai Isan yaje Dauko ta ba"
Jakar Hannuna na Sauke tare da Musty na karisa gaban Goggo na Duka ina fadin"Goggo kada kice min da gaske ne abunda aka fadamin a asibiti wai Tamadina ta rasu..?
Ina mgana sai hawaye sharr Goggo ta rike kafadata tana fadin"Sai hakuri Fa'iza duk wani mai rai mamaci..Tamadina ta amsa kiran Mahallincinta yau da asuba basu jima da dawowa daga makabartan ba"
Ni dai naji ni na sulale jikin Goggo na fashe da wani kuka,Kukan da yasa Dakin ya rikice Ahmad dake baya na ya fara kuka jin na Dannesa haka ma Musty da Anum Amir ne kawai bai saka kuka ba Goggo ta jani ta sunce goyon ta Dauki Ahmad,Ya Asiya kuma ta mike tana sharan kwallah tana Fadin"Hafsatu riko Amir ga shi chan"
Dukkansu kukan suke yi ammh na zucci ta mike ta rikosa suka zo suka zauna sai ya kalleta yana fadin"Anty Hafsatu Maman Umman ce ta mutu.?
Sai ta gyada mai kai Lokaci d'aya ta Rumgumesa tana kuka.
Bansan adadin Lokacin da na Dauka ina kuka ba, nan da nan wani malolin abu yazo ya taremin makoshi ya kasa wucewa hakuri kawai su Goggo ke bamu Daga baya sai kuka na ya Dauke sai dai Tafarfasan zucci kawai.
Har washegari ban iya saka komai abakina ba Hafsatu ce ke ta Dawaniya da su Anum,Ahmad kuma yana Hannun Goggo har ta da su Yaya mariya sai da na dawo ina basu tausayi suka koma suna Lallashina naci wani abu Dakyar adaran na sha Farau Farau sai dai ko minti goma bai yi ba acikina na amayar da shi na koma ina Numfarfarshi
Bakina