Showing 90001 words to 93000 words out of 96493 words
kenan auran mace mai kyau da samun ya'yan Turawa,ga shi ya samu sai kuma ya fara ganin mike ai bazata sabu ba,Anty Binta da Mama kamar su mutu da bakinciki ba so su Zainab din ta sakarmin ba sun so yadda suke min wulakanci itama ta wulakantani sai Allah ya fisu.
Ammh duk da haka basu kyaleni ba, su dai in basu tozartani ba basa jin Dad'i a gaban Ishaq din da Jamal da yace cikin satin nan ya dawo Badariya ce kad'ai bata nan tana gidan Anty mahma,Allah yasa yaran suna chan suna wasa hankalin su baya kanmu Mama ta kalleni cikin yanayin kaskancinta gareni tace"Ke kuma wani gantalin kike zuwa kwanaki Binta tayi ta zuwa bakya nan..?
Sai na maida kaina kasa na kasa mgana Domin nayi alkwarin bazan ce mata komai ba..
Anty Binta ne tace"Ai bazata fada miki ba ta fara zama gagararriya.Shi kan Shi Ishaq din ta fara fin karfinsa,da na kirasa na fad'amai ga halin da ake ciki bude bakinsa sai cewa yayi na kyaleta tayi duk abunda taga dama"
Mama tace"Uhm nima ai haka ya fadamin sai na kawo ido na saka musu daga shi har ita.Ni damuwata d'aya in ta fice ta bar masa gida ba kowa a shiga a sace wani abu ai shi ke da asara ba ita ba"
Kaina na kasa ban dago ba araina nace ina abun sata a wannan gidan..?shi kan shi yasan bai ije komai ba kamar yadda ban yi mgana ba shima kala bai ce ba sai faman dannan waya yake yi ita kuma Zainab waya aka kirata daga gidan bata tashi daga Falon ba ammh ta sauya yare zuwa Fillanci..
Nan Mama tayi nata cin mutumcin Anty Binta na tayata daga karshe Mama tace"Ai tunda Uwar su ta rasu naga tana wani tashen iskanci, mutuwa ai d'ayace kuma duk abun ki dai baki isa ki dawo da ita ba.Ni Allah na tuba mq cewa nayi gwara da ta rasu ta Huta rayuwa ko'ina ba inda tayi kyau"
Subhanallah na fada a fili na Dago ina kallon Mama bata damu ba tacigaba da Fadin"Shiyasa yana kirana yace suna tafe nace ya sauke Zainab anan yadda bata jin dad'in nan ga shi Fa'iza kuma ta saka Mugunta a ranta ai sai ta bar Yar mutane ta shiga wani Hali mu shiga uku"
Anty Binta tace"gwara da kika yi haka Mama"ni dai ban ko kara Dago kaina ba,zaman duk ya isheni ga shi Badariya bata nan zainab kuma tana gama waya ta tashi ta shiga ciki zata kwanta Yaya ishaq ya bita har sai da na gaji da jiransa sannan ya fito yaran har sun fara barci,Mama Tuni ta Dauke Farhan ta shiga da shi Ciki Musty da Ahmad ne suka yi barci nan saman Cafet ammh Mama bata damu da su ba,Anty Binta ta rigamu tafiya mu bayan mun fito Mama ta kira Yaya Ishaq ya koma ciki fiye da minti goma sannan ya fito muka tafi har muka isa gida ci kanki bai ce min ba nima haka, Domin naga yana wani shan kamshi ne da cin mgani a raina nace Indai ta fa'iza ne kayi a banza domin ban ma san ka nayi ba.
A satin yara suka yi Hutu daman sun gama jarabawa,karshen Team,Na lura wannan karon zasu dade tunda bayan zainab ta kwashe Kwana hudu gidan Mama sai ya maidota gida nan shashen shi inda ta fara sauka,su Anum nata murnan Farhan ya Dawo gidansu da kuma suka Dawo sai naga baya cewa nayi abinci da su, sai dai ya Rika fita yana siyo musu nima sai na kama kaina.Daman ba abincin gareni ba Shinkafa kad'ai ta ragemana itama Saboda wanchan cefanen ya siyo ta da yawa ne,Yadda bai nema ba nima ban Tusa kaina ba,Sai dai ina na shiga kullum da Safe mu gaisa da Zainab wani Lokacin ita takan fito falo mu gaisa har mu taba hira tana da Sakin jiki komai ta gani sai tace Maman Amir kaza maman Amir kaza.
Shi megidan nakan gaishe sa, sai dai ba kullum yake amsawa ba sai yaga Dama ni ko ban damu ba saboda ban ga abun da nayi mai masa da zai nemi kara Rataye ni a sama ba,Farhan kuma ya zama d'an wajena nike dawaniya da shi har kwana yana yi a wajena,nasan Ko Yaya ishaq din yayi mgana ita Zainab zatace ya kyalesa a wajena Saboda ta taba cemin wai bana gajiya da goya yara da Dawaniyar su..?
Ni kuma sai nayi Dariya nace mata ina son yara, kuma Dawaniyar su bai taba bani wahala ba. cikin mamakina tace zata kawo min Farhan nan da zarar ta yayesa bata son wahala ga aiki bata zama Allah yasa ma tana da mai renon sa ,ko ta kaisa gidansu a bakinta nake jin dukkansu sun samu Hutu ne shiyasa zasu fi sati kafin su koma.
Ranar da suke da kwana takwas da zuwa sai ga Goggo da Yaya isa,ya sake kawota na rika ina zan saka da Goggo da tazomin da su garin kunu garin Tsaki da garin masara,yaji kayan kamshi wake mangyad'a da su manja,sai garin Danwake da Taliya yar Muji ina ta Murna sai dai ashe zan ninka Murnata Dubu Dari.Goggo ta kawo min tace Dubu Hamsin ya'yan Dakinta suka hada'min Dubu Hamsin yan'uwana Yaya Asiya da Yaya Mariya har da Hafsatu ta saka Dubu Biyar kunsan na fada muku tana kunshi kuma Sosai take da mutane.
Kuka ya gocemin na karb'i kudin ina Fadin"Duk ni kad'ai Goggo.?
Goggo tace"Duk Fa'iza ita kad'ai yar gatan Mutanen karofi sun ce ki kara jari.Allah ya sanya ma wannan sana'ar da zaki fara albarka"
Na amsa da Ameen ina zuba musu Godiya ni muna Dakina ne ni da Goggo shi kuma Yaya isa yana falo shi da su Amir.
Sai da muka fito domin muji shawaran Yaya Isa kan abunda za'a siya,Goggo ta lura da Farhan ta tambayeni waye nagayamata sai ta rike baki tana fadin"Ikon Allah girman dan mutum ba wuya.."
Ta daukesa Dayake ba shi da kiwuya sai Dariya yake mata Goggo na shirin mgana sai ga Yaya Ishaq ya shigo falon da farko yayi mamakin ganin su Goggo, Daga baya sai ya basar ya kariso suka gaisa da Isa. ya kuma gaida Goggo sannan ya shige shashensa Goggo ta kalleni tana Fadin"Har amaryan nasa na gidan kenan..?
Nace"Eh tana ciki ko zamu je ku gaisa ne.goggo itama aiki akayi mata aka cire tsakuwar ciki fa"
Goggo bata damu da cewa bai taba kai mata Zainab ba,tace min sai mu shiga ta Dubata kafin mu wuce yanzu dai mu fara abunda ya kawomu.
Su Anum na fattaka zuwa Waje Farhan ya sauka a hannun Goggo ya Bisu duka kudin na zube ma Yaya Isa bayan nayi mai godiya sannan nace"Yaya isa ni dai a siyamin babban Fridge saboda zan fara gwada zobon da kunin ayan nagani"
Yaya isa yace"Hakan shine Daidai ne Nayi mgana da wani abokina suna kawo su masu kyau daga Parthercourt, kayan suna jirgin ruwa sun kusa isowa yanzu abunda za'ayi zan tura masa kudin fridge din da katon sitafileza,Tunda kuna samun wuta basai kin had'a da injin ba. Sauran kudin kuma sai ki rike a Hannunki saboda siyan abubuwan hadin da zaki fara sana'ar da shi ko ya kuka gani..?
Goggo ta jinjina kai kafin yace"Hakan ma yayi.Allah yasa zata fara cikin nasara"
Muka amsa mata da Ameen nan take ya kira abokin nasa sukayi mgana yace a turamai dubu Dari da Hamsin dubu hansim sai na rike a Hannuna,Muna cikin mganar sai ga Yaya Ishaq ya fito ya sake fita ko sannu bai ce mana ba, muma ba wanda ya kara bi ta kansa, kamar yadda bai taba tambayata ba nima ban taba Tunanin na fadamai komai a kan abunda na je na koya ba
Da gaske nake yi na zab'i Rayuwata da rayuwar ya'yana sama da nashi muradin.
Bayan Yaya isa ya cire kudin sai ya bani Dubu Hamsin a hannuna,sannan suka yi shirin tafiya har Goggo ta manta na tuna mata na rakata har Shashen Yaya ishaq,Zainab din na ciki ni na leka nayi mata mgana ta fito tana mika nace mata Goggon mu ce tazo Daga chan karofi, bayan sun gaisa Goggo ta mata sannu da jiki ta amsa tana kallonta Lokaci d'aya tana kallona kafin tace"Ammh suna kama da Momyn kano sosai Maman Amir"
Sai nayi Dariya kafin nace"Eh kanwartace fa Goggon"
Sai ta rike baki tana fadin Honey bai taba min mganarta ba.Dagani har Goggo yake mukayi mun kasa bata amsa,Tana tambayana yadda muke nace mata da goggo da Momnyn kano da Mahaifin su Yaya ishaq da mahaifin mu Uban su d'aya,Ta jinjina kai cikin karin mamaki daga gani bata san wani abun ba sai abunda aka nemi ta sani kawai ta sani
bamu jima ba Goggo ta mata sallama muka fito ta Daura After dress saman kayanta ta fito anan ne ma Yaya isa ya taba ganinta suka gaisa nace mata Babban yaron Goggo ne ta jinjina kai tana fadin"Suna yana yi da Honey"
Sai da ta fad'a na kara kallon Yaya isa naga suna da'n dibar kama kamar yadda ta fada d'in.
Mun rabu da su Goggo kan sai an kawo Fridge din Yaya isa zai kawo min Goggo tace na aika makotan mu na kusa nace zan fara saida Zobo da kunun aya da ruwa, saboda na samu masu siya aiko ban zauna ba su Goggo na tafiya na zari Hijabi nace ma zainab zan fita yaran kuma sukace sai sun bini Amir ne kad'ai ya zauna a gida haka na tasa har da Farhan gidan Sa'adatu na fara shiga na isketa tana yin shasshaka,kusan yara da Rigima su Anum suka saka Rigiman sai sun ci ina zare musu ido tayi dariya kafin tace"Kaji maman Amir kina zare ma yara ido ku zauna a gama sai kuci"
Dariya kawai nayi ta mana shimfidar Tabarma a tsakar gida Farhan ta Dauka tana fadin"Basu koma ba kenan..?.Sai na Daga mata kai, Saboda ranar ta shigo taga zainab din sun gaisa sai a ranar tasan ma ina da Abokiyar zama,domin ko a hira ban Fad'a mata ba.
Tana aikinta muna Taba hira cikin Hiran nan ne nake gayamata sana'ar da zan fara tayi murna cikin Murnan ne take fadin"Aiko zan aika miki kusa damu ana siya fa a baya, chan gidan akwai matar da ta zauna tayi sana'ar kuma wlh tana samun ciniki da kuma suka bar anguwan sai ba wanda ya kama gashi muna samun Wuta sosai za'a siya in sha Allahu"
A fili na furta Allah yasa daga shiga na gayamata sai ga shi na shantake ba yara ba nima sai da ta zubo mana Shasshakan muka ci da manja da yaji. sannan na Tarkata su muka koma gida Yaya Ishaq da Zainab na Falo suna cin gashashiyar kaza, yaran suka nufesu ni kuma nayi dakina Zainab ce kad'ai tamin mgana Gogan kuwa ko kai bai ma Dago ba.ni ko a jikina nasan yana mamakina ya Dauka irin da ne da zan rika binsa jikina na bari yana min wulakanci,Sai dai yanzu shi kanshi yasan takun ya sauya.
Sati biyu suka yi a katsina suka koma Abuja,har na fara sabo da Zainab sannan ga Farhan, da zasu tafi Yara har da kuka shima yaro ai yafi son inda yara yan'uwansa suke. shima Rigiman ya saka Uban ya lallashesa Dakyar,Anum kuka Musty kuka suma sai sunje sai Zainab tace na had'a musu kayan su ta tafi da su kamar zan ce a'a sai kuma naga bani da wannan Hurumin balle da naga Uban gayyar bai ce komai ba., sai na shiga Daki na Hada musu kayansu a jaka,ba masu yawa ba saboda bana so su rasa din Tahfiz din su,Allah ya taimakeni Ahmad na barci da shima za'a sha Rigima da shi.
Ji na yayi ina fad'a ma Zainab kada su Anum su jima saboda hadda Karaf ko sai a kunnensa cikin Kaushinsa ya kalleni kafin yace"Kada ki kara nuna min iko akan ya'yana Fa'iza, ki kiyaye ni Wlh"
Har yana nuna min hannu a raina nace shi kuma wannan me akayi masa..?sai nayi kamar ban jisa ba. Saboda Zainab da ya'yana yasa nayi musu Rakiya daganan gidan Mama suka biya suka musu sallama sai gida ya zama Dagani sai Amir sai Ahmad.
Sun tafi ko sati ba su yi ba Yaya Isa ya kawomin Dankareren Fridge dina da Starplayzer,murna ta kamani sai da nayi kwallah na Shafa na taba nayi addu'an da Fatan nasara da Yaya isa zai tafi nace yace ma Goggo Hafsatu tazo ina nemanta haka ko akayi washegari sai gata ita nasaka ta zauna ta Rubutamin duka abunda zan bukata, ina so mu shiga kasuwa na siyo kayayyakin mahad'in sana'ar mai yawa yadda zai jima bai kare ba.
Kamar Badariya tasan ina nemanta sai gata tana ganin Fridge din tace"Allahu akbar Anty Fa'iza wannan abun arzikin haka.?
Ni dai sai Dariya nake yi,Farinciki ya kasa boyuwa a saman fuska ta, albarka tayi ta sakawa itama, sai bayan ta zauna nayi mata bayanin kudin da aka had'anin Daga Korafi taji dadi tace"Allah yasa a mizani"Zuwanta yasa sai ita da Hafsatu suka dinga tsara yadda komai zai fara sun yi mganar goruna, nace ina da wasu da na tara Badariya tace duk da haka za'a karo Saboda abun fa so suke ya habaka kuma ya shahara.
Hafsatu tace"Kuma nan gaba kad'an har da Sticker zata buga a saka sunanta ajiki"
Badariya tace"in sha Allahu muna fatan ya zagaya nageria gabad'aya wannan kunin ayan da zobon namu ai ba irin nasu ba ne"
Dariya nake ta yi musu naga sun fi ni zagewa,Ranar bamu je kasuwan ba sai Washegari Badariya ta dawo muka tafi mu uku dayake nasan abubuwan hadawar shiyasa sai siyayyan bata Dauki Lokaci ba kudi basu fi dubu Goma ba suka Rage bayan mun Dawo gida mun siyo sabbin Goruna,na wajena wanda na Tara Hafsatu ta wankemin su tas a daran na Dafa ganyen zobon da Safe kuma na Had'a shi ni da Hafsat muka dura su a gorinaa muka saka su acikin Fridge dayake ba waje a kitchen falo na ijiyesa, kunin aya kuma nace sai naga yadda wannan ya fara karbuwa Ruwa daman Tun jiya Hafsatu ta saka aka siya aka Dura aciki.
Bayan yayi sanyi na Dauka na aika ma Sa'adatu da Habiba guda uku uku, Dayake Hamsin hamsin nayi saboda Farkon Farawa ne,Shi lamarin Ubangiji daman haka yake ballatana ga wanda yasan Allah ke yi sannan ya maida lamarinsa a wajen sa, cikin Sati uku da fara sana'ata sanu a anguwanrmu,balle su Sa'adatu sun ta min tallah,Da D'aya d'aya Biyu biyu aka fara zuwa siya sai gashi an gane ni, da ina yin na mudu da rabi na zobo sai na Dawo na Tiya har da rabi,Ni kad'ai nake abuna Hafsatu ta koma gida Karofi Satin su Anum hud'u babansu ya Dawo da su kwana D'aya yayi ya koma kuma yaga komai tunda yana gidan masu siye siye suke shiga suna fita yadda bai min mgana ba nima ban damu da yasan komai ba,To ina ruwan kaska da kifi..?
ni alokacin ma Sabgan gabana ta isheni.
Ko wata biyu ban rufe da farayin zobo ba na fara had:awa da kunin aya, Ruwa kuwa Mota ke saukemin Haruna yayi min Hanyar motar ruwa take kawomin har Kofar gida tana Saukemin.Saboda Hidiman yara sun koma makaranta yasa sa'adatu takan shigo ta tayani Wani Lokacin kuma Badariya na lekoni,Itama ta bangaranta ba abunda zan ce mata sai godiya tunda taje da shi makaranta kawayenta suka sha suka fara santi, Tundaga b'atagwara suke zuwa siyan zobo na da kunin Aya na, Har kuma Lokacin Mama ko Anty Binta basu san halin da ake ciki ba.
Ban rufe wata shidda da fara wannan sana'ar ba,na sanu sosai a rana na kanyin zobo fin ma Tiya hud'u kuma ya kare,Sannan na chaba Lokacin azumi nayi ciniki,sai na Dafa zobo sau biyu arana kunin aya kuwa na Tiya Biyar shidda duk yana karewa Musamman daga gidansu Raliya Direban su ke zuwa ya siya fin na Dubu uku in ji Hajiya balle da yake sanyi ga Dad'i ga gard'i sannan cikin Tsafta ba kazanta.
Na aika da shi har Karofi Goggo da su Yaya mariya sun sha sun kuma saka albarka,Yaya Asiya ce kadai bata sha ba tayi nisa,na yarda da mutane da suke fadin in kana da abun yi na sana'a damuwa ma bata da wani muhalli a wajenka,to hakan ne ya faru dani ne, ni mantawa ma nake yi da ina da wata matsala tunda nasan dadin Goma Biyar shikenan Rayuwata ta sauya Daga duhu zuwa haske cikin Lokaci kalilan Allah ya Daukakani,Sannan nayi amfani da Damar haka na tallata ma mutane na ina had'a Turaren wuta humra da na Kamshin Daki, da kwallacha sannan ina yin Dikar Amare da Halawa.
Duk da Ribar zobo da kunin aya na siya kayan amfanin wannan bangaran,Aiki na farko da na fara na Hajiyar su Raliya ce diyar kanwarta zatayi aure ta bani kwangilan had'a Turaren wuta na Rushi da na Humra,Sannan ni nayi ma Amarya Gyaran jiki,kuma ta bani kwangilar abinci,Kafin na rufe shekara na yi suna ta wannan bangaran Domin ina yin Girki a gida in dai bai wuce Takeway ashirin ba ko Hamsin,in ya wuce haka sai dai naje gidan masu sha'anin sai dai bana kwana wasu ni nake siyan komai na girki sai dai su bani kudin a Dungule in kuma yana da yawa sai dai na amshi kudin sallama.
Taimakona D'aya da Hafsatu ta gama jarabawarta ta Dawo wajena ta na taimakamin,Su Mama sun ji na fara sana'ar kunin aya da zobo, to azaton su Sana'ar bata D'ore ba shiyasa basu damu ba.shi kuma Yaya Ishaq yana ganin komai ammh kamar an Daure masa baki bai taba min mgana ba, nimana zama Busy women ban da Lokacinsa balle na tsaya masa bayani.
Sai dai na gayamai sana'ata ta jama'a ne,sannan ina zuwa kasuwa kuma in fita ta kamani ta bangaran kwangilan girki zan fita,sai yace min ai na zab'i Rayuwata sama da aure nayi duk abunda naga Dama babu ruwansa dani,tunda yace haka na fita Sabgan sa,to ni zai gayama aure..?
Auran da a D'ofane ya ke..?
Daganan ban kara bi ta kansa ba harkan Gabana nake yi,Ya'yana kuwa ba na yarda na shiga Lokacin su ko ya yane ina basu Lokaci na domin sune dukkan karfin gwiwata.
*******
*BAYAN SHEKARU BIYU..*
Katsina.
*Layout*
8:12pm.
Zaune nake saman sabon gadona da ban