Showing 21001 words to 24000 words out of 96493 words
Hajiyar Karofi Sai ga Baba ya zo shi da Ya ishaaq,wanda ya gama gudun nasa ya Dawo jiya da Daddare ya samu labarin An daura masa aure dani Ya Ishaq ya kasa katabus domin Baba ya Daga mai murya yace in har yaki karb'ata a matsayin mata to sai dai ya chanza wani uban ba shi ba.
Wannan mganar shine Sarka na Farko da ya fara kulle aurena da ya ishaq,Baba ya bama Goggo kudi ta yi min siyayya sannan ya kama mana Haya a katsina cikin gari in da zamu zauna ni da Ya Ishaq,har suka tafi ban gansa ba shima bai nemi ba,Tun kuma Daga Lokacin Baba ya fara shirin Tarewata Mama kuwa tayi Kukan har tagaji ta Saduda ganin Da gasken Baban bazai fasa ba.
Kafin Ranar arba'in din Hajiya karofi hatta jere na Goggon Karofi da ya'yanta da Yan'uwana sun gama min komai Domin Baba yace ranar addu'ar arba'in Zan tare agidana Yaya Mariya ita takaini gidanta ta tsifemin kai ta wanke ta kaini akayi min kitso da Kunshi Ina ta ce mata ta barshi kunshi da gyaran jiki sai Mata masu kyau ba irina ba ban taba manta kalamanta alokacin Kaina ta Dafa kafin tace"Kema kina da kyan ki Fa'iza sai dai in ba'a gansa yanzu ba ne..Ammh na tabbatar miki nan gaba zasu ga abunda nake gayamiki"
Alokacin mirmishi nayi mata Domin nasan ta fada ne ni kaina nasan bani da kyau sannan ina da nakasu ta bangaran Ji na da mganata
Aranar da Hajiya ta cika kwana arba'in a kushewarta ranar na Tare agidan Ya ishaq aurena ba irin na mata masu kyau da gata ba ne,Daga ni sai kayana da Goggo ta d'inkamin Sabbi ita da Baba domin da Goggo Taso su yi min Rakiya sai ya Ishaq yace baya Bukata dagani sai shi a mota sai Baba da Direbansa.
Daga Mama har ya'yanta ba wanda ya Leko karofi,Baba da kansa ya shiga Dani karamin flat din da ya kama mana mai Falo da Dakuna Biyu sai kitchen da Tsakar gida,Shi ya damka Amanata Hannun ya Ishaq da karin wasu manya manya sarkunan da Tun abaya na fada muku su suke rike da wannan auran namu yau har da nike baku wannan Labarin,Domin cikin kaukkausan murya yace mai"Ishaq ga Fa'iza nan na baka auranta ba Domin ta rasa me son ta ba sai domin cika Muradin mahaifiyata..Wlh tallahi ko da Rana daya in ka zalunce ta ban yafe maka ba Ishaq..Kuma ko da rana d'aya kabi Hudubar mahaifiyarka ka Tozarta Fa'iza shima nace ban yafe ba..Daga karshe matarka ce ta sunna ka Kula da ita kuma in ka Danne mata Hakki Allah na kallon ka sannan nima bazan yafe maka ba Sannan kasani Ranar gobe kiyama bazaka Rabauta ba Ishaq in dai ka saba ma Umarnina.."
Kafin ya tafi sai da ya kara Jadaddamai in ya danne min hakkina na aure ko guda d'aya ya sani bazai kara samun albarkarsa ba,ya tafi bayan yayi min nasiha hakuri sannan ya sanar dani na zauna nayi ma aure Biyayya bazan taba Tabewa ba Duniya da Lahira Tabbas wannan Biyayyar da Baba ya Rokeni har bayan mutuwarsa ban sauka daga kanta ba,nima ita ke rike dani acikin rayuwar aure na da Ya Ishaq.
Warware tarin kalubalen da na Fuskata a zama na da Ya Ishaq abu ne mai yawa da bazasu fadi a cikin k'urarren Lokaci ba sai dai abu d'aya na Sani mun yi zama ne na Biyayyar Iyaye shi Mganar Baba ke rike sa da Bakinsa a kansa nima kuma Karfin Biyayyan da ya Rokeni akanta na ke zaune.
Tunda na auri Ishaq daidai da rana D'aya bai taba kallona ya yab'amin ba,Bai taba jin dadin zama dani ba bai taba godemin ba,Bai tab'a godema Baba Bisa aurena da ya basa ba,Bai tab'a sona ba bai tab'a kallona da Idon Rahma da Salama ba bai tab'a jin zai iya bani matsayin matarsa mai kima ba nayi Rayuwa dashi cikin k'askanci da Tozarci ko da yaushe cikin aibatani yake yi da Kusheni,Ni fa'iza na Fuskancin Guilt din kushen miji har tsawon shekaru Takwas da auran mu,Ya kulleni agida cikin tozarci bai barni nayi zumunci da yan'uwnaa da Dangi ba,Alwashin da Mama ta Dauka ta cikashi bata bari na kara jin Dad'in Rayuwa Sai da tabbattar da duk abunda tace ma Ishaq akaina shi yake amfani dashi bai horar dani da yunwa ba Yana sauke min kayan abinci duk wata sutura kuma yana yi min ta Hannun Mama sai ta ga Dama sannan na saka abu mai kyau cewarta kullum abu mai kyau bai dace da mace irina ba,ina jin Tsoron Ishaq kamar yadda nake jin Tsorom Mama Tunda muka yi aure bai taba yarda ya nuna ma wani ni matasar bace ko abokansa ba su san yayi aure ba, acewarsa matar Ishaq sai an zo a ganta Mai kyau ce mai ilimi ce sannan yar gata gaba da baya ni kawai wata Tsani ce wacce nayi kutse tare da Ruguzamai dukkan Farincikinsa.
Da gaske yake yi ya fad'i gaskiya ni kaina in na kallesa na kalli kaina sai naji Tabbas na yi mai kutse acikin mafarkin sa Ya Ishaq dogon Namiji ne kyakyawan gaske fari mai Hanci d'an Fafa mai ilimi dan alfahari da son komai mai kyau da Tsari ni kuma Bakace Gajera mummuna,wacce bata da gata,ba ilimi kamar ta bakinsa yace Total Zero Fa'iza komai nata ba sa'a acikinsa.
Ya Ishaq kunyar nuna ni yake yi a matsayin matarsa domin bai taba gayyato wani inda nake ba yace shi kan shi kunyar kallo na yake yi a matsayin matarsa ma ballatana wani,Ko Ya'yan da na Haifa tare da shi Kaddara ne da Rabon su daman Domin Tunda Baba ya kawoni wannan gidan nake rayuwa ni kad'ai Sai dai ina aikace aikace na bana ganin kowa Dagani sai ni kamar mayya Ba ni da waya bana jin kowa sannan bana ganin kowa sannan ya min gargadin ko kofar gida na fita sai na raina kaina shi kuma sai chan dare yake dawowa da Farko gidan Mama yake biyawa yaci abinci Baba d'aya lura da Haka ya mai fad'a sai ya daina Daman na Fada muku yana morata ta bangaran abinci zai ci kafin ya fita in ya Dawo yaci acewar Mama Ai abinci daman bani na siya ba dafawa ne kawai nawa Saboda haka na Dafa daman Mata ire irena da Bauta muka dace,Sai suzo gidan ita da Anty Binta su yi ta zagina da Gore gore Ishaq na zaune kanzil bazai ce ba Wani Lokacin Anty Mamah ce kan musu mgana sai su Sasaauta.
Bazan manta da muna da wata biyar da aure Anty Hure kanwar mama tazo katsina suka zo ita da Mama Ya Ishaq na gida ranar baije aiki ba,Naje kitchen na kawo musu ruwa ina rawan jiki na fice ashe Mama ta kira Sunana ban ji ba, tamin uzuri bani da karfin ji ammh sai Mama tace naji kawai yanzu na raina ta ne agabansu Ya Ishaq ya mareni ya sani na Duka na bama Mama Hakuri taki hakura Anty Hure ta yi ta Dukana tana rankwashina Ya Ishaq na zaune ko ajikinsa haka suka tafi suka bar ni ina kuka kukan da ya riga ya zame min jiki.
Ko wata rana na Shafin Rayuwata ba ranar da bazan yi kuka ba babu wannan ranar,Sai da na fara tara ya'ya sai suka zamemin sanyin idanuwana ko Ya Ishaq ya kunsamin Takaicinsa in na Kallesu sai naji raina yayi sanyi Tabbas ko wacce uwa ya'yanta sune Duniyarta.
Muna da wata shidda da aure,Baban katsina ya kawo mana ziyara yayi mana Fad'a da kakkausan murya musamman ma Ya ishaq ni kuma yace na rame na lalace yayi tambayan Duniyan nan ko Ishaq na min wani abu ne nace mai a'a bakomai haka ya tafi bayan ya kara fadama Ya Ishaq cewa in bai Sauke hakkina dake kansa ba ya sani Allah na kallonsa.
A wannan Daran Ya Ishaq yazo min ya karbi Mutumcina da kimata ta y'a mace cikin kaskantattacen yanayi,Cikin Tozarci da bana jin wata mace ta taba Fuskarta ban sani ba ammh a kasa raina naji cewa mata marasa kyau ire irena bai kamata su fuskanci wannan tozarcin ba.
Tunda ya gama dani ya tsallake ya barni cikin mayuwayacin Hali,Halin da ni na tallafi kaina bazan iya fadin irin wahalan da nasha ba,ba wanda ya kula dani sai ni kadai,Nafi Sati bana ji na Daidai da taamakon Allah na Samu na Dawo cikin Hayyacina Tun kuma daga wannan Had'uwar tamu bai kara kallo na ba ko da yaushe ni ke mai Hidima ina rawan jiki a kansa shi kuma kalamansa Daya ne Hajiyar karofi da Baba sun cucesa har fadi yake yi tasan zata mutu ammh kafin hakan sai da ta jefa rayuwarsa a wani Hali sannan ta bar Duniya har yau bai taba gode musu ba ban kuma jin akwai ranar da zai gode musu.
Ashe wannan haduwar tamu itace sillar Zuwan Amir(Kabir) duniya ne Wata uku tsakani nayi ta ciwo a tsaye,Zazzabin Dare da amai kasala da yawan barci,Ya Ishaq baisan Rashin Lafiyata,baisan komai akaina ba ban da na girka mai abinci yaci yana ci yana bi na da mganganun kushe da Tozarci.
Fahimtar ma ban da lafiya girkin da na kasa yi ne yasa ya lekani ya ganni kwance Ba domin yaji Tausayina ba sai Domin Harshen Baba akansa yasa ya Daukeni ya kaini asibiti,Gwajin farko aka tabbatar da ina da shigar ciki dan watanni biyu da wani abu Bansan wani yanayi Ya Ishaq ya shiga ba, ammh nasan muna Hanyar komawa gida ya kalleni kafin yace"Ke haka kike daga tabaki sai ciki Fa'iza..?
Yaushe na tsara ma kaina aure ballatana har na haihu?
Ya manta Haihuwa na Allah ne,Bani na bama kaina ba Allah ya bani ammh da Gudummuwarsa,Cikin Amir ciki ne da nayi sa mai Laulayi na sha bakar Wahala acikin gida ni kadai,ina haka watarana Goggon Karofi ta zo ganina ita da Yaya mariya su suka iskeni ba yadda nake suka kwasheni sai asibiti dalilin kwanciyata a asibiti Cikina ya fallasa ga su Mama kowa yaji ina da ciki sai kowa mamaki ya kamasa.
Mama kuwa mamaki yasa ta kasa mgana,Anty Binta sai kallon Ya Ishaq take yi basu taba zaton zai iya kallona na da sunan auratayya ba.
Baba kuma sai murna yake yi shi ya Kira Ya Ishaq da kansa ya fadamai da yazo asibiti ga Halin da nake ciki Sanda yazo,Baba sai da ya Rumgumesa yana murna lokaci d'aya yana sakamai albarka.
Mama ta fad'a agaban kowa da kowa Bata kaunar hada zuru'a dani,Goggon Karofi tace Tunda Allah ya had'a ita bata isa ta raba ba,har sai da suka yi ta Hayaniya,naji jiki sai da nayi sati a asibiti likita nata fadan bana cin abinci sannan jinina yayi kasa Goggo kamar ta wuce dani karofi Baba ya Hana Akace gidan Mama tace ai har Abada na gama zaman gidanta Dole gidana aka maidani Goggon Ta zauna Dani tayi sati,Yaya Mariya ita kadai ta koma Karofi,A bakinta Ya Asiya taji tazo har Katsina ta Dubani bana ganin Tamadina bata taba zuwa gidana ba na Tambayi Goggo tace min tana gidanta ni nasan rayuwata cike take da abun Tausayi.
Har Amir yazo duniya ni Fa'iza babu abunda ya sauya gareni daga zuciyar,Ishaq a kaina na wahala wajen Haihuwa kamar bazan rayu ba sannan Amir yazo duniya wanda yaci sunan Baban katsina Kabir,lokacin da na Haihu Anty Binta na asibiti ana kawo musu abunda na haifa ta duba kunnensa ta Kira mama tace"Mama sai hakuri Dangin tsiya yaron ya Debo"
Nayi kuka sosai da wannan kalmar sai dai a kallah na samu wanda zai san zafina wani abu daya fito daga Tsatso na wanda kila shi zai kaunace batare da ya Duba yanayin Halitta na ba ko nakasun jina ba,An kai ruwa Rana kafin Ya Ishaq da su Mama su amince Goggo ta tafi dani karofi nayi jego shima sai da Baba ya saka baki,sannan ya amince a cewarsa wai Goggo sai tayi ta nuna yana zalunta ta na sannan baya so naje na had'u da su Yaya mariya wai ana zaginsa mganganu dai haka yayi ta yi kan yan'uwana da iyayena bani da tacewa.
Sai da na koma karofi sannan Tamadina tazo ta ganni ta rike Amir gam a Hannunta kafin ta mikamin shi ta dafa kaina kawai tayi miirmishi na kalleta sai naji kuka duk ta lalace ta rame ta kara tsufa kamar ba ita ba,Bazan taba mantawa da Goggon Karofi ba domin ita ta kula dani ba,da kila sai da na Rub'e ni kadai ban san komai ba.
Ina yin arba'in ba Dadewa Goggo Karofi ta maidani gidana Ni da Amir mun yi bulbul duka duka sau biyu Ya ishaq yaje ya ganmu kamar Amir din ba D'ansa ba ne,Goggon Karofi da yan'uwana sun yi kokarin wajen gyarani ni kam ban ce musu komai ba, to ina zan fada musu sau daya tak Ya Ishaq ya taba hada jiki dani Rabon Amir ne..?
To kamar na Amir itama haka Rabon Saudatu(Anum) ya had'amu shima duka Duka Haduwar bai wuce sau uku ba ma na samu ciki Amir nada wata Goma sha hudu wannan karon Ishaq yafadamin sai dai a zubar da cikin ni kuma nace ban amince ba Karo na Farko da na taba kai karas gaban Baba Dalilim da yasa Baba Ya mari Ya Ishaq ya kuma nunasa da yatsa yace"Kada na kara jin wannan mganar a bakin ka..kasan baka son cikin ka yi sa..?
Ka kiyayi ranar da Fa'iza da ya'yanta zasu zame maka inuwa wacce zaka iya rab'ar ta ina jiye maka watan watarana kada kayi nadamar abunda ka aikata"
Wannan marin ya jamin abubuwa Dadama tsakani da Ya Ishaq,kamar ni na bama kaina cikin Dalilin Baba yasa Saudatu tazo duniya(Anum),Da kulawarsa na haifeta Lafiya ita ma kamar Amir ne Baka ce irina,Basu da yadda zasu yi su sauya wannan kaddaran tunda haka Allah ya Tsara Mama ta tsane ni ammh ta kasa Tsanar jokokinta Amir ma ita ta karbesa ta yayesa sai wahalan tamin Sauki,Goggon Karofi Sati daya tamin ta koma ni na mike na Rika kula da kaina har nayi arba'in din Anum.
Ya Ishaq baya barina fita ko'ina Sai gidan Mama ko gidan Anty Binta Su kuma har naje na Dawo bana samun kallon arziki,Karofi kuwa Tun da nayi jego ban kara komawa ba Har Haihuwa Ya mariya tayi ya Ishaq yace gulma zai kaini bazani ba.
Gidan Yaya Asiya kuwa tun bayan auranta kafata bai kara taka kano ba,Ya Ishaq ya rabani da kowa ciki har da mahaifiyata domin har Haihuwa tayi yaron bai zo da rai ba bai barni naje ba wai zan kwaso ma Anum Sanyi Baya sona ammh kuma yana kaunar ya'yan sosai yake kula dasu kamar yadda yake kula da kansa.
Anum na da wata Hudu watarana Baba ya fara rashin Lafiya anje asibiti an yi gwaje gwaje sai aka gano Hantarsa ce ta tabu ba'a sani ba,Ya kwanta asibiti yafi sau hudu duk Hankalin su Mama ya tashi ni kaina Hankalina baya kwance domin Baba shi kad'ai ne ya ragemin Saura gata na,Kwanciyarsa asibiti na Karshe an sallamosa Da ya ishaq zai fita yace na shirya naje na Dubasa Amir daman yana chan tun yaye bai Dawo ba.
Naje na dubasa yana kwance ne yana ganina sai da ya mike,Ya miko min Hannu na Kwanto Anum daga baya na mika masa ita yana ta mata wasa Baba yayi ta min Nasihan hakuri da kuma Umrtana da na zauna nayi Biyayyan aure zan rabauta Ranar gobe kiyama..
Ashe wasiyya yake barin mu yace na kula da ya'yana na basu tarbiya kada na Biye ma Ishaq,nayi hakuri dashi Sannan na kara hakuri da su Mama watarana dani da ya"yana duk sai mun zame musu Inuwar Rab'a,na dawo gida da Tunanin mganganun Baba ashe bazai kwana ba adaran Allah ya Dauki ransa.
Alokacin mutuwar Baba na kara yarda Tabbas ban da sa'a domin duka wada'nda nake gani agata na sun kare bani da kowa anan duniya da zan kallah nace Gata na ne duka sun tafi Na tabbata ko Mama bata kaini kukan mutuwan Baba,na fade lokaci d'aya nayi zuru zuru tabbas Mutuwar Baba ya sanyaya ma Ishaq zuciya sannan ya sa ya rage wasu abubuwan.
Rasuwar Baba ba'a rufe shekara ba Ya ishaq ya samu karin girma zuwa Abuja,chan ya koma aiki sai bayan Sati biyu yake zuwa katsina sai nauyin su Mama da su Jamal duk ya koma wuyansa abubuwa duk suka Tabarbare daman karfin zumumcin Baba ne to yana Rasuwa sai ahankali Hajiyar Dala ta matse kanta gefe itama Goggon Karofi sai ta kama kanta itama Daman basa shiri da Da Mama sai ta Dade bata zo katsina ba ba ita kadai ba Saboda Sanin Halin Ya Ishaq yasa ba mai son Rabata abu kadan yace munafunci ake yi shiyasa Dole dai su Mama ne bani da kowa a garin katsina sai su da ya'yana.
Samun karin girman Ya Ishaq yasa sai ya samu rufn asiri fiye da baya ya gyara ma Mama gida ya koma Fasalin na zamani shi kuma ya siya Fili ya fara gini a Anguwan layout,Jamal kuma ya shiga jami'a sai Badariya da ta zama yammata yanzu sai ni da ya'yansa wanda Darajan su yasa yake Ragamin shima ba wai don ya daina Tozartani ba ne A'a har yau har gobe ni Fa"iza ba kowa bace a wajen Ishaq kabir Karofi
Cikin mustapha ko ni bansan ina da shi ba sai da yakai wata Biyar Mama data ganni da ciki ta Dinga bala'in na zama kamar beran masar bani da aiki sai Haihuwa ta manta ba ni kad'ai nake samar da cikin ba har da Gudumuwar D'anta ammh bata ganin Laifinsa sai nawa,Na haifi Mustapah ba Dadewa muka tare a sabon gidan da Yaya Ishaq ya gina katon gida mai shashe biyu,Shashen farko mai 3Bedroom da Falo sai kichen,Nawa daya sai na yara sai guda d'aya na baki,Ya ishaq shi ya Zuba Sabbin kaya agidan komai bamu Dawo da Tsoho ba, Mama ta kwashe su ta kyautar ni ko da har nayi Tunanin na aika ma Tamadina da su Dakinta Sai leda ba kujeru ganin Mama tace akwai wacce zata bamawa ban yi mgana ba, Sanin Halinta.
Haihuwar Mustapah yazo da Budi sosai Ya Ishaq har motar hawa