Showing 63001 words to 66000 words out of 96493 words

Chapter 22 - Kana Naka Book 1 Hausa Novel Complete

Janafty   

07 Dec 2024

535

ni suka bari da kwashe takalma da jakunkunar su da suka watsar a tsakar Falon.
Anum dakina ta Shige Saboda na maidata da ita da kayanta tare dani,ina shigowa na iske ta watso kayanta kan gado da karfi nace"Anum ba na hanaki watso kaya ba..?
Cikin rigima tace"To umma ban ga wanda zan saka ba ne"
Riga da sikat na Dauko mata na bata ina Fadin"Duk na goge fa kayan nan ammh ji yadda kika wargazasu Anum"
Ganin ban ji dadi ba yasa tace"Kiyi hakuri Umma"
Kanta na shafa ina fadin"Bakomai yar Umma muje aci abinnci"
Musty kuma Amir ya cire mai kayan makarantar ya sakamai, na gida suka fito falo na zubo musu abinci Farar shinkafa da miya,Sa'adatu ta aiko min da Kayan Miya itama daga gidansu aka aiko mata dashi kamar babanta aikin gwari yake yi.
Dukkansu waje daya na Hada musu kamar yadda na saba sun fara ci,Anum da Musty suka fara rigima kamar kullum nace su bari suka ki sai na kalle su ina fadin"Anum zan mai da ke cin abinci ke kad'ai tunda bakya jin mgana"
Jin haka yasa Da sauri Amir yace"Umma ki yi hakuri Musty ke Tsokananrta ki barta mu rika ci tare"
Sai na gyada kai ina fadin"Musty kana son Bulala ne..?
Na fada ina nuna masa hannun alamun duka kafada ya makale dariya nayi kafin nace"To ka daina tsonakar Yaya Anum in baka son duka"
Da sauri ya gyada min kai Lokaci daya yana fadin"To umma"
Cikin Salom mganarsa ,cin abinci suka cigaba da yi a natse ni kuma Farhan dake baya na ne ya motsa sai na mike ina Jijjigasa Daidai da Bude kofar falo da Shigowar Yaya Ishaq bayansa Jamal ne da manyan Ledoji,Nasan har ga Allah bai kalleni ba,ballatana ma yasan wanda na Goya Sannu da zuwan ma da nayi mai ban ji ya amsa ba Jamal ne yake kokarin Sauke Lodijin hannunsa a falon da Sauri ya Juyo yana fadin"Jamal bani Lodojin Hannunka"
Yafada daidai da yaran zasu tashi suna kiran Daada da karfi nace su koma su gama cin abincin su duk da ban kallesa ba nasan sai alokacin ya bini da kallo ni kuma sai na Dauke kaina ba domin ina jin Haushin sa ba sai domin nasan ba ni da wata Daraja a wajensa shiyasa nima na koyi kama kaina.
Jin abunda nace ne yasa ya kalli yaran yana fadin"Ku gama cin abincin ok.?
Atare suka gyada mai kai Jamal ya mika masa ledojin hannunsa ya shige Bangaransa sai da ya shige na Dawo da kallona wajen Jamal wanda ya zauna saman kujera su Amir na gaishesa ya amsa yana fadin"My Childreen how far"
Amir ne ya amsa mai da We are fine Uncle"Dariya yayi yana fadin"Daddy na ya fi kowa gane karatu a makaranta ko Amir..?
Anum ta tura baki tana fadin"Nifa Uncle"
Kallonta yayi kafin yace"Mommy nama tana ganewa itama"
Jin haka yasa ta washe baki Musty kuma ya tayata,Sai alokacin ya Dago muka gaisa,cikin yanayin mganata nace"Ya su Mama..?Daga ina haka da yammah nan..?
Yana sauke ajiyar zuciya na gajiya yace"Wlh Dad din Anty Zainab muka kai Masauki  sannan muka je Restaurant  muka yi oder abinci muka Biya gidan Mama muka kai mata kinsan Mom din Anty Zainab din wajen Mama ta sauka"
Na jinjina kai ban yi mgana ba ya cigaba da fadin"Shine duk najini a gajiye me kuka dafa ne..?
Kai tsaye nace"Farar shinkafa da miya ne a zubo maka ne..?
Kai ya girgizamin kafin yace"Bari mu yi sallah naji an fara kira ma"
Ina shirin mgana Yaya Ishaq ya fito Daga bangaransa, da Sauri bayan sa Zainab ne da kanwarta,Wacce ke jan Hannun yarinyar da suka zo da ita baiwar Allah tana ta kuka.
Ganin su hankali tashe yasa Jamal ya mike cikin wani yanayi yana fadin"Me ke faruwa ne..?
Zainab ne cikin rawar murya tace"Farhan..Ba mu ga farhan ba"
Sai abun ya bani mamaki suna nufin basu ga Farhan goye a bayana ba..?
Kafin na iya mgana Zuzu ta mari yarinyar nan Lokaci d'aya tana Hankadeta cikin fada tace"Ina Farhan.?wa kika bama shi..?
Yarinyar sai ta kasa mgana sai kuka Ya Ishaq ya fara fadin"To ku ina kuka shige ku bar ta dashi..?
Zainab ta fara fadin"Muna ciki ni da zuzu muna mgana mu ka bar Farhan hannun Shema'u"
Ganin abun nasu ya koma kan yarinyar har Ya Ishaq ya fara fada ita kuma sai ta kasa mgana ta Dago tana kallona kafin nayi mgana da Sauri Anum tace"Jaririn Anty..?ga shi nan Umma ta goyasa"
Sai kallo ya koma kaina ni kuma sai na juya bayana suka ga Farhan goye a bayana,yana barcinsa cikin kwanciyar Hankali ina jin su suka Sauke ajiyar rai a tare Zainab tace"Thank god.."
Cikin yanayin mganata nace"Na shiga ne na iske yana ta kuka na karbesa ashe cibiyarsa ke ciwo shiyasa yake Rigima"
Kamar kiftawan ido nagansu a gabana,suna rige rigen kwancen goyen bayana ba Ya Ishaq ba,sannan ba Zainab ba kanwarta ba,zuzu ce ta kalleni tana fadin"So kike ya karye kafarsa..?ba'a fara goyasa ba"
Ni dai ban damu ba da Sauri na Sauko shi Tare suka karbesa ita da Zainab din Mamaki ya rufeni Lokacin da Ya Ishaq ya faramin fad'a meyasa ban yi mgana ba ina ji ana neman Farhan.
Na kallesa cikin yanayina Kafin nace"kayi hakuri na zata ka gansa a bayana"
Cikin Fusata yace"In da na gansa zaki ji muna neman sa..?
Kuma kada ki kara goyasa tunda bai saba ba,Ba irin yaran ki ba ne da kika Saba goyasu ba"
Kamar wata wawiya haka na bisa da kallon Zainab ta kara fadin"Honey kafarsa bata samu matsala ba ko..?
Tafada tana nuna masa suka Taru suna kallon kafarsa yaron suna Tattabasa kamar na shafamai mugun abu,Cibiyar Ta bude tana kallo Zuzu ta leka tana fadin"What is this..?
Wannan kayan fa..?
Tafad'a a wulakance,karbansa tayi Tun anan ta cire mai kayan da na sakamai,Ita da kanwarta suka koma ciki Shi kuma ya bisu,kamar wani bita zai zai,ni dai da kallo na bisu Jamal ne, ya koma zauna yana fadin Allah ya kyauta.
Yaran kuma duk sun yi wani iri,ganin abunda ya faru ni Dariya ma suka bani wai kafarsa zata samu matsala Saboda goye,Allah sarki rayuwa da goye na illa da tuni mu kan mu mun samu illah Tunda a baya kafin zamani ya zo da sauye sauye goyen aka sani ba wani gayu da feleke feleke irin na yan zamani masu nasaba da boko ya gama ratsasu ammh irin mu yan gargajiya ai goyen muka sani.
Daganan dakina na koma Dauke da Ahmad araina nace in na goya nawa ai ba mai cewa zan karya masa kafa,Amir da Musty tare da Babansu da Uncle suka tafi masallaci ni kuma muka yi namu ni da Anum.
Daganan ta tafi bangaran Baban nasu,Ta damu sai taje sai nace ta tafi,Su Amir kuma sai da suka yi Isha'i suka dawo suma ban kara ganin su ba Bangaran suka shige Jamal kadai ne afalo na zubo mai abinci yaci muna dan Taba Hira sama sama bai jima ba yayi min sallama ya tafi.
Daki na koma nayi wanka nayi ma Ahmad,na shiryasa nan da nan sai barci yau bai yi rigima ba sosai su Anum sai goma saura suka Dawo Daki  suna bani labarin sun ci nama da Ice Cream,Amir dai bana jin bakinsa sai bakin Anum da baya gajiya da mgana.
Washegari ba makarantar Boko sai Tahfeez tun safe nayi musu shiri suka wuce,Shinkafar jiya data rage na Dumama ma yara sukaci suka tafi,Sai Sauran Taliyan data rage na Dafa musu da miyar suka tafi da shi ni kaina Sauran Shinkafar naci bamu da dankali ba kwai ba komai na Kayan breakfast ballatana nayi  musu sai na kama kaina,ina gama abunda zan yi na koma daki bayan na tattara kayan yara da suka zubar afalo.
Dakin su na shiga nayi musu kaye kayen kayan da suka watsar sannan na koma nayi wanka na yi ma Ahmad daman na Dama mai kunninsa na dura masa yasha sai ya cigaba da Wasan sa,Ganin ban da wani abu da zan yi sai na dauko Qur'ani na fara karantawa ina cikin karatun ne naji Muryan Yaya Ishaq na kiran sunana sai da na kai karshen Ayan sannan na Tsaya Daga bakin kofa ya tsaya Ahmad na ganinsa ya fara tafiya wajensa yana Washe mai baki ya Dauke sa ya daga sama yana fadin"Ahmad ka zama kato yanzu"
Shi ko sai bangala Dariya yake yi.
Hijabin jikina na gyara sannan na kallesa ina fadin"Ina kwana.."
Ya amsa ba tare da ya kalleni ba ya cigaba da fadin"Ba abun karyawa ne..?
Kai tsaye nace"Babu komai na cefane shinkafar jiya ce da nadafa ta rage muka dumama muka ci ni da yara"
Shuru yayi bai kara mgana ba daganan ya fice Dauke da Ahmad ashe kasuwa ya tafi yayo mana Cefane duk da bamai yawa ba ne zai iya isa har bayan sun tafi muma yayi mana Saura.
Na rana kadai yace nayi Inaga a waje ya siya musu wanda zasu karya da shi,couscouss nayi musu da rana mai Hanta da kayan lambu,basu fito ba nima ban bisu ba sai bayan La'asar na shiga muka gaisa sama sama Farhan na Hannun kanwar ta kamkamesa sai ban zura kaina wajen karbansa ba,na fito na koma Daki Ahmad kamar ya sani yaki ko sauka yaje wajen zainab din data ke kiransa ya lafe ajikina.
Tunda suka zo suna bangaransa komai sai dai na shigar musu da shi ban damu ba domin nasan lada zan samu ciyar da su din da nake yi sannan Gidana suka zo akwai hakkin abinci su a wuyana.
Kwanansu uku da zuwa Ya Ishaq yace na shirya zamu je gidan Mama na gaida iyayan zainab,Da daddare mukaje dukkanmu har da yara da ita Zainab din sai da naga mahaifiyarta da mahaifinta naga inda suka Dauko Kyan Fuska Mahaifiyarsu Hajiya Halima mun gaisa cikin Sakin Fuska Mahaifin su Dr.Lawal ya amsa min a Wani karkace ya kalli yarsa yana fadin"My dota wannan ce abokiyar zaman taki..?
Ta dagamai kai tana fadin"Yes Daddy"
Ya kalleni ina Duke gabansa Ahmad na Hannuna kafin yace"Sannu"
Nayi shuru domin ban jisa ba Itace tace"Daddy ta na da problem din Hearing sai ka daga murya"
Ido ya ware kafin yace"is that serous.."?
Kai ta gyada mai sai naga ya daga glass din sa sama yana kare min kallo araina sai naji girmamsa ya zube ai shi Babba ne kuma namiji irin kallon kurillah dayake bina da shi bai Dace ba.
Su Amir kuwa da suka gaishesa ya amsa yana fadin"Bakaken ya'yan Ishaq kuna lafiya..?
Naji abunda yace sai naji ban ji dadi ba saboda su yara ne abu kad'an za'a fada su dauka wani abu ne Jikansa ya amsa yana ta mai wasa Anum nata son ya bata ta Dauka yace"No..No..baza ki iya ba kada ki kada shi..Kinga farin yaron da babu a gidan ko..?
Duka har su Mama suna falon Ammh ba wanda ya damu da mganarsa sai ma Dariya da Mama tayi tana fadin"Wlh kuwa Alhaji uwar ai sai dai in ta Haihu su dauko bakin Fatarta"
Hajiya Halima ce duk bataji dadin Mganganun ba sai ta juya tana yi ma Zainab mgana,ni dai ina zaune kamar wata yar aikin cikin su na kosa mu koma gida,aiko sai wajen goma muka koma gida,Da safe ina yi ma su Amir shirin makaranta Amir ya kalleni yana fadin"Umma menene baki..?
Gabana ya fadi na kallesa na kasa mgana ya kara cewa"Umma baki ba abu ba ne mai kyau..?
Da Sauri nace"Da baki da fari duk abu ne mai kyau Amir kaji ko..?
Ban kara basa damar mganar ba saboda bansan me zan ce mai a gaba ba,Bana so ya'yana su fuskanci abunda na Fuskanta tsawon shekaru
Ashe basu tsira ba Dole dai sai an goranta ma ya'yana kwanansu shida Zainab din tagayamin washegari zasu koma saboda ayyukansu sun zo sun gaishemu tunda naki zuwa nace mata zan zo in sha Allahu.
Zainab ba ruwanta macece Faram Faram ko ta na da wani abu aranta bata taba nuna min ba Kanwarta ne mai D'agawa da isa harta su Amir basa Rabanta,Har Anum da take da Son Jama'a basa zuwa kusa da ita ta cika Fad'a da isa da fadin rai.
Ni ban isa na hana su Amir shiga bangaran Mahaifin su ba,Suna son Daukan Kaninsu ni kums ban isa na Hanasu ba ai dan'uwansu ne ni bansan abunda ya faru ba da yammah bayan sun dawo daga makaranta Kayan su kadai suka cire ko abinci basu tsaya ba suka tafi chan wajen Farhan har da Amir da bai cika shiga ba in dai ba Tare da Babansu ba.
Ina kitchen ina Zuba musu abimci Amir ya shigo har da hawaye a gefen Idanuwansa na kallesa ina Fadin"Babana wa ya tabamin kai..?
Bai min mgana ba ya fita nima na Dauki abinci zuwa Falo na ijiye Saman Cafet din dake Falon na isa ga Amir daya zauna yayi Tagumi.
Na cire hannun Tagumi ina Fadin"Uhm..gayamin wa ya tabamin kai..?ko Anum ce ta tsokane ka..?
Cikin ido ya kalleni yace"Umma kin ce baki abu ne mai kyau..Ammh yar'uwan Anty tace min ni baki ne kada na Shafa ma Farhan baki na"
A rarrabe ya fadi mganar kuka yaci karfinsa Amir na da zuciya shiyasa bai cika Hayaniya ba.
Jawosa jikina nayi na Rumgume ina Fadin"Ya isa..Shiii..Ya isa"
Na dagosa na Share mai Hawaye ina Fadin"Kada ka damu da mganarta Da fari da baki duka Hallitan Ubangiji ne sannan Duka d'aya suke a wajensa.."
Zai kara mgana na girgiza kai ina Fadin"Ya isa zauna ka ci abinci"
Bai yi musu ba ya zauna sai dai sai ajiyar zuciya yake saukewa Raina sai naji ya baci taya zasu rika Gurbatamin Tunanin yarana Amir dan Shekaru tara da wani abu suna neman sakamai Tunanin banza.
Ina cikin Tunanin naji yace"Umma su Anum suna wajen Anty"
Kai na gyada mai ina fadin"Bari naje na taho da su"
Kai Tsaye bangaran nashi na shiga Zainab din bata falo sai kanwar nata,Sai yarinyar dake kula da farhan Tana rike da shi ita kuma Zuzu tana danna wayarta Anum da Musty suna ta wasan su ya'yan Anty ne su.
Ina shigowa kai tsaye ita na Nufa ina Fadin"Me kika fad'ama Amir..?
Da yanayin mganata ta Dago tana kallon kafin tace"Ni..?
Lokaci daya tana nuna kanta tana wani tabe baki ban damu ba nace"Baki Tunanin shi yaro ne..?in bazaki bari ya Daukesa ba,sai ki hanasa  ba wai ki gayamsa mganar da Hankalinsa bazai iya Dauka ba.."
Ta kuramin ido tana kallona ban damu ba na cigaba da fadin"Kada ki kara gayama yara na abunda zai Dame su bana so..Ke bakuwace ki gama bakuntarki ki tafi bana so ki shiga Tsarin Tarbiyan yara na"
Har na juya na juyo ina kallonta Lokaci da'ya ina Fadin"Sannan in baki sani ba ki sani da Bakin da Farin duka Hallitun Ubangiji ne sannan d'aya suke a wajensa Launin fata bazai taba zama wariya ga musulmin kwarai ba"
Daga haka na juya na kama Hannun Anum Da Musty muka fice ina kallo Har Zainab din ta fito daga cikin Dakin ta tsaya tana kallona ni kuma ko kallonta ma ban yi ba.
Haka kurum naji ni zan iya Daukan kowani cin zarafi ammh bazan aminta arika cin zarafin yarana ba a bata musu Tunanin su ba Shiyasa naja mata kunne tun da wuri.
Ni ban san ashe wannan mganar tajawo min bala'i ba sai da Daddare sai ga Mama da mahaifan Zainab din Har da Anty Binta sun zo gidan,Ya Ishaq da bai yini a gida ba shima ya Dawo Kirana kawai  yazo yayi da kansa Fuskar nan tasa a hade kamar Hadari Allah ya taimake ni yaran sun kwanta da wuri da a gabansu za"a cimin zarafi.
Ima fitowa tun da naga mama da Anty Binta na sadakar wannan taron nawa ne sai kanwar Zainab da ke jikin Mahaifinsu tana ta sharban kuka Fuskar kowa ba fara'a na samu gefe na zauna ina gaida su Mama ko amsani batayi ba ta fara dakamin Tsawa tana fadin"Rike gaisuwarki mara Mutumci me wannan yarinyar tayi miki kika zageta kika ci mata Mutumci..?
Sai da ta fad'a na Dago ina kallon Zuzu din har tana wani matse kwalla da majina sai alokacin na Fahimci komai ban ji nayi nadama ba cikin yanayin mganata nace"ni ban zageta ko naci mata mutumci ba..nayi mata fad'a ne"
Anty Binta tayi zaraf tana fadin"Fada..?Sannu uwarta yarki ce da zaki tasata kina mata fada ishasshiya.?
Hajiya Halima ce tace"a bi a sannu Hajiya"
Mama tace"Hajiya ai bata da mutumci ne..Daman bata so auran Ishaq da Zainab ba,kuma  tun tuni take neman daman cin mana mutumci bata samu ba sai yau"
Ni dai sai na kasa mgana Yaya Ishaq ya kalleni ya watsamin Harara yana Fadin"Daga kawai ta hana Amir Daukan Farhan Saboda bazai iya Daukansa ba sai ki bita har Daki ki zageta ki zagi iyayanta sannan har kina ikirarin cewa gidanki ne uban wa ya ce miki nan gidan ki ne..?
Ko da sunan ki na siya gidan ban sani ba..?
Kaina na kasa na kasa mgana ina jin wannan cin mutimcin Mama tayi kafyci tana fadin"Ahto tambaye ta dai"
Sai kawai na samu bakina da Fadin"Ku yi hakuri ba.."
Muryan Dr.Lawal ta katseni a Fusace yana fadin"Sorry for ur self..Akan ya'yana zan iya shari'a da koma waye..Daga tazo gidanki sai ki ci mata Mutumci..?ke ba domin Ishaq ba kin isa ki ga Zuzu a inda kike..?ai kalan zaren ba kalan yadin ba ne..Ba domin ina jin kunyar shi da iyayansa ba da sai kin gayama aya zakinta akan kukan da kika sa yata tayi kin san wacece ita..?ko ni bana sakata kuka Koda yaushe ina Tattalin Dariyan ya'yana ne ba Zuzu ba ko Zeey da kuka Hada miji kika kara yarda kallon Banza ma ya had'aku sai nayi maganinki sai na saka an batar dake da Dangin ki gabad'aya"
Yafad'a cikin Kaushin murya Hajiya Halima kunya ya kamata ta kasa mgana ta Dafe kai Zainab ce tace"Is ok Daddy. "
A fusace yace"No zeey kinsan ba na Had'a ku da komai a nan duniyan ko..?
Ko mommy ku ta sa ku kuka ina jin Dalili ballatana wata shara chan"
Hawaye suka wankemin Fuska ni ce shara..?ina jin Zainab din na fadin"I know Daddy..Forgive her bata sani ba ne zuzu plz ki bar kuka kada kanki ya fara ciwo..Gobe zamu koma Abuja is ok  kin ji..?
Kai ta d'aga mata ta koma ta lafe jikin Baban nasu yana share mata hawaye yana fadin"Am sorry Angel..am sorry"
Mama tayi kayci kafin tace"Ai daka Dauki matakin da kayi niyya Alhaji da sai tafi gane matsayinta"
Hajiya Halima tace"Hajiya komai ya wuce insha Allahu"
Ni ko ina zaune jikina ya gama mutuwa hawaye suna zubomin na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login