Showing 15001 words to 18000 words out of 96493 words
safe in naje baya na fara sai yammah watarana ma bana ko samin zuwa islamiya,Washegari kuma Baba na fita zan dasa guga har sai bayana ya kage ba ci ba sha sai na gama in kuma nace zan tashi ko sallah in yi sai Mama ta kai min duka tana Fadin"Me kika sani a karatun sallar..?Ni fa jin baban su kawai nake in yana Fadin kina da ilimin addini ke da kike Bebiya gaki ba kyau ba fasalin y'a mace ai bautar da ta dace da irin ku kenan.."
In ta fadi haka bana damuwa sai naga gaskiya ta fada domin na fahimci in baka da kyau ko Asali da gata ko kana da wani nakasun Hallita baka da wani amfani Domin wad'anda suka fi kusanci dakai sune suka fi kowa kyamatarka to inaga na waje wad'anda basu san ka ba, mu'alama ce zata hadaku..?
Ina tuna Lokacin muna Malumfashi Iyayena sun san ina da Lalura ammh ko sau daya basu taba nuna gazawar su ba sun min dukkan gata a malumfashi makarantan da aka kaini ina gane karatu tunda ana yimin yadda zan gane sannan bamai kyamatata Saboda ina da gata alokacin ammh daga Lokacin da gata na ya kare sai nima nake fama da guilt din shiga cikin Mutane ina ganin ban kai ko wani matsayi ba sannan na aminta da mganar Mama iri iren mata irina Bautace ta Dace damu..
Shiyasa duk wahalan da nike sha bana Damuwa ina ganin ahakan ma ni kila nafi wasu ma ire irena,Baba duk baya sanin wasu abubuwan tun da in ya fita tun Safe sai Dare,in kuma ya Dawo yayi sallah yaci abinci zai kirani falo yayi ta kokarin na bayyana mai abunda nake bukata ko nake so ammh bana iya mgana Saboda Mama ina bala'in jin tsoronta kamar wata mala'ikar Mutuwa.
Baban katsina irin mazan nan ne marasa Bibiyan al'umuran gidansu shiyasa Mama ta samu dama tana Damawarta,Komai na Cefane Mama yake bamawa,Duk watan Duniya ita kuma sai ta samu nata aciki Mama tasan kan kasuwanci,Tana saida dikkakun kayan mata da maza anan ake dinka mata tana aika ma yan'uwanta dake yamai suna Siyar mata kuma har anan tana samun ciniki sosai tana harka da manyan mata bayan dikakku har Tamfofi da Lesuna tana saidawa da takalma Shiyasa take da tarin kawaye da Mutanen arziki da ke shiga suna Fita agidan,Shiyasa ko Sutura ita Baba ke bama kudin ko na Mutanen karofi ne kuma baya Bibiya,Shiyasa sai wanda taga dama ta bawa,ba kuma wanda ya isa yayi mgana duk sallah har da su Yaya Asiya Baban katsina ke yi ma Dinki adadin yadda yayi ma Badariya dani ammh ni ko Sabo daya Mama bata bani na saka sai tace Mace irina da kwance ta dace ni kuma sai mganarta ta zaunamin kayan alfarma masu kyau sai ajikin kyawawan mata wad'anda basu da wani nakasu Mata kuma irina da kwance muka Dace yawancin kayan yaran kawayen Mama nake sakawa Domin na badariya bazai min ba Na girmeta sosai alokacin,Su Yaya Asiya kuwa Kala dai'dai take jifan su dashi Yaya mariya bata da matsala ita da Hafsatu Goggo macece mai Tsayawa akanta ita da iyalanta Yaya Asiya kuma tace duk mugunta Hajiyar Dala tana barinta da Suturu Saboda ita yar gayu ce sannan mijinta Soja ne ya'yanta fes suke itama haka saboda haka Itama Yaya Asiya badai a ganta da kama mara kyau ba.
Ni dai ko da yaushe cikin Tsumma da Ragga In Baba ya gani yayi mgana Mama ta lawayance zance ni kuma bana iya karyatata agabansa,bazan taba mantawa da wata sallah ba,Sallah da na fara yinta a gidan Baban katsina Lokacin na kwashe wajen wata Tara a katsina,kuma tunda nazo ko Karofi kafata bata kara takawa ba Ga Hajiya na raina in Baba zai tafi gaisheta sai naji kamar na bisa,tunda duk karshen wata yake zuwa wani Lokacin shi da Mama suke zuwa wani lokacin shi kadai da Direba ko shi da Jamal.
Hajiya na rai na ita da su Yaya Asiya musamman Hasfatu kewar Tamadina kuwa har na cire sa araina tunda ba samun ganinta zan yi ba Tun bayan dawowata Ko mutum daya Daga karofi bai leko mu ba na dai ga Hajiyar Dala da suka taba zuwa Bikin Dangin mijinta ta sauka anan kawaye ne ita da Mama sai muguntar su tazo daya sai dai ita tafi mama ji da kai da nuna ita din watace.
Sallar azumi ne Dama da azumi duk na Rame na kara lalacewa,Ni bansan gayu ba, bansan komai mai kyau ba ni na dauka abu mai kyau a wajen mata masu kyau ake samun sa,Wani Riga da Sikat na saka cikin kwancen kayan ya'yan kawayen Da mama ke bani ne wuyan zamemin yake haka ma Sikat din yayi min yawa sai da na saka Tsumma na Taresa ajikina Hijabi ne kadai Sabo Shima Anty Mahma ce ta dinkamin domin jiya gidanta na wuni na tayata soyan Nama da aikin cinci Sai Dare ita da mijinta suka maidoni gida ita ta na da kyauta in nayi mata wahala tana min alheri takalmin kafata na Roba ne shima din Na jamal ne da ya daina amfani da shi na Dauka
Da farko Mama bata so aje dani Sallar idi ba,Sai Baba yace dani za'a tafi Ya Ishaq ya dawo agida yayi azuminsa Shi na lura kamar baya ma san kallo na shiyasa ban cika giftawa ta gabansa ba.
Lokacin da na fito Kofar gida Baba ya ganni sai da yaji kwallah ta cikamai ido,Ya kalli Badariya ta kure adaka ita da Mama,Jamal da Ya ishaq sun ci Fararan Shaddodi sai Faman sheke suke ni kuma bazar bazar kamar mahaukaciya wata yar aikin ma tafini kyan gani ni kuwa bakina kamar zai Tsage Saboda murna zan fita masallaci naga jama'a Tun kafin Baba yayi mgana Mama ta rigasa da fadin"Ke Fa'iza meyasa kika saka wadanan kayan..? Ina naki irin na Badariya..?
Sai na kasa mgana Saboda ni dai bansan da wani kaya ba,ba'a bani ba ganin Baba ya saussauto yana kallonta yasa ta kara karya murya tana Fadim"Bansan meke damun Yarinyar nan ba Abban Ishaq ko da yaushe bata da aiki sai saka Tsumman kaya nama ce ta hada su in zaka Karofi ka tafi da su arabama mabukata"
Ban yi mamakin kalaman Mama ba Domin tun zuwana gidan ba Dadewa,Ta daina Fada da Baba akaina sai ta koma aiki da Kissa shima shawaran wata kanwartace daga Yamai hure ita tace mata in tana so taci Ribar Rayuwa to ta daina tada Hankali ta yi amfani da kiss,kuma Tabbas kissanta tana Tasiri wajen Baba don nan take ya kalleni kafin yace"Haba Fa'iza ya zaki saka wadanan kaya..? Baki ga sauran yan'uwanki ba ne.?maza je ki sauya kaya mu tafi kada mu makara'"
Da Sauri Mama tace"Zamu bata Lokaci Alhaji muje in mun dawo sai ta sauya"
Sanin Halinsa na rashin bincike kan al'umura yasa tace haka,Haka muka tafi su kamar zara cikin wata ni kuma kamar yar aikin su Shikenan ko da muka Dawo Baba yayi baki yana falon waje har Dare bai kara bi ta kaina ba,Sai da Washegarin Sallah da kwana Biyu mukaje Karofi ranar dai Mama ta bani Sabon kaya na saka ta kuma ja kunnena in taji wata mgana sai na Raina kaina ni ko araina nace wazan gayamawa.?bata san ina da zurfin ciki ba ba tun yau ba,bakomai ake jinsa bakina ba.
Duk da Sabon kayane ammh da na sanya kamar wata Dussa komai ba Tsari ni kaina nasan ba kyakyawa bace ban mallaki komai na mata masu sa'a da gata ba,Kusan daman Hausawa kan ce in kana da kyau ka kara da wanka to ni bani da kyau din sannan ban iya wankan ba ballatana na kara dashi,Wani Lokacin sai Dare nake samun Damar yin wankan Tunda Dakin da nake ciki akwai karamin Tiolet to iya wankan ne ko shi ba don kyau nake yi ba Komai bazar bazar ne bansan iyakarsa ba.
Da mukaje karofi na hadu da su Ya Asiya har sai da sukace har baki na kara na rame sun yi tambayan Duniyan nan kan wani irin rayuwa nake yi agidan Baban katsina naki ce musu komai sai dai in kallesu ina mirmishi naji dadin ganinsu haka barin ma Hafsatu da ta zama kamar ba ita ba ta kara wayau da girma.
Ina jin su a tsakaninsu suna tattauna yadda Rayuwa ta jefa su a inda suke ni dai bana ce musu komai nadai san na Tambayesu tamadina suka fadamin tana Lafiya Yaya mariya na zuwa Dubata ita da Goggon Karofi sukace In Baba ya barni gobe sai muje na ganta.
Ganin Goggon Korofi yasa Mama batayi mgana ba,Baba kuma ya amince washegari chan muka wuni sai yammah muka dawo ita kanta Tamadina ta na cikin wahala gida cike da yara,wahalar tayi mata yawa sai dai ba yadda zatayi ne kwanan mu biyu muka koma Katsina,Na koma da Tausayin Hajiyar Karofi ganin jikinta duk ya kara rikicewa yanzu ma dayan barin shima ya Daina aiki Goggon Karofi da ya'yanta suna matukar kokari kan Hajiya.
Haka rayuwata ta cigaba da tafiya a gidan Baban katsina duk da irin azaban da nike sha achan ban taba jin na gaza ba sai ma nake ganin Sun yi min komai tunda zan ci na sha na kuma samu wajen barci Baba na jin Takaicin rashin Karatu na ko da yaushe naje gaishe shi da Safe sai ya kalleni yace min"Fa'iza kin k'i makaranta ko..?
Baki san ilimin zamani ginshiki ne ga rayuwar ya'mace ba..?
Ni kuma bana iya mgana sai dai na Dukar da kaina cikin Tausasawarsa yake cigaba da Fadin"Da kin Daure Fa'iza ai kina jin mgana zaki gane komai sannan zan yi ma malaman ku bayani kamar yadda nayi ma malamanki na islamiya bayanin Laluran ki"
Ina Dagowa muka Hada ido da Mama ta Sakar min harara sai jikina ya fara rawa cikin yanayin mgana ta nace"Baba shi na addinin ba Ilimi ba ne..?
Sannan shi ba Ginshiki ba ne ga rayuwar mu ba..?
Baba ya jinjina mganata kafin yace"Ginshiki ne Fa'iza babban ginshiki ba kuwa..Sai dai ka hada duka fufukan guda biyu sai ka samu na zaman duniya da Lahira"
Alokacin sai nace ma Baba"Baba ka barni haka..na islamiyan kadai ya isheni"
Zai matsamin sai Mama ta taresa tana nuna mai Tunda ban so to ya kyaleni,Shi kuma bai da Zafi sai ya Rabu dani ammh ko da yaushe kalamansa akaina na alheri ne har ya bar duniya ko kallona yayi sai yace"Fa'iza Allah yayi miki albarka In sha Allahi bazaki Taggyara ba..Ina ji ajikina kina da wata baiwar da Sanadinta zaki Daukaka watarana"
In naji haka sai nayi Dariya araina Domin bana hango ma kaina hakan
Na amince Baban Katsina ya karbo ni Hannun Goggo karofi ne domin ya inganta Rayuwa ta,sai dai bashi da Mafita ne Mama ta fi karfinsa ammh har yau bazan manta kokarinsa akaina ba.
Shi ya fadama malaman islamiyan da nake zuwa yanayina suke bani kyakyawan horo ko an gama karatu gabadaya sai an kara min bita ni kadai,Bani da wata kawa shiyasa ni kadai nake zama iyakata da kowa Mirmishi ko Sannu nasan ana mgamata ammh da yake bana ma ji Sosai ban cika Damuwa da su ba.
A farkon zuwa na gidan Mama cikin kasuwar katsina take zuwa siyayyarta ammh sai Kawarta Hajiya Barira irin masu son kudin nan ne ita ta bata shawaran ta rika zuwa kano kwantin kwari tana saro kaya alokacin Mama sai tace"Kai Barira ya yi nisa ni kinsan ban san wahala"
Hajiya barira ta rika nuna mata yanayin komai tare da fadin nachan sun fi sauki sannan zata hadata da yan kasuwar chan tunda itama tana siyayya achan har sai da Maama ta amince bazan manta ba na zo kawo ma Hajiya Barira abinci na juya naji tana ce ma Mama"ko wannan bakar yarinyar kika tara sai kuje tare ta rika Daukan miki kaya"
Mama ta kalleta kafin tace"Ko Hajiya barira"?
Tace to zauna Daman meye amfanin irin su in ba aikin wahala ba.
Da wannan shawaran Mama ta zauna tana fadama Baba ya amince tunda shi ba mutum ne mai Takura ga iyalansa ba.kuma da tace dani zata bai yi gaddama ba domin nuna mai tayi ina kokari zata nuna min komai Domin tana Tunanin nan gaba ko ban yi karatu ba zan yi kasuwanci to ai Daman haka take fadamai ko na wahalan da nake yi ne,Girki ma Baba yace nayi kankanta Mama tayi Karaf tace gwara na koya Saboda gaba gidan wani zani Daganan Baba bai kara mgana ba.
Daman tun anan ni nake kaimata Dinki chan batagwara kusa da gidan Anty binta,in ba'a gama ba sai na zauna an gama Wani Lokaci anan nake wuni buhu ne shake da kaya zam Dauko akai zuwa bakin Titi na samu Daidaita sannan in na Dawo na Hau ware ma masu kayan nasu,wad'anda za'a tafi da su yamai kuma duk ni ke shirya su Mama na gefe tana lissafin komai ban isa nace nagaji ba.
Ranar da muka fara zuwa kano sai da na raina kaina Wuni guda acikin kasuwa kuma bata Dauki dan dako ba ni ke daukan mata kaya akai kamar mahaukaciya ga yunwa ga kishi Takalmi a Hannu hijabi a hannu Wlh ko abinci bata siyamin ba Da muka Dawo sai da nayi rashin Lafiya Saboda na Jigata matuka alokacin Mama fada ta Dinga min akan na fara zama mai son jiki to in zam mike tun wuri gwara na mike Bani da wani amfani in ba Bauta ba.
Ni ba kyau ba,Ba ilimi ba,Ba ji ba,ba komai na inganci rayuwa ba,bai kamata na rika nuna gazawata ba tabbas gaskiya ta fada ba ni da wani gata a Duniya Bautar dai da ta Fada shine ya fi dacewa da mata marasa galihu ire irena
zuwa Lokacin da na shafe shekaru Shidda Cif a wajen Baban katsina bazan iya fadin irin bautar da nayi ba abu daya na sani ni Fa'iza ban sauya ba Sai dai na kara girma ammh ba Domin na sauya Daga yadda nake ba Ina nan a mai raunannan ji,Mara gata baka Mummuna mara sa'an rayuwa in ji ya Ishaq in ya ganni yakan ce Bai taba ganin mace mara sa'a ba irina komai Total zero ne a bangarena ba wani abun so ko sha'awa tare dani nima nasan haka ko badariya dake tasowa mai kyau ce sannan yar gayu kuma yar gata ni kuwa ban ma san me ake kira da gayun ba,Ni dai kawai nayi wanka na suturta jikina mganar gyaran jiki da Tsaftan jiki ban san shi ba Ba kuma wanda ya ke zaunar dani ya koyamin Ko kitso sai ni nagaji da kaina na tsefe shi kitso kuma sai in Mama taga dama zata bani kudi naje,ayi min.
Zuwa Lokacin rayuwa ta Daga,Sosai ba kamar baya ba,kawayen Mama da suka sani tun abaya in suka gani sai like sai suka rika ce ma Mama Daman wannan mummunar dangin mijin naki na nan baki aurar da ita ba.?
Mama kan basu amsa da cewa wazai kwashi Baki da muni da bebanci sannan uwa uba ba ilimi sai su yi ta Dariya suna cema Mama shikenan ta samu yar aiki to ai daman ba marabata da mai aiki maraban mu daya in da Daukoni akayi da sunan aiki za'a rika biyana albashi,Shine kawai bambamcina da mai aiki acikin wannan gidan.
Su Yaya Asiya duk sun yi aure ita da Yaya Mariya Ya Asiya acikin garin kano tayi aure wani malamin makaranta ne yana da mata da yara,Mai karamin karfi ita kuma Yaya Mariya A karofi tayi aurenta wani dan kasuwa ta aura mai rufin asiri.
Kusan tare akayi Bikin su sai dai na Ya Asiya aka fara yi ,Duka naje bikin su ammh na Ya Asiya sai da Goggon Karofi ta kira Baba ta mai mgana domin tasan Halin Mama munje kano mun yi kwanaki Tunda Bikin tare da manyan ya'yan Hajiyar Dala babansu ya Hada, da Asiya harta duka kudin siyayyan kayan Daki tare ya bada ammh Mama ta zuga Hajiyar Dala akan su ya'yanta suna da gata Asiya kuma ayi mata na Daidai da ita Daga karshe ma ita taci kudin domin duka Dawaniyar Yaya Asiya Baban katsina yayi mata shi,Duk ciki ita kadai ta auri mai karamin karfi gidan falo daya ne sai Dakuma nata da na uwargidan Ba Shakka Baba yayi mata kokari sosai,Bangaran Yaya mariya Goggo da Mijinta sukayi komai ita gidanta ita kadai wannan bikin ne har Tamadina tazo,na Yaya Asiya ne bata je ba, in naga yadda Rayuwar Mahaifiyarmu ta koma sai na kara tabbatarwa lalle bamu da gata gatanmu ya fadi tun Lokacin Rasuwar Baba.
Da ace Hajiyar Karofi na Da lafiyanta da kila abubuwa sun sauya ammh kuma tana kwance sai dai a kwantar a tayar bama wanda ya zata kai haka araye,ana zuwa gida ana Dubata har yau tana nan jiya iyau bata ko mgana Sai wanda ya kara kunnensa yake ji me take fadi in naje Hajiya ta rika kallona kenan na rike hannunta ina Fadin"Allah zai baki lafiya Hajiya"
Sai dai kaga Hawaye na Bin gefen fuskarta Hajiya na bani Tausayi sosai shekaru kusan bakwai tana jinya tana kwance waje daya,Gidan su na karofi Babban Yaron Goggo Yaya Isa ya gyara da yayi aure yake zaune da matarsa kada abar gidan ba kowa ya mutu Baba ya matsa sai ya zauna da Farko Goggon Karofi bata so hakan ba gudun Rigiman zumunci.
Ya Ishaq ya dawo gida ya gama karatu har ya samu aiki a Hukumar Tattara Haraji na kasa reshen jahar katsina,Shekaru uku da suka gabata,Sai dai baya zaman gidan in ya fita tun safe sai dare in kuma ya Dawo yana Dakinsa na fada muku tun a baya shi baima son ganina shiyasa bamu cika Haduwa ba, bana zama inda nasan zai ganni Saboda yafi kowa iya kallon wulakanci da kaskanci.
Akwai watarana tana cikin cikin Ranakun da bazan manta da su ba acikin kaddarorina ba,Muna gabda Riskan kaddaran auren mu ni da Ya Ishaq al'amarin ya faru watarana ya kira Mama a waya yace yana son abincin Mutum hudu abokansa zasu zo su yi Dinner anan biki sukayi na wani abokin aikinsu.
Nan da nan Mama ta tasoni na shiga Kirchen daman na fada muku a bangaran girki ni Fa'iza bani da makusa,Harta Mama yanzu in ba girki na