Showing 36001 words to 39000 words out of 104658 words

Chapter 13 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

215

ganshi a wajen.
     Yara ƙanana ƴammata duk an tsundumasu wannan ƙazamar harka, mafi yawansu kuma saboda abin duniyane, gashi idan kana sauraren hirarrakinsu zaka fahimci sanadin waya suka haɗe da hajiyoyin a yanar gizo, bansan hawaye sun fara wanken fuskaba, sai da naji ɗigarsu akan hannuna, nai saurin gogewa ina haɗiyar rai.
        Kowa ya ganni sai ya yabama ƙoƙarin Hajiya, suna kurantata wai ta more, dan inada karuwan jiki, dukda ba wata ƙyaƙyƙyawa bace a fuska kuwa.
          Wasu mata kuwa su biyu sai hararata suke, ni ban saniba ashe wai matan hajiyarne, waisu nan kishina sukeyi.
    Kai jama'a, ALLAH kai mana tsari da asararriyar rayuwa dai.

      Anmin wankin kai saikace wata amaryar data samu miji, sannan aka kawo mai kwalliyar da zatamin, bansan yanda zan musalta muku ɗunbin tashin hankalin da nake cikiba a wannan lokaci har aka gama kwalliyar.
      Duk wannan shiri da akeyi bikin zai gudana ne bayan sallar isha'i, amma abinda zai baka tsoro babu wanda naga yayi salla a cikinsu koma ambatarta a bakunansu.
      An kawomin wata riga mai ƙyau da zan saka, harda takalma da sarƙa da nake zaton ta gwal ce, dan ƙyawunta a ido kawai ya isa ka shaida hakan.
        Dakatar dasu nayi akan inason sai nayi sallar isha'i, da mamaki kuwa sai naga abun ya basu dariya, ni dai ban kulasu ba naje nai sallata, bayan na idarne na duba takardar da saurayinnan ya bani ɗazun da rana a ɓoye, bayanin danaga yayi a ciki ne ya sakani miƙewa da sauri, kaya na buɗe drawer ɗin Uwargida na ɗauka, na saka tare da gyara jikina tamkar ba niba, a yanda na fito inba sani kaimin na tsiyaba bazaka taɓa gane niceba, balle dama tunda akaimin kwalliyar babu wanda ya ganni a cikinsu har Uwargida.
         Cikin taimakon ALLAH na fito falon cikinsu ina taku da yauƙi, na saki jikina tamkar nima irinsu ce, duk da na fahimci wasu suna min kallon rashin sani, amma  harkar ta wayewace sai kowa ya amsheni ba tare da bincikeba.
        Uwargida ta miƙe akan zataje ta fito dani, hakan yasa wasu manyan mata suka bita ɗakin, suna shiga watar gidan na ɗaukewa baki ɗaya.
      Jikina har rawa yake na ajiye takalma da jakka tare da sarƙar danasa ta gwal ta uwar gida na fito da lalube, dan dama a hanyar ƙofar fita na zauna kamar yanda saurayin ya shawarceni.
     Ina fitowa kuwa ana kama hannuna, cikin raɗa yace, “Karki damu nine”.
       Bansan inda muke jefa ƙafa ba, kasancewar gidan babban gidane, maido wutar da akayine ya saka gabana faɗuwa, ni dashi duk mukaja birki ba tare da mun shirya ma hakanba.
      Surutai muka fara jiyowa wanda da alama ni suke nema, wasu na faɗin ta gudu, wasu na cewa ai da alama wata baƙuwace data shigo ta saceta kota kuɓutar da ita, dama su basu yarda da baƙuwar fuskarba.
     Cikin hanzari yaja hannuna muka faɗa ɗakin mai gadi dake a bakin gate, hawaye kawai nake jikina na rawa.
      Duk bidirin nemana da sukeyi muna jiyosu, wata naji tana tambayar Uwargida ko ina Sani?.
      Uwargida tace tun da rana ta turashi can wani ƙauye danya bar gidan ma tace ya kwana acan da safe ya dawo.
     Kallonsa nayi, dan da alama na lura shi ake nufi, kenan wasu sun fara zargin akwai saka hannunsa.
    Tun suna ɗaukar neman nawa wasa har abun ya fara caja musu kai, dan haka suka rabu, akabar ƙalilan a cikin gidan, ɗaukar kowa na fice, saboda sun iske gate buɗe.
     Saurayin ya ɗan leƙa ta Window, sai da ya tabbatar babu kowa kusa yay min nuni muje, hijjab ya bani na saka, ta bayan ɗakin mai gadin muka iske tsani, duk da tsahon katangar nan haka na hau tsanin nan ga tsoro na cina ga hawaye, da taimakonsa muka dira can baya, dayake ta canma ya saka tsani, kuma akwai abokinsa dake tsaye yana jiranmu.
     Duk naji ciwo a jikina, amma sam tashin hankalin da nake ciki baisa na damu da ciwukanba.
          Babu ɓata lokaci muka bar wajen, muna matsawa muka jiyo hayaniyar su Uwargida suna faɗin “tanan ta biyo” kugafa harda tsani, aiko tabbas akwai waɗanda suka taimaka mata ta gudu kenan. Buɗar bakin wata sai naji tace “kodai su ƴar daɓas ne”.
       Bamu jiyo amsar da Uwargida ta bata ba mai adaidaitar da suka sakani ciki yaja yay gaba.
      Na damƙe jakkar da saurayin ya bani a jikina sosai ina cigaba da yin hawaye, yanzu kuma ko ina zan dosa kenan?.
     Wata zuciya ce tace, “Bilkisu duk kibar wannan guje-gujen, kibi shawarar zaɓi biyu, kodai ki miƙa kanki ga ƴan sanda, kokuma ki nema gidan ƴan uwan mahaifinki ko mahaifiya kije ga wani, idan sun riƙeki shikenan, idan sun nuna bazasu iyaba sai kisan mafita”.
      Wannan shawara itace tai tasiri a raina, koda mai napep ya tambayeni batare da na shiryaba na faɗa masa anguwar da zai kaini.
    Ganinai ya tsaya da napep ɗin yana kallona, “Hajiya kinsan kuwa mi kike faɗane? Anguwar nan gaskiya tana da nisa, nikuma wanda ya bani ke ya cemin tashar mota zan kaiki”.
     Hawayen fuskata na share, murya na rawa nace ka taimakeni bawan ALLAH, kaga ni mace ce, tashar mota kuwa wajene mai haɗari musamman da daddare, amma anguwar da zaka kaini yanzu akwai wanda na sani, wajenta zanje kafin safiya idan ALLAH ya kaimu”.
      “Gaskiya Hajiya bazan ɓoye mikiba, a darennan bazan iya zuwa har canba, yanzu idan mun tafi sai mukai goma na dare bamu isaba, to yaushene na ajiyeki harna juyo nikuma na dawo gida. Ki dai faɗi wani wajen bayan wannan ɗin”.
         “Shikenan na gode” nai maganar cikin jan majina ina sharce hawaye, zuwa can wani tunanin ya sake faɗomin, bara naje gidan Inna zainaba, ko arziƙin kwana ɗaya tamin, da safe saina doshi gidan baba manu ɗin da nai niyyar zuwa, duk da dai bana zaton samun alfarma daga ko ɗayansu, amma zan gwada, karya zam na yanke hukunci akan gaibu.
     Sake faɗa masa anguwar da zamuje nayi, dan haka ya tada napep muka cigaba da tafiya, sai yake cemin to ai shima cannema anguwarsu.
     Wani daɗine ya kamani, dan dama dai bawani iya gane gidan inna zainaba ɗin zanyiba sai na haɗa da tambaya.
     Shiru mukai na wasu mintuna, lokacu-lokaci ina cigaba da sharar hawayena.
    Muryarsa na tsinkayo yana cewa, “Baiwar ALLAH kibar kukannan, ita rayuwa duk jarabawace, haƙuri kawai kesa a cimma buri, da alama dai wanda ya sakaki a keken nan mijinkine ko?”.
       Shiru na masa ban tankaba, jin haka shima sai ya tsuke bakinsa, mun ɗan ƙara tafiya na sake jiyoshi yana faɗin, “Dai-dai ina zan ajiyeki baiwar ALLAH?”.
        Muryata a dasashe saboda kukan dana sha nace, “Kace nan anguwar kake ai kaima? Dan ALLAH ko kasan gidan dogo kafinta?”.
     Da sauri ya juyo ya kalleni, bakinsa har harɗewa yake wajen faɗin, “Can gidan zakije?”.
      “Eh” na faɗa cikin mamakin razanar danaga yayi.
     Yace, “Kai, to ai babanane dogo kafintan hajiya? Dan ALLAH kozan iya sanin ke wacece?”.
      “Gidankune? To ko dai Yaya Shu'aibu ne?”.
     “Ikon ALLAH, tabbas kuwa kin canka dai-dai, Shu'aibu ne kuwa, wacece ke dan ALLAH? daga ina kuma?”.
      Murmushin yaƙe mai haɗe da takaici nayi, ganin yanda taɓarbarewar zuminci tasa ko juna bamu saniba dukda kusanci mai ƙarfi da muke dashi, shi kansa sunansa kawai nakeji a bakin Innata, amma ban taɓa ganinsa ba a ido, “Da wahala ka sanni, sai dai bansan ko kasan Asiya gurguwa data rasu kusan shekara ɗaya kenan?”.
       “Tabbas na santa, dan gwaggona ce ma ai, tunda ƙanuwar innatace”.
     Murmushi nayi mai ciwo, na maida kallona ga wata tukubar mai nama da muka tsaya dai-dai satinsa, mazane cike da wajen saboda mai shayi dake gefe, daga can kuma gabansu kaɗan mai doya da ƙwai, zaman masu wannan sana'a ne ya maida wajen dandali, harda masu suyar awara, gaddamar siyasa kawai kake jiyowa a wajen kamar zasu fara danbe, cikin share hawaye nace, “To ita mahaifiyata ce, ni kaɗaice kuma ƴarta tilo data bari a duniya”.
        Jinai kawai yanata jero salati da sallalami, na maida hankalina sosai a garesa, cike da tsagwaron mamaki yace, “Yanzu nan dama Gwaggo Asiya nada ƴa amma ban saniba? Har tambaya nayi wlhy a randa mukaje zana idarta sai akace ai bata haihuba, to kodai dama baƙya tare da ita?”.
      “Muna tare” kawai na iya cemasa saboda abinda ya tokaremin maƙoshi.
     Saurin tada Napep ɗin yayi yana faɗin, “Kinga yi haƙuri na tsareki da tambayoyi a titi, muje gida duk a yisu............

________________________
JAZUGA
________________________

            Alhaji, ina baka shawara muyi amfani da maganat likitannan, gara ka ɗauke yaronnan ya koma yin jiyya wani waje, mukuma saimu fito mu sanarma duniya ya rasu, a ajiye wata gawar a maimakonsa kamar yanda mukai na yarinyarnan.
      Wlhy wannan sabon d.p.o ɗin baida mutunci, sannan baya amsar cin hanci, kaga dai yau kwanansa uku kawai da kawowa ko? To wlhy harya lalata wasu ɓoyayun cases guda huɗu da wancan d.p.o ɗin yaci ƙuɗi a kansu, to kaga kafin yazo kan bayanan case ɗin yaronka gara dai musan mai yuwuwa. Saboda tsaf zai gano gaskiya ta tashi mana mu duka wlhy”.
     Wani irin nishin damuwa Alhaji lado yaja, yace, “Zanbi shawararku, amma lallai naso ace burina ya cika an kama yarinyarnan, dan shine kawai zai kawo ƙarshen wannan case ɗin”.
      “Indai dan kamatane karka damu, zamu cigaba da ƙokari har sai mun ganta, kuma bazamu bartaba, tunda kaga yanzu kowa zai ɗauka yaronka ya mutune ai”.
     “To shikenan yallaɓai, nagode sosai da ƙoƙarinka, zan shirya mota a darennan abar asibitin da Jazuli, da safe kuma saiku bamu sabuwar gawar a maimakonsa”.
        “Hakan yayi Alhaji, na barka lafiya”.

    Bayan tafiyar ɗan sanda Alhaji Lado yata kai kawo akan zancen, tsarin likitan shima ya masa, amma fa yana burin a kama yarinyar kodan ya wulaƙantata, ya ɗaukama yaronsa fansa.

Nace, “Humm”.

     Duk yanda suka shirya haka aka tsara, washe gari saiga gawa a zuwan ta jazuga, mutane da yawa sunyi farin ciki, dan koba komai saji sakat, waɗanda sukaima wannan muwa kuma mutanene ƙalilan, suma na jikinsa, mutanen gari dai ko a fuska basa nuna jin kunyarsu akan gakan.
     Haka akayi zana idar gawa aka kaita makwancinta, yayinda acan bayan fage Jazuga ke cigaba da jiyya.

★★★★

     Haka abubuwa sukaita shuɗawa, jikin jazuga na samun sauki, sai dai da alama dukan da Bilkisu tai masa ya taɓa masa ƙwalwar kai, dan idan abun ya motsa haka zaita dukan kansa yana wata irin ƙara har sai an bashi maganin barci, idan kuma ya farka sai ka ganshi normal sai kuma ya sake motsa masa.
         Sunje asibiti akan matsalar, suma dai magani suka bashi, tare da tabbacin inhar yabi soka komai zai dai-daita.
      Dalilin sun sanarma duniya Jazuga ya mutu dole ya haɗa kayansa da yaransa suka bar garin akan sai komai ya lafa zai dawo.
     Wannan abu ya sake masa ciwo, tare da dasa tsanar Bilkisu mai tsanani fiye da farko ma a zuciyarsa, yakuma saka a ransa duk randa suka haɗu kasheta kawai zaiyi kowa ya huta.

😱🙆🏻‍♀️.


_________________________
JAWAAD
_________________________

                 Duk da ɓacin ran Shahudah daya fito dashi a rai, hakan bai hanashi zagewa ya maida hankali akan aikin da suke son farawa ba shi da su Aliyu abokansa.
       Duk suna zaune ne a cikin falon gidan da ya kaisu, Jawaad yace,
      “Tabbas a cikin satar kokino akwai lauje cikin naɗi, kuma tare dana kusa dashi akai hakan, bayanan dana samu yanzu haka sune, tare da amaryarsa suka dawo daga ƙasar Colonbia, kowa ya kasa gane yanda har aka sacesa babu wanda ya gani, hakanne yasakani ɗaura alamar tambaya akan wannan matar tasa, lallai tasan wani abu akai, dan a yanda tsarin saukarsa da baro airport ɗin ta kasance babu wani mahaluki dazai iya kutse wajen aikata hakan, kunsan a yanda tunanina da nazarina ya bani an sacesa?”.
      Dukansu kai suka girgiza masa cike da mamakinsa, duk da dai dama sunsan Jay mayene akan bincike da bin ƙwanƙwanto.
    Murmushi yayi yana komawa jikin kujera ya kwanta, sai kuma ya tashi zaune sosai fuska a haɗe yana tsaresu da idanu, “Tabbas lokacin da aka faɗi sacesa yana cikin gidansa ne, daga baya aka fita dashi acikin gidan”.
      “Kamarya kenan Jay? ALLAH ka sakamu a duhu, danni kam wannan case ɗin ban fahimci komaiba akansa, tayaya hakan zata kasance bayan kowa ya shaida Alhaji Kokino lafiya ya fita a jirgi, agaban kowa kuma ya shiga mota direbansa yaja shi, kuma basu tsaya ko inaba sai a cikin gidansa.........”
     Cikin katsesa Hafiz yace, “Ni kasan mina fahimta Jabeer, kamar Jay kanason kace mana dai babu wanda ya sace Alhaji Kokino ko? Kawai matarsa tayi ƙarya da hakanne saboda wani dalilinta ko manufa ko?”.
       Kai Jawaad ya shiga girgizawa, ya miƙe tsaye hannunsa goye duka a baya, “Fahimtata tasha banban da taku, nakula kuma irin Fahimtar da sauran jama'a sukaima abin kukeyi a yanzu, “Tabbas an sace Alhaji Kokino da gaske kamar yanda zancen ya fita duniya taji”.
        “To waya sacesa kenan? Miyasa kuma ka kawo matarsa cikin zancen?”.
      Aliyu daya tsare Jay da idanu ya faɗa.
      Murmushi Jay yayi kawai ba tare daya amsawa Aliyu tambayarsa ba, ya taka a hankali zuwa gaban Window yana leƙa harabar gidan, kusan sakwan goma kafin ya juyo gasu Jabeer da suka zuba masa idanu kamar wani magiji.
       “Aliyu wannan shi nake so ku fahimta nima? Ni kaina inason nasan miyasa matarsa ta shigo cikin zargina”.
     Dukansu ajiyar zuciya suka sauke.
         Hafiz yace, “To yanzu dai saimu tsunduma aiki kawai, sai dai ina ganin Jay lokaci yayi da zaka yafema Rose ta dawo tare damu, kowa yasan amfaninta a cikinmu, bai kamata muyi sakaci da itaba ko a wannan lokacinma”.
     Gaba ɗaya fara'ar fuskar Jawaad ta ɗauke, sai dai baice komaiba ya tako ya dawo wajen zamansa ya sake zama.
     Maimakon ya taya zancen Rose da Hafiz ya ɗakko sai ya ɗakko wani maganar daban ma.
     Sunsan bazai tankaba, dan wannan salonsa ne idan baya buƙatar abu, suma duk sai suka ƙyalesa kawai akan zasu cigaba da lallaɓashi har itama Rose ɗin ta dawo tare dasu su koma su biyar ɗinsu tamkar yanda suka saba a baya.....


_________________________
SHAHUDAH
_________________________

          Tunda Jawaad ya fice tai tsaye a wajen, bata motsaba amma ta dasama takardun daya bari manyan idanunta.
      A wannan yanayin Hajiya Humaira tai sallama ita da ƙanwar Shahudah ɗin mai suna Aamila.

       Ko kusa bataji motsinsu ba, sai da Hajiya Humaira ta taɓata ne tai saurin juyowa a tsorace, dan tazata Jawaad ne ya dawo.
     Ajiyar zuciya ta sauke tana faɗawa jikin momynta ta fashe mata da kukan shagwaɓa............✍🏻

Page 16

...........Wai nikam kukan mi kike Sister? Ni yanzufa lamarinki har mamaki yake bani, akan Brother Jawaad duk kin zama wata lusara.
     Hararar Aamila Hajiya Humaira tayi, hakan yasa ta ɓame bakinta.
        Ta mai da kallonta ga Shahudah dake kwance a kafaɗarta, “Babie na tashi muyi magana”.
    Tashi Shuhudah tayi zaune, Hajiya Humaira tace, “miya sakaki kuka?”.
        Cikin tsagwaron taɓara Shahudah ta fara magana da shashshekar kuka, “Momy wai ni yau Bb yake iya cewa na zaɓi ciki koshi? Harni yake iya furtama zai saki akan cikin da bai gama zama mutumba ma, dama ashe baya sona ban saniba....”
    Ta rushe da kuka tana faɗawa jikinta.
      Hajiya Humaira tai murmushi tana buga bayan Shahudah, “Ba sonkine bayayiba Shahudah, wannan abun daya ambata miki ma shine ya nuna yana tsananin sonki, duk wanda yake son haɗa jini da kai aikuwa yana sonka Shahudah”.
       Shahudah ta ɗago da sauri baki a kumbure, “Wlhy Momy baya sona, tunda har bazaiso abinda nake soba, ni gaskiya ban shirya haihuwa yanzuba, salon nazo na tsufa yaje yana kallon wasu a waje ko?”.
       Dariya Aamilah ta kwashe dashi tana faɗin, “Tab ashe su wata ta kusa komawa jagwal, na rantse karma ki yarda, toke ta yaya kikai sake ciki ya shiga jikinki ma?”.
       “Zanci ubanki Aamila, tashi kibar ɗakinnan” Hajiya Humaira ce tai maganar a zafafe.
    Hakan yasa Aamila tashi ta fita tana ƙunƙuni da buga ƙafa na rahin samun isashshiyar tarbiyya.
      “Mamana karki biyema Aamila kinji, ki kwantar da hankalinki akan wannan cikin tunda yazo a kuskure, koshi kaɗai kika haifa ya isa haka, zuwa nan gaban idan kinso saiki ƙara ɗin, kinsan dai Jawaad yanada Zuciya idan aka ƙure haƙurinsa, kaɗan daga aikinsa ya aikata dukkan abinda ya faɗa, kuma Abbanku ma yaji faɗa zai miki, insha ALLAH haihuwar wannan cikin sai dai ya ƙara miki daraja a wajen Jawaad badai ya rage mikiba, ALLAH yasa ki haifa mana little Jawaad dai mu shine babban fatanmu”.
      Shahudah dai da maganar bata gama shigarta ba tace, “Yanzu kowa dai baya sona a gidannan, ni wlhy barmuku ƙasar zanyi to, dama saboda shi na dawo cikinta, tunda ya fara wulaƙantani gara nai gaba abuna”.
     “Kefa wata sa'in baki da man kai Shahudah, lokacin da ake nuna miki Annabi saiki ta ƙoƙarin rimtse idonki haba, banason shashanci mana, to wlhy ki tabbata inhar kika zuba da cikinnan ba Jawaad kaɗaiba hatta ni da Abbanku mantawa zamuyi dake shasha kawai mai girman banza”.
      Yanda Hajiya Humaira ta fusata sai abun ya bama Shahudah mamaki, hakane yasaka ta tsura mata ido kawai, miyasa kowa kejin haushinta akan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login