Showing 102001 words to 104658 words out of 104658 words
Chapter 35 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete
shiga da hanzari.
Kamar yanda ya umarta hakan nayi, ina fitowa na iske wanda aka turo ɗin yazo, shima yana sama dani, dan haka nai masa gaisuwar girmamawa kafin bashi takardun na koma ciki.
Duk da na iske su Mummy a falo ban iya zama ba, gashesu kawai nayi na shige ɗaki abuna, dan ina buƙatar samun filin yin tunani akan abinda muka tattauna da Amina.
Sosai komai yake neman ɗaure kaina, duk da kuwa Alhmdllh yanzu na samu ilimi sosai game da bincike, dan ko a wajen horaswa da muka samu, nafi maida hankalina anan sosai, alamu sun nuna Qaseem da Salman basa gida, shin akwai wanda ya dawo daga baya kenan s cikinsu? Ko kuwa kuku zan zarga kai tsaye ne? Baba mai gadi tsoho ne, duk da dai tsufansa bai kai ace bazai iya aikata makamancin hakanba, to amma miyasa zan zargesa ne? Lallai ya dace nama fara bincikarsa akan shiga da fitar kowa a wannan ranar.
Da wannan tunanin naɗan samu nutsuwa, amma koda nai shirin barci na kwanta sai ya gagara, babu abinda nake sai saƙawa da kwancewa tare da tunanin iyayena.
_______________________________
Washe gari litinin muka tashi da shirin aiki, tunda na gama shiri naga harna shiga kicin ina shan tea Yah Qaseem bai shigoba nasan bai kwana gidaba jiya kenan?.
Tea ɗin kawai na iya sha na fito, babu wanda ya tashi har yanzu a mutanen gidan.
Nai addu'a na fita tamkar yanda na saba. Yau kam sai driver nabi, muna isa tamkar jira na samu saƙon kira.
Na nufi inda ake kiran namune na haɗu da Yah Qaseem, murmushi mukaima juna, na gaishesa cikin girmamawa tamkar yanda na saba.
Shima ya amsamin da kulawa yana tambayata yaya gidan?.
“Alhmdllh Yah Qaseem, yaya aikin naka? Ai ni bansan baka kwana gidaba sai yanzu da safennan?”.
Yace, “Oh, wannan wace irin matace dani? Ban kwana a gidaba amma sam bama ta saniba”.
Haka kawai sai maganarsa ta sakani jin kunya, naja baby hijjab ɗina na rufe muskata ina murmushi, matsowa yay kusa dani gab tamkar zai shige mini jiki, ya kai bakinsa dai-dai saitin kunnene yana faɗin, “Baƙauya”.
Baya na ɗan ja saboda kusancin da muka samu yayi yawa, na janye hijjabin zan bashi amsa karaf idona akan mutumin ga, gabana yay wata masifaffiyar faɗuwa saboda cin karo da wata shegiyar harara daya watsomin, tuni fara'ar fuskata ta ɗauke baki ɗaya saboda bugun da ƙirjina yakeyi.
“K lafiya?”
Ƴah Qaseem ya faɗa cikin tsareni da idanu.
Cikin rawar baki da hadiye yawu da ƙyar nace, “B..babu k..omai”.
Idanunsa ya ɗauke da ga kaina ya maida saitin inda nake kallo, sai dai yana juyawa shi kuma yana shigewa Office.
Sake juyowa yay gareni, “Wai haushi kikaji dan nace miki baƙauya?”.
Murmushin ƙarfin hali nai masa ina girgiza kai, nace, “A'a yayana”.
Ƙaramar dariya yayi ya dungure min kai tare da zagayeni ya wuce abinsa da faɗin, yaje gida sai ya dawo.
Ko a dawo lafiyar ban iya ce masaba, na kuma kasa ɗaga koda ƙafata a wajen saboda tsabar yanayin dana tsinci kaina.
“Haba Bilkisu! Ke kin cika matsala wlhy, tsayuwarmi kuma kike anan?”.
Nannauyan numfashi na sauke jin muryar Ummie a kusa dani, taja hannuna ba tare da ta sake magana ba zuwa inda ake jiranmu.
Sosai mamaki ya kamani ganin inda ta kawo mu, zan iya kiransa Office kai tsaye, amma mazauna cikinsa da zasuyi amfani da shi aƙalla mutane goma cif.
Tunda naji zuciyata ta dai-daita nasan baya wajen, dan haka nakai dubana ga kowa, iya dai mune da aka tara ranar, tare da yallaɓai Hafiz.
Ya gyara tsaiwarsa yana mana bayani yanda zamu fahimta sosai.
“Wannan Office ne da zai kasance na musamman ga waɗanda boss ya aminta da ƙwazonsu, dan haka sai kowa ya duba, idan kaga sunanka to kana cikin waɗanda ya zaɓa, idan baka ganiba to ba hakan yana nufin bazai iya aiki da kai bane ko bai yabama ƙoƙarin kaba, kawai dai kasan a ranka hakanne mafi alkairi a gareka”.
Duk cikin girmamawa muka amsa masa.
Ni kasama dubawar nayi, sai Ummie ce tabi sauran itama tana dubawa, inajin wasunsu suna murna, alamar dai sunga sunayensu.
Nima a bazata naji Ummie ta rungumeni tana faɗamin ni da ita duk muna ciki.
Ban san miya saba, banji baƙin cikiba, kuma banji wani murnaba, kawai dai nayi murmushi ne dan karta zargi wani abu..
A cikin mu goma ɗinan bakwai mazane, mu uku mata, ni Ummie sai ɗayar mai suna Divine.
Komai na wajen an yisane da tsari, dan an saka mana shingai da kowa bazaiga abinda ɗan uwansa keyi a sashensaba sai idan yaso hakan.
Naji daɗin yanda aka saka Ummie kusa dani, duk da ba'a layi ɗaya mukeba wajen zamanta yana kallon nawa, sannan mune ƙarshen bangon wajen.
Duk wanda yake cikin wannan tafiya yayi farinciki, saɓanin ni da bansan manufar zaɓin da zuciyata ta ɗauka ba.
Shigowar Yah Qaseem station ɗin ya samu labari, bansan dalilinsaba naga ya fara faɗa tamkar zai cinyeni ɗanya, ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba.
Tun ina saurarensa da mamaki na koma al'ajab, daga al'ajabi nakoma ban haushi, har takai abin ya bani tsoro, danni bansan minene laifina a cikiba? Kuma ince nan wajen aikine, bamu da dalilin cewar sai inda muke buƙata za'a zaɓamana.
A cikin masifarsa ta yau ne nakeji cikakken suna mutumin nan, wato *_Jawaad Abdul-aziz yusif_*.
Ni dai bance ƙalaba har yaci jarabarsa ya tsire, daga ƙarshe yace na fitar masa a office.
Na fito ina share hawayen da suka ziraromin babu shiri, sai shi kuma naci karo da shi.
Tafiya yake a fusace tamkar wani ingarman doki, yana ƙoƙarin saka bindiga a aljihun wandonsa na baya, yayinda su yallaɓai Jabeer ke take masa baya suma fuskarsu babu walwala.
Yana ƙoƙarin shiga motar da aka buɗe masa ne ya ɗago, sai ko idanunmu cikin na juna.
Saurin janye nawa nayi ina kauda kai, a ƙasan zuciyata ina mamakin miya fusatashi har hakane?.
Bani da mai bani amsa, dan haka sai ma tashin motarsu na jiyo.
Har na bar Office ban kuma sakashi idona ba, hakan na nufin dai basu dawoba daga fitar da naga sunyi ɗazun kenan.
Sai kuma har naje gida abin na damuna, haka kawai naji na damu da tsagwaron damuwar dana karanto a fuskarsa, ranar da wannan abun na kwana a raina.
______________________________
Washe garin safiyar talata muka tashi da dawowar aunty Shahudah ƙasar haihuwarta tamkar yanda naji a bakin su Aunty Aamilah, danni dai babu wanda ya sanarmin hakan.
Ban damuba, dan nasan koba'a faɗaba bani da muhimmancin sanin irin waɗanan abubuwan tunda basu ɗaukeni dai-dai da suba har yanzu, Dad ne kawai yakemin kallon na mutum mai muhimmanci a cikinsu, sai ko Ya Qaseem da shima nake ƙyautata masa zato akaina.
To ni daima aiki nai ficewata abina, dan shine mai muhimmanci a gareni a yanzu, nabar saƙon sannu da zuwa a faɗa mata wajen Aunty Aamilah, dukda dai a ɗage ta amsamin ban damuba nai wucewata driver ma yau ya ɗaukeni, dan Yah Qaseem ma yau bai kwana gidaba.
Na fiskanci akwai aiki mai mihimmancin gaske da yakeyi a kwanakinnan, musamman ma yanda ya maida kansa busy ko'a Office bai cika zamaba sosai.
____________________________
Ƙarfe biyar na yamma jirgin su Shahudah zai sauka, dan haka tun ƙarfe biyu su Mummy suketa shirin tarbarta, ansa kuku ya shirya mata abinci na musamman kala-kala tamkar ba cikinta kaɗai zai ciba.
Tsabar gata Mummy da kanta ta tisa ƙeyar Aamilah suke gyara ɗakin Shahudah, Aamilah sai tunzura baki take gaba dan bata saba da aikinba.
Jitake tamkar taje ta kira Amina, dan ta fahimci amfaninta sosai a gidan a yau, hakama Bilkisu, dan tasan badan wannan ƙaddararran aikin da Bilkisun keyiba ai da yanzu itace zatai gyaran.
Haka dai suka kammala Mummy ce ƙarfin aikinma, dan danan ɗakin ya ɗauki ƙyau da haske tamkar ba shiba, shima yau yasan maishi zata dawo garesa.
Huɗu nayi Salman ya baro office ya taho gidan domin zuwa tarbar gimbiya Shahudah😝.
Gudun karma a ɓata mata rai huɗu da rabi suka bar gidan, sun gwammaci su suje su jirata, amma ba ita taita jiransu ba.
Zaman da baifi mintuna ashirinba kuwa jirgi ya sauka, fasijoji suka fara fita, sosai idanun su Mummy nakai.
Can sai ga zillaziyya zankaɗaziyya gimbiyoyi mandiyoyin oga Jawaad ta fito cikin takun ƙasaita da gayu.
Sanye take cikin wandon blue da yay masifar kama jikinta, sai riga ruwan hoda an rubuta Beauty da ado mai ƙyalƙyali a gaba, siririn gyalenta data yana a kai shima ruwan wandon, sai rigar sanyi data ɗaura a ƙugu, ta toshe fuska da eyeglasess mai nuna blue a jiki.
Tabbas tayi masifar ƙyau, kuma duk wanda ya gani tilas ya ƙyasa dan ta cancanta.
Aamilah ta tafi da gudu gareta, hakan yasa Shahudah sakin akwatinta da jakkarta ta hannu a ƙasa ta rungume ƴar uwarta, takalman ƙafarta masu masifar tsini badan sunada maɗauri ba babu abinda zai hana su sakata ta faɗi.
Wasu daga cikin mutane sai kallonsu suke, musamman irinmu ƴan ƙauye da bamu waye ba😒, dan harda bakuna muka hangame lokacin da Salman yazo ya rungumeta shima.
Yanda suka ƙanƙame juna lamarin zattakaici, ta sakeshi ta nufi Mummy ta rungume itama, sai kuma suka sake rungumeta baki ɗaya, hakan dai na nuna suna cikin tsantsar farin cikin ganinta duk da sukanje su ganta a can musamman ma Mummy da Aamilah.
A sabuwar motarta da Dad ya saya mata akaje ɗaukarta ita kaɗai, ta kalli Mummy ta kalli motar cikin alamun tambaya.
Dariya duk sukai mata, Aamilah ta sanar mata ƙyautar Dad ce.
Wani ihu Shahudah ta saki tana ɗane Mummy, motar da kullum take nafarkin mallakarta, ta ƙiyasta kuɗinta bazasu kai ta sayaba shiyyasa ta haƙura, ashe Dad zai cika mata burinta.
Yanda take matuƙar murnar ne yasa mutane suka sake maida hankalinsu a kallonsu, wasu zato suke ko daga karatu Shahudah ta dawone akai mata wanna irin tarba da ƙyauta mai tsoka, har dai suka shiga mota zuwa gida idanun mutane na kansu.
Daɗi ya ishi Shahudah sosai, dan Dad yay mata bazata irin wadda bazata taɓa iya mantawa ba, sayen motarnan yay bala'in kai mata ko ina a cikin ƙoƙon ranta, har tana tunaninma wace kalar murna zatai masa yasan taji daɗi.
Murnar motama ta hanata nutsuwa taci abincin kirki a cikinta, duk da tarin abincin da aka shirya matan kuwa.
Wayar Aamilah ta amsa ta kira Dad ɗin, maimakon tai masa godiya da addu'ar fatan alkairi sai kawai taita masa ihun murna da faɗa masa ya cika mata burinta, shi dai yana saurarentane yana murmushi, yanataso yaji ta masa godiya tamkar yanda idan yayma Bilkisu ƙankanin abu take masa amma sai yaji tsit.
Maimakon hakan ya taɓa ransa sai ya danne kawai, yama cigaba da nuna mata farin cikinsa na dawowarta, ya kuma tabbatar mata a satinnan shima zaizo ƙasar kodan ita.
★★★
Duk yanda Mummy taso tai haƙuri Shahudah ta huta sannan suyi zancen Jawaad ta kasa, haka ta zayyane mata halin da ake ciki yanzu na tallar ƴammata da ake masa a cikin family ɗinsu.
Ran Shahudah ya matuƙar dugunzuma, ta shiga masifa da faɗin Jawaad natane ita kaɗai, duk yarinyar datai gigin shigar mata rayuwar miji wlhy sai ta halakata.
Tai shiri akan a daren zataje family house ɗin su Jay, amma sai Mummy ta hanata, ƙin sauraren Mummy tayi, sai da ƙyar, dan ta nuna mata abinfa YAƘIN SUNƘURU yakeso yanzu, dan haka kar tayi gaggawa, ta jira taji abinda suka shirya akan al'amarin............✍🏻
Alhamdullahi ala kulli halin🙏🏻😢.
Anan na kawo ƙarshen littafin ƘWAI CIKIN ƘAYA na ɗaya. Abinda na rubuta daidai ya rabbi ka haɗamu a ladan baki ɗaya, wanda nayi kuskure kuma ALLAH ya yafe mani da ku da kuka karanta🙏🏻😭.
Wannan shine wasa farin girki.
Ga dai Bilkisu ta kafa alƙalamin bincike akan al'amarin da ya faru da Amina. Shin zata dace da gano wanda yayi? Ku fans ma to wa kuke zargine akan wannan al'amari? (Ina jiran amsarku).
Ga Shahudah ta dawo, kuma da burin komawa gidan mijinta, sannan ga burin iyayenta da bamusan manufarsaba sam, shin zatayi nasara kokuwa dai iskace ke wahal da mai kayan kara?🤔🤒.
Ya maganar zaɓar matar aure da family nasa keson yayi? Kuna ganin zasu haƙurane? Kokuwa zasu sake amincewa da wautar Shahudah a karo na biyu?.
Ga Bilkisu alamu sun nuna zata koma tawagar Jay, yaya kuke tunanin wasan zai kayane? Faɗuwar gaba da kallon kallo da sukema juna tsakanin ita da Boss ɗin minene manufarsa?😌.
Qaseem ya ɗau zafi da komawar Bilkisu tawagar Jawaad, yaya kuke ganin za'a kwashe, zai bartane? Kokuwa zai canja salon wargaza tafiyar?🤫
Ina Jazuga? Ina Firdausi da iyayenta? Ina labarin gidansu Uwargida? Ina labarin gidan hayar dasu Bilkisu suka rayu da iyayenta? Shin duk Bilkisu zata waiwayesu ne kokuwa dai sun zama labari?🙃
Mahaifiyar Jawaad babu wanda yasan inda take, akwai kuma maganar da ta taɓa shiga tsakanin Jawaad da dattijuwar dake aiki gidan Alhaji kokino ba giyar yaroba, shin kuwa babu lauje a cikin naɗi? Dan zaurancen nasu yayi kama da🤫🤭.
Kenan dai akwai ƙurori da cakwakiyoyi sosai kenan, duk kuma a cikin littafin ƙwai cikin ƙaya kashi na biyu🤓🥱⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀.
BILKEESU IBRAHEEM MUSA
(Bilyn Abdull ce😘🤫)
Inama ɗaukacin musulmai barka da shigowa sabuwar shekarar musulinci, Alkairin dake cikinta ALLAH ya tabbatar dashi a garemu, saɓanin haka ALLAH ya karemu a duk inda muka tsinci kayinmu, idan ta kasance shekararmu ta ƙarshe a duniya rabbi ka ɗauki ranmu muna cikin masu imani da soyayyar MANZON ALLAH a ruhinmu, ALLAH ka gafarta mana baki ɗaya🙏🏻😭
Duk wanda naima ba daidaiba a rayuwata ta online ya gafarceni, nima na yafema duk wanda ya cutamin, ALLAH yasa dalilin hakan nima ALLAH yay min rahama bisa nawa kurakuran🙏🏻😭
Bilyn Abdull ce🤙🏻
ALLAH ka gafartama iyayenmu da mu baki ɗaya🙏🏻😭