Showing 54001 words to 57000 words out of 104658 words
Chapter 19 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete
cikin Lamcy ga Abdul riƙe da ita ya ciza bakinsa yana ƙara dannama Lamcy.......
“Abdul mikakeyi haka kuma? Kasheta fa kayi?”.....
Dariya ya kwashe da ita yana jan wuƙar ya fitar daga jikin Lamcy, “Bata da wani amfani a yanzu a gareni, ta gamamin aiki mizaisa na barta? Dolene ta wuce kafin ɗan uwana da ke ku bi bayanta, ni kaɗaine na cancanta da wannan dukiyar hhhhhhhhh!!!!!!!......”
Tsagwaron tsorone ya bayyana a zuciyar Hajiya Usaina, ta zabura baya da sauri tana ƙwalalo idanun mamakin Abdul, kanta yay gadan-gadan, ya ɗaga hannu zai daɓa mata wuƙar aka riƙe masa hannu ta baya.
Juyowa yay yana huci dan duk zatonsa Lamcy ce bata mutuba ta riƙesa, amma a mamakinsa sai yaci karo da fuskar jami'in dake bincike akan ɓatar yayansa, Jawaad Abdul-aziz yusuf.
A wani irin razane ya zaro idanu yana sakin wuƙar, zaiyi magana Jabeer ya ɗora yatsansa kan bakinsa yana faɗin, “Shiiiiii!!”.
Sai kuma ya daki ƙafar Abdul ya zube ƙasa jiki na rawa.
Aliyu yay ƙoƙarin kwance Alhaji Kokino da Jawaad ya ɗaure, Hafiz kuwa nakan su Abdul da binduga, sai Rose dake ƙoƙarin bincikar Lamcy wadda da alama da wuyama takai labari.
A take suka tattaresu, ana ƙoƙarin fita dasu, tuni jiniyar motor ƴan sanda da Ambulance dasu Jawaad suka buƙata tunkan su shigo bacar har sun iso.
Alhaji Kokino da Lamcy asibiti aka wuce dasu, yayinda Abdul da hajiya karima aka nufi ofishin su Jawaad dasu.
__________________________________
Da daddare duk muna zaune a falo ana hira, duk da ni a takure nake daga can gefe, ina dai saurarensune kawai, na murmushi nayi na mamaki da takaici na girgiza kaina, dukda suna tsangwamata idan na zauna cikinsu hakan bai hanani son zamanba, dan koba komai ina ƙara ilimin sanin duniya daga garesu, sannan ina rage kaɗaici da damuwa.
Aunty Shahudah da dama ita kaɗaice babu a cikinmu ta sakko daga saman bene cikin wando da riga, sai siririn gyale data yano bisa kai, ganin key ɗin mota a hannunta da bag ya saka mummy faɗin, “ke kuma ina zuwa haka mamana?”.
Tana ƙoƙarin ƙarasowa cikin falon sosai take fadin, “Mummy jirgin su my friend ya kusa sauka, kin sanshi bayason jira”.
“Okey amma ai baƙya fita ke ɗaya ba adaren nan, Salman ya tashi kuje, tun ɗazunma da driver kika tura da bai ɗakkosa ba?”.
“Mum driver kuma? To da wane yaran zai ɗakkosa?”.
Dariya duk suka sanya, banda ni dama na kasa fahimtar zancen, duk da tun ɗazun dama naji tana faɗin zuwan matafiyin dana kasa yarda a raina namijine duk da yanda take alaƙanta komai nasa da suffofin namiji.
Tashi Salman yay yana tuttura baki irin shi baiso zuwanba, ta jefa masa key ɗin hannunta tana harararsa, amma batace komaiba.
Juyawa tai ta kalleni cikin yamutse fuska tana faɗin, “K karna dawo naga wannan baƙar fuskar taki a falon nan, dan jack ya ganki wlhy zaima iya amai, dan bai saba ganin trash irinki ba”.
Murmushi nayi idona na cika da ƙwalla na miƙe na nufi ɗaki ina maimaita kalmar trash data kirani dashi, sai dai kuma abin mamaki abun baimin zafi sosai ba, dan zuwa yanzu a halayyarta kuma kaɗanne bata zubar na ganiba, gado na haye abina, na faɗa duniyar tunanin da yazamar min abokin rayuwa da ɗebe kewa.
Ban sake sanin hidimar da masu gidan keyiba har washe gari, duk da bayan kusan awa biyu da tafiyar su Aunty Shahudah na fara jiyo ƴar hayaniyarsu, sai kuma gidan ya koma tsitt.
★★★★★★
Da safe ƙin fita nai har lokacin da nakeda tabbacin sun kammala yin breakfast, sai da naji gidan yay shiru sosai sannan na fito, babu kowa a falon hakanne ya bani ƙwarin gwiwar nufar kicin, Amina mai aiki nata ƙoƙarin gyara kicin ɗin, gefe kuma kuku na shirin ɗaura abincin rana, gaisawa mukai duk da suna bani girma kamar kowa na gidan, amma hakan baisa na ɗauki kaina sama da suba, Amina maƙwaftan suke da gidan namu, sai dai su ba masu ƙarfi bane, hakan yasa take shigowa aiki a nan duk wata ana biyanta, tacemin da can ita da mamanta sukeyi, da ciwon ƙafane ya takura mata sai ita tacigaba dayi ita kaɗai.
Itace ta nunamin abincina, dan haka saima na zauna a kujerar kicin ɗin kawai nahau karyawa muna hira da ita, inda shima kuku ke ɗan sakko nasa zancen da turanci, sai hausa ɗai-ɗai wadda sam babu daɗin ji daga harshensa.
Wani irin kuka naji a bayan Windown kicin ɗin, hakan ya sakani kallon Amina ina faɗin, “Minene haka ke kuka?”.
Ƴar dariya tayi tana bani amsa da cewar, “Jojon big Aunty ne”.
Nasan Shahudah suke cema hakan, dan haka nace, “Jojo kuma? Waye mai wannan sunan?”.
Yafitoni tai da hannu alamar nazo na gani, na ajiye dankalin dana ɗauka zansa a baki na miƙe zuwa gareta, kaɗan taja labulen Windown ta yanda zan iya leƙa wajen.
Aunty Shahudah na hango zaune cikin korayen ciyayin da aka gyara wajen da wani ɗan ƙaramin kare mai kama da jikin zaki a saman cinyarta tana shafawa, sai wani tsamurarren bature zaune gefenta daf, Aunty Aamila kwance itama a wajen kanta kamar bisa cinyar baturen suna dariya.
Labulen na saki ina sauke ajiyar zuciya, na dubi Amina sosai, “To Amina wanene jojon a ciki? Dan da alama dai wannan shine baƙon da yazo jiya kenan?”.
Tace, “Karen dake cinyarta shine Jojo, baƙon kuma Jack, a farkon fara aikina gidannan nazo na iske Big aunty da wani karenta jojo, sai dai wataran tsautsayi Boss yazo gidannan ya takashi da mota ya mutu, lokacin har a asibiti ta kwanta jiyyar saboda mutuwar karennan kuwa”.
“Tofa, ALLAH ya ƙyauta to, akan karen? wanene Boss ɗin to? Dan nasan kam ba ƙaramin fin ƙarfinta yayba da har bata ɗauki wani matakiba?”.
Dariya Amina da kuku sukayi, Amina tace, “Aikam kamar kin sani yafi ƙarfin nata, dan har yanzu batayi ko tari hakan a gabansa ba saboda mutuwar karen, ballema ayi tsammanin bin ba'asin yanda abun ya faru, ba kowa bane face mijinta”.
Kaina kawai na jinjina, na koma wajen abincina batare dana ce komaiba, nikam harma naji inason ganin wannan miji na aunty Shahudah, dan kuwa lallai yana ganin shashanci tsantsa daga gareta, inhar shima ba irinta baneba.
Ina cigaba dacin abincina ina sauraren hirar Amina da kuku harna kammala na tashi na fita.
A falo naci karo da Yaya Qaseem daya shigo ransa a matuƙar ɓace, hannu yasa ya wurgani gefe saboda na shigo masa gaba ba tare dana saniba, kaɗan ya rake fuskata bata bugi tebir din gilas dake wajenba.
Na sauke numfashin ambaton Alhmdllh ina binsa da kallon mamaki harya gama haurawa saman benen yana ƙwalama mummy kira tamkar zai tsaga gidan biyu dan azaba.
Tashi nai tsaye jikina har yanzu rawa yake, na shiga murza hannuna daya bugu da kujera yanamin zogi.
Yaya Qaseem ne ya sake sakkowa yana zage-zage da harshen turanci Mummy na biye dashi tana ƙoƙarin riƙesa da masa magana da hausa ita kuma, amma sam yaƙi saurarenta.
Saiga su Shahudah sun shigo suma daga waje da ɗan gudunsu ita da jack da Aamila.
A take falon ya hautsine da hayaniya, nidai ina daga gefe ina kallonsu, sai dai bana fahimtar komai banda wani suna *Jawaad* danaji Qaseem nata ambata, yayinda Shahudah ke masifa tana nunashi, yako kai mata duka sai da jack ya kare shi aka sameshi.
Abu kamar wasa saiga gidan ya harmutse sosai, Mummy sai fama take dasu amma sunƙi suyi shiru, ganin hakanne ya sakata fashe musu da kuka.
Tsitt falon yayi kuma, sukai kanta banda Qaseem da ya fice abinsa rai ɓace, da sauri jack yabi bayansa, Shahudah da Aamila kuma suka zagaye Mummy, Salman baya gidan dai da alama.
Wannan lamari nasu yayi matuƙar bani mamaki, har yamma kuma ban samu jin abinda zai fahimtar daniba, sai abu ɗaya kacal ne kawai na ɗan gane, da alama dai daga wajen aikine aka fusatar da Qaseem, kuma wanda ya sakashi fusatar yanada alaƙa dasu musamman ma Shahudah da haushin Qaseem yaso ƙarewa a kanta...............✍🏻
Page 22
...............Tun shigowar Qaseem hukumar tasune ya tabbatar akwai abinda ya faru, dama kuma ya samu kirane daga sama akan yazo da gaggawa.
Shigarsa wajen da manyansu suke tare dasu Jawaad ya saka zuciyarsa tsitstsinkewa, musamman tozali da ƴan tawagar Jawaad da yay su Hafeez.
Shi Jawaad ma yana zaune ne kansa a ƙasa saboda ciwon da yake masa, baima san da shigowar Qaseem ɗinba.
Bayan shigowar Qaseem an jira mutane biyu da ake jira suma sun shigo, kafin a fara gudanar da yabo da jinjina akan namijin ƙoƙarin da su Jawaad sukai.
An kuma tabbatar da wanke su Aliyu daga laifin da ake zarginsu dashi wanda yay sanadin zamansu cikin jail.
Take wajen ya ɗauki tafi.
Abinfa zai baka mamaki ko motsi Jay baiyiba a wajen, duk da laifin abokansa da aka wankesu baisashi ya ɗago yama kalli kowa ba sam.
Qaseem ya buƙaci yin magana, dan haka aka bashi damar yi.
Duk da son danne fushinsa da yaketa ƙoƙarin yi hakan ya gagara, sai da muryarsa ta fallasashi, a kausashe yake magana akan yanda aka maida aikin ta bayan fage bayan kuma shi aka damƙawa, ya cigaba da maganganun da suke nuna sukar Jawaad kai tsaye tareda muƙarrabansa, harma yana nuna akwai shiri a cikin lamarin, sai dai idan Jawaad ɗin dama yasan inda Alhaji Kokino yake.
Jay da duk yake sauraren komai yaɗan taɓe bakinsa ba tare daya ɗago ba, ɗakin taron kuma yay tsit an rasa mai bama Qaseem amsar tambayoyinsa, kowa ya zubama Jawaad ido ana buƙatar ƙarin bayani daga garesa, amma abin mamaki tamkarma baisan sunaiba.
Hakanne ya saka Aliyu dake kusa dashi taɓashi kaɗan.
Jawaad ya ɗan ɗago ya kalli Aliyun idanunsa sunyi jajur na gajiya da barci,
“Boss kanafa jin mi yake faɗa”.
Guntun murmushi Jay yayi kawai ya maida kansa yanda yake yana lumshe idanu, sai da Qaseem ya gama ɓaɓatunsa har sir Ahmad ya dakatar dashi sannan ya dawo ya zauna yana huci, ba ƙaramin haushin ƙin kulashi da Jawaad yayba yaji.
Sir Ahmad ne yay bayanin da kowa ya gamsu a wajen bisa shakkun da Qaseem yaso jefa musu akan Jay, daga nan sukai abinda ya tarasu aka sallami kowa.
Dan Jawaad yaƙi cewa kowa komai, koda aka buƙaci jin ta bakinsa Jabeer yaba damar yin bayani, acewarsa shi kansa na ciwo, da yake kowa yasan yanada lalurar ciwon kai da sam idan ya motsa masa bayason takura sai akai masa uziri.
Wannan abunne ya sake fusata Qaseem matuƙa, koda suka fito sai ya tare Jawaad ɗin bisa hanya.
Ko kallonsa Jay bai yiba ya raɓa ta gefensa zai wuce, nanma Qaseem ya sake taresa.
A fusace Jawaad ya fisgo bindigar dake jikin Rose ya nuna Qaseem da ita, dan zuciyarsa a maƙoshi take, shiyyasa sam yaƙi kula Qaseem ɗin tun farko.
Babu wanda yay zaton da gaske Jawaad yake saida ya saki harsashin ciki gadan-gadan akan Qaseem, Aliyu ne ya hankaɗa Qaseem ɗin gefe harbin da Jawaad yayi ya sami ƙofar wani Office dake a wajen.
Nan take wajen ya hargitse da ihu, inda shima Qaseem ya fiddo bindiga wai zai harbi Jawaad, da ƙyar aka rirriƙesa.
Cikin huci Jawaad ya nuna Qaseem ɗin yana faɗin, “Wlhy idan baka fita hanyata ba duk abinda nai maka kaine ka jasa, ka kama kanka Qaseem, karkai wasa da ɗaga maka ƙafan da nakeyi.....?”
Jan Hannun Jawaad da sir Ahmad yayine ya sakashi yin shiru, sai da ya kaisa har Office ɗinsa sannan ya sakesa.
Faɗa ya shiga masa akan waya kaisa aikata wannan gangancin? Yafa tuna Qaseem a samansa yake, baya tsoron abinda zai iya biyo baya?, duk da kowa yasan Qaseem yana shiga rayuwarsa hakan bazai hana a juya abun ta wani ɓangarenba, musamman da akasan Jawaad ɗin yana aiki tuƙuru, wanda hakan yana ɓatama wasu a cikinsu rai da ruguzasu ta hanyoyi da dama sosai.
Ganin Jawaad ɗin baice komaiba shima sir Ahmad ɗin sai yay shiru, dan yasan Jay yanada haƙuri, amma tabbas yanada zuciyar jaraba idan ka kaisa maƙura.
Ruwa ya fiddo a firij ya miƙa masa, babu musu Jawaad ya amsa ya hau sha, sai da yasha fin rabi sannan ya ajiye yana sauke numfashi a gwame.
Ya tsani takura a rayuwarsa, shiyyasa shima bai san takurama kowa, amma Qaseem yaƙi ya riƙe girmansa, ya rasa miya tare masa a wannan duniyar?, tun suna ƙanana Qaseem bayason yaga cigabansa ko farin cikinsa, baisan miyasa hakanba?.
Nannauyan numfashi ya kuma saukewa yana maijin kewar mahaifiyarsa, sosai yake bukatar ɗumi irin na uwa a kusa dashi, sai dai shi tashi ta masa nisan kiwo.........
Sir Ahmad ya katse masa tunani ya dafashi a kafaɗa, ɗago jajayen idanunsa yay yana kallonsa, cikin sigar lallashi sir Ahmad ɗin yake ma Jawaad nasiha akan yacigaba da haƙuri da lamarin mutane, haka rayuwa take, kai kana harkokinka baka damu da kowa ba amma wani shi idanunsa na bisa kanka gaba ɗaya, kowa a rayuwa da kagani akwai tasa gaddarar, maƙiya kuma sune gishirin zaman duniya.
Jawaad ya gamsu da jawaban ogan nasa, dan haka yay masa godiya sosai.
A waje kam sosai hayaniya ta ɓarke, su dai sauran waɗanda ke wajen sun zama ƴan kallo, dan kuwa dai faɗan na manyane.
Inda su kuma manyan hankalinsu ya tashi, da ƙyar aka saka Qaseem a mota aka bar wajen dashi, amma sai iƙirarin kashe Jawaad yakeyi.
Wannan shine dalilin shigowarsa gida yana banbamin masifa🤦🏻♀.
_______________________________
Washe gari da yamma Jack da Aunty Shahudah suka fita yawo, basu dawo gidan nanba sai kusan sha ɗaya na dare, tunda yazo gidan kuma ban yarda mun haɗa hanyaba kamar yanda ƙawarsa ta buƙata, duk da ma dai na lura yau bata da walwala, kallo ɗaya zakai mata ka fahimci ma bata da lafiya, dan tunda suka dawo daga yawo ita da Jack take ƙudundune a cikin kujera a falo, inaji tanama Amina masifa akan ta kashe mata ac.
Washe gari da safe kuma Abba ya dawo, kowa a gidan yayi farin cikin dawowarsa, dan ranar tare akai zaman cin abinci baki ɗaya har Yaya Qaseem da rabon dana gansa tun randa ya dawo a fusace.
Na zata Abba zaima Aunty Shahudah faɗan ganinta a gida tare da zuwan jack, amma sai naga luf, saima taɓara take zuba masa salo-salo wai ita ciki ya dameta, sannan hannu biyu ya amshi jack ɗin da shikuma yakemin kallon mamakin wannan kuma daga ina?.
Ni dai inda yakema ban kallaba, haka kuma ban saki jiki naci abincinba saboda harar da kowa ke jifana da ita a wajen, idan ka cire dad da lokaci-lokaci yakan kalleni yana maganar miyasa banason cin abinci?.
Amsa ta ɗayace kacal, “Dad inaci”.
Yanda Aunty Aamila keta faman takamin ƙafa ta ƙasan tebirin yasa na miƙe badan na ƙoshiba nace ya isheni, dad ne kawai yay min faɗan hakan, amma kowa baice uffanba.
Nidai nabar wajen ina murmushin yaƙe, ina shiga lungun ɗakinmu kuwa hawaye suka fara rige-rigen zubowa, ban sharesuba kuwa, haka na faɗa saman gado inayinsu, ban sake sanin hidimar da sukeba har washe gari da safe, inda Dad ya buƙaci ganina afalonsa.
Albishir ɗin da Dad yamin akan zanje na zana jarabawa duk sai ya mantar dani komai, bakina ya gaza rufuwa saboda tsantsar murna da farin ciki, yinin ranar da wannan abu na yini, shiyyasa duk abinda akaimin baiko ɓata raina ba.
_________________________
Har Jawaad ya baro office ya dawo gida ransa babu daɗi sam, ya kumazo ya iske Shahudah bata dawo ba, tsaki kawai yaja yay shigewarsa ɗakinsa, wanka kawai yay ya kwanta dukda masifar yunwar dake cinsa, amma gajiyar dake tare dashi har bishi-bishi yake ganin gari.
Yana kwanciya kuwa barci mai ɗan karen nauyi yay awon gaba dashi, bai sake sanin wane hali ake cikiba sai gabda sallar magriba.
A rikice ya tashi saboda salloli da suka wucesa, yay azamar yin ramuwarsu yana jero istigifari ga UBANGIJI.
Bayan ya idar yay shirinsa tsaf ya fice zuwa gidan kakansa daya haifi Mamansa, mijin kakarsa mama maryam kenan.
Ya iskesa yana da baƙi, dan haka bayan ya gaishe da baƙin yay wucewarsa cikin falon tsohon, kuloli yaci karo dasu, dan haka ya zauna yana buɗewa, yasan dai bai wuce tuwo ba, kuma daga gidan Ummansa ne ake kawoma baba, dan tunda mama maryam ta rasu bai sake aureba, shi kaɗai yake zaune a bunsa a gidan saisu idan sunzo.
Tuwonsa ya zuba yaci ya ƙoshi yanamai jin nishaɗi, yaushe rabonsa da abinci mai nagarta irin haka? Yanama zaton tun masar da umman ta aika masace.
“Kai ja'iri, tuwon nawa kake cinyewa?”. Baba dake shigowa ya faɗa yana harar Jawaad da wasa.
Dariya Jawaad ɗin yayi idonsa akan kakansa da tsufa ya kama sosai, “Haba mai ran ƙarfe kaimafa tuwon na gidan Umma nane, tunda kaƙi fita a gwaurantaka kayo mana amarya”.