Showing 57001 words to 60000 words out of 104658 words

Chapter 20 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

212

  Dariya sosai tsohon yayi, yasa sandarsa ya daki kafaɗar Jawaad da saida ya sosa wajen saboda zafi.
       “Dan gidanku, ni da kai munada banbanci ne? Kaima da kake da matar baka da banbanci da tuzurun da baima taɓa aureba”.
      Murmushi Jawaad yay yana ɗan taɓe bakinsa, saboda tsoho dai ya taɓo masa inda ke masa ƙaiƙayi, aiko bai bada amsaba ya miƙe yaje ya wanko hannunsa sannan ya dawo ya zauna.
     Baba dake binsa da kallo yace, “Daga ina kake a darennan?”.
         Jawaad ya zauna kusa da baba yana jingina kansa da kafaɗarsa yace, “Daga gida”.
       Shafa kansa baba yayi yana maijin tausayinsa, yace, “Yau an tuna da tsoho kenan?”.
        “Nikam dama kana raina, wani aikine kawai ya dabaibayeni sai yau na sauke nauyinsa”.
       Murmushi baba yayi, “Naga komai ai a tv Jawaad, shiyyasa a kullum bana haufi a gareka, sai yanzu ne nake sake gaskta maganar mahaifinka da tun bakasan kanka ba yake dangantaka da aikin ƴan sanda, ashe shiya san miya hango mana”
        Murmushi kawai Jawaad yay yana haɗiye abu mai ɗaci a maƙoshinsa, daga nan ya cigaba da sauraren yabo da kakansa keta jerawa akan ƙyawawan halayyar mahaifinsa, a haka barci ya sake sacesa.
      Baba yakai dubansa ga fuskar Jawaad, ganin yay barci sai yay murmushi yana kai hannunsa ya shafa kumatun Jawaad ɗin.
     Ido Jawaad ya buɗe a hankali ya kallesa, baba yace, “Tashi kaje ɗaki ka kwanta”.
      Bai musaba ya miƙe ya shige bedroom ɗin baba, lafiyayyen ɗaki dayasha gyara tamkar bana tsohon da rayuwa taima nisa ba, lallausan gadon baba Jawaad ya haye, yaja bargo ya rufe jikinsa yana lumshe idanunsa, kafin kace mi nan nauyan barcin ya sake ɗaukesa kamar wasa.

Yau dai kam Jawaad anan ya kwana tare da kakansa, sai da yay sallar asuba ya karya da breakfast ɗin da Faisal ya kawo daga gidan Umma sannan yayma baba sallama ya tafi gida akan yana nan dawowa anjima zasuyi wata magana da baba.
       Baba yace “to ALLAH ya kaimu saika dawo, ALLAH ya tsareka akoda yaushe”.
       “Amin” Jawaad ya amsa yana fita.


_________________________
       BAYAN SATI BIYU 
_________________________

                  Har wannan lokacin Aunty Shahudah da dai na gida, bata komaba kuma mijinta bai zoba, sannan jack na nan bai tafiba sai kace gidan tsohonsa.
          Nikam tun ranar da mukaci abinci tare ban sake zama inda yakeba, saboda har ɗaki ta biyoni ta ƙaremin zagi da cin zarafi akan ko Dad ne ya kuma buƙatar na zauna dasu cib abinci nasan yanda zan zame, idan ba hakaba wlhy saita ci mutuncina.
     Haƙuri kawai na bata nikam, dan yanzu ni bana ɗaukarta sahun masu isashen tunani.
         Tamin wannan abun ma da kwana uku Dad yace na shirya zuwa makarantar da zanje na zana jarabawata, ranar dai kamar anmin gafara naji, har kukan daɗi nayi kuwa.
    Kwana biyu na cika na tattara komai na sayayyar da Dad ya yo mani domin tafiya, dan makarantar boarding school ce, sai dai yanda naji su Aunty Aamila na faɗin wai ban dace da makarantar ba nasan babbar makarantace.
     Ranar dazan wuce na lura kowama murna yake da tafiyata, dan Salman harda faɗin, “ALLAH raka taki gona, koba komai sa huta da kallon baƙar fuskata abin amai”.
      Dariya mummy da aunty Aamila suka sanya, dan mu kaɗaine a wajen, Shahudah da jack suna can baya suna hira.
        
      Har bakin mota Amina da kuku sukai min rakkiya, sai da sukaga na shiga mota mun fice a gidan sannan.
      Na share ƙwallar data zubomin ina murmushin kewa da farin ciki.  


😅👏🏼ALLAH ya bada nasa takwara, sai dai fa ni ƴar team Shahudah ce😆😜, bara na fece kafin naci mazga⛹‍♀.

_________________________

               Tunda Jack ya bata shawarar zubar da cikinnan burinta ya dawo sabi fil, dan ya tabbatar mata Jawaad burga kawai yake mata babu wani sakinta da zaiyi tunda yana masifar sonta.
      Ta shafa cikinta da ayanzu haka yake mata ciwo, tabbas tana wahala akan wannan cikin da bata shiryama zuwansa ba, gashi harya fara sakata ƙiba, abinda ta tsana kenan a rayuwarta, duka shekarunta nawa da za'ace ta ɗauki ciki? Kamar yanda Jack ya faɗa, ita kanta tasan dan tayi gaggawar yin aurene kawai, bakomai ya jawo hakanba kuma sai ƙaunar Jawaad data tunzurata, da shawarar Mummynta, anya kuwa bazata zubarba kawai ta huta? Iyakaci dai ayi badakalar da za'ai na ɗan lokaci ta wuce, daga baya komai zai lafa a wuce wajen.
       Zama tai a bakin gado ta dafe kanta tare da cije bakinta saboda murɗawar da cikinta ke mata, kusan min tuna uku tana a haka kafin ta samu ya lafa mata, sai wani zazzaɓi da takeji wanda ya zame mata jiki a yanzu kullum yamma saita yisa.
       Wayarta ta ɗauka ta kira Aamila, babu jimawa sai gata ta shigo ɗakin.
       “Sisi lafiya kike kirana?”.
       Miƙewa Shahudah tayi idonta akan Aamila, “Aamila na yarda da shawararku zan zubar da cikinnan kawai”.
      Zaro ido Aamila tayi tana ɗan ja baya, “Wai da gaske dan ALLAH?”.
       “Na taɓa miki maganar hakan?”.
      “A'a, ai abunne da mamaki, keda kike mugun tsoron Brother Jawaad karya rabu dake, amma yanzu lokaci ɗaya kizo da batun amincewa”.
        Tsaki Shahudah taɗanyi, “Karki damu, ni nasan barazanace kawai, son da bb kemin bazai taɓa yarda ya rabu daniba wlhy, kawai yanamin burgane dan karna zubar, idan kuma yay haƙuri nan gaba ai zan haihun, amma gaskiya ba yanzu ba”.
       “Kinyi ƙyan kai gaskiya, yanzu ke mikike buƙata?”.
        “Shawarar da nake buƙata kenan daga gareki, ɗazun jack yace yasan maganin da zaimin aiki ba tare da nasha wahala ba, inaga kije kufita tare kozaku samu a wani pharmacy ɗin, sai dai dan ALLAH karki bar Mummy ta sani”.
       “Karki damu, insha ALLAHU babu wanda zaiji”.
  
      Koda Aamila ta fice sai Shahudah ta koma ta zauna, wayarta ta ɗauka ta dannama Jawaad kira, sai dai harta katse bai ɗagaba.
       Text massege ta tura masa kamar yanda suka shirya da jack, kodaga baya cikin ya zube wai bazai zargeta akan itace ta zubarba.
        Mummy batasan mi suke shiryawa ba, a gabanta Aamila da jack suka fita a gidan.
     Sun bazama neman maganai cikin manyan pharmacy's ɗin garin, amma samunsa ya gagara, saboda ba kowane ke saidawa ba, dabara ce ta faɗoma Aamila a rai ta kira number Munira cikin yaran gidan su Jawaad, dan ta taɓa bata labarin wata ƙawarta da ta raka zubar da ciki.
          Sun sanar mata abinda suke buƙata sai dai basu faɗa mata gaskiyar wanda zaiyi amfani da shiba, itace ta kira likitan daya bama ƙawarta wancan maganin ta haɗasu dasu Aamila, shi kuma yay musu kwatancen inda zasu sameshi.
          A asibitinsa da ya kasance privet suka samesa, babu ko ɗar suka biya kuɗin daya yanka musu ya basu allurar da za'ai amfani da ita, a cewarsa itace tafi aiki shap-shap kuma bata cutarwa.
     Sai da jack ya duba sukkan bayanan allurar ya kuma tabbatar da maganar Doctor sannan ya suka amsa suka nufi gida.

            Jack bashi da shamaki da shiga ɗakin Shahudah a duk sanda yaso, dan haka koda suka dawo a gaban idon Mummy ya shiga, Aamila kuma ta zauna a falon dansu ɓadda hankalin Mummy wai.
    Ƙudundune ya iske Shahudah zazzaɓi ya rufeta, ya yaye bargon data rufa yana taɓa gefen wuyanta, buɗe idanunta tayi, ganin jack ne yasata miƙewa da ƙyar tana kallonsa, “Kun samo?” tambayar data fara jefa masa kenan cikin harshen turanci.
     Kansa ya ɗaga mata, ya ciro allurar daga aljihunsa yana nuna mata.
       Amsa tayi ta jujjuya allurar a hannunta, sai kuma ta kallesa da tambayarsa wai miyasa basu sayo maganinba? Yafasan batason allura.
     Bayanin duk yanda sukai ya bata, ya kuma tabbatar mata wannan allurar tafi maganin inganci, hakan ya saka ta aminta da batunsa.
       Hannu ta bashi yay mata allurar tana matse baki, can ƙasan zuciyarta kuwa cike take da fargabar abinda zai biyo baya daga Jawaad.............✍🏻

Page 23


..........Tunda aka buɗe mana katafaren gate ɗin makarantar muka shigo nake baje idanu da hanci ina kallon wannan tsararren gini da tamkar ba makaranta ba.
        Yanzu nan ni Bilkisu ɗiyar malam Ado makahoce cikin wannan makarantar? Abu kamar mafarki kamar kuma almara. Niko tayaya zan manta da Dad a rayuwata.
       Ƙwallar data cikamin ido na share ina fitowa daga cikin motar, ɗalibai duk suna cikin aji, hakan yasa security kawai kake iya gani na shawagi sai malamai.
          Mun samu tarba ta musamman ga wani malamin da nakeda tabbacin yazo garemune bisa umarnin Dad, na gaishesa cikin girmamawar da naga nuna jin daɗinsa saman fusakarsa.
      Bisa jagorancinsa muka isa har Office ɗin shugabar makarantar, bayan an bani wani form na cike aka haɗani da malamai uku sukaimini interview, duk da karatun bai kasance ɗayaba sun yabama ƙoƙarina.
         Na sauke nannauyan numfashi da naji cewar komai yayi, duk da dai ba ɗari bisa ɗari na ƙoƙartaba amma sun amsheni, to dayake kuma abun ya haɗa da harkar kuɗi sai babu wata matsala aka kammala komai tsaf.
       Malamin nan dai yana tare dani muka fito, sallama mukai da driver ya tafi domin shi ya gama aikinsa, sai kuma naji hawaye sun cikamin ido, a gaban idona ya wuce.
           Malamin ya kalleni yana murmushi, “Ki kwantar da hankalinki komai zaiyi dai-dai kinji, alkairin Alhaji a gareni bazaisa na zuba ido kiƙi nasara ba, sai dai idan ALLAH ya ƙaddaro hakan, akwai yarinyata anan makarantar insha ALLAHU zan haɗaki da ita, zata taimaka miki sosai kafin ku fara zana jarabawar, tunda akwai tazarar kusan 5weeks yanzu haka insha ALLAHU”.
           Cikin girmamawa nace, “Nagode sosai, ALLAH ya saka da alkairi, ya kuma bada ladan zuminci”.
       “Amin” ya faɗa yana maijin daɗin addu'ar yarinyar da yaba tarbiyyarta, dan kuwa yakuma tabbatarwa ba'a gidan Alhaji ta tashiba, saboda sanin da yayma yaransa da sam tarbiyya bata gama wadatar da suba.
       Security ɗin dake kusa ya kira, shine ya kwasar min kayana muka nufi inda yace min Hostel ɗinmu kenan, dan lokacin an tashi Ɗalibai duk sun shige ciki.
      Mun iske hostel ɗin shiru babu wata hayaniya a cikinsa, sannan ɗalibanma ɗai-ɗai muke gani suna shawagi, kowa kuma harkar gabansa yake babu ruwan wani da wani, a ƙofar wani ɗaki mukaja birki, security ɗin ya ƙwankwasa ƙofar, babu bata lokaci aka buɗe.
          Budurwa da bazata gaza sa'a taba ce ta fito, sai dai shigarta zai tabbatar maka da wahala ta kasance musulma.
      Ganin malamin dake tare danine yasakata juyawa da gudu ciki tana dariya, ko minti biyu bata rufaba sai gata sun fito itada wata mai tsananin kama da malamin.
       “Daddy baƙuwar harta iso?” ta faɗa cikin zumuɗi tana ɗan tsalle a gabansa.
        Murmushi yayi mata, ya jinjina kansa tare da faɗin “Eh Ummie na ta iso, gata nan ma sunanta Bilkisu Adam”.
      Juyowa tai gareni cikin ɗoki tace, “Barka da zuwa Bily cikin makarantarmu”.
        Haɗiye hawayen farin cikin da suka cikamin ido nayi ina amsa mata, banyi zaton zanje waje a karbeni lokaci gudaba kamar yanda Ummie tai mini yau, gata dai da gani itama ƴar gatace amma sam babu fuskar wulaƙanci a tare da ita.
      Ta kama hannuna cikin nata tana sauraren bayanin da daddynta ke mata a kaina cikin nuna zaƙuwa da ɗoki, ya maida dubansa gareni yana faɗin, “Bilkisu wannan itace ɗiyata kamar yanda na sanar miki, karkiji komai ki saki jikinki da ita, insha ALLAHU zakiji daɗin zama da ita kamar yanda nima nake ƙyautata mata zato a kanki, komai na tsarin makarantar zata fahimtar dake, karkuma ki cutama kanki, duk abinda ya shige miki duhu ki tambayeta kinji”.
       Kaina na ɗaga masa ina risinawar girmamawa a garesa, nace, “Insha ALLAHU Daddy, ngd sosai da karamcinka a gareni”.
        “Karki damu Bilkisu, Alhaji Aliyu ya wuce hakan ma a gareni, ALLAH ya bada nasara ni bara na wuce”.
      Sallama yay mana Ummie nata masa shagwaɓa ya wuce ya barmu.
        Itako ta rungumeni tana sake min barka da zuwa, ta shiga ƙwalama wasu kira da nake ƙyautata zaton ƙawayentane, dan kuwa daga cikin ɗakin suka fito harda wadda ta leƙo ɗazun, su uku ne, kuma duk bazasu wuce sa'anni naba.
        Biyu a ciki sun amsheni hannu biyu, ɗaya kam dai sai yamutse fuska takeyi, ban damuba dan na saba ganin irinta tun shaiɗan na yawo da ɗan kanfai cikin duniya.
       Sune suka kwasar min kaya har cikin ɗakin dake da gado biyar kacal a cikinsa, sannan komai tsaf tamkar ba makaranta ba.
       Zaunar dani Ummie tayi a gado na ƙarshen ɗakin tana faɗin, “Wannan shine gadonki, akwai mai shi da, amma ALLAH ya mata rasuwa hutun da mukaje ɗinnan, yaya tace, tanada ciwon sikila ne.
        Nace, “ALLAH sarki, ALLAH ya gafarta mata, kukuma ya baku haƙurin rashinta”.
      “Amin” Ummi ta faɗa tana sharar hawaye.
       Tace, “Sunana Sumayya Sadik, amma anfi sanina da Ummie saboda sunan Momy na aka saka min”.
      Murmushi nayi mata, nace, “Nice name, nima zance Ummie ɗin tunda sunan Momynmu ne”.
     Ƴar dariya tayi tajin daɗi, ta nuna sauran su ukun, “Waɗanan ƙawayenmu ne, mu biyarne a guruf ɗinmu kafin rasuwar ƴar uwata, mu ƙawayen junane, ajinmu ɗaya, abu ɗaya muke karanta, kuma burinmu ɗaya. Wannan sunanta Nazifa Sulaiman, wannan kuma Rebecca Emanuel, sai Zuhrah Abbas”.
       “Masha ALLAH, sunayenku masu daɗi dukan ku”.
    Duk Dariya sukai am ma banda Nazifa da tun farko ta Nuna bata ra'ayina, yanzunma dai tana kwance a gadonta sai latse-latsen wayama take.
       Nima na faɗa musu sunana Bilkisu Adam.
       Rebecca tai saurin faɗin, “Bilkisu muna fata zaki cike mana gurbin guruf ɗinmu da muka rasa a yanzun”.
     Murmushi nai bance komaiba, dan bazance zanyi saurin aminta da suba tunda banga halayyarsu ba........
     Zuhrah ta katse tunanina da faɗin, “Please Bily karkice a'a, muna buƙatarki a cikinmu dan mudai kin mana”.
      Nanma murmushi nayi dai, a raina ina mamakin ni da kullum su aunty Shahudah ke kushe munina da ƙyamata ce kuma har suke iƙirarin na musu su kuma?.
    Magiya suka shiga min da roƙon karnace a'a, dan haka kawai sainace musu su bari zanyi tunani to.
      Murna sukaitayi wadda ni taita bani mamaki, sai dai ina jiyo tsakin da Nazifa tayi kaɗan.
     Ban damuba, dan amsar da ƴan uwanta kawai sukaimin ta wadatar dani, da taimakonsu na kintsa kayana tsaf, daga nan muka zauna sunamin lissafin abinda makarantar ta ƙunsa.
        Zakuyi mamaki idan nace muku harna kwanta barcin dare ban tuno ko ɗaya daga cikin su aunty Aamila ba bayan Dad kawai da tunda muka iso nake jerama addu'a a zuciyata.

_________________________

            Kamar yanda dokar allurar take sai bayan minti arba'in zata fara aiki, dan haka Jack ya fita yabar Shahudah a ɗakin ita kaɗai, kwanciya tai luf a gadon, sai kuma lokacinne wani mashahurin tsoro da fargaba suke shigarta, babu abinda ke mata kaikawo cikin rai sai Jawaad.
     Tabbas ita kanta tasan ta taro match na haƙiƙa a filin da bata da ƙarfin buga ƙwallon, fatanta dai ALLAH yasa tsarin da sukai ya tafi dai-dai, shine kawai zai zama mafita a gareta daga buyagin Jawaad mai zuciyar masifa idan aka ƙuresa.
      Da wannan tunanin wani barci mai daɗi ya kwasheta.

★★★★★★

          Haka kawai gaban Jawaad yaketa faɗuwa, kuma sai Shahudah kezo masa cikin rai baisan dalilin hakanba, zaune suke a Office ɗinsa shi dasu Aliyu suna tsara yanda zasu fuskanci case ɗin da aka basu dangane da ƴan fashin nan a safiyar yau.
       Tsayawa yay daga rubutun da yake a blackboard ya matse maker ɗin hannunsa yana dafe ƙirjinsa.
       Zuba masa idanu su Hafeez sukai, Jabeer yace, “Boss lafiya kuwa?”.
       Numfashi ya sauke a hankali yana musu murmushin yaƙe, yaɗan girgiza kansa sai kuma ya cigaba da abinda yakeyi.
       Badan sun yardaba suka barshi, shikuma zuciyarsa na cigaba da tsitstsinkewa.
       Lallai yanaji a ransa wani abu zai faru dashi kuwa, to amma minene?
    Wannan amsarce baida ita, dan haka ya share abun yana cigaba da karanto addu'a cikin ransa da maida hankali gasu Aliyun.......

★★★★★★

        Wani azababben ciwon marane ya farkar da Shahudah daga daddaɗan barcin daya ɗauketa, ba tare data shiryaba ta fasa ƙarar data jawo hankalin su Mummy dake falo, a matuƙar rikice suka shigo ɗakin har suna ƴar rige-rige kuwa.
      Dukansu kanta sukai suna tambayar lafiya kuwa?
     Cikin kuka take nuna musu cikinta, a razane Mummy tabi santaleliyar farar ƙafar Shahudah da jini kebi da kallo, har taune harshe take wajen ambaton “Jiniii!!?”.
        Cikin ruɗewa Aamila itama ta maimaita “Jini kuma Mummy?”.
     Shi dai jack baice komaiba, saboda da hausa su Mummy sukai magana baiji mi sukace ba, sai ƙoƙarin ɗaura kan Shahudah ma yake bisa cinyarsa yana jero mata sorry.
        Gaba ɗaya Mummy ta rikice, jikinta sai rawa yake tana jerama Shahudah tambaya akan miya sameta? Miya kawo zubar wannan jinin kuma?.
      Bata samu amsa ko guda ba, dan haka ta fice kamar zararriya, Dad ta kira a waya tana sanar masa yazo gida babu lafiya.
      

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login