Showing 99001 words to 102000 words out of 104658 words

Chapter 34 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

209

buƙatar mutum biyu, dan haka zai gwada ƙwazon kowa.
Mun amsa da girmamawa, kafin kowane rukunu a haɗasu da waɗanda zasuyi nusu gwajin.

Ni dai har muka bar wajen ban sake yarda na kallesa ba, hasalima gaba ɗaya na kasa samun sukuni, na sauke ajiyar zuciya ina dafe kaina, tare da fatan ALLAH ya kawo mani sauƙi akan wannan *Sabon al'amari* dana tsinci kaina a ciki.
Mun isa wani ɓoyayyen wajen sirri na hukumar mai ban tsoro, dan kuwa yau naga abinda a films kawai nake gani, wato manya-manyan makamai masu ban tashin hankali, yanzu dama a ƙasarmu akwai irin waɗannan manyan mahaukatan makaman irin haka?
Gaba ɗaya ganinsu ya saka karsashina guduwa, sai binsu muke da kallo tamkar wasu sokaye, mun daɗe munaji a labari babu jami'an da suka kai hukumar DSS mahaukatan bindigu. ban taɓa gasgata hakanba sai yau da idanuna suka ganemin zahiri......
Jin takun mutum a bayana ya sakani saurin juyawa, nai saurin matsawa gefe ƙirjina yana bugawar da bai taɓa yiba, dan sam bansan sanda ya shigo wajenba balle isowarsa kusa dani irin haka.
Baiko nuna yasan dani ba a wajen ya zuge glass ɗin da nake dab, hakan ya sakani yin gaba da sauri.
Jawaad dake hidimarsa cikin halin ko in kula ya ciro wata ƙaramar bindiga mai ƙyau ruwan Silver, sannan ya taka zuwa kujerar dake tare da tebir ya zauna yana ɗora bindigar da harsasai kusan guda takwas.
Jabeer da suke tare ya ɗauki bindigar da Jay ya ajiye ya ɗura harsasan robar dake tare da bindigar a cikinta suna magana da Jay wadda sam su bily basajinsu.
Bayan Jabeer ya kammala ya nufi su Bily dake tsaye suna jiransu.
Umarni ya bamu akan mutum ɗaya yazo, dama dukanmu mu bakwaine, na rasa yanda zanyi na iya samun cikakkiyar nutsuwa a wajennan, nikam a raina nama fara zargin wannan mutumin ko yanada aljanin da baya sonane shiyyasa yake kiɗimani? Kokuma shine aljanin kansa?.
Ta yaya dukkan mutane ina mu'amula dasu hankalina kwance, sai shine a duk lokacin da muka samu kusanci gabana zai keta faɗuwa? Wannan lamarin da mamaki wlhy...........
Ƙarar harbin da ɗaya a cikinmu tai bisa allon gwajine ya maidoni a hayyacina babu shiri, danma harsashin robane, amma a hakan ba ƙaramar firgita nayi ba.
Kallon da sukemin ya sakani yin murmushin yaƙe, shima na saci kallonsa, sai na tsinci idonsa a kaina, amma saiya janye kamar ba haka bane, ya maida ga allon da wancan yay harbin.
Sai kuma mukaga ya taso zuwa garemu, hakan ya sakani sake aro nutsuwa na azama kaina, ya karɓi bindigar hannun Oga Jabeer ɗin, a wani salon kai tsaye ya harba harsashin saɓanin mu da sai ka tsaya wajen nutsuwar ina zaka harba.
A tsakkiyar inda ake buƙata harsashin ya shiga anan kuwa ya shige jikin allon, ya juyo yana fuskantarmu sosai,
“Wannan shine wajen da nake buƙatar kaɗai harsashi ya shiga”.
Iya abinda yace kenan ya wurgama Oga Jabeer bindigar shiko ya caɓe.
Na ƙagara yabar wajen, amma sai naga yama gyara tsaiwarsa alamun babu inda zaije.
Ɗaya bayan ɗaya muke zuwa kowa yana gwada ƙwazonsa, amma ni na kasa tafiya, dan ji nake tamkar bazan iya komaiba a gabansa.
Wanda daga shi sai ni dana rage ta ƙarshe yayi shima, hakan na nufin dai duk wayon amarya sai ansha manta, dan ta laɓe-laɓe ta ƙare kuma.
Haka na taka nima na amsa, sai dai hannuna rawa yakeyi, gashi duk sun wani zubamin idanu.
Cikin karanto addu'a na fara dake raina da maida hankali akan abinda ke gabana.
Amma sai babu zato naji ƙamshin mayen turarensa mai daɗin shaƙa ya sake kusantoni..............✍🏻

Page 39

.............“Ki maida hankali akan abinda kikeyi”.
Muryarsa mai tarin nutsuwa da amo ta daki dodon kunnena, yayinda zuciyata tai wata irin bugawa tamkar zata faɗo ƙasa, idanuna suka cika da ƙwalla.
Ruɗanin dana shiga na babu zato babu tsammani ya sakani danna kunamar bindigar ba tare dana saniba.....
Ji nai kawai sautin tafi na tashi, nai azamar kallonsu kafin na maida ga allon harbin, sai naga na harba ainahin inda ake buƙata.
Bansan murmushi ya suɓuceminba, na saci kallonsa sai naga wayam yabar wajen ma gaba ɗaya, yana daga can gaban kantar da aka zagaye ɗakin da ita aka kuma rufeta da glasess baki ɗaya, wasu bindigu yake zubama harsasai tamkarma baisan mi akeba.....
Maganar oga Jabeer ta sakani maida kallona garesa, yace, “Lallai kin cancanci a kiraki gwanar harbi”.
Murmushi nayi da faɗin, “Nagode sir”.
Dai-dai Jawaad ya dawo wajen kalamar godiya da Bilkisu kema Jabeer ta shiga kunnensa, yay musu kallo ɗaya yana ɗauke ido da ƙara tamke fuska ya miƙama Jabeer bindugun hannunsa.
Amsa Jabeer yayi ya miƙama kowannenmu a hannunsa, sannan ya nuna mana inda kowa zai harba ba tare da ya mana bayanin dalilin hakanba.
Duk jeruwa mukai, kowanne ya zam cikin shiri kafin Oga Jabeer ɗin ya irga uku sannan ya bamu umarni.
Koda muka harba nidai idanuna na lumshe dan nasan dai bai zama lallai na zam cikin masu nasara tamkar ɗazunba,
“Inhar zakuyi harbi ku rufe idanunku da tunanin rashin nasara to lallai wataran a filin daga wani zai fasa kayinku da nasa harsashin”.
Maganarsa ta shiga kunnuwan kowannenmu babu zato, saurin buɗe idanuna nayi da mamakin jin furucinsa, musamman ma da naga ba'a kusa dani yakeba, hasalima ya nufi ƙofar fitane zai fice daga wajen.
Dukanmu da kallo muka bisa harya fice. kafin sauran ƴan uwana su shiga ma juna kallon-kallo, kowa nason fahimtar wanene ya rufe idon a cikinmu?, sai dai babu wanda ya samu amsarsa.
Jabeer yay murmusa yana girgiza kansa kawai, da maida kallonsa gasu Bilkisu.
Shima sallamarmu yayi, dan haka duk muka fito kowa yana ƴar maganarsa da wanda halinsa ya saɓa, mu biyune mata a ciki kawai, ita kuma tunma a wajen training bama shiga sabgar juna da ita.
Koda muka fito sai na shiga neman Ummie, na iske su basu fitoba, komawa nai bakin aiki, sai dai duk yanda naso ture abinda ya faru a raina yaƙi turuwa, sai kai kawo yakemin a zuciya da ƙwaƙwalwa.
A wannan yanayin Ummie tazo ta sameni, tun tana kallona harta kasa jurewa ta jehomin tambaya,
“Madam wai yaya dai?”.
Kallonta nai da mamaki,
Nace, “Kamarya?”.
Dariya ta ƙyalƙyale da ita tana girgiza kanta, “Kinga bar zaromin idanu tambaya kawai nayi”.
Ƙwafa nai mata ina ɗauke idanuna daga kanta da faɗin, “Gulmammiya”.


★★★★★

Kwanaki huɗu kenan da faruwar wancan gwajin wani abu bai sake tasowa ba, hasalima ban sake ganinsa ba.
A ɓangarena ma nima nayi shiri tsaf na fara binciken wanda ya keta martabar Amina a cikin gidanmu, shiyyasa yau data kasance lahadi banje ko inaba na sameta a gidansu, nayi amfani da lokacin zuwa islamiyyata ne dana maida duk ranar lahadi, yau sai haƙura nayi da zuwa na yada zango a gidansu Amina.
Da sallama na shiga, Amina dake zaune a ƙofar ɗakinsu tana tsintar shinkafa ta ɗago tana amsamin fuskarta ɗauke da murmushi, sai kuma ta fara tsokanata da faɗin, “Wai! Yau babbar baƙuwa garemu ashe?”.
Hararta nai ina jan kujera na zauna kusa da ita, na kalli mama dake mana dariya tana ta ƙoƙarin haɗa wutar abinci nace, “Mama kina jinta ko?”.
Mama tace, “Toni ai wannan faɗan bana shigarsa daga baya azo a matseni”.
Dariya mukayi gaba ɗaya, sai da muka tsagaita na shiga gaida mama, ta amsa min cikin kulawa tare da tambayata yaya aikina?.
Nace, “Alhmdllh mama munata gwaji, dan har yanzu ba'a gama sabawa ba”.
“Karki damu Bilkisu za'a saba, harma ya zama jiki wataran kuzam kune ake ambata a ƙasar mugaye su tsorata”.
Murmushi nayi kawai. Sai Amina ta amsa da “Insha ALLAHU kuwa mama” muryarta a kausashe na alamun tasowar ɓacin rai.
Tausayinta ya kamani, na dafa kafaɗarta ina shafawa alamun lallashi agareta.
Tai murmushi mai ban takaici ba tare data iya cemin komaiba.
Shiru na mintuna kusan biyu ya biyo tsakaninmu, ita tana cigaba da tsintar shinkafarta ni kuma ina buɗe littafin da nazo dashi gidan, ɗagowa nai na kalleta, itama sai ta kallenin.
“Amina nazone mu fara magana akan wancan abun da ya faru a waccan ranar, ina fata ban shiga uzirinkiba?”.
Murmushi tayimin, “Kai Bilkisu, ni wane uziri gareni, kimin duk tambayar da kikeso, ni kuma zan baki amsa inhar na sani”.
Kaina na jinjina mata, kafin na jeho mata tambaya, “A waccan ranar da abin ya faru, kowa yana gidan?”.
Shiru Amina tayi na kusan sakanni goma, kafin tace, “Eh to, lokacin dana shiga kowa yana nan, dan kinsan da zaran nayi sallar asuba nake shiga, sai kuma azhar na dawo gida, na koma bayan sallar la'asar sai goma nake dawowa gida, sai idan Alhaji na nanne yakan ce da nayi sallar magriba naje gida na huta, to a waccan ranarma ina idar da salla na shiga gidan, bayan mun gaisa da baba mai gadi ya tsokaneni kamar yanda ya saba, sai na wuce ciki, na fara gamo driver yana wankema Yah Qaseem mota, shima muka gaisa na shige. Ban iske kowa a falonba sai motsin kuku a kicin, na shiga muka gaisa da shi, shima ya tsokaneni tamkar yanda ya saba mukai dariya kafin na fito na fara ƙoƙarin gyaran falo.
Harma na kammala gyarawar ina morping Yah Qaseem ya shigo, duk da bansan lokacin daya shigoba ma dan jinai kawai tamkar kallona ake, shine na juya na gansa tsaye, a ɗan rikice na gaishesa dan bansan dalilin kallonba, shima ya amsa yana wucewa kicin ba tare da ya sake kallon nawa ba. Nai ajiyar zuciya ina cigaba da aikina, harna kammala na hau sama shima na gyaro, lokacin dana sakko na iske Yah Qaseem ya fita”.
Ta sauke numfashi tana share hawaye, kafin ta cigaba da faɗin,
“Kinsan sai sun tsashi nake samun damar ƙarasa aikin? To ranarma saina wuce kicin tamkar yanda na saba na zauna muna hira da kuku ina karyawa, banfi zaman mintuna gomaba Mummy ta ƙwalan kira, na amsa ina ajiye filet ɗin hannuna ina fita. Na isketa cikin shirin fita, na gaisheta cikin risinawa, tana laluben abu a jakka take amsamin, ta bani umarnin zuwa na taso mata Yah Salman. Da to na amsa ina ficewa.
Nayi sallama a ƙofar ɗakinsa yafi sau biyar, sai dai babu amsa, sanin halinsa ya sani tura ƙofar na shiga kawai, yana kwance ɗai-ɗai a gado da ga shi sai guntun wando, nai ƙasa da kaina ina kiran sunansa. Kamar yanda ya saba ya tashi a fusace yana mai zagina akan ubanmi nazoyi?. Amsa na bashi da cewar Mummy ce tace na tasoshi, wawan tsaki yaja nidai na fice abina naje na sanar mata cewar gashinan”.
“Bayan na sanar mata ta cemin zata fitane, idan Aunty Aamilah ta tashi na sanar mata taje can ta sameta inda sukai magana jiya, na amsa da to na nufi sama dan ƙarasa aikina”.
“Bansan fitar Mummy ba, dan inacan ina aiki, bayan na kammala na sako na nufi kicin, ina ƙoƙarin shiga Yah Salman zai fito, dan jaka mukai karo da juna harna faɗa jikinsa, muguwar mamuƙar da yaymin ba ƙaramin tsoro ta baniba, dan bilhaƙƙi da gaskiya ya rungumeni tare da matseni tsam a jikinsa, nai saurin turesa ina hawaye.......”
Ta kasa ƙarasawa tana sharar hawayen yanzunma, ni kaina idona ya cika da ƙwalla, handkherchief ɗin hannuna na miƙa mata, ta girgiza min kanta da cewar, “Kona goge waɗanda suka fisu zasu zubo, tuni alƙalamin ƙaddara ya fahimtar dani share hawaye a gareni bashi da wani amfani Bilkisu”.
Da ƙyar na iya haɗiye yawun daya tokare min maƙoshi, nace, “Sai mi ya faru kuma bayan hakan?”.
Ta ɗan taɓe bakinta tana ajiye tiren shinkafar da take tsinta, tace, “Tsaki yaymin ya fice a binsa, nima sai na samu kaina da jan tsakin ina shigewa, dama da shirin fita aiki na gansa, dan haka muna daga kicin ɗin mukaji fitar motarsa, itama Aamilah bata jimaba ta tashi a barcinta ta karya tabi bayan Mummy, ya rage gidan daga ni sai kuku da baba mai gadi”.
Can baya na koma nai zamana a wajen ni kaɗai tamkar yanda na saba, da ga baya da naji na takura saima na fita a gidan na dawo gida, sai dai na iske mama bata nan itama, dama kuma ta faɗamin zataje gaisuwa, jinai nan ɗinma babu daɗi, na sake fita na koma can gidan, na kwanta a falo, anan barci ya kwasheni, ban farkaba sai ana kiran sallar zuhur”.
Bayan na idar da salla ne na shiga kicin na samu abinda zanci, banga kuku ba, bankumaji motsinsa ba sam, abinci na ɗiba na zauna naci, tsautsayi ya sakani ɗaukar lemo nasha, abindama bai cika damunaba, duk da kuwa ba'aimin iyaka da dukkan wani nau'in abinci dake gidanba, duk abinda masu gidan zasuci Dad ya bani umarnin nima na ɗaukesa naci, kuma sam dukda halayar Mummy bata da ƙyau tanan ɓangaren dolene a yaba mata, ko wanene kai bata ƙyashin kaci komi zasuci, dan duk abinda sukaci shine ma'aikatan gidan keci, kuma za'a baka yanda zai isheka kaci ka ƙoshi”.
“Wannan lemo shine sanadin komai, daga shansa ban sake sanin ina hankalina yake ba, sai dai tashi nai na ganni a mawuyacin hali a gidannan.....”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”, naketa maimaitawa, na share hawayen dake zubamin a ido ina riƙo hannun Amina.
“Amma Amina wa kike zargi a cikin gidannan da aikata miki wannan abun?”.
Hawayenta ta share tana murmushi mai ciwo, “Bilkisu ni bana zargin kowa, sannan kuma duk ina ƙyautata musu zato”.
“Humm Amina su kuma basa ƙyautata miki zaton, dan da suna miki ƙyaƙyƙyawan zato da basu biyema son ƴaƴansu ba da zuciyarsu wajen kasa fahimtar an cuta miki, tabbas a wannan gaɓar abin yazo mini da ruɗani, dan zuwa yanzu hatta kuku da baba mai gadi suna cikin zargina”.
Amina ta zaro idanu tana kallona, hakama mama daketa aikinta tana saurarenmu sai da ta kalleni, sai dai babu wanda ya iya cewa uffan a cikinsu.
Nace, “Karku damu, shi laifi kowama yana iya aikatashi, musamman ma irin wannan”.
Dukansu kai suka jinjinamin alamar gamsuwa, na miƙe zan tafi mama tace babu inda zanje sai naci abinci, dan yau ɗanwake takeyi.
Dole nabi Umarninta na koma na zauna ina murmushi, ganin Amina tana tattare da damuwa na fama mata ciwon da nayi sai na shiga bata labarin wajen aikinmu, musamman inda na nuna ragwantaka a wajen trianing, aiko taita kwasar dariya mama na tayata.
Bansan yaya akaiba har abinda ya faru dani a airport akan mutuminnan sai da na bata labari.
Aiko taita kwasar dariya harda hawaye, wai mazari sunga mazaje.
Ganin ta shiga cikin farin ciki nima sai naji sanyi a raina, koda mama ta kammala tare mukaci abinci mu uku a kwano ɗaya munatama mama santin ɗan waken da yaji daddaɗan yaji daketa ƙamshin tafarnuwa da kayan kamshi.
Ban bar gidanba har sai da kiran yah Qaseem ya shigo wayata, ina tunanin ya dawo gidane, dan shi yau ya fita akan wani aiki da yakeyi.
Sallama nai musu na tafi ina jera musu godiya suma sunamin tare da addu'ar fata alkairi...........✍🏻

Page 40

.............Ina ƙoƙarin shiga gida kiransa ya sake shigo mani, ɗagawa nai da nufin faɗa masa ganinan zuwa gidan, amma sai naji yana magana mai alamar ba'a gidan yakeba..
Ya bani umarnine akan na duba ɗakinsa akwai wasu takardu ɗaya daga cikin jami'inmu zaizo ya amsa, na amsa masa da to kafin na yanke wayar na ida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login