Showing 93001 words to 96000 words out of 104658 words
Chapter 32 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete
masa office muci acan kamar yanda wasu daga cikin manyan keyi.
Kallon bawan ALLAHn can da yaymin lokacin dazai shiga mota ya mugun tsayan a ƙahon zuciya, duk yanda naso turesa hakan ya gagara, sai sauke ajiyar zuciya nake ina tsakurar abincin badan yaymin daɗiba.
Shi kansa Yah Qaseem na lura bawai cin abinci yakeba sosai yau, dan ransa a ɓace yake, na kuma rasa dalilin hakan sam.
Haka dai muka tsakura sama-sama muka bar wajen, kafin mu wuce na roƙesa muyima Ummie takeaway.
Atm ɗin nasa ya miƙamin kawai ya fice, na bisa da kallo ni dai kafin na amsar mata abinda nasan tanaso na fito, sai dai zuciyata na mamakin miya fusata yaya Qaseem haka wai ne?.
Ban iskeshiba hakan yasa na tafi ni kaɗai, dan da alama ya shige abinsa.
Yau bamu bar Office ba sai kusan takwas na dare, tare da Yah Qaseem muka tafi gida, sai lokacin ne na bashi ATM card ɗinsa, inason tambayarsa mike damunsa? Amma wani gefen zuciyata na karantamin na sharesa kawai.
Sharesan kuwa nayi nama maida hankali wajen cheating da Rebecca da taimin magana.
Har muka isa gida ni da shi bakin juna bai saɓaba, yanata driving ɗinsa, duk da na lura akwai tuƙin ganganci a ciki, wanda na jima da fuskantarsa ya haddace gudu a titi tunba yanzuba.
Amina ta taɓa bani labarin yanada driver da aka bashi na office da, sai dai rashin haƙurinsa yasa ya sallami direban, ya gwammaci ya tuƙa kansa da kansa.
★★★★★
A gidanma haka yayta tsumewa, nidai koda na gaida su Mummy dake falo ɗakina na shige, dan yanzu ganin batason sakarmin fuska sai na sake janye mata, aikin dake a gabanama ya isheni gayya basai an haɗamin da damuwa mara dalili ba.
Sai da nai wanka naji daɗin jikina sannan na fito falon domin neman abinci, ganin abinda aka dafa a gidan, ni kuma ba sonshi nakeba sai kawai na haɗa tea.
Ina daga dani ina shan tea ɗin nake jiyo hirar Mummy da yaranta, harda Yah Qaseem daya zama ginshiƙin hirar, shima da alama yana yin wanka fitowar yayi, jinai yana sanar mata wai Jawaad ya dawo.
Da yake ban fahimci kan maganar tasuba sai bansan akan wa yake maganaba, ni dai nayima na tashi na shige ɗaki abuna dan na kwanta na hutama rayuwata.
Dan tunda na fara aikinnan Yah Qaseem ke tafiya dani da dawo dani a motarsa Mummy ke haushi dani, inaji ranar tana masa faɗa akan hakan, harma da gargaɗi akan ya fita harkata, inba hakaba kuma yay kuka da kansa.
Bandaiji ya tanka mataba, bai kuma fasa ɗaukata a motarba.
Niko ina ruwana, tunda bani tama gargaɗinba banbi takai ba na cigaba da binsa kamar yanda Dad ya faɗamasa ya ringa tafiya dani da ɗakkoni tunda ALLAH yasa wajen aikin namu ya kasance ɗayane.
_________________________
JAWAAD
_________________________
Tarba maiban mamaki Jay ya samu ga ahalinsa, dan kuwa hardasu Umma duk sun taru a family house nasu.
Danne mamakinsa yay shima ya nuna girmamawa ga wannan tarba tasu, bayan gama amsa sannu da zuwa suka bashi damar shiga sashensa domin watsa ruwa.
Kaya yake cirewa yana jan ƙaramin tsaki shi kaɗai.
“bansan miya kawo dalilin yawan tsakinba ni kaina, sai dai mucigaba da bibiyar jay ko zamu sami amsa”😉😹⛹♀.
Yanda aka gyara sashen da ƙamshin da yakeyi ya ƙayatar dashi, sai dai yanaji a ransa aikin nan sai dai idan batool ɗin Umma ko Nabeelah wani yayisa.
A wajen wankanma ya samu nishaɗi saboda yana son tsafta a rayuwarsa, ya dai gama ƙaƙale-ƙaƙalensa ya fito ɗaure da tawul yana tsane jikinsa da ƙarami.
Sosai jarumin na Shahudah ya kuma canjawa, dan dai-dai da gaɓoɓin jikinsa sun sake murɗewa, ga wata gogewa da fatarsa ta sakeyi, yanda ruwa ke gudu a jikinta zai tabbatarma da mai kallonsa hakan.
Komai yana yinsane a yanayin gajiya, inda son samune kwanciya zaiyi ya hutama ransa basai ya sake fita a waccan hayaniyarba.
Amma yaya ya iya, dolene ya koma kamar yanda suka buƙata tunda sunce danshi suka taru.
Sama-sama yay ƴan shafe-shafensa ya saka wando da riga ruwan siminti marasa nauyi, kayan sun masa ƙyau tare da fidda ainahin ƙirar da UBANGIJI yay masa, ya fesa turare kaɗan sannan ya fito harabar gidan daga can baya inda dama anyi wajenne domin hutawa, an gyarashi sosai da korayen ciyayi da filawoyi masu ƙamshi.
Sam Jawaad baya zuwa wajen, saboda ƴammatan gidan sun maidashi lambun shaƙatawarsu ko ajiye samarinsu suyi hira, shi zaima iya rantsewa tun bayan daya mallaki hankalinsa baizo wajen sau ukuba, mantawama yake dashi gaba ɗaya, zuwa ukunma da yake kyautata zaton yayi shima duk mitin ne da Uncle's nashi suka shirya ya halarci wajen a wancan lokutan..
Sosai kuwa walimar cin abinci aka shirya, sai dai ya fahimci tamkar da biyu ne, danshi jami'in tsarone mai matuƙar basira da kaifin tunani, hakanne ya taimaka masa wajen gayyato ɗunbin nasarori a cikin rayuwar aikinsa.
Yanda ƴammatan Family ɗin nasu kowacce taci ado na ƙure wankane ya sashi fahimtar komai a buɗe.
Yay ƙwafa a zuciyarsa kawai yana sake shan toka, baisan miyasa akeson takurama rayuwarsa da awaɗanan yaranba, dan haka sukai maƙurar takura masa ta waya yanacan, kullum babu fashi sai yaga text messeges nasu ɗaya bayan ɗaya, harda masu masa a shafukansa na yanar gizo.
Bai taɓa kula koda ɗayarsu ba, danshi a ganinsa hakan rainine.
Ƙin cin komai yayi a wajen sai kunun aya kawai, wanda Batool ta tabbatar masa itace ta haɗa masa shi, dan dogon tabirne aka ajiye sannan aka zagayesa da kujerun da adadainsu yakai Hamsin koma fin hakan, manya maza da mata na family ɗin kowa ya samu muhallin zama, su kuma yaran an shimfiɗa musu leda mai ƙyau a ƙasa anan suke nasu shagalin bisa kulawar ma'aikatan gidan.
Sai da ya gaji da harar da Umma ke masa akan cin abinci sannan ya ɗau cokali badan yaso ba ya fara cin abinda yasa aka zuba masa cikin nutsuwarsa.
Sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska ya saka dukkan ƴammatan dake fama da rawar kai suka nutsu, dan dama sunsan shi baya son wargi, bakuma shiga sabgarsu yakeba tun fil azal.
Sai dai sai faman satar kallonsa suke ta wutsiyoyin idanu, shiko baima san sunaiba, abincinsa yakeci yana ɗan jefa magana cikin hirar mazan gidan sa'anninsa.
Dukda shine ƙarshen fara cin abincin shine kuma farkon fara ajiye cokali, babu wanda bai bisa da kallon mamakiba amma sai ya fuske cike da basarwa kamar baisan miya aikataba, sam saima yaƙi kallon sashen Ummah balle ta sake sakashi tilas akan yacin.
Abubuwan da Jay yakeyi ba ƙaramin ɓata ran Uncle's nashi sukeba, amma duk sai suka danne zukatansu da addu'ar ALLAH yasa karya watsa musu ƙasa a idanunsu yadai zaɓi matar aure kamar yanda manufar taron take.
Dukanin tunaninsu bai gama tsayawaba sai da Jawaad ya miƙe bayan mintuna biyar da ajiye cokalinsa, cikin nutsatstsiyar muryarsa yay musu sallama tare da miƙa kalamun godiya na wannan tarba daya samu daga garesu, yay addu'ar sake samun haɗin kai na wannan family mai ɗorewa, tare da jaddada musu abinda sukai masa yau din ya ƙayatar dashi kuma ya bashi farin cikin da bazai mantaba har sai ya rubutashi ya ajiye.
Kowa fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallon Jawaad ɗin, kowa yaji daɗin kalamansa kuwa, dan basuyi zaton jin hakan daga gareba.
Shikuma yay wani munafikin murmushin da ya kusa zautar da dukkan ƴanmatan wajen, shikuma shi kaɗai yasan ma'anar kayansa, kafin ya nema alfarmar tafiya domin ya huta saboda ciwo da kansa ke ɗan masa kaɗan-kaɗan na alamar gajiyar tafiya.
Basu da yanda suka iya dashi, amma dai Uncle Nasir ya dakatar dashi har ya miƙe yay ɗan guntun bayani na sake masa sannu da zuwa, tare da roƙon Jawaad ɗin ya sake jikinsa tare da yafema duk wanda yake ganin ya masa ba dai-dai ba akan abinda ya faru wancan karo har yayma gidan yaji na kusan shekara.
Nanma dai godiyar Jawaad ya sakeyi sannan ya tabbatar musu shi komai ya wuce a ransa tuni, suma yana fatan hakan daga garesu, daga ƙarshe yay musu sallama ya koma sashensa.
Murmushi kawai Umma tai tana girgiza kai da bin Jawaad ɗin da kallo harya ɓacema ganinsu.
Barinsa wajen ya saka taron ya fara watsewa a hankali, mafi yawansu zukatansu babu daɗi a ciki, musamman ma ƴan matan da suka ƙwallafa rai a kansa babu gaira babu sabar.
Shi dai baimasan sunaiba, dan yana barin gurin ƙwafa yay yana maijin takaicin rainin da ake neman jawo masa wajen yaran gidan, zama yay a falon yana jiran shigowarsu Umma domin su gaisa kafin ya kwanta.
Zaman nasa kuwa baifi da mintuna goma ba sai ga Umma dasu batool sun shigo.
Dariya Batool ta fara masa tana tafa hannaye.
Harara yaketa zabga dan yasan tsokanarsa zatayi, mata amma baice komaiba, dan itace kawai ke iya taɓasa kasancewar sa'anni suke dashi ta kwana lafiya, wani lokacinma har yakan biye mata, batool bata taɓa aureba, munadai tayata fatan samun miji na gari.
Ɗauke idonsa yay akan Batool ɗin data zauna a kujerar gefensa tana faɗin, “Kaga mai ƴammata buhu-buhu na Shahudah bada kanka a sare kazo gida kace ya faɗi”.
“Umma ALLAH kicema yarinyarnan ta kama kanta kota fita falonnan da ƙafa guda”. Jay yay maganar cikin matuƙar ɓata fuska.
Murmushi Ummah dake zama tayi, yayinda Batool ta bushe da dariya, hakama su Nabeelah duk sai gyale sukasa suna kare fuska dan karya gani.
“Manta da ita kaji My son, yau ba ranar ɓata fuska bace ba, ina fatan dai ka dawo cikin ƙoshin lafiya?”.
Numfashi yaɗan sauke mai haɗe da ajiyar zuciya yana faɗin, “Alhmdllh Ummana, sai dai kewarku kawai, yaya jikin Baba?”.
“A jikinsa Alhmdllh, ai yama samu sauƙi dama murace ta canjawar wannan yanayin, sai kuma jikin tsufa da aketa rarrakawa”.
Jawaad yace, “ALLAH sarki baba, ALLAH ya ƙara tsahon rai”.
Da amin suka amsa su duka.
Su Nabeelah suka sake gaidashi cikin girmamawa, yayinda shima yake amsawa da ƴar kulawa.
Batool kam cayay bazai amsa mata gaisuwaba.
Tace, “Karka amsa mana Jay, duk dai wani ɗacin ranka kayisa ka gama Aurene sai anyi makashi, danni harma na zaɓa maka waɗanda suka dace dakai a ƴammatan nan da aketa faman maka talla kana wani fuskewa, auren gata zamuyi maka, ƴammata uku zuƙa-zuƙa sai Shahudah uwar gida ran gida”.
Remote dake center table ya ɗauka ya jefeta dashi, ta tashi ta fice daga falon tana dariya, shi kuma ya kuma haɗe fuska yana ƙwafa.
Su Nabeelah ma dai ficewa sukai dansu bashi waje ya tattauna da Umma.
Dariya Umma ma taɗanyi kaɗan tana faɗin, “Da gaskefa Fatima keyi, waɗanan yaran daka gani dansu aka shirya maka wannan tarbar, ni kuma naga bakama nuna wata alamar zaka zaɓa ɗinba”.
Cikin takaici Jay yace, “Na sani Ummah, amma dan ALLAH karku biyema shirmensu, zan kuma taka musu birkine dan wannan neman jawomin rainine wajen yara kawai, bansan minene matsalarsu da aurena ba ko rashin yinsa? Nace musu ina buƙatar aurene ko yaya? Za'a wani ringa cusamin yara ƙanan kamar wani ɗan iska......”
Cikin tare masa numfashi Umma tace, “Dole zaka buƙaci aure Jawaad, dan koba komai ka rigada ka ɗanɗani zama da mace, kuma koba hakaba ma cikar mutuncinka shine auren, babu wanda zaka sanarma kai kamiline ya yarda bayan mu da mukasan kai wanene, ka daure koda ba'a cikin yaran nasuba ka sami matar aure, idan kuma matarka kakeson maidawa ka maidota dan maybe ta canja zuwa yanzu, tunda na fahimci son da kake matane ya hanaka sake kallon wata mace da sigar auren, baba kansa yana damuwa sosai da rashin sake aurenka, shekarafa huɗu kenan da wasu watanni da rabuwarka da matarka, da aurenma kayi ƙila da yanzu ƴan jikokinmu na kai kawo a falonnan, sannan akwai wasu takardun dukiyarka masu matuƙar muhimmanci dake da alamar tambaya, dan sune silar komai da lokacine kawai zai buɗe kowanne sirrin da mu da kai zamu fahimta baki ɗaya....”
Shiru Jawaad yay yana nazari dason ƙarin bayani akan maganarta ta ƙarshe, sai dai bata bashi wata damar masa tambaya akan hakanba, shiyyasa yay shiru yana kallonta, sai kuma ya sauke numfashi yana faɗin, “Shikenan Ummah, kuyi haƙuri indai aurene zanyi da izinin ALLAH, duk da har yanzu babu wata mace a raina, kuma ba hasashenku bane ya hanani aure na cewar son Hudah ne har yanzu, sai dai kodan farin cikinku zanyi insha ALLAH, amma ku kwantar da hankalinku ku bani lokaci, dan banason a sake komawa ƴar gidan jiya kamar aurena na baya”.
Umma tace, “To ALLAH ya tabbatar mana da alkairi. ya kuma kawo mana ta gari wadda zata zo mana da alkairai”.
Bai iya ce mata komaiba, dan gaba ɗaya sun dagula masa lissafi, basu san yanda yakejin haushin mata bane a ransa da sunbar ambatar aurenan da suka damu ransu akan sai ya ƙara..............✍🏻
Page 37
............Bayan shigewar Qaseem da Bily babu daɗewa Mummy na zaune tana saƙawa da kwancewa ta yanda zasu ɓulloma zaman Shahudah da Jawaad kira ya shigowa wayarta.
Ɗauka tayi babu ɓata lokaci, dan kuwa kirane mai matuƙar muhimmanci.
Sama-sama sukai gaisuwa mai kiran ta fara zayyane mata abinda ya faru a family house ɗin su Jay a yau, wato dai walimar cin abincin da aka shirya masa mai taken yaɗa manufar tallar matan aure.
Ran Mummy ya ɓaci ƙololuwa, dan a ganinta wannan tsagwaron munafurci ne kawai ƴan uwan nata suka shirya, taya zasu nema aikata haka?, bayan sunsan akwai soyayya mai ƙarfi tsakanin Shahudah da Jawaad ɗin, saɓanine kawai da sharrin shaiɗan ya gitta har wancan matsalar ta faru, maimakon su nema hanyar da za'a sulhunta shine zasu haɗa wannan annamimancin? To lallai lokaci yayi da za'ai uwar watsi kuwa ashe, yanzu ace har mahaifiyarsu ta gaza kiranta ta sanar mata balle ƴan uwanta su Uncle Uwaisu, dan bata saka Maimuna ƙanwarta a wannan sabgar, tunda tuni ta nuna musu bata tare dasu ita dama.
A wannan dare gaba ɗaya barci gagarar idanun Mummy yayi, gashi Dad baya gari, tayi kiran wayarsa yafi sau goma taƙi shiga, ta kuma kira Mama Atika ba'a ɗaukaba, ta kira Shahudah shima bai shigaba.
Gaba ɗaya sai kanta ya ƙara ɗaukar zafi, sai sauke ajiyar zuciya takeyi a jere a jere.
Gari na wayewa duk da uban barcin dake cin idanunta haka tai shiri tunda farar safiya ta fice a gidan, ko jiran driver bata tsaya yiba, dan aganinta kafin yazo an gama ɓata mata lokacinta.
Tun shigowarta falon mama Atika dake zaune tana lazimi ke kallonta, Mummy sai sake cika take tana batsewa, ganinfa mahaifiyartasu ba ida addu'ar nan tata zataiba ya sata faɗin, “Wai nikam mama wannan addu'ar bata ƙarewa ne?, nifa a ƙage nazo”.
Mama Atika batace mata komaiba, hakama bata tsaya da addu'arta ba sai da takai aya, ta shafa tana faɗin, “Ke dai Wlhy Ai'sha sam baki da ɗabi'ar ƙwarai, ba ƙaramin lalacewa rayuwarki taiba a garincan na marasa sallah, mike faruwa na ganki da wannan uwar safiyar?”.
Cikin sake ɓata fuska Mummy tace, “Ba dole ake ganina da farar safiya ba, yanzu mama dan ALLAH munafurcin da ake shirin ƙullawa ya ƙyautu kenan a gidannan?, kowa yasan alaƙar dake tsakanin Shahudah da yaron nan na wajen Abdul-aziz, amma shine za'a shirya wani annamimanci ta bayan fage ba tare