Showing 51001 words to 54000 words out of 104658 words
Chapter 18 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete
ɗaki, kaida kazo cin arziƙi miye naka na zaƙewa?.
Kwannanta uku a gidan, duk da kuwa tun a daren da tazo naji suna tafka bala'i da mijinta a waya akan kwannan nata, dan naga tanata magana a zafafe akan dan tazo gidansu zata kwana dole saita sanar masa.
Da alama ma yanke mata waya yayi kafin takai zancen ƙarshe, dan kuwa sai faman faɗin, "Hello hello takeyi, daga ƙarshe cikin takaici tai jifa da wayar saman kujera tana masifa iya iyawarta akan ya kashe mata waya.
Itako Aunty Aamila sai zugata take akan wulaƙancin da yake mata yayi yawa, ni dai banji ƙarshen zancenba na shige ɗaki, dama daga kicin nake na zubo abinci, suko suna a tebir zasuci nasu.
________________________
Ran Jawaad ya ɓaci da ya dawo ya iske Shahudah bata gida, hakanne ya sakashi kiranta amma saita sanar masa tana gidansu, ya tambayeta da izininwa? tahau kansa da masifa, shine kawai ya yanke wayar ba tare daya gama saurarenta ba.
Sam bayason jin zafinta da yake ya cigaba da girmama cikin ransa, dan haka ya tashi yay shirin fita dukda kuwa lokacin ƙarfe tara da rabi na dare, kuma dawowarsa gidan kenan ko hutawa baiyiba.
Da kansa yaja motar dan yabama gimba damar zuwa ya kwanta ya huta.
Kansa tsaye gidan dattijuwarnan ya nufa, yanabin address ɗin da su Hafez suka bashi dalla-dalla.
A ƙofar madaidaicin gida ya tsaida motar dajin tabbacin nanne, dankuwa duk abinda aka kwatanta masa a jikin gidan ya gansa, kashe motar yay sannan ya fito cikin nuna alamun tsantsar gajiyar dake tattare dashi.
Ya kulle motar amma sai bai fitoba ya fara ƙoƙarin yin kira cikin ƙaramar wayarsa.
Bugu uku aka ɗaga, "Gani a ƙofar gida" ya faɗa idonsa akan murfin gidan.
Bansan amsar da aka bashiba daga can naga dai ya kashe wayar yana fitowa a motar, bindigarsa ya ɗauka ya tura a aljiyu sannan ya rufe murfin motar yana mai kulleta gaba ɗaya.
Dai-dai nan dattijuwa mai aiki gidan Alhaji kokino ta fito sanye da lulluɓi.
Da hannu tai masa nuni alamar su shiga, babu musu ya bita, bayan yaɗan wawwaiga bayansa yaga babu alamar kowa a wajen, dukda ma anguwar babu wani isashen haske saboda rashin wutar lantarki.
Gidan bawani babba bane ammafa yasha gyara, dan fes yake sannan kuma da gani babu ƙananun yaran da zasu ɓata.
Zama yay a farar kujerar roba dake ajiye a bangon yamma da yake ƙyautata zaton kicinne, itama ta zauna a ƙofar kicin ɗin bayan ta kawo masa tea tamkar tasan yana buƙatarsa a halin yanzu.
Godiya yay mata kuwa ya ɗauka yana sha.
"Bani da tabbas amma inaji a jikina kasan inda Alhaji yake".
Jawaad dake ƙoƙarin kai kofin shayi bakinsa ya dakata yana kallonta, leɓensa na ƙasa ya tura cikin bakinsa yana tsotsa tare da kafeta da wani kallon nazari na seconds biyar, sai kuma yay murmushi yana ƙara damƙe kofin shayin da hannu biyu yakai bakinsa ya kurɓa.
Itama kallonsa takeyi har yanzu, sai dai bata sake cewa komaiba.
Jawaad ya cigaba da shan shayinsa kawai idonsa na kallon yanda iska ke kaɗa labulen ɗakin matar.
Yasha kusan rabin kofin shayin sannan ya ajiye yana sauke ajiyar zuciya, idonsa akanta.
"Mama shekararki nawa kina mata aiki?".
Murmushi dattijuwa tayi tana kallonsa, "Yarona ai mai son kama fara sammako yakeyi"
"Hakane" Jawaad ya faɗa yana shafa kansa cikin murmushi.
"Miyasa take ɓoyemin kanta har yanzu?".
"Bani da wannan amsar a zahiri da baɗini".
Kansa ya rausayar kawai, idanunsa na sake rikiɗewa zuwa ja sosai, sai haɗiyar numfashi yake da zafi, hakan yasaka zuciyarsa gudu tare da tsitstsinkewa.......
Mama ta katse masa tunani da faɗin, "Ta bani saƙo na baka".
Ɗago kansa yay ya kalleta, amma baice komaiba.
"Tace ka sadaukar, a cikin hakan akwai alamar tambaya? Idan kabi diddigi zaka fahimta".
"Zanyi biyayya, sai dai zan cutu kuma".
"Shiyyasa nazo maka da maganin hakan".
Miƙewa Jawaad yay yana kallon agogon hannunsa, "Ina saurarenki, dan lokacina ƙararrene".
"Karka damu nima komai inayinsa da ƙa'ida. iya ruwa fidda kai, amaryar alhajice mafitarka".
Jawaad ya juyo yana kallon dattijuwa hannuwansa duka a cikin wandon jeans ɗinsa, "Mimene nata burin?".
"Kisa da mallakar abinda ya tara".
Kansa ya jinjina yana murmushi, ahankali ya furta "Abin birgewa".
Kallonsa mama tayi tana murmushi itama.
Takowa yay ya dawo gabanta yana ɗan jingina da bango, yace, "Shine kikaji a ranar da kika faɗi kenan?".
Cikin sauke numfashi mama tace, "Kusan haka yarona, sai dai tsoron ya gauraya ne da cin amanar aure, kuma da makusancinsa".
Hannu ɗaya Jawaad ya ciro a aljihu yana mai shafa fuskarsa, "Idan babu kuskure a hasashena auren manufa tayi da haɗinkan ƙaninsa kenan?".
"Hasashenka yana kan dai-dai, kamar yanda sukuma ka ruguza musu nasu a ranar da Alhaji zai dawo daga tafiya shi da ita".
"Zan samu dukkannin bayanan?".
"Ƙwarai kuwa, harma da wanda baka tambaya ba" tai maganar tana kunce ƙullin haɓar zaninta ta ciro wani ɗan abu ta miƙa masa.
Amsa yay yana sauke numfashi, "Nagode ƙwarai da gaske mama. A sanar mata ina buƙata matuƙa, sannan ke kuma yaushe aikinki zai ƙare a gidan?".
"Eh to, inada zaɓi biyu ne, sannan dama ɗaya kacal, a koda yaushe za'a iya nemana a rasa".
"Shikenan, ni zan wuce, a daren yau zan ƙulle bakin zaren".
"Kariyar ALLAH ta tabbata a gareka tareda rahamarsa akowane lokaci".
"Amin ya rabbi mama, nagode sosai, da safe Yazeed zai dawo gida".
Murmushi kawai tai masa, shikuma ya fara taku cike da kasala ya fice daga gidan.
Buɗe motarsa yay ya shiga sannan ya rufe kansa, ya buɗe hannunsa dake rumtse da abinda mama ta bashi, idanu ya tsira masa yana kallo, kusan mintuna uku sannan ya ajiye yana tada motar ya fice daga anguwar.
Tuƙi yake amma hankalinsa kashi sittin baya a wajen, gefen titi ya samu jikin wani ƙyamiz yay fakin motar, ya cire babbar wayarsa a caji ya danna kiran Jabeer, bugu ɗaya ya ɗauka, sai dai yanda yaji muryarsa ya bashi tabbacin ya fara barci ne.
"Barci kake?".
Jawaad ya faɗa a ƙasan maƙoshi.
Daga can Jabeer yace, "Wlhy kuwa barcine ya figeni a falo ma, yaya kana office ne?".
"Eh to badai a cikiba, amma ina akan aikine, inasu Aliyu?".
"Duk gasu muna a tare".
"Yauwa ku kasance cikin shiri yanzu nima zan iso".
Bai jira amsar Jabeer ba ya yanke wayar.
Rose ya kira, itama bugu ɗaya ta ɗauka, ko gaisuwarta bai sauraraba ya fara faɗin, "Yanzun nan ki kira number dana baki ranar, ki kirata da wayar dana baki ki sanar mata tazo bayan kamfanin robobi na kwanar gulbi ta sameki, wannan wayar ta ƙawartace wadda da ita suke haɗa komai, dan haka zatazo da sauri".
"To amma boss kana ganin zatazo a darennan?".
Tsawa ya daka mata wadda ta sakata firgita har tana neman yadda wayar, ta daiyi nasarar damƙeta da sauri tana faɗin, "Sorry Boss".
Tsaki mai ƙarfi Jawaad yaja yana katse kiran, dama zuciyarsa a saman maƙoshi take sosai.
Motar ya tayar yaja da uban gudu zuwa gidansa dasu Aliyu ke ciki, shigowarsa falon yasasu miƙewa su duka cikin girmamawa, hannu ya ɗaga musu kawai ya wuce ɗakin da ke cikin falon, mintuna kamar uku sai gashi ya fito da mace da shekarunta ba zasu gaza talatin da biyu ba.
Dukansu sunsan da zamanta, dan haka basu wani damuba, Jawaad ya ciro waya a aljihunsa yay danne-danne yana miƙa mata, karɓa tayi tana kallonsa a yanayin tsoro-tsoro bariki-bariki....
"Ki kira number nan, ki sanar masa kina tare da Alhaji Kokino, yanzunnan tazo bayan kamfanin robobi na kwanar gulbi ta sameki, kuma yanzunnan".
Bakinta ta taɓe tana kallon Jawaad ɗin, "Yallaɓai to miyasa zanyi hakan? Bayan kasani na sani Alhaji baya tare dani?".
Bindiga ya ɗora mata a saman kai ba tare daya ce komaiba.
Take jikinta ya fara mazari, ta shiga ƙoƙarin yin abinda yace.
Yace, "Ki tabbatar muryarki ta fita normal babu gargada a cikinta".
Zufar data fara jiƙa goshinta ta goge tana haɗiye yawu da ƙyar ta saka wayar a kan kunnenta.
Duk yanda Jawaad ya shaida mata haka tayi, su dai su Hafiz suna tsaye suna kallonsu duk da sun kasa gane kan abokin nasu ma, tunda bai musu bayanin komaiba.
Bayan ta kammala wayar Jawaad ya maida bindigarsa a aljihu yana kallon su Hafeez.
"Zan barta tare daku, nanda mintuna ashirin zan iya kiranku, zakuzo bayan kamfanin kuma ku sameni".
A tare suka jinjina masa kawuna, ya fice da hanzarinsa.............✍🏻
Page 21
...........Guri Jawaad ya samu yay fakin nesa da gidan Alhaji kokino, ya ɗauki ƙaramar wayarsa yay kiran Rose, bugu biyu ta ɗaga.
Kafin yace wani abu tai saurin faɗin, “Sir komai ya tafi dai-dai, yanzu haka ina ƙyautata zaton kowane lokaci zata iya tahowa”.
“Yayi, yanzu haka ina ƙofar gidansu, zankira su Aliyu suzo da ƙawar tata, duk yanda za'ai karki bari tazo ta sameki a wajen koda ta rigasu zuwa”.
“Okey sir”
Rose ta faɗa cikin girmamawa.
Wayar ya katse, ya tada motar ya ƙarasa ƙaton gate ɗin gidan Alhaji kokino.
Horn yayi, babu ɓata lokaci baba mai gadi ya buɗe dan yasan da zuwansa, yay fakin motar ya fito, a kuma dai-dai wanna lokacinne Hajiya Usaina ta fito kamar a rikice, motarta da Jawaad ya kare ta nufa, sai da ta zira key zata buɗe ta juyo da nufin yima baba maigadi magana ya buɗe mata gate idonta ya sauka akan motar Jawaad, yanayin da take cikine ya hanata fahimtar motar bata gidan bace ba.
Ranta a ɓace ta shiga kwala kiran “Baba Dauda! Baba dauda!!”
Jikin Baba mai gadi na rawa ya rugo zuwa gareta yana amsawa da “Na'am hajiya, afuwa naɗan zagaya banɗakine wlhy”.
Batako sauraresa ba ta nuna motar Jawaad, “Uban waye yay fakin mota a gurin nan? Bayan ansan ko yaushe zan iya fita tunda inada mara lafiya a asibiti”.
“Kiyi haƙuri hajiya baƙone yanzu kuma ya shigo shima” ‘Baba yay maganar yana nunamata Jawaad dake tsaye jikin motar yana waya hankalinsa kwance tamkar baisan mi sukeyiba, nanko dukkan hankalinsa na kansu’.
Kaɗan ya rage key ɗin motar data zare daga jikin motar ya faɗi, tai saurin damƙesa dan ba ƙaramin razana tai da ganin Jawaad ɗinba, fasa buɗe motar tayi ta nufo inda Jawaad yake tana ma baba maigadi alamar ya tashi da hannu.
Jawaad ya janye wayar daga kunnensa yana maida hankalinsa gareta, cikin harɗewar harshe tace, “Yallaɓai lafiya kuwa a daren nan? Ko anga Alhaji ne?”.
Fuskarsa ya kauda daga gareta tamkar baiji mi taceba, ya tura wayar tasa a aljihu yana komawa jikin motarsa ya jingina, cike da nutsuwa ya maida hankalinsa gareta, “Nazone inason magana da ɗaya a cikinku, ke ko Hajiya babba”.
“To Yallaɓai nidai amin afuwa jikin mamana ne ya motsa, shine aka kirani asibiti”.
“Okey babu damuwa, bara na bari sai da safe na dawo, ALLAH ya bata lafiya”.
“Amin ngd” tai maganar tana barin wajen cike da sauri, dukta rikice, da alama kuma ganin Jawaad ne ya kawo hakan. Cikin gida ta koma ba tare da tasan mizatayo ba kuma.
Murmushi Jay yayi yana ɗauke ido daga kanta, ya maida dubansa ga baba maigadi yana faɗin, “Buɗemin gate, ina fatan komai done?”.
“Komai dai-dai ƴallaɓai, ALLAH ya ƙara nasara”.
Murmushi Jawaad yay masa, ya buɗe motar ya shige ya bar gidan saboda baba ya buɗe masa gate ɗin.
Yana ƙoƙarin harba motar kan titi yana kiran waya, ya ajiyeta a saman cinyarsa bayan ya saka a hansfree.
“Hello Hafiz!, kuyi maza mu haɗu acan ɗin, idan kun rigani zuwa saiku jirani, inaso saina fara ajiyeshi kafin ku sauketa kuma, saboda tsarin yayi dai-dai”.
“Okey Boss” Hafez ya amsa daga can yana gimtse wayar, zuwa yanzu kam ya fahimci mi Jawaad ke shirinyi, dan haka ya kalli su Jabeer da suma sunji komai saboda a hansfree ya saka.
Dariya sukayi gaba ɗaya, dan sun fahimci inda aikin ya dosa yanzu kam.
“Daga jikin kamfanin ta baya yay fakin motar, ya fito a ɗan hanzarce bayan ya saka baƙar safar hannu a hannunsa, bayan motar ya buɗe bayan ya wawwaiga babu alamar mutun ta ko ina, yakai hannu ya jawo mutum a seat ɗin baya da ƙyar, dan babu laifi yanada jiki, kuma da alama a sume yake ma. Da ƙyar ya iya saukeshi ƙasa, sai hakki yake, ya sake ɗagashi da ƙyar zuwa wani ƙaramar baca ta kwano dake wajen ya ajiye saman kujera, igiya ya saka ya ɗaɗɗauresa kafin ya zaro allura a aljihun wandonsa yay masa a hannu, bai jira komaiba ya zare abinda suka rufe masa fuska ya fice da hanzari yayo waje.
Mota ya koma, da babaya yajata yaɗan koma nesa da wajen sannan ya kashe ya sake fitowa, wayar dake hannunsa ya ɗora a kunne yana fadin, “Zaku iya kaita”.
Bai jira misu Aliyu zasu ceba ya yanke wayar ya koma kiran Rose wadda tana daga can ɗan nesa da kamfanin itama, tana ɗagawa yace, “Kin ajiye wayar da kika kiratane a bacar?”.
“Yes boss, tun ɗazun ma”.
“Okey kizam cikin shiri, dan bayan awa ɗaya kacal zamu far musu kafin suyi tunanin kashesa”.
“Angama boss”.
Katse kiran yay yana lumshe jajayen idanunsa tare da dafe kai, babu abinda yake buƙata sai hutu, dan a matuƙar jigace yake.
A haka Su Jabeer suka ƙaraso inda yake, dan Aliyu ne kawai yakai matar cikin bacar da Jawaad ya ajiye Alhaji kokino.
Fitar Aliyu da kamar mintuna biyu Alhaji Kokino ya farfaɗo saboda Allurar da Jawaad yay masa, mutsu-mutsu ya fara yana ƙoƙarin buɗe idanu da ƙyar, hakan ya saka matar da Aliyu ya kawo miƙewa jiki na rawa ta nufesa, dan itama tunda Aliyun ya jefota kanta a juye yake bata fahimtar komai, ta rasa dalilinsu na aikata hakan.
Da yake kuma akwai duhu sai bata san ita da waye bane a wajen, da lalube ta isa inda yake, tana ɗora hannunsa jikinsa wayarta da Rose ta ajiye a bacar ta hau ring.
Cikin tsananin firgita ta juya ta kalli wajen, inda shima Alhaji Kokino ya sauke wani nannauyan numfashi, wayar ta nufa dan ɗan hasken screen ɗin ya haska bacar kaɗan, mamaki ya kamata ganin wayartacema ashe, kuma Hajiya Usaina ce ma ke kira, kasa ɗagawa tai harta tsinke.
Aka sake kira, cikin rashin sanin abinyi ta ɗaga, daga can Hajiya Usaina amaryar Alhaji kokino tace, “Lamcy gani a wajen kamfanin, ke kina ta inane?”.
Sosai Lamcy ta zaro idanu waje, amma sai cikin rawar baki ta amsa da cewa, “Ki duba akwai baca ta kwanon langa-langa daga gefen gabas, sai dai karkizo da mota Usaina, wannan lamarin akwai lauje cikin naɗi ba shirinmu bane”.
Katse kiran Hajiya Usaina tayi, dan tafi buƙatar su karasa ga Lamcy komaima sayi acan, fita sukai daga motar itada Abdul ƙanin Alhaji kokinon, dan tare sukazo, kuma yaji komai da Lamcy ta faɗa.
A baca kuwa ɗunbin mamaki da al'ajab ne ya kama Alhaji kokino saboda ganin Lamcy aminiyar matarsa Uswina, ga kuma furucin datai a waya, wanda ya tabbatar masa cewar da Usainar tai waya, “To minene shirin nasu?” yay tambayar a zuciyarsa.
Kafin ya samo amsa ne Abdul da Usaina suka shigo cikin bacar.
Gaba ɗaya sai tunanin Alhaji kokino ya sake birkicewa, ya kafe ɗan uwan nasa da kallo yana faɗin, “Abdul!” sai dai muryar tasa bata fita sosai.
Dariya Abdul ya kwashe da ita yana maida hankalinsa kan Lamcy dake ƙokarin musu bayanin wannan fa sam ba shirinsu bane, karsu ce zasuyi wani yunƙuri a zagaye suke.
Saurin dakatar da ita Abdul yayi da faɗin, “K dalla malama a zagayenwa? Kefa kika kiramu kika kuma sanar mana komai, ni yanzu babuma maganar ɓata lokaci anan, mu aikashi kawai, dan yanzu ƙarfe biyu saura, ya kamata ace nanda uku mun kammala komai munbar wajennan” ya ƙare maganar yana buɗe jakkar da sukazo da ita.
Duk yanda Lamcy taso su fahimceta hakan ya gagara, sai ma ƙoƙarin saka Alhaji kokino suke akan dole yana saka musu hannu a takardun dake cikin jakkar, waɗanda duk na kamfanoninsa ne da kaddarorinsa dake ƙasashe daban-daban harda na nan ƙasar.
Haushi ya kume zuciyar Lamcy, dan ta kula gaba ɗaya kawunan su hajiya Usaina a toshe suke, da ƙarfi ta hankaɗe Abdul daya kama hannun yayan nasa yana sakashi saka hannun dolen.
Kallonta yay da mamaki mai haɗe da ɓacin rai, “Wai ke mike damunki ne? Kokinsha wani abu dayafi ƙarfin kankine?.......”
“Ba nice banda hankaliba Abdul, kune baku da hankali, to idanma barci kuke ku farka wannan shirin duk wasune da nima ban saniba suka tsarashi!!!”.
Yanda tai maganar da cikakkaiyar gaskiyane ya sakasu kallonta su duka, amma sai hajiya Usaina tai tsaki kuma, “Lamcy karki kawo mana wani ruɗani anan, indai akan maganar abinda kikace za'a bakinne munji zamu baki, ke ni harma wani kaso zan ƙara miki a cikin nawa, ai burinmu ya gama cika, dan yau dai ta Alhaji ta ƙare, kudin da muketa wahalar gadi tsahon shekara shidda gasu komai ya dawo hannunmu, nanda sati ɗaya sunayenmu zasu fito cikin manya-manyan masu arziƙin duniya, hhhhhhhhh!!, sai ni Usaina ɗiyar malam garba, mace ta farko mai arziƙin da babu kwatankwacinsa a wannan yanki, Abdul ka kawoma duniyata haske dalilin buɗamin hanyar auren ɗan uwanka, wanda toshewar basira ke sakashi kallon sonsa nake, besan ina cikin waɗanda zasu zamo ƙatshen rayuwarsa bane, hhhhhhhhhh!!!!!!”.
Ta sake kwashe da wata mahaukaciyar dariya Abdul na tayata, hannu yasa ya fisgota ta faɗo jikinsa, a gaban idon Alhaji kokino dake ɗaure suka hau sumbatar juna tare da yamutsa kansu.
Hawaye masu zafi ne suka wanke fuskar Alhaji kokino, ya duƙar da kansa domin daina kallonsu, wuƙa Abdul ya zaro a aljihunsa, babu wanda ya lura ya sokama Lamcy dake ƙokarin jan hannun Hajiya Usaina, so take ta sake fahimtar dasu ko zasu fahimta, idan sunƙi ta gudu itadai ko ranta ta tsira dashi idanma babu dukiyar.
Ƙara ta saki mai ƙarfi tana ƙanƙame Hajiya Usaina.
Da sauri Hajiya Usaina ta saki Abdul da maida kallonta ga Lamcy.
Sosai ta zaro ido ganin wuƙar dake gefen